← Book details Karuwan Cikin Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 15

Sashe 3

Karuwan Cikin Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kama kugunta to yanzu ina ta dosa kenan gaskiya ba zata kashe kan'ta ba dan haka , ta dauki mayafin'ta ta yafa ta fito ɗauke kai tayi lokacin da ta gan su hannun su a tsarke da na juna suna saukowa daga kan stair case tamkar wasu tattabari taɓe baki tayi tace '' aikin banza wannan aunty jawaher din yar uwar karuwa ce sai wani nanike mai take shi kuma tattabari sarkin aure yana biye mata ..., tafaɗi haka a cikin zuciyar ta Cikin barikan ci tace '' sister akwai abin da kike bukata ne....?, ajiyar zuciya ta sauke tace '' uhmm daman bazan iya cin wannan abincin ba ne zan girka da kai na., dafe goshin ta jawaher tayi tace '' oh na fa manta baki saba ba cin irin wannan abincin ba sai local dishes.., murmushi tayi tace '' ai yana da kyau mutum karya watsar da al'adar sa, good girl haka ake so ga kitchen din can kije ki dafa abin da kike so. cewar jawaher. bata ce komai ba ta juya tabar gurin dining table suka nufa Jawad ya ja mata kujera ta zauna shima yaja ya zauna serving ɗin'sa ta fara yi tace '' am sweet ba ka ce komai ba maganar tafiya Turkiyya da zanyi bikin zeey yana fa matsowa ya kamata muyi abin da za muyi wallahi su mami ma ni suke jira one month kaɗai fa zan yi amma duk kabi ka ɗaga hankalin ka za mu dinga video call nasan abin da kake nufi komai za mu iya ta video call... kasa kai chokali bakin sa yayi yace '' video call me zai saka ban da ya ƙara tun zurawa ?, wani numfashi ta furzar me wuci tace '' sweet idan ka hana ni tafiyar nan bakai min adalci ba mutane nawa ne suka amfani da video call kuma suna in joy mode din Please i begging you Ka barni yanzu siyayyar zeey na kasa zuwa ka tuna lokacin auren mu mene ba tai min ba , dan yanzu zata sake aure sai kuma ni na kasa yi mata abin da tai min bana bukatar kudi kawai so nake na taya ta zaɓen kayan dakin ta da wasu abubuwan tun da daga can har Katar za mu.., limshe idanuwan'sa yayi ya dauki tissue ya goge bakin sa yace '' zan duba na gani.., riƙe hannunsa tayi tace '' kai ma fa tafiya za kayi ka temaka ka barni.., hannunta ya riƙe yace '' school fa ya zakiyi da karatun ki wa zai zauna a gidan..?, gumi ne ya karyo mata ta san shi sarai da dabi'ar son tayi karatu tace '' am yanzu muna first semester ne so karatun be kankama ba kafin na dawo komai ya kankama gida kuma ga Najlah nan me zai faru da ita da ace tayi aure da yanzu tana gidan mijin ta .., kura mata ido yayi ya hura mata iska da sauri ta limshe idanuwanta. murmushi yayi yace '' zan shiga study room zanyi aiki ki huta lafiya.., binsa tayi da kallo ranta duk ba dad'i kullum addu'a ta Allah ya saka ya barta ta tafi wannan tafiyar tashi tayi ta shiga dakin ta ta murza key dauko waya tayi a cikin aljihunta ta lalubo wata number ta yi dialling ringing ɗaya kai picking call din cikin sauri tace '' ka bani lokaci mana har yanzu yaƙi amincewa kasan ba zan iya tafiya wank guri ba , batare da izinin sa ba amma ka kasa fahimta, ta Jawad yana da kafiya da tsayawa akan ra'ayi ɗaya na lura duk irin kokarin da nake yi baka gani kullum da kai nake kwana nake tashi idan ka faɗi haka bakai min adalci ba , mutumin nan yanzu abubuwan da take yimin kamar ya fara zargina dole mu bi komai a sannu kar kwabar mu tayi ruwa.., shiru tayi tana saurarawa domin jin me zai ce kit taji ya kashe wayar ciro wayar tayi tana jan ƙaramin tsaki buɗe dakin tayi ta fito bata gansa a parlour ba zama tayi akan kujera tana girgiza kafa ranta duk a ɓace idan jawad ya hanata tafiyar nan tabbas ya gama da ita ga wannan kaddarar da tazo mata kan'ta gaba ki ɗaya , ya kulle tama rasa ma za tace da sauri wata shawara ta fado mata zuciya duk yadda akai ummin jawad bata san da zuwan Najlah ba. da sauri ta dauki wayar ta , ta samo laluban number ummi bugu ɗaya ummin jawad ta ɗauka jawaher tace '' Assalamu alaiki ummi barka da yamma ya su taufiq.., cikin isa da nuna ƙatsai ta ummi tace '' wassalamu alaiki barka dai suna lafiya da fatan kuna lafiya.., gyara zama tayi tace '' eh wallahi ummi lafiya qalau alhamdulilah.., Ummi tace '' masha Allah haka ake so ya kaɗaici kuma.., wani murmushin jin dad'i tayi domin an tabo mata inda yake mata kaikayi tace '' yama dawo ɗazu abin da ya sakani dad'i ma tare suka dawo da Najlah za tayi karatu anan.., da sauri ta tashi hadiman da suke mata tausa a kafa sai da suka tsorata saboda tashin da tayi na baza ta da kuma hanzarin ta tamkar ta ga wani abin ƙi cikin tantance zancen jawaher tace '' wacce NAJLAH..? yaushe JAWAD ya dawo ƙasar nan ban sani ba kuma be sanar dani ba..?, murmushin jin dad'i tayi tace '' Najlah Hajiya Farida ɗazu ya dawo be dade da dawowa ba ina ga sai ya nutsu zai kira ki ya sanar da ke..., cikin tsananin ɓacin rai tace '' yanzu haka tana cikin gidan ki lallai yaro be san wuta ba sai ya taka , da zaki ce kina ga sai ya nutsu wannan wanne irin kinibibi ne tafiya yayi fa YOLA daga dawowar sa ina JALINGO be sanar dani ba balle ya zo Nagode da sanar da ni da ki kayi sai an jima..., kit ta kashe wayar ta wani tsalle dad'i jawaher tayi tare da rawa wannan game din tasan ita ce za tayo winner wata kila zuwa gobe ta yardar da kwallon mangaro ta huta da guɗa ummin JAWAD lafiya ce. Wannan boom ɗin tasan gaba ki ɗaya ahalin alkali mudassir ɗan muzu da su zai tashi sai ummi ta ya mutsa hazo zama tayi tana cewa duk mutumin da zai hanani kwanciyar hankali a gidan miji na to tabbas ina da boom me tashin rayuwar mutum gayawa jini na wuce. wata dariya ce ta zo mata , ta mugunta lokacin da taga NAJLAH da plate ta fito daga kitchen uhmm babu a house ta faɗi da dan karfi domin NAJLAH ta ji ta. sarai ta ji furucin ta sai dai bama ta nuna tasan me take faɗi ba. wuce ta tayi ta koma dakin ta.
Chapter 3 · 0% Book details