← Book details Karuwan Cikin Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 15

Sashe 5

Karuwan Cikin Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunda ya shiga yake aikin office da ya tarar mai kwana biyu da yake yayi busy ba ya ƙasar sai yanzu ya samu yake rage wa kan'sa ne ya dauki chaji gaba ki ɗaya wayoyinsa ya kashe su, yana bukatar hutu da kaɗaici domin yayi aikin sa ba kuskure.. ji yayi an yi knocking kofar sa yasan wace dafa goshin sa yayi yace '' abu ɗe yake.., jin haka da sauri ta murɗa handle din ta shigo zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun da suke study room din tace '' ummi ce ta bugo duk layin ka a kashe yake ce maka.., ajiyar zuciya ya sauke shi ya amshi wayar tare da karawa a kunne yace '' Assalamu alaiki ummi barka da yamma..., JAWAD riƙe gaisuwar ka bana so bana so wallahi ai baka mai dani mutum ba wayancan Mutanen da na raba ka dasu sune mutane har ka iya zuwa yola baka zo gurina ba ina matsayin mahaifiyar ka , ka kyauta dole suyi min abin da suka ga dama su nuna min ban isa da kai ba sai su, suka isa dakai ban ce maka ba , na rabaka da duk ahalin ɗan buzu musamman ma Hajiya farida bani da wata wacce na tsana sama da ita dan haka kai gaggawar mai da mata da yar ta , wallahi wallahi wallahi JAWAD idan ka sake kayi abin da na ke zargi to bani ba kai ban da iskanci tun wuri ka rabu da ita mana to wallahi alkali mudassir ya taro abin da yafi karfin sa domin duk abin da yake faruwa ina sane wato za su fage da guzuma su harbi karsana ko to sunci karya bakai ba jinin Hajiya farida da Alhaji Sharif.., kifa kansa yayi akan table rasa ina zai saka kan'sa yayi anya kuwa Mahaifiyarsa, tana tsoron Ubangijin'ta me wannan baiwar Allah tayi mata tun da ya taso be san dadin uwa ba , watan sa takwas ita da mahaifinsa suka rubu dan haka bata tafi dashi ba ta bar shi ba ruwanta ya mutu ko yayi rai sai bayan ya kammala digree dinsa na farko yana shirin tafiya egypt ƙaro karatu ta bayyana be rayu da ita ba , tun daga bayannara ta zuwa yanzu kullum cikin saka shi take a damuwa da farko da ta bayyana yaji dadi be taɓa zaton ba hajiya ce mahaifiyar sa ba suma haka su NAJLAH sai a lokacin suka san me yake faruwa ajiyar zuciya ya sauke yace '' ummi insha'Allahu zan kiyaye duk abin da kika shinfiɗa min wallahi bawai haka kurum naje yola ba a'a na can na sauka gobe nake so na zo mu gaisa.., kashe wayar tayi saboda ai ta riga da ta isar da sakon'ta miƙa wa jawaher yayi, amsa tayi tace '' amma sweet lafiya ko ba wani abu ne ya faru ba..?, bece mata komai ba ya nuna mata hanyar fita sum sum ta fice tana danne dariyar ta , ci gaba yayi da aikin sa bayan ya gama ya tashi ya fito ba kowa a parlour kai tsaye bedroom din sa ya nufa tana kwance tana waya tana ganin sa ta katsai wayar tace '' badai la gama ba ? Amma kuwa idan haka ne kayi saurin gamawa..., zama yayi bakin gado yace '' eh na gama kije kice NAJLAH ta haɗa min coffee.., tashi tayi tana cewa to an gama oga kiss tayi mai a kumatu tace Allah ya bar min kai ya makantar da idon yan mata akan ka..., dan murmushi yayi mata yace '' amin..., da sauri ta dawo ta zauna riƙe hannun sa tayi tace '' idan har hasashena ya faɗa min gaskiya kamar akwai abin da yake damun ka amma kaki sanar min idan ma tafiyar ce baka so nayi sai na fasa shikkenan magana ta ƙare amma wannan haɗa ran ban saba da shi ba kullum na fiso mu ɗore cikin so da kaunar juna da fahimtar juna shekara biyu da auren mu bamu taɓa samin matsala ba kar yanzu akan tafiyar nan mu samu beb idan haka ne ni wallahi na hakura ma da nayi tunani ko wani abu ummi ta faɗa maka da na kuma ƙara wani tunanin sa naga ita uwa ce me son farin cikin ɗan ta ba za ta taɓa faɗa maka abin da zai saka lokaci kali lan ba ka shiga cikin damuwa , ina kyautata zaton nice sanadin komai, saukowa tayi ƙasa ta damƙe hannuwansa idanuwan'ta ya taru da kwalla fal sakin hannuwansa tayi ta haɗe hannuwanta biyu alamar ban hakuri ta ci gaba da cewa. Dan Allah ka yafe min mijina bana so ka kwana kana fushi da ni bana so na zama sillar bakin cikin ka , ka dawo daga tafiya kamata yayi na faran ta maka be kama ta na bakan ta maka ba... Kwantar da kan'ta tayi yasha kan'ta yayi yayin da wani sanyi yake ratsa zuciyar'sa hakika annabi yayi gaskiya da yace idan namiji ya dace da mace ta gari to kamar ya samu rabin addini ne yana kaunar jawaher yana son ta fiye da son da yake wa kan'sa baya iya kallon ko wacce mace a matsayin mace , Hakika jawaher rabin jikin'sa ce.. cikin daddaɗan sauti yace '' wallahi baki yi min komai ba idan ma kwai na yafe miki sweet stress ne yayi min yawa ina bukatar hutu amma ni baki min komai ba jeki, ki faɗa mata , ta haɗa min kafin na fito daga wanka.. Hmmm ku biyoni dan jin wanne darasi wannan labarin ya kunsa # KURUWAN CIKIN GIDA EPISODE 3 Ɗago idanuwan'ta tayi cike tab da hawaye share mata yayi yace '' bana so na ganki cikin damuwa.., Murmushi tayi ta tashi, ta karasa share hawayen ta , fita kai tsaye bedroom din NAJLAH ta shiga turawa tayi ba tare da tayi sallama ba , tana kwance wayar ta na hannun ta taɓe baki tayi ta kalle tace '' sweet yace ki haɗa mai coffee.., ajiye wayar hannun ta , tayi bata ce mata komai ba ta miƙe ganin haka ita mata fita, tana shiga tarar dashi tayi ya shiga wanka zama tayi tana charting da wayar ta fitowa yayi yana tsane jikin sa batare da ya kalli inda take ba yace '' kin faɗa mata..?, ajiye wayar ta , tayi tace '' na faɗa mata amma bata ce min komai ba bama ta kalli inda nake ba balle nasan taji me na faɗa.., ajiye towel din hannun sa yayi ya fita a hankali yake saukowa cikin nutsuwa kamar ba sauri yake ba yana sauka kai tsaye bedroom din NAJLAH ya nufa murɗa handle din kofar yayi da sauri ta dago tare da ja da baya tun da take dashi a rayuwar'ta bata , taɓa ganin sa acikin makamancin wannan yanayi ba ko exercise zai yi da dogon wando yake tafiya balle wannan daga shi sai towel a ɗaure a kugu lallai auren da yaya yayi ya mai dashi wani iri, ƙasa tayi da kan'ta tace '' yanzu zan kawo maka.., okay ita da kikai mata shiru kenan raina ta kika yi..?, ya jefo mata wannan tambayar bata , taɓa tunanin jin wata magana makamancin haka abakin sa ba. turi ƙaramin bakin ta , tayi tace '' nace mata to.., karya kenan take miki..? da sauri ta ɗago kwallah har ta fara taruwa a idanuwanta ja da baya tayi tana sauke ajiyar zuciya ganin ya matso kusa da ita tamkar zai shige jikin ta da sauri ta, tashi tace '' bara naje na duba kar ya gaji da tafasa.., ratsawa tayi zata wuce riƙe hannunta yayi da sauri ta juyo anya kuwa yaya Jawad lafiyar sa qalau ko kallon ta ya ke kamar jawaher ta shiga uku da sauri ta saka ɗaya hannun nata , zata cire hannunta da ya riƙe wani irin shock yaji ajikin sa da sauri ya cika mata hannu kasa koda motsi yayi dakyar ya iya ɗaga kafar sa ina yaga abin ba zai yiwu ba hannun sa ya saka ya kashe switch din fitilar dakin a gigice ta ɗago da kan'ta sai dai kafin ta gama tantance wanne yanayi take ciki ya hanka ɗata kan gadon ta yunkurawa tayi zata fita aguje amma ina be bata damar haka ba , domin ya danne ta kuka ta sakar mai , sosai ta shiga kici niyar kwace kanta amma ina ya ƙi bata damar haka. ji tayi an buga mata pillowcase agigice ta , tashi tana zabga uban gumi ganin shine gaban tane ya faɗi tunowa da tayi da abin da ta gani a cikin mafarkin ta , da sauri ta ja baya gaban ta na faɗuwa cikin haɗe girar sama da ta ƙasa yace '' NAJLAH sannun ki na saka ki aiki shine , kika zo kika kwanta har kikai bacci daman ai tace baki bata amsa ba .., cikin sanyin murya tace '' nace mata to wallahi ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba na ɗora akan gas Allah ya saka me kone ba bara na tafi na duba kafin yace wani abu ta fita cikin sauri, ko ina na jikin ta rawa yake daman ya lafiyar kura balle tai hauka, tana tafiya a hankali jikin ta na motsawa balle yanzu da ta fita da sauri zama yayi ya ɗora ƙafafuwan'sa ɗaya kan ɗaya ciro wayar sa yayi daga aljihun kayan baccin da ya saka farare tas dasu fara operating din ta yayi har ta kawo ta ajiye mai be ɗago ba. cikin daddaɗar murya me dadin sauraro tace '' yaya gashi nan na kawo maka a ina zan ajiye maka..?, akaina zaki ajiye.. da sauri ta ɗago ganin ita yake kallo sai tai sauri ta ajiye tare da matsawa daga gurin zama tayi agefe tana wasa da gefen mayafin'ta so take yi ya dauki kayan sa ya fita. wayar tace tayi ringing da sauri ya kalli gefen sa BLOOD LINE sunan da yaga tayi saving number din dashi ajiye coffee ɗin hannunsa yayi ya dauki wayar tata ya soma juyawa nan ɗanan ɓacin rai ya bayyana afuskar sa kallon ta yayi yace '' wanne wannan...?, bakin ta na rawa tace '' yaya muneef ne.., ɗaga kan'sa yayi ya kalli agogo ƙarfe goma saura minti
Chapter 5 · 0% Book details