← Book details Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 17

Sashe 4

Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na samu mintuna goma sha biyu a haka, sannan na ji kamar an sumbaci bayana, na yi saurin ɗagowa, amma ban ga kowa ba, na yi murmushi na miƙe na nufi banɗaki. A banɗaki na cire kayana duka na shiga ruwan wanka mai ɗumin gaske,wai ko abin da nake ji ya sake ni. Tsayin mintuna biyar na yi kawai na miƙe da sauri, saboda tunanin da ya faɗo mini a lokaci ɗaya.

Na É—aura tawul na fito da saurina,wai ji nayi kamar an bugo mini waya,ba abin da ya faÉ—o mini kuwa sai maganar Sarki.

"Zan turo a kira mini ke kin ji."

Hankalina ya tashi matuƙa, gobe, gobe lallai zan shiga damuwa kenan in an rabani da Yarima.

Na yi saurin tunano Anwar a zuciyata, take sai na ji bana son tunaninsa,na fi son tunanin Yarima,shin ina son Yarima? Ba amsa, na ɗauki rigar bacci ta da su Mansura suka ajiye mini na zura a jikina, da ƙyar na iya ɗaga ƙafata na zura ɗan diras ɗin da ke kusa da ita, na isa ga madubi na taje kaina tare da ƙara gyare shi.

Rigar baccin doguwar shimi ce har ƙasa, orange colour da ƴan hannuwanta guda bibbiyu a kowanne ɓangare sai ɗan leshi da ya ratsa saman ƙirjinta, ruwan lemo ce mai santsin gaske. Na feshe jikina da turare madadin in haye gadona sai na ji na kasa, buɗe ƙofar barandar gaban gidan na yi na fita.

Kamar yanda na saba a kullum yau ma haka na yi, shi ne in ware hannayena duk biyun,yau ma kuwa na samu sa'ar garin yana fitar da iska mai sanyin gaske, wadda ta taimaka da wasa da gashin kaina, idanuwana kuwa a lumshe suke, amma na kasa tunanin komai a yau.

Cikin wani sanyin jiki da sanyin zuciya, na ji tunanin Yarima ya faÉ—o mini a zuciyata a iya nawa tunanin, sai na ji dama Yarima ya iso yanzu,can É—ayan gefen na zuciyata kuwa, sai ya dinga karanto ni a jikin Yarima,a cikin tunanina ne na ji kamar an bi nawa hannayen a hankali, wani daÉ—i ya dirar mini a zuciya.

Cikin tunanin kuwa na ji an haɗe ƴan yatsun hannuna da nashi waje ɗaya an runtse su, cikin ƙwanciyar hankali ya rungume bayana a ƙirjinsa, sumbatar da ya kaiwa wuyana shi yasa na saukar da ajiyar zuciya mai fitar da sauti.

Hankalina gaba ɗaya na ji ya ɗauke har ya zamo na manta mai nake ji a jikina, ƙwaƙwalwata ta fara karanto mini da in buɗe idanuwana da suka yi nauyi in ga ko zan ga Yarima a barandarsa.

Cikin sakan biyar na ji hankalina ya dawo a jikina, madadin in jini ni kaÉ—ai ina tunanina, sai kawai na tsinci kaina da jin É—umin mutum a jikina, gaske ne,ko dai har yanzun mafarkin tunanin ne nake yi,jin sautin numfashi na tashi a kunnuwana yasa na buÉ—e idanuwana da sauri.

Na razana, na tsorata, duk a lokaci ɗaya da na ji bakina ana Yarima, na yi ɗan gaggawar fizge jikina na ja baya, kenan mafarkin tunanin da nake yi da gaske ne, na girgiza kai tare da ɓata fuska.

"Me ke damun ka haka? Bana son abin da ka ke yi mini,ba na..."

"Yasmin ya isa haka nan,don Allah, na san na yi miki laifi a baya, ya kamata ki zamo mai yafe mini."

Ya matso ya tallabo fuskata Wacce gashi ya rufe ta, yasa hunnunsa ya gyara gashin zuwa baya.

"Yasmin."

"Ni fa ba zan..."

"Yasmin kada ki faɗi abin da zai ƙara tayar mini da hankali."

"Ka manta gobe ne ranar ƙarshena da kai,ka ga ba zancen wani gyara a nan."

"Na sani Yasmin,ki yi tunani kada kiyi tunanin ko yaudara ce tsakanina da ke, wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Tun a ranar da na gan ki a titin Ahmadu Bello Waya, har zuwa yau ban taɓa daina tunaninki ba, matsalar da na samu shi ne ban san gidanku ba, ina shirin in bincika Allah ya haɗa ni da ke a wajen fati,a ranar na so mu daidaita sai ma ta ƙarasa ƙwaɓe mana."

Ya ɗan tsaya ya mayar da numfashi, ya saki fuskata, ya durƙusa a gabana. "Please Yasmin ki taimakeni,ki zauna da ni." Na tsugunno nima na fara magana a hankali, kamar yanda yake yin tasa.

"Ba zai yiwu ba Yarima,ba zan iya zama da kai a wannan matsayin naka na mulki ba,ko tari na yi duk gidan nan an sani, har zuwa gidanku." Na miƙe na koma ɗaki na zauna gefen gadona.

Mintuna baƙwai da zamana ya shigo ɗakin shi ma ya iso gaban gadon ya tsaya.

"Ba zan taɓa cewa na haƙura da ke ba, ba kuma zan gaji da baki haƙuri ba, ba zan taɓa mantawa da cewa ina son ki ba, Allah ya gani, na yi miki abubuwa ne domin ki so ni, nima amma na yi kuskure." Ya juya ya tafi ya ja mini ƙofar da har sai da na ɗan tsorata.

Na koma na ƙwanta a rigingine, na dafe kaina da hannayena na yi tsaki, na juya na tashi zaune, na mayar da numfashi na tashi na je na rufe ƙofar gaba, na koma na kulle ƙofar ɗakina, na zare makullin na kashe dukkan fitilun ɗakin, na ɗaga filo na saka makullan, na koma na shige bargona, kaina ne kawai a waje, inda idanuwana ke kallon duhuwar ɗakina, duk da hasken da ke shigowa ta kafar labulaye ya ɗan taimakawa ɗakin da rage duhu sosai.

"Yarima!" Shi na faÉ—a a fili, na tuna da maganar Sarki, na tunano Mama da ta ce Sarki ba ya magana ya tayar da ita, hawaye na ji sun gangaro mini,wata zuciya ta tambaye ni, "Shin ko ina son Yarima Faysal ne?"

Anwar shi ne mutumin da ya fara saka ni hanyar soyayya, mutumin da ya shayar da ni ɗanɗanonta. Anwar Mutum ne wanda ya rigaya ya karanci halayyata, har ta zamo ba ta ɓata masa rai.

Anwar ba wai ƙyakkyawa ba ne, sai dai sam ba ya layin munana,kalar fatar jikinsa kuwa mai ɗan duhu ce, amma da ganinsa ka san yana cikin hutu. Anwar babban ma'aikaci ne shi, wanda har ya kai matsayin babba a ofishin da yake (Cooporate Affairs Commission).

Mahaifinshi ya tsufa, mahaifiyarshi ce mai ɗan jini a jika, wanda gidansu su huɗu ne kacal,yayyansa biyu, mace da namiji, sai kuwa ƙaninsa namiji ɗaya. Ni kaina na san ina son Anwar, Mutumin da muka shekara uku da shi muna (Friending), amma rashin auranmu da shi tun a baya, na san laifina ne, tare da ƙaddarar auran Yarima Faysal.

Iyayensa ƴan asalin Kano ne, aiki ya kawo mahaifinsa na Likitan dabbobi, suna da arziƙinsu daidai gwargwado, ga shi mutum ne mai tausayin gaske ni kaina na san Anwar na matuƙar ƙaunata.

**** **** ****

Wazirin Sarki,Galadima,Tafida, Talba da Durɓi,su ne a tebirin shawarar Sarki, wanda Sarki Jafar Sada ya tarasu ne a kan hukuncin da ya yanke a raba auran Yarima Faysal da Gimbiya Yasmin,saboda su ne mutanen da suka fi kowa kasanci da shi fiye da kowa.

An ɗauki ɗan tsayin lokacin da za'a iya ba shi sa'a ɗaya (awa ɗaya), ana mahawara a kan maganar, wanda a ƙarshe magana ta koma ta basuyi na'am da hukuncin da Sarki ya yanke ba, saboda dalilai da suka kawo irin nasu na manya, kamar dalilin waziri.

Ya Kawo dalilinsa ne a kan nan gaba idan suka nemi aure za'a iya hana su, saboda za'a ga ba sa riƙe aure da daraja, dalilinsa na biyu kuwa shi ne,a bar yaran da kansu su zo su ce basa son junansu,in sun zo da zancen haka, ina ga in an raba su ba za'ayi laifi ba wajen kowa.

Galadima kuwa cewa ya yi a kan samu haka a tsakanin ma'auratan da aka haɗa aure, ma'ana waɗanda ba su suka zaɓi junansu ba. Shi kuwa Tafida cewa ya yi abin kunya ne a garesu a ce sun yi wa ɗansu aure wanda suka tara jama'a ba iyaka daga garuruwa, jahohi, ƙasashe, amma a ce ƙwanakin da ba su wuce arba'in ba aure ya rabu, alhalin muna taƙama da cewa shi ne magajin Sarkinmu a nan gaba.

Shi kuwa Durɓi cewa ya yi anyi daidai da aka ja masu kunne aka tsorata su, amma maganar rabuwa ma bata taso ba,a kira su dai a ƙara ba su lokaci, idan har ba su sasanta kansu ba, to sai a haɗu da iyayen yarinya a ƙara tattaunawa, daga nan sai a nemi shawarar da ta fi cancanta, sannan yana mai baiwa Sarki shawarar ya je ya samu iyalinsa ya lalubi wani abu daga gare su na game da yaran, saboda su mata ne za su fi mu samun labarinsu.
*ƘASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 4

A nan dai suka tashi saboda ganin juma'a ce za'a fita Masallaci da wuri. Sarki ya shiga ya kira iyalansa,Mama Mariya ita ce mahaifiyar Yarima, sai kuwa Hajiya Kilishi wacce take mahaifiyarsu Ahmad ga ta amarya.

Ya gaya masu shawarar da ya yanke a kansu Yarima, amma yana mai tambayarsu shawarar ya suka gani.

Hajiya Kilishi ita ta fara magana,haba Shugaba ya za'a yi a ji irin wannan maganar daga bakinka, alhalin ku ne manyan da ku ke yankewa ƙanana hukunci,haba mai girma,ai ka san auran haɗi dama ya gaji haka kafin ma'auratan su saba. Ka tuna kanka mana,watana nawa a gidan nan ban saba ba, yanzu fa ka ga a sai mutuwa kawai ta rage mini a cikin gidanka.

Ni a shawarata mai girma a sa masu ido, tun da an ɗan tsorata su, balle ma yanda naga shi Yarima na yawan zuwa gidan nan,a lokacin da aka dawo da Yasmin nan gidan,kai a taƙaice sai na kore shi gida yake tafiya in dare ya yi. In kuwa suka shige ƙuryar Mama sai su ƙwashi awanni, sallah kawai ke fito da shi,don ma yarinyar na da kunya,waya kuwa in dai har ba ya cikin gidan nan har gajiya muke yi da ɗauka, sai na cewa yarinyar ta taimaka ta ɗauka, sannan zai bar mana kunnuwa su huta. A fahimtata dai Yarima ya sauko, ita ce dai ke da saura, kuma ka san dan tana mace, akwai kunya irin ta mata,ko Mama kin yi shiru?"
Chapter 4 · 0% Book details