← Book details Karuwan Cikin Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 15

Sashe 8

Karuwan Cikin Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Copy is not allowed 🚫

EPISODE 5
Da sauri ya saki bakin jawaher da yake mata wani irin kiss jikin'ta a sanyaye ta miƙa mai wayar tace '' anni ce take son magana da kai..,
amsa yayi, ya kara akunne gaisawa su kayi sannan ta tambaye shi ya iyalin nasa alhamdulilah yace ,
anni tace '' to JAWAD na sanka ba dai iya mugunta ba yadda kasan kurtun soja ne ya raine ka , dole sai kai hakuri da halin NAJLAH yarinya ce a sannu a hankali kana nuna mata nan zaki bi wannan hanyar tafi zata koma yadda kake so, dan Allah ban da nuna isa su ya'yan yanzu lallabi da nasiha ke aiki a jikin su kar kuma inji wani abu ya biyo baya nasan ka sarai tun kana yaro dan haka , ka kular min da jika karatu tazo dan haka bana son jin wata magana..,
sosai ƙarshen maganar ta , ta bashi dariya shafa kai yayi yace '' insha'Allahu zan kiyaye amma ita ma ku ja mata kunne jiya video's naga ni a wayar ta , a haka za tayi karatun ga kallon fina finan yan Japan da Philippines..,
Dan Allah dai a kula kaji dan Allah barka
to yace sukai sallama miƙa mata wayar yayi lokacin jawaher ta bar gurin amsa tayi jikin ta na rawa ita kuma haka Allah ya haɗa ta da kaddarar zama da wa'yannan mutane da ba su san mece kunya ba juyawa tayi tana tafiya a hankali tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki.
tana shiga daki ta rufo dakin ta , ta kwanta dan ya mutsa fuska tayi tsoron ta ɗaya lokacin period dinta yazo ba karamar wahala take sha ba shiyasa kama abinci ta ci shi kaɗan, duk hankalin'ta ba a kwance yake ba.
sosai take juyo saboda cikin'ta ji tayi anyi knocking da kyar ta iya tashi gumi duk ta wanke mata fuska ta buɗe kofa yaya ne fa shirin tafiya wajen aiki zama tayi a ƙasa tana matsar kwallah tace '' yaya JAWAD mutuwa zanyi cikina ciwo yake min..,
da sauri ya ɗurkusa kasa ya tallafo habar'ta yace '' Najlah me yake damun ki..?,
cikin ta tayi mai nuna dashi ba ƙaramin tashin hankali take ciki ba kuka ta rushe dashi ta kifa kan'ta akan cinyarsa tana kuka jawaher ce ta shigo ta gama haɗa trolley din'ta tace '' to me yake faruwa sallama na shigo nayi mata..?,
kallon ta yayi yace '' har kin shirya..?,
kai ta ɗaga mai fuskar'ta cike da alhini ta durkusa tace '' me yake damun ta..?,
ta ƙara mai maita masa tambayar da dazu tayi mai ajiyar zuciya ya sauke yace '' cikin'ta ke ciwo..,
innalillahi sannu normal ciwon cike ne ko na period ta faɗa tana kallon Najlah.
ƙasa magana Najlah tayi sai juya kai take yi hannunta na kan mararta jawad ya kalli jawaher yace '' sweet kawai ki tafi Allah ya kiyaye hanya ba zan samu damar kai ki ba zan kirawo doctor kar na ɓata miki lokaci tun da shi jirgi baya jira..,
haka ne wallahi to Allah ya bata lafiya ta faɗa tana tashi daga tsugunan da tayi ranta fas tamkar zata , taka rawa fita tayi tare da ja musu kofa ɗago kan Najlah yayi yace ''sannu kinji ko bara na kirawo doctor ya duba ki..,
ƙara rushewa tayi da kuka ta girgiza mai kan'ta tare da riko hannun sa tace '' karka kirawo shi allura zai min a hankali zai sake ni bana so a ka kirawo doctor..,
haɗe rai yayi yace '' bana son zancen banza sai ma kin zaɓi abin da za ayi miki bacin kuma baki da lafiya..,
kuka ta ƙara rushewa dashi cire mata mayafin'ta yayi sannan ya balle mata riga ya cire ganin irin gumin da take yi itama ba tayi kokarin hana shiba saboda bata cikin nutsuwar ta.
kwantar da ita yayi a akan gado ya cire rigar sa ta lauya da wular da ya saka ya matsar da briefcase din'sa da wasu folder's da ya fito da su daukan wayar sa yayi ya dannawa doctor Kira bugu ɗaya ya ɗauka yace '' doctor Dan Allah kazo gidana akwai mara lafiya...,
doctor yace '' wallahi bana gari amma bara na turo maka sister zuwairat insha'Allahu zata so cikin gaggawa itama tasan aikin ta..,
okay ba damuwa sai ka turo ta ɗin ya faɗa yana kashe wayar sa ,
zama yayi kusa da ita kuka ta ƙara rushewa da shi ta riko hannunsa tace '' kiramin Hajiya ta zan mutu yaya..,
da sauri ya kalle ta , shi be san ya zai yi da yarinyar nan ba rakinta yayi yawa dauke kai yayi yace '' ina wayar ki, ki kirata da ita mana..,
kuka ta rushe dashi ta kwantar da kanta a cinyar sa tace '' yaya cikina ciwo..,
ya buɗa baki kenan zai magana wayar sa tayi ringing da sauri ya ɗauka saboda yana kyautata zaton doctor ce ɗagawa yayi ai kuwa ilai itace sallama tayi mai tare da gaishe shi cikin girmamawa amsawa yayi tace '' ina bakin gate masu gadib gidan sun hana ni shigowa...,
Okay karki damu suna kan aikin su ne , zan musu magana yanzu.
to tace mai ya kashe wayar gyara mata kwanciya yayi ya fita kuka ta ƙara rushewa dashi har suka dawo bata sani ba doctor zuwairat ta durkusa ƙasa tace '' innalillahi wainna ilaihir raji'un sannu me yake damun ta..?,
ta ɗago da kan'ta tana kallon Jawad cire medical glasses dinsa yayi yace '' ciwon ciki..,
oh Allah ya bata lafiya idan tana yi allura ake mata ko magani ake bata da sauri Najlah ta firgita tare da ja da baya hawaye wani na bin wani gaban ta na faɗuwa tace '' dan Allah karki yi min allura karki bani magani yanzu ma ya fara saki duk wata haka nake yin sa..,
dariya abin ya so ya bawa doctor sai ta danne ta zauna akan gado tace '' yanzu idan ban miki wa'yannan abubuwan da kika faɗi ba , me zan miki..? kefe mace, ce wannan ciwon da kike gani ko kwatan ciwon haihuwa be kai ba..,
da sauri Najlah ta ɗago lokaci ɗaya suka haɗa ido da Jawad hawaye ta share ta kalle sa tace '' cikin nawa ya dena yi min ciwo ba sai tayi min komai ba..,
haɗe rai yayi yace '' ni sa'an kine ko ita da kike faɗa mana haka..?,
murmushi doctor tayi tace '' na lura yar daru ce kawai bara na rubuta mata magani idan taci abinci ta sha zai saka ta bacci insha'Allahu kafin ta tashi cikinta ya cika kuma period din zai zo batare da ta ƙara wahalar da ita ba..,
okay ba damuwa rubutu tayi mai a takarda ta miƙa mai kuɗin'ta ya dauko ya bata tai mai sallama tare da godiya ta fita be biya takan Najlah ba , ya fita ya bawa me musu aike ya siyo mai zama yayi a parlour yana jin sautin kukan ta ransa duk a ɓace yake ciwon kai kuka yake saka shi , ga wannan kukan da take har tsakiyar kan'sa yake jin kukan nata.
tsaki yaja jin anyi knocking ya tashi ya buɗe kofa ya karbi ledar maganin yace '' riƙe canjin...,
godiya yayi mai ya rufe kofar kai tsaye kitchen ya nufa rasa me zai mata yayi gwara ya tambaye ta me take so komawa yayi dakin ya ajiye ledar maganin a kan bedside drawer ya zauna yace '' me za kici..,
ɗago da kan'ta tayi ta kalle sa tace '' dambu...,
da sauri ya kalle sa shi tun da yake a rayuwar sa ya taɓa kwatan ta dambu ko da yayi zaman hostel bayayinsa tunda wani aikin sai mata cikin mamaki yace '' dambu kuma...?,
kai ta gyaɗa mai ba tare da tayi magana ba
ajiyar zuciya ya sauke yace '' sai dai na yi miki oder take a way ni ban iya dambu, ba bana jin jawaher ma ta iya gashi ɗazu ta bawa me yin girki hutu sai ta dawo tun da gaki a cikin gidan zaki saboda tafiya za tayi..,
dauke kai tayi wato gata baiwa ko ta girkawa mijinta ban da ita mara hankali ce bama ta damu abincin wannan shi ake cewa mijinta ba Allah ɗaya gari bamban.
jin tayi shiru yace '' magana fa nake miki..?,
ya tsuna fuska tayi cikin ta na murɗawa tace '' a'a barshi kawo min yogurt..,
tashi yayi ya fita bajimawa ya kawo mata tsiyaya mata , yayi a cikin kofi amsa tayi ta tashi ta fara sha tas ta shanye sannan ya ballo mata magani da ruwa ya miƙo mata kwalla ce ta taru a idanuwanta ta kura mai ido zuciyar'ta tamkar zata faso kirjinta ta fito saboda tsabar fargaba hade rai yayi, dan haka ba shiri ta amsa ta saka a bakin ta amai ne ya taso mata , da sauri ta shiga toilet ta fara kwara amai gaba ki ɗaya abincin da taci sai da ta amayar dashi.
hankalin sa ne ya tashi da sauri ya shiga toilet din duk ta ɓata jikin'ta da amai gashi jikin ta ya saki dole sai ya temaka mata ta gyara jikin'ta,
KARUWAN CIKIN GIDA

Copy is not allowed 🚫
Chapter 8 · 0% Book details