← Book details Karuwan Cikin Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 15

Sashe 12

Karuwan Cikin Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

https://www.youtube.com/@nasreenminallah

Juyi za tayi da sauri ya dauke hannun sa tare da tashi tsaye ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaga bata buɗe ido ba ta koma baccin ta ja mata kofa yayi ya fita daga dakin kai tsaye part din sa ya nufa ba
zama yayi tare da zuba uban ta gumi abubuwa da yawa ne suka hana shi sakat.
daukan laptop din'sa yayi ya soma aikin sa domin tunanin da yake ya ragu.......
amma ina kasa komai yayi dafa kansa yayi da ya soma sara mai matsar da laptop din tayi ɗaukan wayar sa yayi ya kai tsaye number jawaher ya kira har ta gama ringing din'ta bata dauka ba ajiyewa yayi sai gashi ta kira Muryar ta ƙasa ƙasa yawa tame maye wannan yanayi nata baƙaramin ƙara saka Jawad tayi ba cikin wani hali tace '' sweet heart baccin gajiya nake wallahi kaga jiki na duk yayi sanyi yakake NAJLAH tayi maka abinci ko restaurant kaje ka siya..?,
hnmm beb ni yanzu ba abinci nake buƙata ba..
kirjin tane yayi wani irin bugu tashi zaune tayi tasan sarai halin mijin nata kar yace ta dawo gobe, kudi ba matsalar sa bane cikin kwantar da hankali tace '' beb me kake bukata..,
Keeeee yaja karshen maganar.
zaro ido tayi tace '' ka saka aranka ka riga ka samu ma..bara na kiran ka video call..,
jawaher video call bazai amfanar dani komai ba sai ma ya ƙara tun zura ni..
my justice to kasha lemon tsami insha'Allahu duk abin da kake ji zai yi ƙasa.
ajiyar zuciya kawai ya sauke yace '' to yanzu yaushe zaki dawo wallahi jawaher bazan iya jurewa ba..,
gaban tane ya ƙara faɗuwa tace ''haba sweet me kuma ya kawo wannan maganar..?,
ajiyar zuciya ya sauke yace '' sai anjima..,
ya faɗa tare da kashe wayar bin wayar ta , tayi da kallo Alhaji kallon ta yayi yace '' me ya faru ya kira ki da wannan tsohon daren kamar besan ban bancin naija da turkiya ba..?,
da sauri ta kalle sa tana mamakin halin alhaji karfa ya manta jawad mijin tane kuma ya na da ikon kiranta a ko wanne lokaci...
bata ce mai ƙala ba ta , tashi tsaye fridge ta buɗe ta dauko ruwa me sanyi gorar sa har hazo hazo take yi ya kusan ƙanƙara balle murfin tayi ta kafa baki bata cire ba , sai da taga ba komai a ciki sannan ta cire jan dogon tsaki tayi tana miƙa jingina tayi da bango tayi shiru ganin yanayin da ta shiga alhaji ya matso kusa da ita kama lips din ta yayi kau da kai tayi tace '' Alhaji in har ba zaka cire tsanar da kake wa Jawad ba, ba shakka alakar mu tana shirin yankewa ina son mijina ya za a yi ka dinga nuna min baka son mijina nima din kenan ba sona kake ba akwai abin da kake so kana samu zaka yardar da ƙwallon mangaro ka huta da ƙuɗa..
JAWAHEER ni kike faɗawa wannan maganar..?,
wani murmushin takaici tayi ta dauke kan'ta daga kallon sa da tayi tace '' wanne dare ne jemage be gani ba ....?.da har kake tunanin zan raga maka..?,
tashi yayi ya zo har inda take yace '' DAREN MUTUWAR SA....,
da sauri ta kalle sa tace '' me kake nufi da haka...?, kardai kwantan ɓauna kake min..?,
ɗage kafaɗa yayi alamar owo miki.. rakiya tayi mai da ido har ya fita daga dakin tsaki tayi ta dauka kwalbar giya da ɗazu yayi musu oder ta , ta fara sha ba kakkautawa..

************ TARABA STATE..
UMMEE ni gaskiya matata tane buƙata ke kirawo yaya yaje ya basu HAKURI tun da dai kin korar min beb ɗina..
da sauri Hajiya bilkisu ta kalle sa tana mamakin halin ALTAB kwata kwata bashi da kunya ƙasa magana tayi sai girgiza kafa tayi idanuwan'ta ya kaɗa yayi jaaa.
cije lips din'ta tayi anya kuwa lamarin nan na ALTAB ba da sa hannun wannan BAKIN mugun me jikim hankaka fatar jikin sa fari , amma naman sa baki dole ta saka a gayyato mata malamai suyi mata abinci ke idan kuwa haka ne ƊAN BUZUU ya taɓo abin da yafi karfin sa..
UMMEE wai ba zaki rabu da mutanen nan ba su basa gaban ki amma ke kullum suna cikin zuciyar ki me ya saka zaki saka sharri ga alkairi kuma auren ki da ya mutu daman can Ubangiji ya nufa rabo nane ya fito dake daga gidan nan ni da bani da wani karatun addini amma nasan haka amma ke , karatun ki be miki amfani ba wallahi... *WALLAHI TAUSAYIN YAYA NAKE DA YAZO DAGA CIKIN TSATSON KI*
hannnu ta ɗaga mai tace '' ya ishe haka haka jawad nace ya ishe haka tun kafin na faɗa maka wata bad magana ka fitar min daga cikin dakin nan shasha komai dan kai nake da ubanka ba wani bane..,
dariya yayi yace '' wallahi bana bukatar Dukiyar haram ubana kuma da kullum kike rainawa alhamdulilah yana da nashi arzkin kina gidan wani amma kina kallon arzikin tsohon mijin ki......NIFA TRUE CE BAZAN FASA FAƊA BA wallahi...,
pillowcase ta dauka zata jefa mai da sauri ya kauce yana fita da gudu daga cikin dakin nata..
dafa kan'ta tayi da yake tsananin sara mata daukan waya tayi tana kallon Luxury watch da yake manne a bango ƙarfe goma sha biyu na dare dogon tsaki taja ta rasa wannan wanne irin meeting Alhaji alee suke kamata yayi ace iyan zu kana cikin gidan ka , ba mamaki Saboda halin sa Ubangiji ya jarrabe su da yaro me halin ALTAB...SIYASA KO MUGUN WASA...
haka ta raya a ranta da sassarfa ta hau stair case cin karo tayi da AFNAN..da sauri ta kalle tace '' AFNAN ina zaki cikin daren nan na ganki da shirin fita wannan liqab din fa...?,
gaban AFNAN ne ya faɗi ta sauki ajiyar zuciya tace '' so nayi na tsorata ki fa nasan yanzu ina ƙasa kina jiran daddy..,
tamkar an zuba mata ruwan sanyi haka yaji a cikin zuciyar ta , tace '' bana son shashancin banza zo ki wuce ai sai ki saka na fara wani tunani akan ki..,
murmushi tayi tace '' haba UMMEE kamar baki san wacece ni ba , ina yaddar da kika bani..?,
AFNAN zo ki wuce bana son jin wata magana..
jin taku suka yi a bayan su gaba ki ɗaya suka juya Alhaji alee ne yana rike da briefcase fuskar'sa ba wata fara'a kallo ɗaya zakai mai kasan yana cikin ɓacin rai cikin tsananin kaushin murya wacce ke bayyana ɓacin rai yace '' KI FAƊAWA ɗan ki bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane idon kuwa yaki ba zai ƙi gani ba..,
Alhaji kome ALTAB yayi be kamata mu juya mai baya ba..
hannu ta ɗaga mata yace '' ya ina zance kina juya min wani guri na dabam danƙi JAWAD nake nufi ya fita daga sabgar mu idan kuwa yaki zamu shafe shi a doran kasa wallahi..,
Alhaji alee ni kake fadawa zaka kashe ɗana...?,
UMMEE ta faɗa cikin tsananin zafin zuciya..
bece komai ya wuce ya barta da sakakken baki kallon kallo aka shiga tsakanin afnan da UMMEE.
kasa cewa komai tayi daukan waya tayi ta soma laluben layin JAWAD kash tararwa tayi switch up tsaki taja tace '' tsiyar Jawad kenan ai ta kiran sa aban za ni ban ga amfanin wayar jawad ba..,
UMMEE be kamata kuyi magana a cikin waya ba kawai gobe mu tafi Abuja sai ayi komai kya ma kori waccan shegiyar idan be mai da ta gidan su ba..
Good idea haka za ayi kin Kawo shawara me kyau.....
tafiya tayi dakin ta sai sake sake take yi har bacci ɓarawo ya dauke ta batare da ta cire kayan jikin ta ba
À bangaren Alhaji kuwa yana shiga ya cire babbar rigar sa sai wuci yake zama yayi akan gado yana girgiza kafa a yanzu babbar matsalar sa JAWAD idan be kawo karshen sa ba to lashakka shi jawad zai kawo nasa ƙarshen duk me son tono sirrin ka , wanda ka bunne tsahon shekara da shekaru baka so kuwa ya san shi ai maƙiyin kane..
babbar matsalar sa abin da boka yace yayi yana tunani akai anya kuwa zai iya , wayar sa ce tayi ringing da sauri ya daga yace '' wallahi Alhaji na kasa yanke ko wacce irin shawara wankin wula yana so ya kai mu RANA tun yaron nan yana yaro naso mu gama dashi tun da tun farko alamu sun nuna yar manuniya ta nuna shi ne zai zama tarnaki a gare mu amma kaki fahimtar haka..,
haka zaka daure kayi ita da man duniya ba'a samun ta , ta cikin sauki, ka manta me muka yi a teluwar mu ta farko wannan ba wani abu bane ita siyasa idan kana so a dama dakai to zubar da jini kaci mushe aljanna ta me rabo ce...
shiru yayi yana sauraren sa sai kuma yace '' to zan gwada na gani..,
wanda ya kirawo yace '' yauwa ko kai fa haka ake so..,
sallama yayi mai ya kashe wayar sa...

OSOKORO ABUJA..
Chapter 12 · 0% Book details