Chapter 13: Nowhere Feels Like Home
Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Nanameera, YOTA/023.
Kusan sati ɗaya kenan da tafiyar Umma Rahmatu kuma har yanzu bata dawo ba, Gabaɗaya Salma ba jin daɗin zaman gidan take ba, Koda yaushe sai dai ta zauna ita kaɗai tana tunane-tunane. Wasu lokutan kuma su zauna tare da Khadijah ɗiyar Hajiya Jinjin tana bata labarin irin rayuwar da ake a Abuja. Yau ma kamar kullum suna zaune cikin ɗakin Khadijah gefen katifa tana ɓarar gyaɗa ta kalli Salman ta ce
“Anjima zan bar gida fa, Ko za ki rakani?”
Girgiza kai Salma ta yi a sanyaye ta ce“A'a ina jiran Ummana ta dawo mu koma gida, Ina son na ci gaba da zuwa makaranta” Taɓe baki Khadijah ta yi ta ce“Ikon Allah, Ai sai ki yi ta zama a nan ke kaɗai, Ko ki samu Ummana ta samar miki wani alhajin yanda ki ke farar nan kuɗi zasu dinga baki ba kaɗan ba wallahi” Shiru Salma ta yi maganganun Abbanta suka shiga dawo mata ɗaya bayan ɗaya, Ta sunkuyar da kanta kawai. Tashi Khadeejah ta yi dan lokacin guraren la'asar ne ta fice daga ɗakin, A tsakar gida ta samu Hajiya Jinjin tana sharar, Ta kalleta ta ce“Umma wai yaushe Ummar Salma zata dawo?” Ajiye tsintsiyar Hajiya Jinjin ta yi ta ce“Mene naki na son sani?” Girgiza kai Khadijah ta yi ta ce“Babu komai fa, Kawai dai inason sani ne, Na ce mata ta zo mu tafi Abuja tare wai ba zata je ba ita Ummar ta take jira” Jin jina kai Hajiya ta yi kafin ta ɗaga labulen ɗakin tana cewa“Salma, Salma” Fitowa Salma ta yi tana kallonta ta ce“Umma gani”
“Ki shirya ku tafi tare da Khadijah mana”
Zaro idanu Salma ta yi, Ganin ta yi shiru yasa Hajiya ta ce“Ko baki ji ba?” Sunkuyar da kanta ta yi tana cewa“A'a Hajiya ni bana son zuwa wallahi, Ummana zan jira” Taɓe baki Hajiya Jinjin ta yi ta ce“Tun da ta ce miki dawowa zata yi?” Tura baki Salma ta yi bata ce komai ba. Khadijah da take son Salman ta bita ta kalleta ta ce“Da zaman da zaki yi ke ɗaya ba Gara ki bini ba Salma?” Maƙe kafaɗa Salma ta sake yi ta ce“Ni A'a” Ta yi maganar a shagwaɓe. Shiru Khadijah ta yi, Hajiya Jinjin ta ce“Ke shige ki yi wanka ki zo ki tafi ki bar wannan” To kawai Khadijah ta ce ta ƙarasa inda bokiti ke ajiye ta ɗiba ruwa ta yi hanyar banɗaki. Harararta Hajiya Jinjin ta yi ta ce“Sai ki nemi waje ki dawwama a nan, Kuma sai ki samu wanda zai dinga ciyar dake, Tun da nasan kina da labarin ubanki bai bar miki komai ba!” Shiru Salma ta yi har sannan kanta yana sunkuye, Hajiya Jinjin ta shige ɗaki ta barta nan tsaye. A hankali ta sanya hannunta tana goge hawayen da suka zubo kan kuncinta. Above 10mins tana tsaye a wajen har Khadijah ta fito daga wanka, Ta kalleta bata ce mata komai ba ta shige ɗaki. Hanyar waje ta nufa dan daman akwai hijabin Khadijah jikinta, Kai tsaye kuma ta nufi cikin Kabayi in da zai sadata da gidansu.
Asokoro, Abuja.
Murmushi Momma ta yi tana kallonsa ta ce“Yanzu yaushe zaka je Companyn? Ko kai fa Zayyad, Ka amshi girman daya zo maka ka daina shashanci dan Allah” Langwaɓar da kansa ya yi yana bayan ya yi sipping tea ɗin dake hannunsa ya ce“Tom Mommah, Na zama serious yanzu shikenan kin ji daɗi?” Gyaɗa masa kai ta yi tana kallonsa fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce“Irin daɗin dana ji ba zai faɗu ba Muhammadu, Kai dai Allah ya yi maka Albarka” Murmushi ya yi ya ce“Ameen Mommah na”
“Yanzu when zaku haɗu da Ahmad ɗin?” Tashi tsaye ya yi kafin ya ce“Ai yanzu ma zan je Mararaban in sha Allah, Sai mu yi maganar acan” Mommah ta ce“Yawwa to gara hakan, Ka gaida min da Mami ka ce ina nan zan zo mu yi maganar”
“Maganar mene Mommah?” Ya faɗa yana ɗaga mata gira, Harararsa ta yi tana murmushi ta ce“Gulma to ba zaka ji ba, Tafiyarka” Langwaɓar da kansa yayi yace“Idan na je na tambayi Mami na san ita zata faɗa min” Jin jina kai Mommah ta yi ta ce“Ta faɗa makan kun fi kusa” Fita ya yi daga ɗakin yana murmushi. Ta sauke ajiyar zuciya tana sake godewa Allah, a kwanakin nan Zayyad ya nutsu sosai, Ko fitar dare baya yi, da wuri yake kwanciyarsa daya tashi kuma ya tafi asibiti.
A main parlon ya tarar da Daddy da Mommy suna magana, Tana ganinsa ta saki murmushi tana faɗin “Babban mutum an fito?” Gyada mata kai ya yi, Daddy ya ce“Ina kuma zaka je?” Murmushi Zayyad ya yi ya ce“Zamu yi magana da Ahmad ne, Ba daɗewa zan yi ba Dad” Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Ya maganar Jidda kana zuwa wajenta kuwa?” kwaɓe fuska ya yi ya ce“But Dad me zan je nayi? Tana kirana a waya ina amsawa, So kwana biyu kuma I'm very busy shiyasa” Daddy ya kalleshi sosai sai kuma ya ce“But at least ya kamata a ce kana zuwa kuna gaisawa ka ji” Kofa ya nufa yana ɗagawa Daddy kai. Da idanu kawai Daddy ya bi sa sai kuma ya yi murmushi, Sai da ya fita sannan ya juyo da ganinsa wajen Mommy yana cewa
“Zayyad ya fara hankali gaskiya, Shiyasa nake ce muku ku rabu dashi da kansa zai gane ya girma”
Ɗan murmushi Mommy ta yi ta ce
“Ai kam dai gaskiya, Dan ko Khalil ya ce min yana abin da ya kamata a asibiti saɓanin kwanakin baya” Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya ce“Allah abun godiya, Allah ya ƙara shirya mana ya'ya” Murmushi Mommy ta yi ta ce“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Yana shirin shiga motarsa wayarsa ta fara ringing, kallon screen ɗin ya yi ya ɗaga ya kai kunnensa, daga ɗaya ɓangaren ta ce
“Bae”
“Uhm”
Ya bata amsa kamar mai ciwon haƙuri.
Tashi zaune Anisa ta yi a shagwaɓe ta ce
“Where are u ne?”
Buɗe motarsa ya yi ya shiga yana cewa
“Like how Anisa? Ina nan mana”
“But you left me, why are u ignoring me?”
Anisa ta yi maganar cike da damuwa. Furzar da iska ya yi daga bakinsa kafin ya ce
“Nothing serious, Kawai I'm busy ne shiyasa, But zan zo anjima idan na dawo”
Ba dan ranta ya so ba ta ce
“Alright, I'll wait for you”
Jin jina kai ya yi kamar tana gabansa ya ce
“Okay”
“Love you bae”
“Same” Ya faɗa a taƙaice sannan ya kashe wayar. Ajiyar zuciya Anisa ta sauke ta sauke wayar tana kallon screen ɗin, Feedy dake gefenta ta ce “Baki ga kamar Zayyad ya sauya ba?”
“I think so”
Anisa ta faɗa a matuƙar dame. Taɓe baki Feedy ta yi kafin ta ce“Maybe fa ya samu wata ne shi ne yake miki hanya hanya, Kin san halin maza irin su” Girgiza kai Anisa ta yi ta ce“Zayyad ba zai taɓa yimin haka ba na rantse miki. Kawai dai he has been busy ne kamar yanda ya ce, Kuma nasan tun da ya ce zai zo zai zo ɗin” Jinjina kai Feedy ta yi ganin yanda Anisa ta koma ta ce“Shikenan kwantar da hankalinki, Yanzu ki tashi ki yi wanka ki tafi gida” Numfasawa ta yi kafin ta ce“Eh daman yanzu zan tafi coz Daddy ya je Kano kuma nasan Maybe yanzu ya dawo, Ina son ya sameni a gida”. Okay Feedy ta ce tana danna wayarta, Anisa ta tashi ta shige toilet ɗin hotel ɗin.
****
A hankali ta shiga tura ƙofar ɗakin, kwance ta hangeta can ƙarshen gado ta yi ruf da ciki. Ta ƙarasa a hankali ta zauna gefenta
“Jiddah”
Saurin ɗago kanta ta yi, Ta tashi zaune tana jan ɗankwalin Abayar jikinta ta ce
“Na'am Mum”
“Na something wrong with you Jiddah?”
Murmushi ta yi tana kallon Mum ta ce
“Babu komai fa Mummy, I'm fine, Kawai bacci nake ɗan ji”
Girgiza kai Mummy ta yi ta ce“Ko zaki ɓoyewa wani abu ban dani Jiddah, Saboda ni na haifeki. Na lura tun da aka fara maganar aurenku da Zayyad ki ka sauya, Akwai wata matsala ne? Ko baki son sa?” Girgiza kai Jidda ta yi, Ta tashi ta dawo kusa da Mamarta ta ɗora kanta bisa cinyarta kawai sai ta fashe da kuka. Da matuƙar mamaki Mummy ke kallonta, Ta shafa kanta murya a sanyaye ta ce
“Ki daina kukan nan dan Allah Jiddah, Kar wani abun ya sameki, Tashi ki faɗa min meke faruwa?”
Kasa magana Jiddah ta yi sai kuka take a hankali, Sosai Mummy ta damu gudun kada wani ciwon ya tayar mata, Sai da ta gaji dan kanta sannan tafara sauke ajiyar zuciya a hankali. Ɗago kanta Mummy ta yi ta zuba mata idanu, Sunkuyar da kai Jidda ta yi Mummy ta ce a nutse
“Hauwa'u”
Muryarta na rawa ta ce
“Na....Na'am Mummy”
“Faɗa min abin da yake damunki, Idan auren Zayyad ne baki so ki sanar dani, Tun da magana bata yi nisa ba a fasa, Koda an ɗaura auren ne ana iya fasawa. But ki daina wannan kukan bayan kin san condition ɗinki, Dan Allah karki saka mu a matsala” Hannunta ta sanya ta goge hawayen da suka sake zubo mata. Cikin cool voice ɗinta ta ce
“Babu komai Mummy, Kawai nafara kewarku ne, Sai nake jin daman ba'a fara maganar auren nan ba”
Murmushi kawai Mummy ta yi sanin halin Yar tata ta ce “Ba zaki sanar dani ba kenan? Anyway, Ki tashi magrib ya kusa za ku je shopping ke da Kausar” Langwaɓar da kanta ta yi ta ce“Ayyah Mum ta je ita kaɗai mana, Wallahi ƙafata ciwo yake min” Shiru Mummy ta yi tana kallonta, Ganin haka ya sanya Jidda sunkuyar da kanta tana murmushi. Tashi Mummy ta yi ta ce“Ki shirya nafaɗa miki, Bana son ku yi dare, Sannan make sure da ruwan zafi ki ka yi wanka, Ki saka kaya mai nauyi okay?” Gyaɗa kanta ta yi Mummy ta juya ta bar ɗakin. Sai da Jidda ta ga ta tafi sannan ta sake fashewa da wani sabon kukan ta kwanta gefen gadon tana rera abin ta, Ita kaɗai ta san masifar da take ciki yanzun.
Mararaba, Nassarawa.
A buɗe Salma ta ga ƙofar gidan nasu, Mamaki ya isheta, Daman Umma ta dawo kenan bata faɗa mata ba? Me yasa zata kai ta gidan Hajiya Jin jin ajiya? Ko dai wata matsalar ta faru? Ita kaɗai ta dinga sake saƙe a ranta. Ganin tsaiwar Tata bata da amfani ya sanya kawai ta saka kanta cikin gidan bakinta ɗauke da sallama. Turus ta yi ganin wasu yara guda biyu mace da namiji a tsakar gidan suna wasa, Ita dai tun da take a rayuwarta bata taɓa ganin yaran ba. Ta sake sallama ganin kamar ba'a ji ba. Wata mata ce ta fito daga ɗakin fuskarta ɗauke da murmushi ta ce
“Wa'alaiki assalam, Maraba”
Salma da mamaki ya gama cikata ta ƙirƙiri murmushi ta ce“Ina yini?” Matar wadda ta kasance mai sakin fuska ta ce“Lafiya klao” Shiru Salma ta ɗan yi can kuma ta ce“Ina Umma take?" Da mamaki matar ta ce“Wace Umma?” Salma ta ɗan yi shiru kafin a sanyaye ta ce“Matar gidan nan, Naga an buɗe gidan nan to inaga ta dawo. Daman kayana nazo ɗauka” Girgiza kai Matar tayi ta ce“Ikon Allah, To ina ga ko gidan kusa da shi ne, Amma ni ce matar gidan nan, Yau kwananmu huɗu da tarewa, siyansa mukayi”
Mutuwar tsaye Salma ta yi tana kallon matar, Gaba ɗaya tunaninta ya kwance, Ta kasa gane in da matar ta dosa. Wane gidan suka siya? Yaushe? A hannun wa? Ganin ta yi shiru ya sanya matar ta ce“Ki shiga maƙotan nan ko nan ne gidan, Amma nan gidan babu wata Umma” Salma bata sake cewa komai ba ta juya ta fita daga gidan tana tafiya a sanyaye. Har ta kai bakin titin Kabayi bata sani ba, Dan tafiya take amma gaba ɗaya tunaninta da hankalinta sun yi ƙaura daga gangar jikinta, Maganganun matar ne kawai ke yawo cikin kanta, Sai saƙawa take tana warwarewa. Ta rasa ta inda zata fara haɗa tunaninta, Bata yi aune ba taji zubar ruwa akanta, Dan ko kaɗan idanunta basu gane mata hadari ba, Ta ci gaba da tafiya a hankali har ta ƙarasa gidan Hajiya Jinjin. Tsaye ta sameta tsakar gida tana tara kayan ruwa, Khadijah kuma na gyara ɗaurin ɗankwali dan ruwan ba sosai yake zuba ba. Ko sallama Salma bata iya yi ba haka suka ganta tsakar gidan kamar an jefota.
“Au ai nayi tunanin zuciya ki ka yi, Ki ka kama gabanki” Hajiya Jinjin ta yi maganar tana kallon Salma, Khadijah ce ta ce“Ina ki ka je ke kuma?” Murya na rawa Salma ta ce
“Um...Umma dan Allah ina Ummata take? Ina ta je? Yaushe zata dawo? Naje gidanmu naga wasu mutane a ciki, Kuma sun ce basu santa ba, Ki faɗa min yaushe zata dawo?”
Salma ta ƙare maganar hawaye na sintiri kan fuskarta. Shiru Hajiya Jinjin ta yi tana kallonta, Can kuma ta ce “Au da gidan naku ki ka tafi kenan? To ai bari ki ji ke da wannan gidan sai dai a lahira idan ana shigarsa. Saboda Rahmatu ta siyar dashi, Ba iya shi kaɗai ba duk wani abu da ki ka sani na cikin gidan ta haɗa dashi ta siyar, Ta kuma tattara kuɗaɗen da sauran waɗannan kudaden na wajenki ta bar garin nan, Tana can ta buɗe sabuwar rayuwa ta samu miji zata yi aurenta. Cewa tayi zata kore ki ni nan na ƙi bari na ce ta kawo ki na riƙe ki, Idan Khadijah zata tafi ku dinga tafiya tare Abujan, Gara ma ki nutsu ki san me ki ke yi! Yanzu babu wani Abu naki ko na ubanki, Kuma kin sani cewa ubanki bashi da wani dangi a garin nan zuwo ne ba'a san daga inda yake, Haka itama mahaifiyar taki, Haka suka zo kamar korarru!”.
# HCD
# Light within the darkness
# Nanameera
08106608363.
*HASKEN CIKIN DUHU*
https://chat.whatsapp.com/GSEDyyyzuMm3woohSiin9W?mode=ac_t