← Book details Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban wani daÉ—e ba ganin dare ya yi, ga shi idanuwana cike suke da bacci, saboda haka ban fi mintuna biyar ba, ina fitowa tun daga É—aki na É—an ji tashin muryar Yarima kaÉ—an kaÉ—an, duk da dama shi ba mai sakin murya ba ne ba,ko waya yake yi za kaga kamar ba a jin abin da yake cewa, amma yau nayi mamakin jiyo muryarsa.

Na buɗe durowa na ƙwaso rigunan bacci uku, na taho da su domin nuna masa ya zaɓa mini,me zan jiyo.

"Mama wallahi lafiya lau muke,tana wanka."

Har na washe baki na taho in karɓi waya mu gaisa da Mama, sai na ji maganarsa ta canja salo, na yi tsaye cak saboda jikina da na ji ya yi nauyi,gudun kada in yi taku da ƙarfi ya jiyo ni.

"Mama ai dabara na yi mata, to gajiya na yi,yau nayi mata ciwon ƙarya a ruwan wankan nunawa na yi na mutu na taso sama,kin ga ɗiyarki na ihu a zo a taimake ta,miji zai mutu. A'a Mama, wallahi dama don in gane tana so na ko har yanzu zaman dole take yi da ni.

Eh, na gane,kin ga yanda ta ruɗe dama na haɗa baki da ƴan hotel ɗin. Mama ai hotel ɗin da Mai Martaba Sarki ke sauka ne,mun saba da su sosai,su na haɗa baki da su na ce su yi mini allurar (B. Complex), kin ga ai na ɗan ci in ƙoshi na ƙwana biyu." Sai na ji ya sa dariya.

A'a Mama, ina zan yarda ta yi kukan da za ta haɗu da wani ciwon, ai ni ma da na kama ciwon gaskiya wallahi Mama lafiya ƙalau,ni yanzu ma na ji ta ƙara shiga raina, saboda hankalinta, wallahi ina son ta,so sosai, Mama ki daina koƙwanto, yanzu mu duka muna son juna.

Mama kenan, na so insa a ɗauki hotan ɗiyarki in aiko miki ki ga yanda take kuka. To na daina za ta ji, ta shiga wanka daga ma ƙasa muke yanzu, abokaina na nan suka haɗa mata fatin murnar auranmu, amma kin san Turawa suna kiran shi da Birthday,amma fa duk sun ruɗe wai na iya zaɓen mata, zan daina, sai anjima. Ki gaishe da Baba Sarki da Hajiya, kowa ma. Ita ma a aika a ce tana gaishe su, to to,bye Mama I love you,I miss you great Mama."

Sai na ga ya kashe yana Æ´ar dariya har da sumbatar wayar, sannan ya tashi tsaye ina jin da niyyar ya zo É—aki sai kawai ya juyo ya ganni a tsaye juyowarshi nima tasa na saki kayan da ke hannuwana wannan kuwa na lura da ta firgita shi,dan kuwa ya gane na ji duk abin da yake faÉ—a.

Ya yi saurin nufo inda nake tsaye, kafin ya iso na shige É—aki da saurina na faÉ—a gado, ya iso ya yi saurin É—ago ni.

"Yasa..."kafin ya ƙarasa kiran har na ji wasu zafafan hawaye sun zubo mini,wannan ne ya hana shi ƙarasa kiran.

"Me za kace mini yanzun kuma?" Na faÉ—a cikin sanyin murya.

"Yasmin sorry,wallahi har a zuciyata na yi haka ne domin na gane kina sona kamar yanda ni ma na daÉ—e da sonki,in za ki tuna ma haka na cewa Mama."

"Ni dai ba zan iya auran ku ba,komai muke ciki kowa sai ya sani."

"Haba My love, ya zaki ce mini haka, alhalin kin san yanda zuciyata take ƙaunarki."

Na sauka ƙasan gado ya durƙusa, "Yasmin ki yi haƙuri ki so ni nima."

*ƘASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 13

Kansa a sunkuye yana É—agowa muna haÉ—a ido na yi saurin sunkuyar da kaina.

"Ka daina yi mini haka,bai dace ba,ka durƙusa mini ina matsayin matarka."

"Kin amince ke matata ce?"

Na koma da sauri na kife kaina jikin katifa, sannan na É—aga kaina. Ya hawo a hankali ya tura kai a cikin wuyana ya sumbace ni.

"Na gode, to tashi in zaɓa miki rigar baccin."

Ya ɗago ni na tashi zaune ya yi saurin tafiya ya ƙwaso kayan ya iso ya zube su a gado har ya zaɓa mini ɗaya daga ciki ya miƙe tsaye.

"Kafin in fito daga wanka kin saka mini ita, kada ki lulluɓe ta na san ki da kunya."

Yana yi yana cire coat ɗin da ke jikinsa da shet (suit) shigar nasa kayan (wedding Anniversary) ɗin kenan. Ina jin motsin fitowarsa na yi saurin miƙewa tsaye tare da sunkuyar da kaina ina faman murza ƴan yatsun hannuna,ni kaina na san rigar baccin ta yi mini ƙyau. Doguwa ce iya wucewar gwiwata amma matsatstsan ƙugu gare ta,siririn hannu gare ta kamar ɗan mariƙin hular sanyin yara, kuma a murɗan yake tamkar ɗan abin ɗaurin hular yara.

Amma tafe take da ƙoƙunan rigar Mama daga cikinta wanda za su iya tallabo maka ƙirjinka ya ɗan bayyana a waje, ya kuma fitar da tsakiyarsu, sai dai sakata ake yi kamar ana saka wando, saboda haɗe take da ɗan diras ɗinta, jikinta gashi-gashi ne kamar gashin jikin jaririyar mage, kenan laushi, amma ba ya tsirar mutum.

Ƙasanta kuwa kamar ƙarshen jelar mage an daddasa sannan kuma sai ka maƙala ɗan siririn maƙallamin rigar mama sannan za ka zuge wani zib da ke cikin bayan rigar, wanda ba a gane shi, sai an laluba saboda gashin jikin rigar ya ɓoyeshi. Ɗan wani guntun mayafi gare ta,ko na ce ɗan abin da zaka rataya a wuyanka, shi kuwa kamar ƙatuwar jelar mage, saboda duk ta rufe mini wuyana.

Kunya ce ta hanani É—aga idanuwana daga tsayuwar murza Æ´an yatsun da na yi, jin shigowarsa É—akin ta sa na É—an É—aga idanuwana na kalleshi, cikin sauri na sunkuyar da kaina saboda ganinsa nayi É—aure da tawul mamadin ya sako rigar wankan shi, É—an tsayin mintuna biyu ya yi ban ji motsin shi ba, gyaran muryar da ya yi ita ta kawar da tsit É—in da É—akin ya yi.

Jin sautin maganarsa na yi yana yi mini magana cikin sarƙaƙƙiyar murya. "Miƙo mini rigar wanka ga ta nan a kan gado."

"Tawa ce wannan taka na ciki."

"Na sani taki nake son sakawa a yau,ko ba za'a ba ni aro ba?"

"Za'a baka." Na faÉ—a a daidai lokacin da na juya domin É—auko masa.

Kaina kuwa a sunkuye nake tafiya har na iso inda yake tsaye, cikin ɗan yanayi na kunyar gaske na miƙa masa rigar ba tare da na ɗaga kaina ba, juyawar da zan yi na koma ta yi daidai da ruƙo hannuna da ya yi ta bayana ba zan iya ƙwatanta yanda jikina ya amsa girgizar da ya yi ba, juyo ni ya yi ya haɗa ni da ƙirjinsa rigar da ke hannunsa kuwa ina ji ta sulale a tsakaninmu ta faɗi ƙasa.

Bai yi magana ba, amma sai na ji ya sa ɗan yatsansa yana zana mini cinyar hannuwana,wanda har ya dire a yatsun hannuna,ɗago tafin hannuna ya yi ya ɗora a saman ƙirjinsa,gashin ƙirjinsa wanda yake cike da lemar ruwa ya haɗu da ɗan sanyin ruwa ya tsirar mini tafin hannuna,na yi saurin lumshe idanuwana tare da kiran sunansa "Yarima."

Cikin kunnena na ji ya yi magana, "Faysal dai, ke ya kamata na kira da Gimbiya, Sarauniya,Yarimiya,kin san kuwa kin cancanci sunayan nan, saboda kin riga kin siye zuciyar Yarima, wanda yake taƙama da mulki.

Wanda bai taɓa tunanin da macen da za tasa zuciyarsa ta koma tamkar ba tashi ba, Yasmin ke zuciyata kawai take tunani,ni a yanzu ma ji na nake ƙarya ne ni ba nine Yariman da kike faɗa ba."

Sai na ji ya yi murmushi mai fitar da sauti tare da É—ago fuskata,"Open your eyes, kalleni."

Da ƙyar na iya kallonsa na sakan ɗaya.

"Yanzun ni naki ne Yasmin,ki daina jin shakkun komai,ki daina jin kunyata,ki fitar da tsorona daga zuciyarki, kin canja mini rayuwata gaba É—aya."

Ina jin shi yasa hannu ya janye É—an dogon gashin da na rufe jikina da shi.

Ya sunkuyo ya sumbaci ƙirjina na yi saurin ƙwantawa ƙirjinsa ya tallabe kumatuna.

"Yasmin you love me sure?"

Na ɗaga kaina alamar eh, ya ɗauke ni cak ni kuwa na koma na ƙwanta a ƙirjinsa ya hau gadon sosai, sannan ya ƙwantar da ni ya janyo filo ya ɗaga ni ya gyara mini ƙwanciyata sosai, ya juya ya janyo bargon da ke maƙale jikin gado ya lulluɓa mini har izuwa ƙirjina,sannan ya sunkuyo ya sumbaci goshina da laɓɓana yasa hannu ya gyara mini gashin da ya sauko mini a saman fuska.

Ni kuwa cikin lumsashshen ido nake kallonsa sannan ya ce, "ina zuwa." A cikin raÉ—a sai na ga ya sauka na buÉ—e idanuwana sosai na bishi da kallo a take sai na ji na tsorata saboda ganin shi É—aure da tawul haka ya nuna min ashe Yarima na da tsokar jiki,ganin wasu cinyoyin tsoka a cinyar hannunsa duk sun yi kusurwoyi kamar ta Æ´an kokawa (Wrestling).

Ga wata tsoka ta ƙwanta a gefunan wuyansa, ban da tsokar da na hango a cinyar ƙafarshi, ya buɗe durowa ina kallonsa sai na ganshi ya juyo yana fesa wani abu a hannunsa, ganin dogon gwangwani ne yasa na gane abun sa ƙamshin ɗaki ne (Room Freshner) duk da ban ga sunansa ba, cikin sakan uku ɗaki ya kaure da ƙamshi mai sanyin gaske, ban da laushin shaƙa da hancina ya yi.

Ya ɗauko wata ƴar ƙwalba bayan ya ajiye wancan sai na ga yana ɗan ɗigata yana shafawa a gashin ƙirjinsa,a zuciyata na ce ashe maza ma suna ƴan gyara irin na mata. Ina kallo ya ɗauko turare ya fesawa jikinsa ya mayar da durowa ya rufe, juyowar da zai yi sai na ga idanuwansa sun ƙara fitowa sun yi ja,dama abu (Barakallah), manya da su, sai ya juye mini kamar na ƙwatanta shi da ɗan fim ɗin nan na ƙasar Indiya (Salman Khan), har da faɗin ƙirjin ga tsokar curi-curi a cinyoyin hannunsa.
Chapter 16 · 0% Book details