Sashe 15
Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Girata kuwa sai na goga mata ƙarin baƙin jagira, domin ta ƙara fitowa, na ɗauki turare zan fesa, sai na ji ya riƙe hannuna har na ɗan ji tsoro saboda ban ga isowarsa ba, ɗan firgitar tsoron da na yi sai ma naga ta burge shi ya kamo hannuna ya miƙar da ni tsaye sai na ga ya sumbaci goshina, kunya ta sa na sunkuyar da kaina ya tallabo haɓata da hannunsa ɗaya.
"Your beauty make you to be the Prince's wife. Yasmin ya za'ayi in samu kamar ki in yi sakaci in rabu da ke,ai ya zama dole in ajiye mulkina in zama bawa a gare ki, saboda in samu in mallake ki da zuciyarki su zamo sun gauraya da jinina."
Idona a nashi amma sai na ji kamar idanunsa sun fi ƙarfin nawa, saboda wasu kunamun haske da suka fito daga cikinsa suka shiga nawa idon, wannan yasa na yi fari da idanuwana tare da lumshe su, wanda ɗan guntun murmushin da na yi, ya nutsar da gefunan kumatuna, abin da na san yana ƙara fito mini da ƙyauna a fili.
*ƘASAITA BOOK 2*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 12
"Sorry,ina baki kunya ko? Tashi na daina."
Ya kamo ni na miƙe tsaye, sannan ya fesa mini turaren da ke hannunsa.
"Komai ya yi sai dai abu É—aya da ki ka manta."
Na É—an yi Æ´an dube-dubena, na ga jikina ba abin da ya rasa, na tambaye shi amma irin tambayar nan ta ido.
Ya warware ɗan mayafin da na ɗaure gashin kaina ya lulluɓa mini shi irin lulluɓin nan na ƴan gayun boko shi ne a nannaɗe kai kawai a saki leɓe ɗaya a baya, ɗaya kuwa gaba, wanda ya bazashi ya rufe ƙirjina da shi, sannan ya zagaya ya fito da gashina ya ƙwanta baya, ya zagayo.
"Tsaya ina zuwa."
Har da ɗan gudun saurinsa ya isa ga aƙwati ya buɗa sai ga ɗan aƙwati ya fito da shi ya iso ya ɗora saman madubi, sannan ya buɗe sai ga sarƙa da ƴan kunne da zobe da agogo, duk shi ya saka mini su,ni kuwa ina tsaye ina kallon ikon Allah.
"Kin san dalilin gyara miki mayafi?"
Na girgiza kaina.
"Saboda You are full house wife." Na yi murmushi.
"To an gama, sai in ce miki yau zan miki wani abin mamaki, amma sai mun sauka ƙasa, sannan zan ɗaure miki idanuwanki da wannan ɗan hankicin sai mun isa."
"Gaya min tun a nan."
"No,sai kin gani da idonki."
Riƙe yake da hannuna muna tafiya har sai da muka iso ƙafar bene,sannan ya rungume ni jikinsa wai kada in faɗi,balle wani irin takalmi mai tsini ya saka ni sawa,ni dai na san mun daɗe muna sauka ƙafar benen,don na ji ya ce in tsaya ya dawo. Na yi tsaye tare da riƙe katakon da ke kare mai tafiya.
Ɗan tsayin mintuna biyu sai ga shi ya dawo, ya kama ni ina ji muka ci gaba da tafiya,ƙafata ta gane an zo irin ɗan filin nan na tsakanin wani hawa da wani sai na ji ya tsayar da ni ya zagayo ta bayana sai na ji ya ce.
"Zan ƙwance miki, amma kada ki buɗe ido sai na ce ki buɗe."
Sai da ya samu minti ɗaya da ƙwance mini,sannan na ji ya ce, "Open your eyes."
Ina buɗewa sai na ga wasu abubuwa masu ƙyalli sun zubo da yawa, waɗanda suka hana ni kallon abin da ke gabana, can cikin mamakin da nake yi sai na ji tafi ya cika mini kunnuwana tare da kiran.
"Happy birthday to you! Happy birthday to you Yasmin, Happy birthday to you."
Can sai na ga kamar an yi sama da wani farin yanki sai kawai na ga hall (É—akin taro), cike da mutane sun saka cake É—in murna a gaba (Birthday cake) Na juyo na kalli Yarima irin kallon murna da mamaki, sannan na ce, "Thank you." A kunya ce.
"Kin fi ƙarfin haka a gare ni." Sannan muka jero muka sauko ana ta tafin waƙar da suke yi tun farko.
Kai tsaye wajen dogon cake mai hawa wajen shida muka tsaya a gabansa, sannan na ji waje ya yi shiru, can daga sama na ji ana cewa.
"Muslim prayers." Sai na ji an karanta Fatiha, can kuma sai na ji an ce, "Christian prayers." Sai na ji suna yin addu'arsu da harshen Turanci, duk da ita kanta fatihar da harshen Turancin aka karanta ta.
Ana shafawa ɗakin taron ya ɗauki ɗan ihun waƙar yanka cake ɗin murna, amma ta waƙar kiɗan Bature, sannan aka zo aka zagaye mu. Wani Bature ya tsaya gefenmu sai na ji ya ce, "Wannan ɗan Sarki ne a Nijeriya, wannan kuma matarsa ce." Haka na ji ya faɗa da harshen Turanci.
Sai ya ɗauki wuƙa ya baiwa Yarima, sannan na ji ya ce, "Prince Faysal Jafar from Nigeria,zai yanka cake ya baiwa matarsa."
Ya faɗa da harshen turanci, sai ya fara ƴar ƙirga, bayan Faysal ya saita wuƙar a jikin cake ɗin sai ya ce, "One, two, three." Yana faɗar muka fara hure wutar (Candle) ɗin da suke cin wuta a saman cake ɗin har izuwa biyu,yana cewa uku Yarima na Kamo hannuna muka datsa cake ɗin waje ya ɗauki tafi.
Sannan Yarima ya yanko yasa mini a baki, a kunya ce na gutsura ni ma na yanko na sa masa shi ma ya gutsura sai É—an tafi ihu ya tashi, shi kuwa Yarima har da saurin rungume ni.
Kai rayuwar Turawa na bani sha'awa, amma iyakacinta kenan sha'awar, tunda ba Addini a tare da su,daga nan sai na ji kiɗa ya canja, cikin ƙanƙanin lokaci na ga suna kama junansu namiji da mace suna rawa suna bin kiɗan a hankali.
Yarima ya miƙo min hannu ni dai na san ban iya ba, na girgiza kaina, "No,taho." Na ɗan maƙale ya janyo ni jikinsa.
"Kalli ƙafafunsu." Ya raɗa mini a kunne na tsaya na kalla.
"Ke ma haka za ki dinga yi."
Ni dai na san kunya zan ba shi sai na ce kunya nake ji, ya dinga sani dole ni kuwa na ƙiya, ƙarshe wata Baturiya ta miƙo masa hannu sai ya sake ni ya kamata ya ci gaba da rawarsu.
Ni kuwa ina tsaye ina kallonsu ganin ta ƙwanta a kafaɗarsa yasa na ji wani ɗan abu ya dakar mini zuciya,wai a take sai na ji nayi tunanin ko dai irin ƴan matan da yake tare da su ne a nan,nan take na ji raina ya ɓaci, idona kuwa ya kasa ɗaukewa daga wajensu.
Can na ga ya ɗago yana ɗan waigen nema na, ya ɗago mini hannu sai kawai na ji na harare shi na juya, sai na ji na rasa inda zan nufa ina tunanin in tafi ɗaki sai na ji ya ruƙo hannuna ta baya ya rungume ni, tare da turo haɓarsa a jikin kafaɗata, sai na ji ya cigaba da rawa da ni tamkar muna rawar tare.
"Sorry my darling,kin san su al'adarsu ce."
"Kai kuma Addininka ne.?"
"Kai, to fa,ki yi haƙuri na yi kuskure babba,ƙato." Sai kawai muka ji kiɗa ya tsaya wajen ya ɗan ɗauki tafi.
Daga nan sai na ga wannan dai Baturan ya É—auki bututun magana (Macrophone) yana cewa duk su tsaya inda suke za'a gabatar da kowa, É—aya bayan É—aya ya dinga gaya mini sunayensu,su al'adarsu shi ne a gaisa ko a É—an rungumi juna, amma mai jawabi ya gaya musu mu haramun ne tun farko ma saboda haka sai dai a É—aga hannu in wuce.
Sannan suka ƙara gabatar da ni,nima da bada ɗan guntun tarihina ga shi duk wanda na zo kanshi sai ya ba ni ƙyauta dama wata mace na biye a bayana da irin kayan ma'aikatan hotel ɗin in aka ba ni in miƙa mata.
Wasu har da ƴar guntuwar fulawa wasu doguwar fulawa, wasu mai yawa, wacce take naɗe a cikin leda, wasu ƙwalaye nannaɗe da ledar naɗe ƙyauta (Wrapping sheet), daga nan kuma aka bayar da umarnin a tafi ɗakin cin abinci, gaba ɗaya muka nufi can.
Waje ne shi ma ƙaton gaske, amma gaba ɗayansa wani tebiri ne zagaye da shi mai kamar an ajiye doguwar gwanda, wato ba zagaye yake ba kamar ƙarfen kuɗi zagaye yake amma kamar Oval shape.
Kowa ya ja kujera ya zauna,mu kuwa muka zauna ƙarshen tsinin tebirin kenan kowa mu yake kallo, duk yawan mutanen nan kuwa kamar an ƙirga su kowa ya samu wajan zama,dama kafin mu isa an gama shirya komai kowa an ɗiga masa lemun ruwan nan nasu,rabin kofi,mukaɗai aka ajiyewa wata doguwar ƙwalba an rubuta concentrated sof drinks.
Ana ci ana yiwa juna tsiya, daga wannan ya ce mini shi ya koyawa Yarima magana a ƙwashe da dariya, sai wancan ya ce shi ya koya masa cin abincinsu, suka dinga hirar makaranta, tsiya dai kala-kala sun yi wa juna,anan kuma suke yaba masa da iya zaɓen mata,wai har cewa suke aƙwai mata masu ƙyau a Nijeriya?.
Nan na ga ashe idan aka yi Birthday yanka cake ɗin ake ashe a baiwa kowa, saboda na gan shi a ɗan faranti gaban kowa, da gani kuma yanka shi aka yi, tabbas na ga yanda turawa ke rayuwa, dole Yarima ya zama ɗan rayuwa,ni har kunya na dinga ji idan na hango wasu na tsotsar bakin juna,ko ƴar soyayyarsu, ga shi a gaban kowa ma yi suke ba wanda ya damu da wani, wani lokacin ma Yarima ke taɓo ni in gani sai in sha masa kunu.
Ba mu tashi ba sai wajen ƙarfe uku na darensu wanda sai da muka zo ɗaki ma na ga dare ya yi, kafin a gama shigowa da kayan da aka ba ni ƙyaututtuka na cewa Yarima zan ɗan shiga ruwan ɗumi saboda na gaji da yawa, shi kuwa har da yi mini kashedin in na fito shi zai zaɓa mini kayan baccin da zan saka, na bishi da to. Ya koma falo saboda tsayawa ya ga masu aikin hotel ɗin sun gama shigo da kayan duka.