Chapter 15: Exiled With the Mad
Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 27 min read
Nanameera, YOTA/023.
Wani irin kallon kin zama mahaukaciya ya yi mata kafin ya ja dogon tsaki, Bai sake bi ta kanta ba ya juya ya buɗe ƙofar ɗakin, Tsaye ya ga Nayla tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ita ma. Ta kalleshi bai ce komai ba ya ratsa ta gefenta ya bar parlon gaba ɗaya, Da idanu kawai ta bi shi sai kuma ta girgiza kanta ta shige ɗaki. Durƙushe ta samu Salma har sannan kuma shassheƙar kuka take, Da sauri Nayla ta ƙarasa gabanta cikin tashin hankali ta ce“Lafiya Salma? Meya faru?”
Shiru Salma ta yi ba tare da ta bata amsa ba, Ta miƙe tsaye ta koma toilet ɗin. Da idanu Nayla ta bita tana mamakin abin da ya sanyata kukan, Tana nan zaune har Salma ta fito amma wannan karan jikinta sanye da hijabinta, Duk da kasancewarsa a jiƙe. Tashi Nayla ta yi tana kallonta ta ce“Ya zaki saka hijab jiƙaƙƙe?, Bari na baki kaya” Ita dai Salma ba ta ce komai ba ta ja ta tsaya a wajen. Press Nayla ta buɗe ta ɗauko mata wata sleeping dress mara nauyi. Miƙa mata ta yi Salma ta karɓa sannan ta koma toilet ɗin, Bata jima ba ta fito bayan ta sauya zuwa rigar baccin wadda ta yi mata kyau sosai. Murmushi Nayla ta yi tana riƙe hannunta ta ce
“Wow kin yi kyau sosai, Zo ki ci abinci”
Ɗan murmushi Salma ta yi tana ci gaba da kallon Nayla. Sakin hannunta ta yi ta ƙarasa in da ta ajiye tray ɗin data shigo dashi, Ta buɗe, White rice ce wadda ta ji vegetables sai miyar kwai, Ta yi serving ɗinta sannan ta ajiye a ƙasa. Kallon Salma dake tsaye har sannan ta yi ta ce
“Common zo ki ci abinci”
Bata yi musu ba ta ƙaraso inda Nayla take, Ta zauna kan rug ɗin. Tura mata plate ɗin Nayla ta yi ta ce“Yawwa ki ci abincin kin ji sai ki kwanta” Gyaɗa mata kai kawai Salma ta yi. Nayla ta tashi ta koma kan gado taja system ɗinta tana ci gaba da kallon da take, Ganin haka ya sanya Salma sakin jikinta ta sanya hannunta cikin abincin bayan ta yi bismillah ta ɗiba ta kai baki, Lumshe idanunta ta yi saboda daɗin da abincin ya yi mata, Ga kuma yunwa wadda ta dameta, Ta shiga tauna abincin a hankali cike da nutsuwa. Bayan mintuna goma ta gama cin abincin, Ta tsince wadda ta zubar a gabanta cikin empty plate ɗin sannan ta tashi tana riƙe da plate, Kallon Nayla ta yi wadda hankalinta ke kan system sai murmushi take a sanyaye ta ce
“Ina zan ajiye plate ɗin?”
Ɗagowa Nayla ta yi ta kalleta sai kuma ta yi murmushi ta ce“No don't worry bar shi a nan, Ki je toilet ki wanke bakin ki ki zo ki kwanta dare ya yi” Toh kawai Salma ta ce sannan ta ajiye plate ɗin gefen tray ɗin ta nufi toilet. Koda ta dawo kwance ta samu Nayla ta kashe system ɗin, Ta kalleta ta ce
“Zo ki kwanta mana”
Shiru Salma ta yi tana kallon Nayla, Wata irin zuciya gareta da har zata bari wadda bata sani ba ta kwana gefenta? Ikon Allah. Salma ta yi maganar cikin ranta, Nayla ta sake murmushi ta ce“Feel free fa, I'm ur friend ki zo ki kwanta nasan kin gaji” Ɗan murmushi Salma ta yi sannan ta ƙaraso wajen gadon, Daga ɗaya side ɗin ta kwanta a hankali kamar me tsoron gadon, Ganin bata ja duvet ɗin ba ya sanya Nayla ta rufa mata ta ce“Sai da safe”
“Allah ya tashemu lafiya”
Salma said.
Washegari da wuri Salma ta tashi, Ta duba gefenta bata ga Nayla ba. Tashi ta yi ta hau gyara gadon dan daman already ta riga da ta yi sallah tun asuba, Tana gamawa ta ɗebi kwanukan jiya ta fito parlon. Da mamaki Mufeeda ke kallonta tana sanye da sport wears da alama daga gurin sport take, Ganin irin kallon da take mata ya sanya Salma rissinawa ta ce
“Ina kwana?”
“Lafiya lao”
Mufeeda ta amsa mata, Sai kuma ta shige nata bedroom ɗin, Da idanu kawai Salma ta bita sai kuma ta tsaya tana tunanin ina zata kai kayan hannunta.
Ganin irin kallon da Mommah ke mata ya sanya ta langwaɓar da kai ta ce“Wallahi Mommah, Sai kin ganta zata baki tausayi, Tana da kirki sosai, I know her before” Taɓe baki Momma ta yi ta ce“Ni ba wannan ya dameni ba Nayla, Cewa na yi shi Zayyad ina ya santa? Kuma ina ya ganta har ya kawota cikin gidan nan?” Nayla ta ce“But Mommah kin san wane Yaya Zayyad ba, Koda a ce yana aikata abubuwan da ba daidai ba amma kin san halayensa, Ya ce min ya ganta ne a hanyar Mararaba some mens trying to rape her, Shi ne ya taimaketa” Jin jin kai Mommah ta yi ta ce“And you believe it?”
“Absolutely ma”
Numfasawa Momma ta yi ta ce“Anyway, Idan haka ne ai babu buƙatar ta zauna cikin maids kawai ku zauna tare har sannan Allah zai kawo mafita” Murmushin jin daɗi Nayla ta yi ta ce“That's our Momma! Thank you so much” Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“Raba ni da shirme, Ki tashi ki je ki kira min Zayyad ɗin” Toh Nayla ta ce sannan ta tashi ta ɗauki veil ɗinta ta ɗora akanta ta yi waje da sauri.
A hankali Salma ke tafiya cikin corridor ɗin, Sai bin kowace ƙofa take da kallo, Kamar daga sama ta ji an ce
“Kee!”
Tsabar yanda ta tsorata sai da ta saki tray ɗin hannunta, Plate ɗin ya tarwatse a wajen, Haka ma ragowar abincin dake cikin food flask ɗin. Ta juya jikinta na rawa dan ganin wnada ya kira sunan nata. General ne tsaye cikin ƙananun kaya t-shirt fara sai wando na uniform. Ƙura mata idanu ya yi yana kallonta kamar mai son gano wani abu, A rikice Salma ta ce
“In... Ina Kwana?”
Bai amsa bata ba, Haka kuma bai bar kallonta ba, Ita kuwa duk sai ta tsargu ta sunkuyar da kanta hannunta na ɗan rawa,
“Daddy”
Ta tsinkayi muryarsa, Zayyad ya yi maganar yana rufo ƙofar apartment ɗinsa. Sai a sannan Daddy ya ɗauke kansa daga kanta ya maida gun Zayyad bakinsa ɗauke da murmushi ya ce“Na'am ka tashi?” Gyaɗa masa kai Zayyad ya yi lokacin da idanunsa suka sauka kan Salma wadda ke tsaye ɗan nesa da Daddy.
“Ina zaka je yanzu?” Daddy ya sake tambayarsa. Ɗauke idanunsa ya yi daga kanta sannan ya ce“Company nake son zuwa, An kawo takardun?” Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Eh, An kawo, An jima idan ka dawo sai mu yi magana” Okay Zayyad ya ce. General ya sake kallon Salma sai kuma ya juya ya bar wajen. Sai a sannan Zayyad ya ƙaraso in da looking in to her eyes ya ce
“Mene haka?”
Rau rau ta yi idanu hawaye na kwanciya cikin kurmin idonta ta ce“Babu komai” Taɓe baki Zayyad ya yi sannan ya ce“Wane ya sanya ki ɗauko wannan kayan?” Girgiza kai Salma ta yi ta ce“Babu kowa, Ni ce na ɗauko”
“Uwar iya ko?”
Ya faɗa yana ɗaure fuska, Shiru ta yi ba ta ce komai ba ya sake kallonta ya ce
“And this is the last warning da zan yi miki akan ina magana ki min shiru, You get it?”
Muryarta na rawa ta ce
“Ka yi haƙuri ba zan sake ba”
Kafin ya yi magana Nayla ta ƙaraso wajen tana kallonsa ta ce“Yaya Momma na kiranka” Okay ya ce mata sannan ya juya ya bar wajen, Ta kalli Salma ta ce“Meya faru?” Girgiza mata kai Salma ta yi sai kuma ta ce“Babu komai, Kawai na yarda kaya ne" Ta ƙare maganar tana nuna mata inda tray ɗin yake. Murmushi Nayla ta yi ta ce“Ayyah ai babu komai, Mu je kawai masu aiki zasu kwashe” Salma ta kalleta, Gyaɗa mata kai Nayla ta yi ta ce“Mu je” Daga haka ta kama hannunta suka bar gurin.
Tun da ta fara magana yake kallonta har sai da ta yi shiru dan kanta, General ya ce“Hajarah ban gane ba, Go straight to the point” Numfasawa ta yi tana kallonsa ta ce“Wallahi Yallaɓai da gaske nake maka, Abin da nake nufi shi ne ni wannan yarinyar ban yarda da kawota gidan nan ba. Akan me? Gaskiya a sauya wannan al'amarin” Da mamaki General ya ce“And what's the matter? Kin santa ne?” Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a ban santa ba, Amma haka kawai naji ban yarda da ita ba, Kuma wallahi tun da na ce haka akwai wani abu a tattare da ita, Shiyasa nake son a yi wa tufkar hanci tun yanzu.” Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Shikenan zan yi magana da Khadijah”
“Au yanzu har sai ka yi magana da ita kafin ka yanke hukunci? Ai shikenan” Daddy bai ce mata komai ba ya tashi ya fice daga parlon, Ta bishi da kallo sai kuma ta taɓe baki.
****Murmushi Zayyad ya yi ya ce“Amma ai Mommah u trust ur son right?” harararsa ta yi ta ce“Duk da haka a have to know Zayyad, Saboda rayuwar yanzu, Ina iyayenta? Ko ance sun mutu ita bata da wani dangi? Ko na uwa ko na uba?”
“Mommahhhh!...”
Haɗe rai ta yi ta ce
“Ko me zaka ce sai dai ka ce amma dole na sani kafin na fara riƙonta” Shafa sumar kansa mai uban yawa ya yi kafin ya ce
“Shiyasa ni na ce kawai ta zauna cikin maids, Kin ga da babu wannan tambayoyin”
Murmushi Momma ta yi tana girgiza kanta ta ce“Kakarta ka maidani ko? Ai shikenan” Dariya ya yi ya ce“A'a Mommah ni na isa” Taɓe baki ta yi, Sai kuma ta gyara zamanta ta ce“Look ya kamata a fara shirye-shiryen bikin na, Ka ga sauran 2weeks fa” Langwaɓar da kansa ya yi ya ce“To Mommah ai kune da shirye shirye ba Zayyad ba” Wani kallo ta yi masa daya sanya ya yi murmushi ta ce“Zan samu na je Mararaba sai mu yi magana da Mami” Okay ya ce sannan ya tashi yana kallonta ya ce“Zan je Company na dawo” Murmushi ta yi ta ce“Tom Allah ya tsare ya kiyaye hanya” Ya ce Ameen Sannan ya juya ya bar parlon.
10:23pm
Cikin ƙungurmin daji ne, Babu gida gaba babu gida baya, Sai tarin bishiyu masu tsayi da kuma ciyayi, Babu abin da ke tashi cikin dajin sai ƙarar ihu da iface-iface na dabbobi da kuma wasu halittu. Saman wani tsauni mai mugun tsayi ake iya ganin hasken jar fitila, Hayaƙi na tashi da kuma dariya mai ban tsoro, Wani ƙaton mutumi ne zaune kan wani buzu, jikinsa babu kaya sai ɗan fante wanda ya rufe al'aurarsa baƙar fatarsa sai sheƙi da kyalli take, Ko ina na jikinsa guru ne da kuma layoyi, Gaba ɗaya fatarsa a zane take da wasu irin zanuka, Wasu wajejen dabbobi ne aka zana wasu kuma rubutu aka yi da wani yare wanda ba hausa ba haka na ba kuma turanci ba. Gashin kansa ya yi tudu tamkar ya sanya hula saboda yawa, Jikinsa ban da tashin ƙarni da wari babu abin da yake. Daga gefensa wata mata ce zaune tana sanye da hijabi ruwan ƙasa ta zuba masa idanu tana sauraren abin da zai ce. Wata irin dariya mai kashe kunnuwa ya saki, Ta sanya hannayenta ta ɗan toshe kunnenta ba tare da ya ganta ba, Ya washe bakinsa haƙoransa masu azabar datti suka bayyana, Cikin ɗaga murya ya ce
“Kun yi sake! Kun yi sake, Baku yi abubuwa yanda na sanar muku ba! Kun kauce hanya”
Muryar matar na rawa ta ce
“Ka taimakemu ya kai boka mai cikakken iko, Ka duba lamarin mu, Kar ka bari asirinmu ya tuno”
Sake tuntsirewa da dariya ya yi, Lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai ya buga gashin hannunsa a ƙasa kafin ya ce“Ai tun da kin zo ki ɗauka buƙatarku ta biya, Wane yake muku tsawon shekaru idan ba ni ba? Ko akwai wani wanda yake baku taimako idan ba ni ba?”
Ta girgiza kanta ta ce
“Babu kai ne abin dogaranmu, Kai ne mai share mana duk hawayen mu, Kai ne wanda ka ke taimakonmu akan duk abin da ya taso”
Ya sake sheƙewa da dariyar jin dadi sai kuma ya ce
“To yanzu ma zan taimake ku. Zan yi muku abin da zaku yaba dashi, Dake da ahalinki duk suna ƙarƙashin kulawata saboda haka damuwa ba taki ba ce! Wannan matsalar ta kau kuma nayi maganinta. Tabbas zaki yi dariya, Zaki dawo nan ki sameni ki faɗa min yanda abubuwa suka kasance”
Ta yi murmushin jin daɗi kafin ta ce
“Shiyasa har abada ba zamu taɓa bijire maka ba, Muna tare da kai, Kai ne wanda ke samar mana da farin ciki. Hajiya na yi maka godiya” Ya bushe da dariyar mugunta wadda ta cika ko ina na dajin.
****
Ranar Lahadi wanda ya kama Salma ta kwana shidda a gidan suka shirya dan zuwa gidan Nimrah. Mommah ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana kallonsu ta ce“Sai kun yi yamma ko?” Nayla dake shafa lip gloss ta ce“Yanzu fa zamu fito Mommah” Mommah ta kalli Salma wadda ke zaune gefen gado jikinta sanye da hijabi ta ce“Ke naga baki yi kwalliyar ba?” Kafin ta yi magana Nimrah ta ce“Wallahi Momma nayi mata magana wai ita bata so, Wai ko ɗankwalin Abayar ba zata yafa ba sai dai ta saka hijabi” Murmushi Mommah ta yi ta ce“Haba Salma tashi kin ji ki shirya ku tafi, Baki son ki ga kin yi kyau?” Sunkuyar da kanta ta yi ta ce“Tom Mommah” Nayla ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da eye liner ta ce“Let me help you” Shiru Salma ta yi ta tsaya ta yi mata lining ɗin sannan ta shafa mata lip gloss, Wani irin kyau ta yi fatarta ta sake fresh saboda ɗan hutun data samu.
“Damsel”
Nayla ta ce tana murmushi, Shiru Salma ta yi. Nayla ta ce“Ki cire hijabin kamar wata me takaba” ɗan murmushi Salma ta yi sannan ta zare hijabin. Wata black Egyptian Abaya ce a jikinta mara ado da yawa, Nayla ta ɗauki pin ta yi mata rolling mayafin, Sosai ta yi kyau kamar wata balarabiya.
“To ko kefa”
Mommah ta faɗa tana murmushi, Sunkuyar da kai Salma ta yi tana murmushi. Nayla ta ɗauko handbags guda biyu ta miƙawa Salma black colour ɗin ita kuma ta ɗauki union ɗin dan ita ce kalar Abayarta. Amsa Salma ta yi ta riƙe sannan ta tashi tsaye, Nayla ta ɗauki wayarta a gefen mudubi ta ce“Let's take a pictures” Daga haka ta fara ɗaukansu hotuna da videos, Ita dai Salma ban da murmushi babu abin da take. Sai da Mommah ta musu magana sannan Nayla ta bari suka fito daga ɗakin.
“Ku gaisheta”
Mommah ta ce bayan sun fito parlon, Okay Nayla ta ce sannan ta kalli Mommy dake zaune ta ce“Ko za'a kai wa Aunty Nimra Saƙo?” Girgiza kai Mommy ta yi ta ce“A'a jiya na bawa Khalil ya kai mata ai, Ku gaishemin da ita” Toh Nayla ta ce sannan ta kalli Mufeeda dake tsaye ta ce“Muje mana” Harararta Mufeeda ta yi ta ce“Idan naƙi fa?” Nayla bata tsaya bata amsa ba, Ta kama hannun Salma suka bar parlon. A compound ɗin gidan suka haɗu da General wanda ya fito daga garden, Tun daga nesa yake kallon Salma har ya ƙaraso gabansu. Nayla ce ta fara cewa
“Daddy sai mun dawo”
Jin jina mata kai ya yi ya ce“Allah ya tsare”
“Ina yini?”
Salma ta faɗa tana sunkuyar da kanta, Kallonta kawai ya yi amma bai amsa ba ya yi gaba abin sa. Da idanu kawai Nayla ta bi shi amma bata ji daɗin abin da ya yiwa Salman ba, Ta kalleta ganin har sannan kanta a sunkuye, Hannunta ta kama ta ce“Muje kin ji” Jiki a sanyaye Salma ta bi bayan Nayla suka shiga motar. Mufeeda ce a driver seat sai Nayla a gefenta Salma kuma ta shiga back seat. Duk hirar da suka dinga yi uffan bata ce musu ba, Dan gaba ɗaya ba daɗi take ji ba. A haka har suka ƙarasa Maitama gidan Nimra.
General na shiga parlon ya samu Mommah da Mommy suna hira, Sannu da zuwa suka masa bai amsa ba ya yi gaba yana faɗin
“Khadijah ina son magana da ke”
Da mamaki Mommah ta kalleshi, Mommy ta ce“Lafiyarsa kuma?” Taɓe baki Momma ta yi ta ce“Kin san halinsa, Bari na je na ji ko mene ne” Okay Mommy ta ce. Mommah ta juya tabi bayansa.
Tsaye ta sameshi tsakiyar parlon sai kai komo yake, Ta tsaya daga gefe ta ce“Yallaɓai gani”
“Ina son yarinyar nan ta bar gidan nan yau ba sai gobe ba!”
Da mamaki Mommah ke kallonsa sai kuma ta ce“Wace yarinya kenan? Wai Salma ka ke nufi?”
A fusace Daddy ya ce
“Wace ta zo gidan nan idan ba ita ba? Ina son ta bar min gida a yau kar na sake ganinta”
Mommah da hankalinta ya ɗan tashi ta ce
“But for what reason? Me ta maka General? Akan me zaka ce sai ta bar gidan nan?”
Daddy ya ce
“Amma ai kana sane da cewa nan gidana ne ko? To na ce ta bar shi, Ko tayi min wani abu, Ko bata yimin ba wannan duk ba damuwarki ba ne. Abin da na ce shi ne kawai ta bar min gida!”
Tuni ran Mommah ya fara ɓaci itama, Ta kalleshi ta ce
“Idan har bata yi maka wani abu ba to babu dalilin da zai sanya ka ce sai ta bar gidan nan, akan me? Ni ban gane irin wannan halayen naka ba, Me ta tsare maka? Yarinyar idan ba kamawa ta yi bama sai ka shekara baka ganta ba, Gaskiya da sake!”
Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Okay, shikenan, Idan kina ganin za ki iya ki bar ta cikin gidan nan Khadijah, Na dawo da daddare na sameta a cikin gidan nan”
Daga haka ya yi waje yana tafiya kamar zai tashi sama, Biyo bayansa Mommah ta yi, Sai dai kafin ta cimmasa har ya kai parlon ɗaga murya ta yi ta ce
“Wallahi muddin baka faɗa min abin da yarinyar nan ta yi maka sai idan ni da ita duk mu bar gidan!”
Cak ya tsaya a in da yake, Mommy dake zaune ta tashi tsaye tana kallonta da mamaki. Juyowa Daddy ya yi ya kalleta sai kuma ya ce“To ki gwada barin ta cikin gidan nan ki ga, Ba ke ba har ya'yan da ki ka haifa sai kun fita kun bar gidan nan!”
Mummunar bugawa zuciyar Mommy ta yi, Ta kalleshi a kiɗime ta ce
“Yallaɓai kana hayyacinka kuwa? Lafiya ka ke? Kasan me ka ke faɗa?”
A fusace Daddy ya ce
“Idan kema za ki shiga ciki ne to Allah ya baki Sa'a”
Turo ƙofar parlon suka yi, Suka shigo a tare da Mamaki suke bin su da kallo Khalil ya ce
“Lafiya?”
Mommy ce ta ce“Tambayesu dan Allah Khalil, Ban gane abin da yake faruwa ba, Ku tambayesu ku ji”
Zayyad idanunsa kan Mommah suka sauka ganin yanda take tsaye jikin stairs fuskarta ta yi jajur da alama ba ƙaramin ɓata mata rai a ka yi ba. A nutse ya ƙarasa gabanta yana kallonta ya ce“Mommah lafiya? Meke faruwa?”
“Zayyad nagaji da halin mahaifinku, Akan me zai ce sai yarinya ta bar gidan nan, Duk yaran da suke zuwa su zauna babu wadda ya taɓa yi ma magana sai yanzu dan wannan ta zo, Akan me”
Kallonta Zayyad ya yi da mamaki ya ce“Wace yarinyar aka ce ta bar gidan nan?”
“Salma”
Mommah ta faɗa. Juyowa Zayyad ya yi ya kalli Daddy wanda ke tsaye har sannan yana huci, Gabansa ya dawo ya ce
“But Dad why? Me ta yi?”
“Kawai bana son zamanta cikin gidana Zayyad! Ta bar gida yau ba sai gobe ba”
Shiru Zayyad ya yi yana nazarin kalaman Daddy, Khalil ya ce“Amma Daddy me Salma ta yi maka? Yarinyar da ko fitowa ba yi take ba?”
Daka masa tsawa Daddy ya yi ya ce
“And who are you Ina magana kana saka min baki?”
Shiru Khalil ya yi Mommy ta kalleshi ta ce“Kar na sake jin bakin ka anan”
Ta maida idanunta kan General ta ce
“Haba Yallaɓai dan Allah ka yi haƙuri mana, Idan ma wani laifin ta yi maka ai sai ka faɗa a saka ta baka haƙuri”
Daddy ya ce
“Ni da gidana na yanke hukunci kuma dole sai ta bar gidan nan!”
“Unfortunately babu inda zata je Daddy! Sai dai ka yi haƙuri!”
Zayyad ya yi maganar yana kallon Daddy, Da wani irin mamaki Daddy ya kalleshi sai kuma ya ce
“Ni ka ke cewa haka Zayyad? Ni ka ke faɗawa babu inda zata je?”
Cikin dakkakiyar murya Zayyad ya ce
“Eh Dad, Salma na gidan nan babu inda zata je, Idan ta yi maka wani abun ne to zan mata magana, But she can't leave this house like this”
Tafa hannu Daddy ya yi sai kuma ya ce
“Weldone! Ka yi kokari Zayyad! Ka kyauta, A matsayinka nawa ka ke cemin ba zata bar gidan nan ba?”
“A duk matsayin daka ɗaukeni a haka nayi maganar Daddy, Salma ba zata bar gidan nan ba in dai Zayyad yana nan, Idan ka ga ta bar gidan nan to sai dai idan bana cikinsa, Domin ba Mommah ta kawota ba ni ne na kawota cikin gidan nan, Idan kuma ban isa ba sai ka faɗa min naji!”
“Zayyad...!”
Ɗagawa Mommah hannu ya yi, Still looking at Daddy ya ce“And that's my decision!” Daga haka ya juya ya fice daga gidan. Da idanu duk suka bi shi, Daddy ya yi sak a wajen can kuma ya yi kwafa ya juya ya fice shima. Mommah juyawa ta yi ta koma sama, Gurin ya rage daga Mommy sai Khalil da har yanzu yake mamakin abin da Zayyad ya yi. Ko da Mommah ta koma apartment ɗinta zama ta yi kan sofa ta fashe da kuka, Dan ta tabbata wannan abun da faru ba lallai ya tsaya iya nan ba.
****
Around 5pm suka fito daga gidan, Nimra ta kallesu ta ce“Daga can zaku dawo nan ko gida zaku yi?” Girgiza kai Nayla ta yi ta ce“Gida zamu shige, Mommah ta ce kar mu yi dare” Okay Nimra ta ce sannan ta shiga motarta ita da Mufeeda, Salma da Nayla kuma suka shiga wadda suka zo da ita. Suna fita ƙofar gidan yana ƙarasowa, Parking tasa motar ya yi ya fito ya ƙaraso inda suke, Sauke glasses Nimra ta yi ya kalleta ya ce
“Da kun jira na kai ku”
Babu yabo babu fallasa ta ce“No, Thanks”
“Ina yini Yaya Farooq?”
Murmushi ya yi yana kallonta ya ce“Lafiya klao Feeda ya karatu?”
“Alhamdulilah”
Mufeeda ta bashi amsa. Motarsu Nayla ya ƙarasa tana murmushi ta ce“Yayanmu” Jan kumatunta ya yi ya ce“Ka ga yar autar gidan Daddy, Ya school ɗin?” lumshe idanu Nayla ta yi ta ce“Ina nan ina fama Yaya” Jinjina kai ya yi ya ce“Allah ya taimaka, Wannan ƙawarki ce?” ya yi maganar yana nuna Salma wadda ta juya kanta. Taɓa ta Nayla ta yi ta juyo suka yi ido huɗu da Farooq. Da mamaki ya ce
“Ummusalma!”
Waro idanunta ta yi sai kuma ta ce“Doctor ina yini?”
Murmushi ya yi ya ce“Lafiya klao Alhamdulillah, Yaushe ki ka zo Abuja? Ya ƙarin haƙuri?” Ɗan murmushi ta yi ta ce“Ban jima ba, Alhamdulillah” Jin jina kansa ya yi ya ce
“Allah ya jiƙansa da Rahama”
A tare suka ce Ameen, Ya ce“Sai kun dawo” Okay Nayla ta ce sannan ta yiwa motar key dan tuni su Nimra suka yi gaba. Sun fara tafiya Nayla ta ce“Ina ki ka san Yaya Farooq?” Tana wasa da fingers ɗinta ta ce“A asibitin da muka kai Abbana, Lokacin shi ne ya duba mu” Nayla ta ce“Au ho, Allah sarki” Salma bata ce komai ba ta jingina da jikin kujerar motar ta lumshe idanunta tana jin mutuwar Abbanta na dawo mata sabuwa.
****Da sallama ya shiga parlon, Zaune ya sameshi kan sofa idanunsa sanye da glasses yana kallon system ɗin gabansa. Ƙarasawa Zayyad y yi ya zauna gefensa, Rufe system ɗin General ya yi ya mai da idanunsa kan Zayyad ya numfasa kafin ya ce“Sorry for what happened kaji, Raina ne ya ɓaci” Girgiza kai Zayyad ya yi a sanyaye ya ce“No Dad I'm the one suppose to apologize, Sorry for what I did” Dafashi Daddy ya yi yana murmushi ya ce“Ba komai ya shige, Allah ya yi maka albarka” Jin jina kai Zayyad ya yi ya ce“Ameen Daddy, Thank you” envelope ɗin gabansa ya ɗauko ya miƙawa Zayyad yana cewa
“Ga takardun Company ɗin”
Karɓa Zayyad ya yi ya ɗan buɗe sai kuma ya mayar ya rufe ya ce“Tom, Allah ya ƙara girma” Ameen kawai Daddy ya ce, Zayyad ya tashi yana kallonsa ya ce“Sai da safe”
“Okay, Allah ya tashemu lafiya” Daddy ya amsa masa, Juyawa ya yi ya bar ɗakin daddy ya bisa da idanu sai kuma ya girgiza kansa..
Ɗakin Mommah ya shiga, Zaune ya sameta gefen gado tana danna wayarta, Zama ya yi kusa da ita ya ce“Barka da dare Mommah” Ajiye wayar hannunta ta yi ba tare da ta amsa ba ta ce“Zayyad ya ku ka yi da General? Na kira Mami na ce Salma zata koma can sai ta riƙeta” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“No need fa Mommah, Mun yi magana da Daddy, So let bygone be bygone zata ci gaba da zama a gidan nan” wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta ce“To Alhamdulillahi, Halin General ne sai shi” Jin jina kai Zayyad ya yi ya ce“Sai haƙuri, Ina su Naylan suke ne?”
Girgiza kanta ta yi ta ce“Har yanzu basu dawo ba” Tashi ya yi ya ce“Okay bari naje bacci nake ɗan ji” To kawai Mommah ta ce ya juya ya fita.
Bai daɗe da fita ba suka shigo, Mommah ta kalli Nayla ta ce“Amma sai da na ce kar ku yi dare ko Nayla?” kwaɓe fuska ta yi ta ce“Wallahi bamu san dare ya yi ba fa” Harararta Mommah ta yi, Ta kalli Salma ta ce“Kin gaji ko? Tashi ki yi wanka sai ki ci abinci” Toh kawai Salma ta ce dan ta gajin da gaske ta tashi ta fice daga ɗakin.
“Zayyad! Zayyad! Zayyad!”
Motsa ƙafarsa ya yi, Kamar zai yi kuka ya ce
“Mommah ki barni bacci nake ji fa”
Tuntsirewa da dariya ya ji an yi, A firgice ya farka daga baccin da yake, Ya tashi zaune yana ƙarewa ɗakin kallo, Kallon Mommah ya yi wadda ke tsaye kansa sanye da Abaya, Ya langwaɓar da kai ya ce“Mommah ki bar ni na kwanta mana”
Murmushi mai kyau ta yi kafin ta ce
“Baka son ka bi ni in da zan kai ka? Zaka ji daɗi sosai fa”
Shiru ya yi yana kallonta sai kuma ya ce“To ki bari sai gobe mana” Dariya ɗan yi ta ce“Ai ba zai yiwu bane, Kawai kai dai taso” Ta miƙo masa hannunta. Girgiza kansa ya yi sai kuma ya kama hannun, Ɓat ta ɓacema ganinsa, A hankali kuma ya ji kamar wani abu nashiga jikinsa tun daga kansa har zuwa yatsun ƙafarsa, Ya saki wata irin razananniyar ƙara sai kuma ya fashe da dariya. Da gudu Nayla ta shigo ɗakin tana kallonsa ta ce “Lafiya dai Yaya? Ka tsoratani” Wani irin kallo Zayyad ya shiga yi mata sai kuma ya sake tuntsirewa da dariya yana nuna ta da hannunsa.
“Yaya Zayyad! Yaya mene haka wai?”
Bai bata amsa ba, Sai dariya ya ke kamar wani zarrare. Juyawa Nayla ta yi ta fice daga ɗakin, Bata jima ba suka dawo tare da Mommah, Tana ƙarasowa ɗakin taji kamar an soki zuciyarta da wani abu, Ta tsaya cak, Nayla ta kalleta sai kuma ta ce
“Mommah mu je mana”
Toh kawai ta ce sannan tabi bayanta suka shiga bedroom ɗin nasa, Zaune suka sameshi yana wasa da yatsun ƙafarsa, Mommah ta ƙarasa gabansa tana kallonsa ta ce“Zayyad!”
Zabura ya yi ya sauka daga kan gadon yana mata wani irin kallo ya ce
“A'a ni ba zan dawo ba, Ba zan dawo yanzu ba, Wallahi ba zan dawo ba” Daga haka ya nufi waje da gudu, Tashi ta yi cikin tashin hankali tabi bayansa. Sai dai har ya kai main parlon na gidan, Khalil ne yaga yana gudu ya yi saurin tare shi yana cewa
“Yaya lafiya? Ina zaka je?”
Ture shi Zayyad ya shiga yi yana cewa“Ni a'a ku rabu dani ba zan dawo ba” Da mamaki Khalil ke kallonsa Dai dai nan Mommah ta ƙaraso parlon, Hannunsa ta rike ya fincike. Ta shiga jijjigashi tana cewa“Kai lafiyarka? Meya sameka?” Tuntsirewa da dariya Zayyad ya yi ya kwace hannunsa daga rikon da Khalil ya yi masa ya zauna nan kan tiles yana nuna Momma yana wata irin dariya, Hayaniyar da suka ji ya sanya suka fito, Daddy ya ƙaraso parlon yana kallon Zayyad dake wata irin dariya har sannan. Mommah na ganinsa ta ƙarasa gabansa ta rike shi tana cewa
“General duba meya samu Zayyad? Ka ga bai san me yake ba wallahi”
Da mamaki Daddy ya ƙarasa gabansa, Ya dafashi.
“Kai naga kana dariya...kai ɗan yaron nan, Meke damunka na baka maganiiii, Ka sha paracetamol...”
Zayyad ya dinga maganar yana taɓa Daddy, Sosai gaban Daddy ya fadi ya ɗago idanunsa yana kallon kowa dake parlon. Mai da kansa ya yi yana kallon Zayyad ya ce
“Kai mene ne haka? Tashi ka je ka kwanta”
Ture shi Zayyad ya yi kawai suka ga ya fashe da kuka, Salma da fitowarta kenan ta ƙaraso in da yake da gudu, Tsugunawa ta yi gabansa tana kallonsa ta ce
“Me aka yi maka Yaya Zayyad? Mene ne?”
“Ita ce! Ita ce ta haukatashi! Wallahi ita ta haukatashi!”
Mommah ta fadi maganar tana nuna Salma da yatsa, Ɗagowa Salma ta yi ta kalleta da mamaki dan bata gane in da maganar tata ta dosa ba, Mommy ta tafa hannayenta tana cewa
“Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una, Mun shiga uku, Ta haukata yaron mutane, Zayyad! Zayyad!”
Daddy kallon Salma ya yi sai kuma ya shaƙe wuyanta kamar zai rabata da ranta ya ke cewa
“Ke me ya yi miki haka? Daga taimako? Akan me za ki haukatashi?”
Salma ta dake jin nunfashinta na ƙoƙarin barin gangar jikinta ta shiga girgiza kanta, Magana take son yi amma irin riƙon da Daddy ya yi mata ya hanata, Da gudu Nayla ta ƙaraso wajen tana ƙoƙarin janye hannun Daddy ta ce
“A'a Daddy na rantse ba ita ba ce, Salma ba ita ba ce, Babu abin da ta yiwa Yaya Zayyad dan girman Allah kar ka kasheta”
Hankaɗeta Daddy ya yi, Mommy ta ƙaraso wajen tana kallonsa ta ce“General cikata kaga” Wurgi ya yi da Salma, Ta faɗi kan tiles, Ta saki wani irin ihu mara sauti tana riƙe wuyanta. Kallonsa Mommy ta yi ta ce“Za'a tambayi Zayyad idan har ita ce to tabbas zai faɗa” Mommah na kuka ta ce“Ai wallahi ma ita ce! Ita ce ta haukatashi” Girgiza kai Mommy ta yi ta ce“Idan ita ce zai faɗa da kansa, Sannan kuma dole su bar gidan nan daga ita har shi”
Girgiza kai Nayla ta yi ta ce“A'a Mommy, wallahi Babu in da zasu je!” Wani wawan mari Mommah ta sauke mata, Tana kallonta ta ce“Idan na sake jin bakinki anan sai na tsine miki albarka” Rufe baki Nayla ta shiga yi tana girgiza kanta wasu zafafan hawaye na zubowa kan fuskarta. Sunkuya Mommy ta yi gaban Zayyad ta dafashi a nutse ta ce
“Kai ka san wane ya yi maka wannan abun? Wane ya aiko ku jikinsa?”
Tuntsirewa da dariya Zayyad ya yi yana girgiza kansa, Mommy ta haɗe rai kafin ta ce
“Ko ku faɗa ko na kashe shi tare da ku"
Langwaɓar da kai ya yi kamar zai yi kuka ya ce“A'a kar ki mana haka zamu faɗa wallahi” Jinjina kai Mommy ta yi ta ce“Ku faɗa a gidan nan wane ya aika ku jikinsa?” Hannunsa na rawa ya nuna inda Salma take a tsawa ce ya ce
“Ita ce! Ita ce ta sakamu” Sai kuma ya fashe da kuka. Ɗora hannu aka Salma ta yi ta shiga girgiza kanta dan ko kalma ɗaya ta gagara fita daga bakinta. Nayla da Mufeeda suman tsaye suka yi a wajen, Mommah ta yi wani irin kukan kura ta cafki Salma ta shiga dukanta ko ta ina. Mommy ce ta janyeta ta ce“Khadijah!" tsam Mommah ta bari ta ja baya tana huci, Mai da idanunta kan Zayyad ta yi ta ce“Yanzu sai ku bar gidan nan” To kawai ya ce sannan ya tashi har sannan yana dariya, Ƙarasawa inda Salma ta ke ya yi bai yi wata wata ba ya saɓeta kamar kaya ya ɗorata a wuyansa. Duk irin ihun da take bai sa ya sauketa ba, Sai dariya yake yana cewa
“Ashe ma bata da nauyi, kilo 3 ce wannan za ki sha paracetamol....” Ya sheƙe da dariya, Matsa masa hanya Mommy ta yi ta ce“Kuma koda wasa kar ku sake dawowa gidan nan” Gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin
“Eh...Eh... Ba zamu dawo ba, Zan kai ta tasha paracetamol....” Daga haka ya fice daga parlon da gudu, Nayla ta yanke jiki ta faɗi haka ma Mommah, Ko da Zayyad ya fita compound ɗin gidan sojoji ƙin barinsa suka yi, Ya fashe da kuka har sannan Salma na kafaɗarsa ya ce“Ni ku bar mu mu tafiyarmu...” Daddy ne ya fito yana kallon su ya ce“Leave him" Juyowa Zayyad ya yi ya jin jina masa kai ya ce“Sai da kai Oga...” Sannan ya yi waje a guje...
_Akwai waɗanda suka haukace, ba saboda rashin hankali ba, amma saboda duniya ta kore su da gaskiyarsu. Akwai waɗanda suka zamo duhu, ba don ba su da haske ba, amma saboda rayuwa ta yanke igiyar da ke riƙe da su. Kuma akwai waɗanda suka ci gaba da rayuwa, amma kowace rana cikin damuwa suke, suna ɗauke da abin da ba zai taɓa faɗuwa a baki ba._
_Kaddara ba ta tambayar shirinka. Sharri ba ya jira shiryawarka. Suna zuwa ne lokacin da zuciya ke jin daɗi, sai su kwashe komai su ce maka: “Daga yau, ba kai ne ba.”_
To wa zai tsaya ya gyara gaskiya idan kowa yana jin tsoron shaidar ta?
*Shin mene ne gaskiyar al'amari?*
*Wane Zayyad? Wa ce Salma?*
*Wace ƙaddara ce ta haɗa su?*
*Wane zai zama HASKE a CiKIN wannan Duhun?*
*Ina dangin Salma suke?*
*Wane ya haukata Zayyad?*
*Shin zai samu lafiya ko kuma shikenan zai ci gaba da zama a mahaukaci?*
*Wace irin rayuwa zasu yi bayan barin su gida*
*Wane General Idris B. Musa?*
*Duka zaku samu amsoshin tambayoyinku a cikin ci gaban littafin nan na HASKEN CIKIN DUHU, Wanda yake na kuɗi akan Naira ₦700 kacal, Payment via 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay sai shaida ta wannan numbern 08106608363, Nanameera.*
_Ki biya ki karanta cikin aminci✌️😍_
# HCD
# Light within the darkness
# Last free pages
# Nanameera
08106608363.
Rate me.
*HASKEN CIKIN DUHU*