← Book details Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 28

Chapter 09: The unfinished rescue

Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

Nanameera, YOTA/023.


Tun da ya fito daga ɗakin yake bin su da kallo, he just can't believe abin da idanunsa ke gani, how? Ɗan tsaki ya yi sai kuma ya nufi hanyar upstairs na hotel ɗin ba tare da ya sake bi ta kansu ba.


Tsaye Salma ta yi bakin ƙofar ɗakin ta kasa shiga ciki, juyowa ya yi yana kallonta ganin irin kallon da take wa ɗakin ya ce


“Shigo mana”


Girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce

“A'a ka barni a nan kawai”


Dafe kansa ya yi ganin zata wahalar dashi ya sa ya ce“To ya za'a yi ki tsaya a nan har na baki kuɗi? Ki shigo ko baki yarda dani ba?” shiru ta yi na wasu mintuna kafin ta shigo ɗakin tana tafiya a sanyaye. Gefen gado ya nuna mata da hannu ya ce


“Zauna ina zuwa”


Kallon wajen ta yi amma bata zauna ba, ya juya ya shige toilet ya barta nan tsaye. Above 10mins kafin ya fito jikinsa sanye da bathrobe, daga gani wanka ya yi. Kallo ɗaya Salma ta yi masa ta ɗauke idanunta, haka kawai ta ji bata son zaman ɗakin, ta juya ta nufi hanyar fita ba tare da ta ce masa komai ba, cikin hanzari ya bi bayanta yana cewa


“A'a cutie lafiya? Me aka yi miki?”


Girgiza kanta ta yi ta ce


“Tafiya zan yi ni”


Shiru Tareek ya yi can kuma ya ce

“But i promised u ko, nace zan biya miki kuɗin aikin Abbanki”


“To ni bana so, ba zan iya ci gaba da zama ina ganinka haka ba, it's totally haram, kai ba muharramina bane, ni tafiya zan yi, kawai ka bani kuɗin”


Salma ta ƙare maganar hawaye na kawowa idanunta, daga sama har ƙasa ya kalleta kafin ya ce


“Then ki zauna na saka kaya, sai mu je na cire kuɗin a bank na baki, kin ga bani da cash”


Tura baki ta yi kafin ta nemi waje nan kan tiles ta zauna tana cewa


“Zan jiraka a nan”


Kallonta kawai ya yi da alama tana da matuƙar wayo, bai sake cewa komai ba ya ƙarasa wajen dressing mirror ya fara shiryawa, yana gamawa ya sanya singlet da 3-quater ya dawo inda take zaune, tashi tsaye ta yi tana bin sa da kallo kafin ta sanya hannayenta duk biyun ta rufe fuskarta tana cewa


“Ni ka rufe jikinka babu kyau, kuma...”


Bata yi aune ba taji ya rungumeta gaba ɗayanta a ƙirjinsa, a matuƙar razane Salma ta buɗe idanu ta fara ƙoƙarin kwace kanta amma ya ƙi sakinta. Duk irin kokawar da ta dinga yi ƙin rabuwa da ita ya yi, kasancewar ba karfinsu ɗaya ba, kuka ta sanya ta sakar masa cizo a gefen hannu, zafi da kiɗimar cizon ya sanya ya saketa yana yarfe hannunsa. Da gudu ta yi waje kamar mahaukaciya. Ta kusa kai wa ƙarshen ɗakunan ta ji an janyota, wani razanannen ihu ta saki ya yi saurin toshe mata baki, ƙoƙarin kwace kanta ta shiga yi amma sam ya ƙi bata dama, sai a sannan ta gane wancan mutumin ba ma riƙeta ya yi ba, dan wannan kwakwaran motsi ta gagara yi, ga ƙamshin turarensa daya gama cikata, da kyar take jan numfashinta. Suna tsaye a wajen Tareek ya ƙaraso wajen yana kallonsu, a fusace ya ce


“Kai malam uban me ka ke da yarinyar nan? Ko baka san ni na kawota nan ba?”


Bata san sanda ta sake ƙamkameshi ba, tana ɓoye fuskarta a faffaɗan ƙirjinsa, tsananin tsoro ya riga da ya gama cikata. Janyeta Zayyad ya yi daga jikinsa ya juya ya kalli mutumin dake maganar. Kallo ɗaya Tareek ya masa ya juya ya bar wajen dan ya san shi farin sani, duk ba ba lallai bane shi Zayyad ɗin ya gane shi, amma duk wanda ke shiga transcorp ya san Zayyad.


Juyowa ya yi yana kallon Salma wadda ta sake riƙe gefen rigarsa har sannan tana shassheƙar kuka, tsaki ya yi ya fizge rigarsa yana harararta. A hankali ta ɗago idanunta wanda suka kumbura ta kalleshi, ɗan ja da baya ta yi dan ta gane fuskarsa, shi ko Zayyad gaba ya yi ya bar ta tsaye a wajen. Kalle kalle Salma ta shiga yi ganin babu wani ɗaki wanda yake a buɗe ya sanya ta bi bayan Zayyad ɗin, a ƙofar room 404 taga ya tsaya, ya saka key ya buɗe ƙofar ya shiga, tana ganin haka itama ta shige da saurin tana sauke ajiyar zuciya. Tsaye ta sameshi tsakiyar luxury room ɗin, ko ina tsaf yake sai sassanyan ƙamshi ne ke tashi wanda ke haɗewa da Ac dake kunne yana bada wani irin amintaccen yanayi. Ɗan ja da baya tayi ganinsa a gabanta dan bata san sanda ya ƙaraso ba, Yana mata wani shegen kallo ya ce


“Munafuka, daman daga ganinki na san ke ba ƙaramar yar iska ba ce”


Da sauri Salma ta kalleshi, gani ta yi ita yake kallo har sannan ransa a haɗe fuskarsa babu walwala, tura baki ta yi tana ɗauke kanta ta ce


“Ni ba yar iska ba ce wallahi, kar ka sake ce min haka”


Wani irin shegen kallo Zayyad ya yi mata kafin ya ce


“Oh karuwa ce kenan? Tun da har kina iya baro Nassarawa ki biyo namiji Abuja, daman kin fi ƙarfin yar iska”


Tuni hawaye suka wanke fuskarta, ta sanya hannunta tana sharewa ta ce


“Ni ba karuwa ba ce wallahi, Ni kuma ba yar iska ba ce, ka daina zargina da abin da ban aikata ba, Babu kyau hakan wallahi, kuma Allah sai ya sakamin”


A fusace ya ce


“Yimin shiru a nan, idan ba karuwa ba me ki ke yi a hotel? Idan ba iyayenki basu baki tarbiyya ba me za ki zo yi a nan? Wane ma ya kawo ki Abujan? Nawa ya biya ki?”


Zama dirshan Salma ta yi a ƙasa ta sake rushewa da wani sabon kukan, har da birgima a ƙasa. Da mamaki Zayyad ke Kallonta ganin yanda take ihu tamkar ya yi mata wani abun, sunkuyawa ya yi daidai fuskarta ya ce


“Da ban yi miki komai ba shine za ki zauna kina min kuka?”


“Ni ba yar iska ba ce wlh, kuma ni ba karuwa ba ce, sai dai idan kai ne ɗan iskan, to mene kai ma ya kawo ka hotel ɗin da daddare!”


Ta ƙare maganar ta ci gaba da kukanta, duk yanda ta bawa Zayyad dariya ƙin nunawa ya yi, in a serious tone ya ce


“Ai ko ni ɗan iska ne cikakke ma, kuma yanzu zan nuna miki”


Daga haka ya ɗagota yana ƙoƙarin cire hijabin dake jikinta, wani irin ihu Salma ta saki, jikinta ya fara rawa, tana girgiza kanta ta ce


“Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan sake ba, da wasa nake maka, kai ba ɗan iska ba ne”


Ko saurarenta Zayyad bai yi ba ya ci gaba da rabata da hijabin jikinta, sanda ya samu damar cirewa kusan shiɗewa Salma ta yi, domin tun da aka haifeta wani namiji bai taɓa ganinta irin haka ba. Doguwar riga yadi ce a jikinta, kanta babu dankwali, kitsonta wanda ya sakko har kafaɗunta sune suka zame mata kamar ɗankwali. Runtse idanunta ta yi tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, Zayyad daya mutu wa kallon gashin kanta ya ma manta da abin da yake shirin yi, gyara zamansa ya yi ya ci gaba da kallonta. Jin ya tsaya ya sanya Salma ɗago kanta tana kallonsa da idanunta da suka kumbura, ganin bai ce komai ba ya sanya ta ɗauki hijabinta ta mayar ta mike tsaye har sannan tana shassheƙar kuka ta yi hanyar fita daga ɗakin. Babu yanda bata yi da kofar ba amma ta ƙi buɗewa ta juyo da niyyar yi masa magana amma ta ga wayam babu shi babu alamunsa. Gajiya ta yi da ƙoƙarin buɗe ƙofar ta zauna a wajen ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta tana ci gaba da koke kokenta. Sai bayan one hour sannan ya dawo parlon, ya ƙarasa bakin ƙofar yana kallonta, ya ɗauki wasu sakanni a a wajen kafin ya ɗago kanta, ganin bacci take yi ya sanya bai tasheta ba, ya ɗauketa ya kai har kan gadon ɗakin ya kwantar da ita, Ac ɗakin ya kashe sannan ya rufa mata duvet ya kashe hasken ɗakin ya fito parlon ya yi zamansa yana danna wayarsa.


Maitama, Abuja.


Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo ɗakin, zaune ya hangeta kan sofa tana sanye da riga da wando ta ɗaure kanta da jersey veil, idanunta maƙale kan wayarta tana hira da wata friend ɗinta. Kallo ɗaya ta yi masa ta mayar da kanta kan wayarta ta ci gaba da dannawa, gefenta Faruk ya zauna yana murmushi ya kalleta ya ce


“Morning love”


Ɗago dara daran idanunta ta yi ta zuba masa, a sanyaye ta ce“Morning” Faruk ya sake cewa


“Kin tashi lafiya?”


“Alhamdulilah”


Nimrah replied. Jinjina kai ya yi, parlon ya ɗauki shiru na wasu mintuna kowa da abin da zuciyarsa ke saƙawa, can kuma ya sake kallonta ya ce


“Idan an jima zamu je gida wajen Mama”


Ajiye wayar hannunta ta yi kan cinyarta ta ce


“Did something happens?”


Girgiza kai Farok ya yi ya ce

“Nothin, kawai zamu je mu gaisar da ita ne”

Ɗan taɓe baki ta yi kafin ta ce

“Allah ya kai mu”


“Ameen” Faruk ya ce. Ɗaukan wayarta ta yi ta miƙe tana ƙoƙarin barin parlon ta ce


“Breakfast ɗin ka yana dinning”


Murmushi ya yi ya ce“Thank u love”


Nimra bata ce masa komai ba ta buɗe ƙofa ta fita.


****

“Yanzu General saboda Nayla ta je gidan Adda shi ne abin laifi? Me za'a yi mata a gidan?” General Idris dake zaune kan sofa ya kalleta ya ce


“Kin ji na ce miki za'a mata wani abun? Kawai na ce Nayla ta dawo gida, bana son ta sake kwana a Nassarawa, that's it”


Tashi Momma ta yi bata ce komai ba ta fice daga parlon kamar zata tashi sama, Daddy ya bita da idanu kafin ya taɓe baki ya maida kansa gurin newspaper ɗin dake gabansa. Kai tsaye ɗakinta ta nufa, tana zuwa ta ɗauki wayarta dake ajiye kan gado ta zauna tana kallonta, ta ina zata fara kiran Mami ta ce a dawo da Nayla? Me yasa General yake haka akan yayansa? Tsaki Mommah ta yi kafin ta yi dialing numbern Zayyad. Ringing biyu ta yi kafin ya ɗauka Mommah ta ce


“Zayyad kana ina ne?”


Daga ɗaya bangaren Zayyad ya ce


“Wani abu ya faru Mommah?”


“Just answer my questions Malam”


Mommah ta yi maganar a ɗan fusace. Numfasawa ya yi yana kallon Salma dake zaune can ƙarshen gado ta cure jikinta waje guda ya ce


“Na ɗan fita ne, but yanzu zan dawo gida”


Shiru Mommah ta yi can kuma ta ce


“Kayi sauri ina jiranka to”

Okay ya ce sannan ya kashe wayar. Ya tashi tsaye yana ƙoƙarin sanya agogonsa ya ce


“Idan kin gama sai ki tashi ki koma gida”


A sanyaye ta miƙe tsaye, ta gyara hijabinta tana ci gaba da kallonsa. Car key ɗinsa ya ɗauka ya nufi hanyar waye ta bi bayansa. Sai da ya tsaya a reception ya basu key ɗin ɗakin sannan ya yi waje, kai tsaye parking space ya nufa, yana zuwa ya buɗe motar ya shiga, tsayawa ta yi a wajen tana kallonsa har ya gama warming ɗin motar. Dan tsaki ya yi ya sauke glasses yana kallonta ya ce


“Idan baki shirya tafiya ba sai ki ci gaba da tsaiwa anan”


A hankali ta buɗe backseat ta shiga ta yi zamanta, ta mirror ya kalleta ya ce


“Kin sakko daga nan ko sai ranki ya ɓaci, did I look like ur driver?” kallonsa kawai Salma ta yi sai kuma ta buɗe motar ta fito ta dawo front seat ta zauna tana tura baki. Bai sake ce mata komai ba ya yi reverse ya bar transcorp ɗin, Sun fara nisa ya yi parking daidai wani keystone bank ya sauka ya shiga ciki, Ita dai Salma sai bin sa take da kallo har ya ɓacewa ganinta. Sai bayan 15mins sannan ya fito daga bankin ya dawo motar da wata yar jaka, a back seat ya ajiye sannan ya shiga motar ya ɗauki hanyar Mararaba.


Ƙarfe 10:23am ya yi parking a bakin titin Kabayi, ya kalleta ganin yanda take kallon hanyar, hannunsa ya sanya ya ɗauko jakar daya shigo da ita ya miƙa mata, amsa ta yi tana kallon jakar ya ce


“here it's 1m naira, sai ku biya kuɗin aikin nasa, Allah ya ƙara sauƙi, but you have to be careful, not all the glitters are gold”


Wasu hanwaye ne suka fara sintiri kan fuskarta wanda ta kasa tantance na farin ciki ne ko akasin haka, ta kalleshi muryarta na rawa ta ce


“Na.. Nagode sosai, Allah ya biya maka buƙatunka, yanda ka taimakeni kai ma Allah ya taimaki rayuwarka, Nagode sosai Yaya Yad”


Taɓe baki Zayyad ya yi kafin ya ce


“Yaushe har ki ka yi hankalin da ki ka ce min Yaya? I'm not ur Yaya, saukar min a mota”


Ɗan murmushi Salma ta yi har sai da beauty point ɗinta suka loma, ta buɗe motar ta sauka tana ɗaga masa hannu, samun kansa ya yi shima da ɗaga mata hannun ta yi hanyar cikin Kabayi tana tafe tana waiwayensa, sai da ya daina hangota sannan ya ja motar, ya so zuwa wajen Mami sai kuma ya fasa tunawa da kiran Mommah kawai ya nufi hanyar Abuja.


Sai da tayi nisa sannan ta tuna da Abbanta na asibiti, kawai ta yanke shawarar ƙarasawa gida ta sauya kaya tun da ta riga da tayi wanka, tun da ta fara shiga layinsu mutane ke kallonta, ta sunkuyar da kanta dan babu abin da ta tsana a rayuwarta sama da kallo, a ƙofae gidansu ta hangi mutane sun ɗan taru, kuma duk maza, a sanyaye ta ƙarasa ƙofar gidan bata cewa kowa komai ba ta shige gidan gabanta na faɗuwa. Turus tayi a tsakar gidan ganin Ummarta zaune gefen mutum wanda aka rufe shi da likkafani kamar gawa sai rusa kuka take, Hajiya Jinjin dake gefenta sai rarashinta take. Baba Asabe ce ta hangota ta ce

“Ga ma yar tasa nan ai”

Duk suka ɗago suka kalleta, Umma ta taso ta ƙaraso wajen ta riƙe hannunta kuka na kokarin kwace mata ta ce


“Ina ki ka je Salama? Salama ina ki ka je Babanki ya dinga nemanki? Salama daga ina ki ke?”


Kasa bata amsa Salma ta yi sai ma zame hannunta daga nata da tayi, ta nufi inda aka kwantar da gawar, zubewa tayi gaban gawar hannunta na rawa ta shiga buɗe likkafanin, zabura ta yi ta saki likkafanin tana yin baya. Ƙarasowa Umma ta yi ta dafata tana kuka ta ce


“Kin gani ko Salama, Abbanki ya tafi ya bar mu, ya mutu Salama, ba zamu sake ganinsa ba”


Girgiza kai Salma ta shiga yi, ta ma kasa kuka sai ajiyar zuciya take saukewa. Tana kallon gawar babanta ta ce


“Meyasa Abba? Ba nace maka ka jirani ba? Ba nace zan samo kuɗin da za'a maka aikin ba? Me yasa za ka yi fushi? Me yasa zaka tafi ka bar ni Abba? Kai ma baka sona? Abba dan Allah ka tashi, na samo kuɗin da za'a maka aikin fa, na dawo dasu Abba. Karka mutu ka barni, dan Allah Abba, Ammina ma ta tafi shine kai ma zaka tafi ka barni? Duk baku sona daman? Ka yimin magana Abba! Ka tashi Abba! Dan girman Allah Abba ka tashi, na haƙura da makarantar fa Abba! Ka tashi na ganka, ka buɗe idanunka”


Salma ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, ta ɗora kanta kan gawar Abbanta tana jijjigashi, ganin hakan ya sanya mutane aka riƙeta, masu ɗaukar gawa suka shigo dan daman ita ake jira ta ganshi, Salma na ganin za'a fita da Abbanta ta fincike jikinta ta tashi da gudu ta bisu, tana kai wa soro ta yanke jiki ta faɗi a wajen Sumammiya.


# HCD
# Nanameera
08106608363.


https://chat.whatsapp.com/GSEDyyyzuMm3woohSiin9W?mode=ac_t


HASKEN CIKIN DUHU
Chapter 9 · 0% Book details