Chapter 16: Kindness become a risk
Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read
Nanameera, YOTA/23.
A hankali ta juya ta kalleshi ganin yaja da baya, Ya tsaya cak yana kallon hanya. Tun bayan fitowarsu suke tafiya bayan ta samu ya sauketa da kyar, Tafiyar kawai suke yi ba tare da ta san inda zasu nufa ba, Bata san kowa ba, Bata san inda ya kamata ta kai su ba, Ina zasu je?. Ta sauke nunfashi sannan ta kalleshi ta ce a sanyaye
“Muje mana”
A madadin ya tafi sai kawai taga ya nemi waje ya zauna, Ya ɗora kansa bisa gwuiwoyinsa. Da mamaki Salma ke kallonsa sai kuma ta kalli hanya, Babu kowa sai ɗaiɗaikun motoci da suke shigewa sakamakon dare daya riga da ya yi sosai. A hankali ta durƙusa gabansa tana kallonsa ta ce
“Ka tashi mu tafi Yaya yad, Dare yana yi”
Kallonta ya yi da daradaran idanunsa wanda suka yi jajur dasu, Bai ce komai ba taga ya ɗauke kansa yana kallon wani wajen, Goge hawayen daya wanke fuskarta ta yi sannan ta sake cewa “Dan Allah ka tashi mu tafi kaji”
Ko kallonta bai yi ba, Shiru ta yi tana kallonsa, A ƙalla ta ɗauki mintuna biyar, Can ya fara jin shassheƙar kukanta. Ɗago fuskarsa ya yi yana kallonta, Sosai Salma ke kuka ya tashi tsaye ba tare da ya ce mata komai ba ya ci gaba da tafiya. Da sauri itama ta tashi sannan tabi bayansa suka ci gaba da tafiyar da basu san inda suka nufa ba.
Hadari ne ya haɗo, Sararin samaniya ta yi wani irin jaa, Iska ta shiga kaɗawa da wani irin ƙarfi, Ƙura ta yawaita a ko ina. Sosai gaban Salma ya faɗi, Ta kalli Zayyad wanda ke tafiyarsa babu ko waiwaye, Yanzu idan ruwan nan ya sakko ya zata yi? Ina zasu je? Bata gama wannan tunanin ba yayyafi ya fara sauka, Da gudu Zayyad ya dawo baya ya riƙe gefen rigarta, Kallonsa kawai ta yi tana jin wani irin matsanancin tausayinsa, Muryarta na rawa ta ce
“Yaya yad mu yi sauri kar ruwa ya dakemu”
Bai ce komai ba, Dan daman tun bayan barinsu gidan bai sake magana ba, Sai dai ya shiga girgiza kansa a hankali. Cikin ikon Allah ruwa mai ƙarfi ya fara sauka, Zayyad ya riƙe Salma sosai jikinsa na wani irin tsuma. Rasa abin yi Salma ta yi, Ta shiga ƙarewa hanyar da suke kallo, Ita kanta ba zata ce ga inda suke ba. Da alama dai sun fita daga Asokoro da daɗewa, Hanyar kuma ta yi mata kama da hanyar komawa Mararaba. Wata tsohuwar container irin na masu cajin waya ta hanga, Ta ƙarasa wajen Zayyad na biye da ita. Tura ƙofar ta yi ta ganta a buɗe, Sai dai duk ƙura da tarkace ya cikata. Juyowa ta yi ta kalli Zayyad a sanyaye ta ce “Cikani to”
Banza ya mata kuma bai cikatan ba, Hannunta ta sanya ta janye nasa hannun daga jikinta, Ya ɗago idanunsa ya kalleta amma bai ce komai ba. Shiga cikin container ta yi, Ta sunkuya tana kallon ƙasan, Hannunta ta sanya duk biyun ta fara share wajen. Duk yanda take jin ƙura na damunta bai sa ta bari ba sai da tattare sharar waje ɗaya. Warware ɗan kwalin dake kanta ta yi, Ta shimfiɗa a ƙasan ya ɗan mamaye wajen kasancewar yana ɗan girma. Numfasawa ta yi sannan ta fito daga ciki, Bata samu Zayyad ba, Gabanta ya wani irin faɗuwa, Cikin tashin hankali ta shiga duba ko ina, Shassheƙar kuka ta jiyo daga bayan container ta ƙarasa tana tafiya a hankali, Zaune ta sameshi gefen container ya rufe fuskarsa da hannayensa yana kuka a hankali. Wata ɓoyyayiyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ƙarasa gabansa, Murya can ƙasa ta ce
“Yaya yad”
Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya sake sunkuyar da kan nasa, Hannunsa ta rike tana cewa
“Zo muje na gyara maka wajen”
Fizge hannunsa ya yi yana ɗauke kansa, Kamar zata yi kuka ta ce“Please mana”
Kafin ya yi magana aka saki wata tsawa mai firgitarwa, Ganinsa ta yi a tsaye ya riƙeta sosai jikinsa na rawa, Sai a sannan ta fuskanci ruwan yake tsoro. Bata ce komai ba ta nufi container, Da kyar Zayyad ya shiga ciki domin ta masa kaɗan, Ta zaunar dashi kan ɗankwalin data shimfiɗa sannan itama ta zauna a gefe, Takure jikinsa ya yi waje ɗaya yana motsa bakinsa a hankali, Duhu ya hanata sakat domin ita a rayuwarta ta tsani duhu, Tun tana ƴar ƙarama Abba ke siya mata fitila saboda duk dare bata iya zama sai da fitila, A hankali ta fara hawaye yana tunanin yanda zata yi. Bayan mintuna biyar ta sake kallon Zayyad, Duk da bata hango fuskarsa amma ta fuskanci gyangyadi yake. Sosai ya bata tausayi cikin rawar murya ta ce
“Yaya Zayyad, Bacci zaka yi?”
Gyaɗa mata kai taga ya yi, Ta sake kallon inda suke zaunen, Wajen ya yi musu kaɗan su kwanta sannan kuma ba son zamanta dashi take waje ɗaya ba tun da shi ɗin ba muharraminta bane. Ganin babu yanda zata yi ya sanya ta ce“Zo ka kwanta anan” Ta ƙare maganar tana dafa cinyarta, Ta cikin duhun ya kalleta sai kuma ya ƙaraso a hankali ya ɗora kansa bisa cinyarta, Ya cure jikinsa waje guda ya rufe fuskarsa da hannayensa nan da nan kuma bacci ya ɗaukesa.
Zubar ruwan ce ta yawaita, Ƙara ta cika ko ina, Ɗigar ruwa ta fara ji akanta, Ta ɗaga idanunta dan ganin ta inda ruwan ke zuba. Bata ga komai ba sai dai ruwan bai daina zuba ba, Da alama container a ɓule yake wannan shi ne dalilin daya sanya babu komai a ciki. A haka ruwan ya ci gaba da zuba kan Salma ta yi shiru tana tunanin halin da rayuwarsu zata shiga, Ta ina zata fara rayuwa da mahaukaci? Ya zata yi da Zayyad? Babu wanda ta sani nasa ballantana ta kai shi wajensa, Itama babu wani nata ballantana taje in da yake. Da wannan tunanin Salma ta kwana a zaune har gari ya waye.
A hankali ya shiga buɗe idanunsa, Kalle kalle ya dinga yi, Ya tashi zaune yana kallonta. Idanunta a rufe suke da alama bacci ne ya ɗauketa a zaunen da take, Ƙura mata idanu ya yi yana kallonta, Can kuma ya kai hannunsa fuskarta. Buɗe idanu Salma ta yi tana kallonsa, Ta ɗan ja baya, Hannunta ta sanya ta murza idanunta still looking at him.
Gani ta yi ya ƙara kawo hannunsa fuskarta, Ta tashi tsaye kamar zata yi kuka ta ce
“Mene haka?”
Cikin zafin nama shima ya tashin, Kansa ya bugi da jikin langa-langar, Ya dafe kansa yana kwaɓe fuska, Kallonsa kawai Salma ta yi sai kuma ta fita daga container. Kallon ko ina ta dinga yi, Ɗaiɗaikun motoci da babura na shigewa, Iska mai sanyi da danshin ruwa na kaɗawa a hankali, Ta lunshe idanunta tana jin nutsuwa na saukar mata. Ta fi minti biyar a tsaye kafin ta buɗe idanunta, Tsugune ta hango Zayyad yana rike da wani kare sai taɓa jikinsa yake. Ƙarasawa wajen ta yi, Ta tsaya a kansa ba tare da ta ce komai ba..
“Baka da lafiya, Meke damunka? To bari daina kuka zan baka magani”
Abin da yake cewa karen kenan, Gegen hannunta ta sanya ta share hawayen daya zubo mata. Ganin ba daina maganar zai yi ba ya sanya ta ce a sanyaye
“Yaya Zayyad”
Ɗaga mata hannu ya yi ya ce
“Haba nurse baki ga ina da mara lafiya ba, Ki bari sai na gama dashi sannan mana haba!”
Salma ta girgiza kanta, Wato duk rayuwarsa a asibiti ce take dawo masa. Komawa wajen container ta yi ta zauna ta zuba uban tagumi, Tunanin abin da zasu ci ne ya dameta, Gashi bata da komai, Ko ya zasu yi?. Tana nan zaune har taga ya tashi ya rabu da karen ya yi tafiyarsa, Ya dawo inda take ya zauna a ƙasa yana kallonta.
“Ka bashi maganin?”
Ta faɗa tana kallonsa. Jinjina mata kai Zayyad ya yi, Wajen ya yi shiru can kuma taga ya tuntsire da dariya. Kamar zata yi kuka ta ce
“Me ka ke wa dariya?”
Bai bata amsa ba, Ya ci gaba da dariyarsa yana girgiza kansa. Can kuma ya haɗe fuska kamar ba shi ba, Cikin kakkausar murya ya ce
“Bazan dawo ba! Ni ki bar ni anan Mommah! Ina son zama anan, Zan duba marasa lafiya nefa”
Da mamaki Salma ke kallonsa jin ya ambaci sunan Mommah, A hankali Memory ɗin jiya da daddare ya shiga dawo mata fresh cikin kwakwalwarta.
“Ita ce ta haukata shi! Ita ta rabamu dashi, Azzaluma, Macuciya, Muguwa, Daga taimako? Sai ki raba shi da hankalinsa, Allah ya isa tsakaninmu dake! Kin cucemu!”
Salma ta runtse idanunta, Ta shiga girgiza kanta tana kuka tamkar yanzu Mommah ke faɗa mata wannan kalaman. Tabbas babu abin da ta masa, Ita ta sani bata cutar dashi ba, Sai dai bata san wace ƙaddara ce ta sanya ya zaɓeta a matsayin wadda ta masa asiri ba. Akan me? Me yasa sai ita? Ga Nayla ga Mufeeda ga Mommah ga Mommy, Ya bar kowa ya zaɓeta. Saboda bata da gata, Saboda ya taimaketa.
Ta sake rushewa da wani sabon kukan, Shiru Zayyad ya yi da zantuttukan nasa ya zuba mata idanu ganin yanda take kuka, Tashi ya ya ya ƙarasa gabanta. Hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce
“Meke damunki? Bari zan baki magani”
Ture shi ta yi ta tashi ta shige cikin container. Ɗankwalinta ta ɗauko ta yafa sannan ta fito. Can ta hangeshi yana kwasar ledoji, Ta ƙarasa wajen ɗago kansa ya yi yana kallonta duk ya ɓata fuskarta da ƙasa hannunsa cike da tarkacen ledojin pure water, Murmushinsa mai kyau ya sakar mata ya ce
“Ga magungunan na samo muje na baki, har da paracetamol”
Takaici da baƙin ciki ya sanya Salma doke hannunsa, Gaba ɗaya ledojin suka zube. Ta nuna shi da yatsa ta ce
“Ka bar wannan haukan ka shige mu tafi”
A tsawace shima ya ce
“Ni ne mahaukacin? Kin san wane ni? Ni Zayyad ki ke cewa mahaukaci?”
Bata ce masa komai ba, Ta juya ta nufi hanyar titi, Ganin haka ya sanya ya biyo bayanta. Tafiya suka ci gaba da yi, Suna tafe yana sata magana, Duk abin da ya gani a hanya sai ya tsaya ya tsinta, Idan ta yi masa magana sai ya ajiye. Wasu lokutan kuma yana ɗan surutansa a haka har suka shigo cikin Mararaba wajejen ƙarfe 10:00 na safe.
Ta dinga kallon garin tamkar ta shekara rabonta dashi, Rasa inda zata je tayi, Ko taje gidan Hajiya Jinjin? Zata taimaketa? Ta tambayi kanta. Tafiya taga Zayyad ya fara yi, Tayi saurin bin bayansa sai da ta cimma masa sannan ta kalleshi ta ce
“Ka daina yin gaba kana bari kar ka je ka ɓata”
Banza ya mata, Itama bata sake cewa komai ba suka ci gaba da tafiya. A bakin orange market ta tsaya, Ya dinga kallon kasuwar kamar mai tunanin wani abu. Wata mai siyar da abinci ya hanga tana zuba miya kan farar taliya, Ya ƙarasa wajen ya tsuguna yana kallonta kamar idanunsa zasu faɗo. Sai da ta gama zuba miyar sannan ta kalleshi ta ce
“Malam me za'a baka?”
Shiru Zayyad ya mata, Ta sake maimata tambayar. Ganin bai da niyyar bata amsa ya sanya ta ce a fusace
“Kai Malam Idan ba siya zaka yi ba ka tashi ka bani waje kaji”
Salma ce ta ƙaraso wajen bayan ta hangeshi tsugune dan bata san ma sanda ya bar kusa da ita ba tana can tunani. Hannunsa Salma ta kama tana cewa
“Yaya Zayyad tashi daga nan”
Miƙewa ya yi ya kalleta sai kuma ya nuna mata abincin..
“Yunwa ka ke ji?”
Salma ta tambaye shi murya a sanyaye. Gyaɗa mata kai ya yi har sannan idanunsa na kan abincin. Wasu sabbin hawayen taji sun fara zubo mata kan fuska, Itama yunwar take ji, Duk da ta saba jure yunwa amma tasan shi ba zai taɓa jurewa ba. Gashi bata da kuɗi balle ta siya masa abinci, Numfasawa ta yi sai kuma ta ce“Muje zan siya maka a wani wajen”Daga haka ta riƙe hannunsa suka bar wajen. Kai tsaye inda take zama siyar da lemo ta nufa, Akwai wata mai abinci a wajen wadda suka ɗan saba. Tana zuwa ta samu Sa'a matar ta fito ta ƙarasa tana murmushi suka gaisa, Matar ta ce
“Salama kwana dayawa kin daina fitowa”
A sanyaye Salma ta ce
“Wallahi Mama Abbana ne ya rasu shine ya saka”
Girgiza kai matar ta yi ta ce
“Allah sarki Allah ya jiƙansa da Rahama”
Da Ameen ta amsa sannan ta yi shiru tana tunanin ta in da zata fara dan sam roƙo ba ɗabi'arta bane. Ganin ta yi shiru ya sanya Matar ta ce
“Lafiya dai Salma?”
Numfasawa ta yi ta ce
“Daman inason zan miki wanke wanke ne sai ki bani abinci dan Allah Mama”
Shiru matar ta yi can kuma ta ce
“Tom shikenna, Daman kayan sun ɗan taro je ki yi Salama”
Sosai Salma ta ji dadi ta tashi ta shiga shagon nata ta kwaso kayan da za'a wanke, Zayyad na tsaye daga waje har sannan yana bin ta sa kallo duk inda ta yi. Sai da ta haɗo komai sannan ta kalleshi ta ce
“Zauna akan bencin nan”
Ta ƙare maganar tana nuna masa wani benci. Bai ce komai ba kuma bai zauna kan bencin ba ya ci gaba da tsaiwarsa yana kalle kalle abinsa. Itama bata sake bi ta kansa ba, Ta fara wanke-wanken. Bata fi mintuna ashirin ba ta kammala wanke duk kayan ta mai da komai inda yake sannan ta fito. Murmushi Matar ta yi ta ce
“Ywwa Salma sannunki da ƙoƙari”
Daga haka ta ɗauko leda ta zuba mata abincin, Amsa Salma ta yi tana godiya sannan ta bar shagon tana kallon Zayyad wanda ya biyo bayanta. Can ƙasan Kabayi ta samu inda babu mutane sai filaye ta zauna kan wani bulo tana kallonsa ta ce
“Ga abincin”
Ƙarasowa ya yi ya ajiye ledojin hannunsa a gefe sannan ya amsa ledar abincin, Ganin yanda yake kokawa da ledar ya sanya ta amsa ta buɗe masa.Ganin hannunsa duk datti ya sanya ta fasa pure water hannunta da Matar ta bata ta wanke masa hannun sannan ya fara cin abincin. Tass ya tashi da abincin dan daman ba wani yawa gare shi ba, Bayan ya gama ta miƙa masa ragowar ruwan ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya. Basu daɗe a wajen ba ta tashi tana kallonsa ta ce
“Mu tafi”
Bai ce mata komai ba kuma bai taso ba, Sai ma kwanciya da ya yi kan yashin wajen yana lumshe idanunsa.
Dawowa ta yi tana ci gaba da kallonsa da mamaki ta ce
“Ka taso mu tafi mana”
Ba zaka taɓa ɗauka da Zayyad take magana ba dan ko inda take bai kalla ba. Ganin ba tashin zai yi ba ya sanya ta haƙura ta nemi gefe ɗaya ta zauna ta zuba uban tagumi.
Tana nan zaune har aka fara kiran sallahr azahar, Ta tashi daga zaunen da take ta ƙarasa wajen wata buga-buga data hanga gefen wata gona ta samu ledar pure water ta buga ruwan a ciki sannan ta matsa gefe ta gabatar da alwala. Tana gamawa ta dawo inda yake kwancen har sannan yana bacci ta gyara mayafin jikinta ta yi sallahrta a wajen. Koda ta idar zama ta yi ta shiga addu'oi kala kala tana neman Ubangiji ya kawo mata mafita.
Zayyad ya shiga buɗe idanunsa a hankali yana ɗan surutansa, Ya tashi zaune yana dafe kansa, Juyi ya dinga yi shi kaɗai kan tarin yashin kafin daga bisani ya saki wata ƙara, Salma ta taso da sauri tana kallonsa ta ce
“Lafiya? Mene ne?”
Bai bata amsa ba, Sai ma tashi da taga ya yi yana shirin barin wajen, Da sauri itama ta tashin ta riƙo rigarsa tana cewa
“Ina zaka je? Mene ne Yaya Zayyad? Ko abincin zaka sake ci?”
Bai bata amsa ba sai huci da yake ta yi, A hankali kuma ya fizge hannunta daga jikinsa ya fara tafiya. Sake bin sa Salma ta yi ta cakumeshi hankalinta a matuƙar tashe ta ce
“Ka faɗa min mene ne? Ba zan bari ka tafi wani wajen ba Wallahi!”
A fusace ya juyo ya shaƙe wuyanta da duk hannayensa guda biyu, Nan da nan idanunta suka firfito waje, Hawaye ya dinga zuba daga cikinsu. Ta sanya hannunta tana ƙoƙarin rikeshi amma ta kasa, Wani bango ya hanga ya shiga janta har wajen bango yana zuwa ya gwara kanta da jikin bangon sannan ya saketa, Salma ta faɗi ƙasa Sumammiya kanta na zubar da jini, Bai ko kalleta ba ya juya ya bar wajen yana tafe kamar zai tashi sama.
# HCD
# Light within the darkness
# Salmerh
# Zayyad
# Nanameera
08106608363.
*HASKEN CIKIN DUHU*