Sashe 2
Karuwan Cikin Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata sassanyar iska ke kaɗawa yayin da bishiyu ke rangaji iskar nan a hankali take ratsa jikin ta na kasan cewar kayan jikin ta marasa nauyi ne miƙa tayi ta , tashi tsaye bata da tsayi sai dai Ubangiji yayi mata kira me kyau me daukar hankalin duk wanda ya kalle ta ɗan ƙaramin tsaki ta ja , ta dauki wayar ta da take neman dauki ta ƙara a kunne tace '' eman yau bana jin zan iya attending lecture so idan kinga da faraga ki min kawai attendance.., saurarawa tayi domin jin me eman din za tace jan ƙaramin tsaki tayi tace '' ni wallahi na manta ma gwara ni da ku yanzu kina ina ne nake jin tashin kiɗa kar dai a club kika kwana...?, dariya eman tayi tace '' no ba'a club na kwana ba ina mai tama ni da su jee a satin nan nake so na koma gida saboda Islam tace momy ba lafiya so ina so naje naga ya jikin ta yake amma kafin nan ina so na yi solving wannan matsalar da nake ciki har yanzu ba mu cimma matsaya ba idan har ya takura zan saki video ba abin da ya dame ni abin kunya baya na bashi.., zama tayi ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tace '' ke wannan ita ce matsalar ki ni ga babbar matsalar da take cikin gidana wannan shegiyar yarinyar me kama da zubin karuwai wai jibi zata ta zo karatu a kuma gida zata zauna.., wannan matsalar ita take damuwa wallahi gashi my man ya kasa fahimta ta , na fiso nayi rayuwa ni kaɗai ni da miji na , kuma kinga idan har tazo zata saka min ido ne a cikin rayuwa ta ni ina tunanin tun da ba sona suke ba C.I.D aka turo ta kuma wallahi wannan yarinyar duk bu ɗewar idanuwana ta fini. Dariya eman tayi tace '' jawaher me kike tsoro ko dai abin da kike wa wasu kike tsoran ayi miki shi..? amma in ba haka ba ban ga abin kin ta zo ta zaunar miki ba idan tayi miki ba sai kici kuttumar uban ta ba ki nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane ba mamaki ke abin da kike yi kaɗan ne akan ta.., shiru tayi tana sauraran ta sannan jawaher tace '' haka za a yi wallahi sai ta gwammace zaman hostel akan zaman cikin gidana yanzu idan ta zo zuwan da kuke yi kuna sakewa babu fa wannan shikkenan magana ta ƙare nima yan wa'yanda nake kawowa muke raƙashewa babu wannan kaf dangin su a rasa wa za ta zauna ta yi karatu a hannunsa sai shi., ke fahimtar dani akwai aure a tsakanin su ne wannan abin da kike yi yayi yawa ko dai kishi ne Eman ta faɗa tana danne dariyar ta. wani ashar jawaher tayi tace '' bara na turo miki picture din najlah zaki zan dole na tashi hankalina kinsan namiji dan kumana ne ba'a shedar sa.., eman tace '' haka ne wallahi kawata karki manta ki turo min picture din ta.., shegiya na fasa ma turo miki saboda tsabar son tsegumi har so kike na turo miki to bazan turo ba duk sanda ta zo kya ganta.. Cewar jawaher. dariya eman tayi tana kashe wayar ta. tashi jawaher tayi ta bar guiding tana fita wanda yake kula da gurin ya kwashe kayan da ta yi amfani da su tura kofar da zata sada ta da main parlour tayi, turus tayi ganin bakon al'amari dakyar ta iya sai ta kan'ta tace '' sweet saukar yaushe...?, gaban ta yana lugudan uku uku har ga Allah bata son abin da ya tsira kwanan nan sai ya dinga dawowa batare da ya faɗa mata ba , zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun alfarma na parlour ta dauke kai daga kallon najlah da take danna waya . ba tare da ta kalli inda jawaher take ba tace '' ina wuni.., lafiya kawai tace ta mai da hankalin'ta kan mijin ta ɗaukan pillowcase tayi ta rungume ta kashe idanuwan'ta tana aika mai da wani irin kallo me rikitar da wanda aka yi domin shi murya ƙasa ƙasa tace '' sweet kace min sai jibi zata tawo chanza rana tayi kenan..?, hannunta Jawad ya kama tare da aika mata wani irin sako yana yin messages din hannun ta . tari najlah tayi domin ta ankarar da su basu kaɗai bane da sauri ya dawo cikin hayyacin sa. idanuwan'sa har sun canza launi yace '' jawaher kai ta dakin da zata zauna.., tashi tayi tana sakar wani shu'umin murmushi tace '' am kanwata ki zaki iya tashi sorry fa na rage miki jin daɗin ki.., tashi najlah ta gyara zaman hijabin da yake jikin ta ta dauki trolley bag din ta ta fara ja tsaya, tsayawa tayi batare da ta juyo ba , ita daman ta dade da sanin cewa zuwan ta gidan ya Jawad akwai babbar matsala tana da gudun hulakanci dan haka wallahi wata ran dole su kwashi yan kallo inhar jawaher ta ci gaba da yi mata haka , wannan wanne irin rashin hakuri ne da rashin kunya a gaban ta suna yun kurin aikata abin da ba dai-dai ba , tana cikin wannan tunani ne taji yace '' jeki zan saka a daukar miki ita , ki dena ɗaukar kaya masu nauyi.., to kawai tace ta bar jakar ta anan bude mata dakin tayi shiga tayi ta kwanta a tamkekem gadon da yake cikin bedroom din, bin ko ina take da kallo tashi tayi ta cire hijabin ta , wayar ta , ta dauka ta lalubo number hajiya bugu ɗaya ta dauka fashe mata da kukan shagwaɓa tayi tace '' Hajiya wallahi bazan iya zama a cikin gidan nan ba auntu jawaher bata da kirki ni nafi son na zauna a gurin ya Aliyu nafi so nayi B.U.K dan Allah ku mai dani can tun da nan ko admission basu fara bayar wa ba.., Hajiya tace ''Najlah yanzu ke da ace aure kai miki ya kenan tun da kika ji zancen tafiyar nan kika daga hankalin ki, kinsan dai halin family din abban ku duk abin da suka tsara ba wanda ya isa ya ja dashi dan haka kiyi hakuri har ki gama zama ki dinga zuwa hutu bawai dindindin zaki zauna ba.., ajiyar zuciya ta sauke tace '' inna su adal suke..?, abban ku ya tafi da su gidan anni Cewar hajiya Najlah tace '' idan sun dawo kice ina gaishe da su, Hajiya tace '' to za suji insha'Allahu . sallama su kayi ta kashe wayar ju yowar da za tayi suka hada ido da Jawad da sauri ta da baya daukan hijabinta tayi ta saka kasa cewa komai tayi kirjinta na tsanan'ta bugu har ga Allah bata son wannan kallon kulla da yaya Jawad yake mata shi ko kunya baya ji ta sha kama shi yana kallon ta sai dai ya waske. trolley din'ta ya shigo mata da ita sannan yace '' duk wani abu da kike bukata ki yi min text messages zuwa gobe insha'Allahu ina ga zan tafi Dubai.., a hankali tace '' Nagode sosai Allah ya ƙara arziki bana bukatar komai, komai abba ya siya mun.., ƙafarsa ya ɗora akan gado ya jingina da bango yace '' bakya jin zafi ne..?, da sauri ta juyo jin maganar sa waskewa yayi ganin rashin dacewar maganar da yayi yace '' baki kunna AC ba kin zauna haka.., ajiyar zuciya ta sauke da har sai da ya jiyo lokacin da ta sauke ta fita yayi ya dafa kan'sa me yake shirin aikatawa ne . cin karo sukai da jawaher tace '' abincin ka ya haɗu wanka zaka fara ko cin abincin..?, kai wa Najlah nata ni sai nayi wanka zanci ban sani ba ko tana jin yunwa.. da sauri ta kalle tace '' She's just girl, ot is this house not hers? If she's hungry, she should just speak up. I'll go and prepare your bath water.., kallon ta yayi da sauri ta hadiye sauran zancen nata kitchen ta shiga ranta duk a ɓace wayar ta ce tayi ringing da sauri ta ɗauka tace '' zan kira ki ya dawo bana cikin nutsuwa ta.., tana kai wa wannan ta kashe wayar ta , tana sakar gauran numfashi cikin takaici ta hada komai a cikin tray zura wayar ta , tayi a aljihu ta ɗauka kai tsaye dakin Najlah ta nufa ko da tace batai knocking ba ta shiga tarar da ita tayi bata cikin dakin sai dai motsinta da ta ji a toilet tsaki taja ta ajiye a kasa zata juya Najlah ta fito daga ita sai towel gaban jawaher ne ya faɗi ta raina kan'ta wani abu ne ya tokare mata maƙogaro tabbas sai yarinyar nan ta bar gidan nan idan fa zata iya tunawa da aure a tsakanin su to idan shi ya zo ya ganta a cikin wannan hali ya ke nan dakyar ta iya saita kan'ta tace '' am gashi nan..., thanks kawai ta ce ta zauna akan stool tana tsane gashin ta hand dry ta dauko ta fara busar da gashin ta na muzayen asali bugo mata kofa tayi murmushi Najlah tace '' mahaukaciya duk wannan abin da kike yi akan yaya ne insha'Allahu sai yayi mata har uku bayan ke.. gama shiryawa tayi ta buɗe trolley din'ta ta dauko duguwar riga ta wani material an mata ɗinkin T line daga sama rigar ta bude daga ƙasa ta tsuke kulle kofar ta tayi ganin ita kaɗai ce ba kowa kawai sai ta cire towel din jikin'ta bra ta saka da pant sannan ta saka rigar dan dai saman da faɗin sa amma duk da haka ya fito mata da kirar jikin ta tubke gashin kan'ta tayi ta saka chantili cap feshe jikin'ta tayi da turare ta zauna buɗe abincin tayi ta dan taɓe baki ita irin wa'yannan abincin na turawa be dame ta ba ɗan danawa tayi ina baza ta iya ci ba daman tun a ido taga ba zata iya ci ba gashi hanjin cikin ta har wani curewa suke guri ɗaya. tashi tayi ta buɗe fridge ban da lemo da ruwa ba wani abu da zai iya tare mata yunwa tashi tsaye tayi ta