← Book details Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma ina shiga sai na ga Yarima ya juyo da kansa ya kalleni ya mayar gefe É—aya, na isa bakin gadon a daidai lokacin da nake zaro takardar da Aunty Salwa ta bayar in kawo masa.

"Gashi in ji Aunty." Ya juyo ya kalleni ya lumshe idanuwansa kamar wanda ake ƙoƙarin ƙara masa ruwan ledar asibiti, domin ceto ransa daga ciwon amai da gudawa da ya yi masa mummunan kamu. To haka na ga Yarima na buɗe idanuwa da ƙyar.

Ya zaro hannu tamkar hannun ya yi masa nauyin É—agawa ni kuwa na É—ora masa takardar a kai, madadin in zauna sai na dawo falo na biyun Hajiya na zauna saboda ba zan iya zama a wajensa ba......

Maganar da Sarki ya fara ita ta katse mini tunanin da na tafi, wanda a cikin mintuna biyar kacal na yi shi.

"Yau ne ranar da muka yi alƙawari da kai zaka zo mini da abin da na umarce ka, ina jiranka."

Yanda na ji cikin naman jikina na rawa haka kuwa na tabbatar Yarima na cikin halin da ya fi nawa, da jin maganar da Yarima yake yi,ka san a tsorace,a firgice,a nadamance da kuma karfin hali irin na maza yake yin ta. Bayan ya miƙe da ƙyar ya koma can kusa da Sarki.

*ƘASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 5

"Baba ka yi mini afuwa a kan abin da na aikata maka na rashin ƙyautatawa,a baya na yi alƙawarin ba za ka ƙara kama ni da wani laifi ba na rashin ƙyautatawa ba."

Sai na ji ya rage sautin maganar ta juya izuwa sanyi da rawar murya.

"Ba..ba yan...zun ina son abin da ka ke so, zan iya zama na har abada da abin da ka ke so." Ya yi shiru.

"Yanzun me ka ke son inyi maka kuma? Bacin ka kunyata ni ka tozarta ni a idon jama'a."

Ina kallo ta wutsiyar idanuwana ya ja jikinsa ya matsa sosai kusa da ƙafafuwan Sarki.

"Baba ka yi mini hukuncin duk da ka ga ya dace da ni, wallahi zan É—auka matsawar dai yin hakan zai huce zuciyarka zai saka ka yafe mini.

"Ka zaɓi ɗaya cikin abu biyun nan,auranka ko sarauta."

"Baba duk wanda ka zaɓar mini ina so."

"In zaɓa maka ka ƙara yi mini yanda ka ga dama."

"Baba ka yi haƙuri, wallahi kuskure ne,ba zan ƙara ba har abada."

"Koma ka zauna, zan yi tunani a kan ka, ke kuma ki gaya mini gaskiya zaki iya zama da shi ko kuwa?"

"Duk hukuncin da ka yanke ya yi mini nima."

"Tashi je ki ciki."

"Na gode." Na miƙe a sanyaye na nufi ciki.

Tsayin mintuna arba'in Yarima ya yi shi da Mai Martaba, amma ni ina ƙwance saman lanƙwasashshiyar kujerar Mama, na yi lamo alamar bacci nake yi, ina ji ya shigo suka shiga ƙuryar ɗaki da Mama sun ɗauki mintuna sun kai ashirin sannan suka fito, ina jin shi ya yi sallama ya fita.

Bayan sallar la'asar ne,Mai Martaba Sarki yasa aka kira ni zuwa fadarsa ta cikin gida, zan iya kiran lokacin da huÉ—u da rabi na yamma,ni da Mama muka shiga fadar wacce ita Æ´ar rakiya ce, wani sanyin daÉ—i na ji ya sauka a zuciyata,a lokacin da Mai Martaba ya ce Mama ta zauna ita ma. Ba mu fi minti biyu da zama ba sai ga Hajiya Kilishi ta shigo.

A nan Sarki ya umurce ta da ta zauna, wanda dama alamar da ta nuna Sarkin ne ya aika a kira ta. Maganganu, misalai,nasihun da suka yi mini yasa a take na ji zuciyata ta karaya a kan duk wani abu da na ƙudura a kan Yarima na game da wahalar da shi.

Lallai Yarima ya samu yabo a wajen mahaifansa, da kishiyar Mama, Hajiya Kilishi, ta faÉ—i irin halayyarsa da suke ji, ita ma, sai na dinga jinsa a zuciyata a take kuma na tunano kalaman Aunty Salwa waÉ—anda ta karantar da ni tsantsar so kuma me ye shi da tafiyar da wanda ake so.

Na dawo hayyacina lokacin da na ji Mai Martaba ya ce, "Ƴata ina fatan za ki gafartawa mijinkin abubuwan da ya yi miki a baya, na rashin ƙyautatawa, saboda ya yi nadama ya nuna ba zai sake ƙwatanta miki su ba, ya nuna mini yana son matarsa."

Yabo, nasiha da maganganun da Mai Martaba da iyalansa suka yi mini shi ya sanyayar mini da jikina, sannan Sarki ya yi mini alƙawarin yi wa Yarima hukunci, matsawar bai gyara halayyarsa ba, ya tabbatar mini da sati ɗaya ya bani idan har na ga ba daidai ba,in sanar da shi. Irin maganganun mutane da suka yi mini sun sa na ji alamar ɗan ɗigon wani abu a zuciyata, wanda na tuno da Aunty ta ce wai shi ne alamomin so.

Ƙarfe shida saura mintuna goma sha baƙwai motocin ayarina suka shiga get ɗin gidan Yarima,wai sai na ji na tsinci kaina cikin wani irin nishaɗin farin ciki. Mu ma muka sauka inda ake ajiye motocin gidana. Yarima na hango a tsaye ya jingina da ɗaya daga cikin ragowar motocin da ke ajiye a rumfar ajiye motocin.

Dukkan hannayensa ya saka su a aljihunsa ƙafafuwansa kuwa ya harɗe su a waje ɗaya, tabbas sai na ga ya ƙara yi mini ƙyau,ko kuwa don baƙar T.Shirt ɗin da ke jikinsa ce ta ƙara haska shi dama abu ga farar fata. Amma yanayinsa ya nuna mini da ganinsa cikin ɗan ruɗani yake, saboda yana hango motocina sai na ga ya yi saurin miƙewa tsaye sosai.

Murmushin da nake yi kuwa,ni na san ya shiga har zuciyata, motocin na tsayawa shi ma na ga ya É—an taho alamar zai iso ga motata, ganin an buÉ—e mini na fito shi ya sa naga yayi tsaye cak, tare da mayar da ajiyar zuciyar da ta fito fili, wanda ya yi ta cikin lumshe idanuwansa duk biyu. A hankali na ga ya zaro hannu É—aya daga cikin aljihunsa ya shafi gashin kansa da shi, sannan na ga ya buÉ—e idanuwansa ya É—an É—aga su kaÉ—an ya kallo ni.

Ni kuwa tuni har na kusa zuwa inda yake a tsaye, saboda ita ce hanyar da zan bi in shiga cikin gidana,ni kaina na san na canja tafiya, amma wani abin ban mamakin da na yi shi ne ina isa inda yake tsaye sai na ji ba zan iya yi masa magana ba balle har ta kai ni ga tsayawa wajensa. Sai dai kawai na yi murmushi na raɓa ta gefensa na wuce.

"Kin tayar mini da hankalina,kin daÉ—e sosai."

Maganar da na ji ya yi daidai lokacin da na zo zan wuce ta kusa da shi, na ɗan juyo da kaina na ɗan kaɗa idanuwana tare da yin murmushin da na san ya ƙara bayyanar mini da ƙyan fuskata,ƴar lotsawar gefen kumatuna ta bayyana a fili (Dimple), wacce na tabbatar ita ce sirrin fuskata.

Na juya na nufi gidana a inda ina shiga falo wayar hannuna na yin ƙara, Yarima na ga an rubuta tare da lambarsa na yi murmushi na kanga wayar a kunnena.

"Hey!" Na faÉ—a.

"Muryarki ta yi mini daɗi a zuciyata, ita kaɗai dama nake son ji ko hankalina ya daɗa ƙwanciya."

"Wa ke magana ne ban gane ba?"

"Yasmin mijinki ne." Na yi murmushi na kashe wayar.

Ina aje wayar ƴan matan suka yi mini sannu da dawowa na amsa masu tare da ɗan ɓata mintuna biyar a wajensu, domin in basu nasu haƙƙin, na lura kuwa hakan na yi masu daɗi matuƙa. Ina hawa ban tsaya komai ba sai hidimar wanka, saboda ganin magriba ta kawo jiki sosai.

Yau kam addu'ata ta sha bamban da ta kullum, tunda yau na yi ta ne a kan Allah yasa Yarima ya ci gaba da sona har abada,ni kuma Allah yasa inji ina son shi,in gane son in aikata shi nima, Allah yasa in dinga yi wa Yarima biyayya a kan duk abin da ya umurce ni da shi.

Ƙarar wayata ita ta ɗan sa na waiga na kallo ta saman gadona, har na kawar da kaina manufata ba zan ɗauka ba, sai na yi tunanin ko Aunty ce, wannan tunanin ne yasa na miƙe cikin ɗan hanzarina na isa ga wayar tawa. Yarima na ga an ƙara rubutawa. Na yi murmushi na kanga a kunnena.

"Don't say hello to me. Saboda muryarki na rikita ni, ina gayyatarki cin abinci ƙarfe taƙwas na daren yau."

Kafin in yi magana har ya kashe. Na koma da baya na ƙwanta saman gadona na lumshe idanuwana haɗe da murmushin daɗi,nan take na tambayi kaina shin ko dai ina son Yarima ne? A take na ji ƙwayar idanuwana na karanto mini fuskarshi,shin ko wannan shi ne son? Na yi saurin tashi ina girgiza kaina,kai a'a,ni na san ba na son Yarima. Na yi tsaki na miƙe na nufi ƙasa wajen ƴan matan gidana.

A hankali suka dinga ba ni labari,a nan har na dinga zolayarsu da cewa ko wacce sai ta gaya mini sunan saurayinta. Muna cikin haka wayar da ke falo ta ɗauki ƙara, tana nuna mana alamun an bugo waya kenan. Mansura ce ta yi saurin zuwa ta ɗauka, cikin sakan ɗaya da kanga kan wayar a kunnenta na ga ta yi saurin durƙushewa ƙasa, sannan na ji tana gaishe da mai maganar. Yanda take yi tamkar tsaye take a gabansa, sai dai na ji ta ce, "To." Da sauri da sauri na ga ta iso gabana bayan ta ajiye kan wayar ta tsugunna tamkar tana neman in gafarta mata daga wani laifin da ta yi mini sannan ta yi magana.

"Allah ya taimaki Gimbiya, Yarima ne ya ce ki ɗauki wayar hannunki." A take na ji gabana ya faɗi, wanda ya yi daidai da kallon agogon da ke manne a kusurwar falon. Ƙarfe tara saura mintuna sha takwas,nan na tunano gayyatar da aka yi mini ta zuwa cin abinci ƙarfe taƙwas na daren yau.

Cikin É—an gaggawa na nufi sama tun kafin na isa falon sama na ji wayar tana ta kukan kirana, na yi saurin gudu na isa, tare da saurin kanga wayar a kunnena.

"Hey." Na faÉ—a cikin muryar da tafi kama da ta marar lafiya.
Chapter 6 · 0% Book details