← Book details Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 28

Chapter 08: Strings Attached

Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

Nanameera, YOTA/023.


Dafe ƙirji Salma tayi ta nufi ɗakin Baban nata da gudu, zaune ta sameshi, idanunsa a rufe sai gumi ne ke keto masa duk da ba lokacin zafi bane, durƙushewa tayi akan gwiwoyinta hawaye na zuba daga kan fuskanta, da gaske tsutsotsine a ƙafar Babanta, ɗora hannunta tayi aka ta fasa wani razanannen ihu, Umma dake tsaye kansu ta ƙaraso tana kuka itama ta ce“Mun shiga uku Salma, meya sami Babanki?” tashi Salma tayi tana cewa“Umma bari na kirawo mai gyara ya duba masa” daga haka tayi hanyar waje, da gudu Umma ta bita ta riƙo hannunta tana cewa“Ina zaki je a daren nan? Sai dai koma menene mu bar wa safiya ai” fashewa da kuka Salma tayi tana girgiza kanta, Umma bata ce komai ba ta kama hannunta suka koma ɗakin, agefen mahaifinta ta zauna tana gursheƙan kuka, Malam Habu wanda yake jin wata irin azaba na ratsa shi ya shafa kanta alamar rarrashi, ɗago kanta tayi ta kalleshi taga yanda idanunsa suka yi wani irin jaa sun kuma kumbura, cikin kuka ta ce“Abba kayi haƙuri, laifina ne, Ban samo kuɗi da wuri mun kai ka asibiti ba, Kayi haƙuri Abba...” Ta ƙare maganar tana riƙe hannunsa, girgiza kai kawai Malam Habu ya yi dan ya garara furta koda kalma ɗaya, Umma ta zuba uban tagumi tana tunanin abin da zasu yi gobe. Suna nan zaune dashi har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba, Salma ta tashi tana kallon Ummar ta ce“Yanzu sun fito sallahr asuba Umma, bari naje na tawo dashi” Bata jira cewar Ummar ba kuma tayi waje da sauri. Buɗe ƙofar gidan nasu tayi tafara tafiya, Babu wasu mutane a hanya sai dai ɗaiɗaiku masu zuwa masallaci, a haka har ta ƙarasa ƙofar gidan Malam Audi mai gyaran. Tsayawa tayi tana ɗan tunani sai kuma ta kwankwasa ƙofar, sai bayan mintuna biyar sannan aka zo aka buɗe, matar ta kalleta da mamaki, Salma ta ɗan sunkuya ta ce“Ina kwana” “Lafiya klao wacece?” a ɗan rabe Salma ta ce“U... Daman Abbana ne wanda Babansu Lawan ya yi masa gyaran karaya ƙafar take ciwo, to shine nazo na kira shi yaje ya gani, ƙafar Tsutsa take” shiru Matar tayi tana kallon Salma can kuma ta ce“Allah Sarki Allah ya bashi lafiya, Malam yaje Masallacin gangare, sai dai ko ki je can ki neme shi” Toh kawai Salma ta ce sannan ta juya ta bar ƙofar gidan tana tafiya da sauri da sauri. Da sauri ta tashi daga kan dakalin data zauna ganin an fara fitowa daga masallacin, hangoshi ta yi yana tawowa ta yi saurin ƙarasawa gabansa tana kallonsa. Da mamaki yake kallonta kafin ya ce“Lafiya Ummusalma?” Salma ta ce“daman Abbana ne bashi da lafiya, ƙafarsa tana ciwo har tsutsa take” ta ƙare maganar tana hawaye, cikin tashin hankali ya ce“Subhanallahi, muje nagani” daga haka ya yi gaba tana bin sa a baya.


Girgiza kai ya yi bayan ya gama kallon ƙafar Abban, ya kalli Salma wadda ke tsugune gefe tana hawaye, sannan ya kalli Umma wadda ke tsaye hannunta riƙe da kofi, jin bai ce komai ya sanya Salma ta ce“Meya samu Abbana?” numfasawa ya yi kafin ya ce“Ɗorin da aka masa ne ya goce kuma ba a lura ba ballantana a sake ɗora shi, yanzu sai dai a kai shi asibiti” ɗora hannu aka Umma ta yi ta shiga girgiza kanta tana cewa“Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una, mun shiga uku” tashi Salma ta yi ta riƙe hannunta tana kukan ita ma ta ce“Ki yi haƙuri Umma, Allah zai bashi lafiya, zamu kai shi asibitin” janye hannunta ta yi ta koma bakin ƙofa tana sake rusa ihu, to yanzu ina za su sami wani kuɗin kai shi asibiti??.


****
4:35pm.

Murmushi Mami ta yi tana ci gaba da yanka lettuce ɗin gabanta ta ce“To me za ki je yi a Orange market ɗin?” Nayla dake tsaye gefenta tana ɓare maggi ta ce“Lemon nan nakeson na siyo Mami” Mami ta ce“Okay, ki bari ko zuwa gobe idan Allah ya kai mu sai muje tare” murmushi Nayla ta yi ta ce“Yawwa Maminmu, shiyasa nake sonki wlh” girgiza kai kawai Mami ta yi tana murmushi. Turo ƙofar kitchen ɗin ya yi ya shigo yana kallonsu, Nayla ce ta juya ta kalleshi sai kuma ta ce“Masoyi ina zaka je haka?” girgiza kansa ya yi kafin ya ce“Zo ki ji” daga haka ya fice daga kitchen ɗin, ajiye ledar maggin ta yi dan daman ta gama ɓarewa, ta wanke hannunta jikin sink sannan ta fita, Mami ta bi su da idanu. Zaune ta same shi kan sofa yana danna wayarsa, ta zauna gefensa tana murmushi ta ce“What's going up Masoyi?” ajiye wayar ya yi kafin ya ce“unguwa nake son ki rakani” shiru ta yi tana kallonsa kafin ta ce“Ina zamu je?”


“Idan ba zaki rakani ba shikenan tashi” langwaɓar da kanta tayi ta ce“kuma sai na ce ba zan raka ka ba masoyi? Lemme take shower” murmushi ya yi ya ce“To agwagwa je ki yi” murmushin itama ta yi sannan ta tashi daga wajen ta nufi hanyar upstairs.


Asokoro, Abuja.

Tunda Daddy ya fara magana Zayyad ke kallonsa, ganin irin kallon da yake masa ya sanya Daddy cewa


“anything wrong Zayyad?”


Girgiza kai kawai ya yi yana danna wayarsa ya ce


“Nothing Dad, ina jin ka”


Gyaɗa kai Daddy ya yi sannan ya ci gaba da fad'in


“As i said before, kaga muna da kyakkyawar alaƙa da General Kabeer, kuma na san shi, na san halinsa, bashi da matsala, na tabbata Family nasa ma basu da matsala. Inason ka je ka nemi yarinyar Zayyad, ka gani idan ta yi maka sai a san abin yi, amma idan har ka ga bata maka ba to ba za'a takura maka ba, ka daure ka je ka ji son” numfasawa ya yi kafin ya ce“Don't worry Dad, I'll.” murmushi Daddy ya yi ya ce“that's why u're always been my favorite” murmushin shima ya yi ya ce“Tanc you Daddy” daga haka ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin barin parlon ya ce“In sha Allah gobe zan je kamar yanda ka buƙata” jinjina kai Daddy ya yi ya ce“Allah ya kai mu, when u're free inason ka yi magana da wannan yaron Farooq, cause ba zan iya tsayawa ina magana dashi ba” okay kawai Zayyad ya ce sannan ya fice daga parlon. Kai tsaye apartment ɗin Mommah ya nufa, ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama wadda ba lallai bane mutanen dake cikin parlon su ji. Zaune ya hangeta kan kujera tana danna wayarta hankali kwance, ya ƙarasa ciki yana kallonta kafin ya ce


“Kee!”

A ɗan firgice ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta, ya zabga mata harara kafin ya ce“Karki kuskura ki kai dare a cikin gidan nan, ki tattara duk abin da ki ka san kin zo dashi ki koma gidanki or else...” ya ƙare maganar yana mata wani irin kallo, bai kuma saurari abin da zata ce ba ya yi hanyar bedroom ɗin Mommah. Da kallo Nimrah ta bi shi kafin ta fashe da kuka, akan me zai ce mata ta koma? Tashi tayi ta ɗauki wayarta ta fice daga parlon ta nufi ƙasa wajen Mommy.


Kamar zai yi kuka ya ce“Yanzu kuma abin da za ku dinga yimin kenan? Dad ya ce naje naga yar gidan general, kuma yanzu Mommah ki ce wai mu daidaita da Fatiha? Wannan yar ƙaramar yarinyar, sa'ar Nayla ce fa Mommah” da mamaki Mommah ta kalleshi sai kuma ta ce“When ku ka yi magana da Dad ɗin ka?”


“Yanzun fa”


Taɓe baki ta yi ta ce“anyway, dan ka je ganin wadda ya ce hakan ba zai hana nima ka ji maganata ba, ni bana son auren ya'yan abokan nan a zo ana faɗa ce faɗa ce irin na Nimra, Amma nasan Fatiha sosai, yar yayata ce fa”


“But Mommah...”


Katse shi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu tana ci gaba da jera kayanta da aka kawo daga wajen guga a press ta ce“Ni fa nagama magana, sai dai idan kana son nuna min iyakata ne” Zayyad ya bita da kallo kawai ganin yanda ta ɗaure fuska kamar ba ita ba, duk abin sa baya son ɓatawa Mommah rai hakan ya sa ya miƙe tsaye yana kallonta ya ce“Shikenan Mommah, I'll” ba tare da ta kalleshi ba ta ce


“Allah yasa”


“But Mommah smile man” ya ƙare maganar yana ɗan murmushi. Kallonsa ta yi tana harararsa ta ce“As if kana son ganin ina murmushin” waro idanu ya yi ya ce“Mommah idan ban so murmushin ki ba nawa zan so?” taɓe baki ta yi ta ce“Ni tafi ka bani guri ban son daɗin baki” ya sha kansa ya yi yana cewa“Amma Mommah yunwa nake ji, yau baki bani abinci ba, gaba ɗaya kin daina son ɗan ki” kallonsa ta yi ganin yanda ya marairaice fuska ya sanya ta yi murmushi ta ce“Shikenan, mu je parlon na baka” juyawa ya yi ya fita ta ƙarasa rufe press ɗin sannan ta fito. Bai ga Nimrah a parlon ba, ya kalli Mommah wadda ta yi hanyar kitchen ya ce“Kar na dawo na tadda yarinyar nan a gidan nan Mommah, wallahi zan ɓata mata rai” Mommah ta ce“Zayyad ka mata magana da kanka, Nimrah bata ji, narasa in da take koyan halayen nan, ko me za'a faɗa mata ba zata yi ba” kwafa ya yi ya ce“Ina zuwa” daga haka ya nufi hanyar fita daga parlon


“Abincin fa?”


“Idan na dawo zan ci Mommah”


****

Ajiyar zuciya Farooq ya sauke yana kallon Zayyad ya ce“Ni ban san yanda zan faɗa maka ba wlh, i can't explain it, Nimrah bata son zama dani Zayyad, Ni ban isa na faɗa mata magana ta ji ba, idan ban yi sa'a ba sai ta haɗa min da masifa, she's always shouting, ban san yaushe ta zama haka ba. Saboda na kawo ƙarshen waɗannan matsalolin nace zan sake aure, amma idan kaga irin abin da Nimra ta yimin sai ta baka mamaki, can u imagine har system ɗina ta fasa min? Na tabbata da ta samu dama sai ta iya dukana, sannan ta sanya ƙafa ta fito without my consent, daman wannan abu ne wanda ta saba yi, ba zan san zata fita ba ba zan san dawowarta ba, ya za'a yi rayuwa ta ci gaba da tafiya a haka?” Zayyad dake zaune kusa da shi idanunsa maƙale cikin wasu shade glasses ya jin jina kansa ya ce“Daman shiyasa na neme ka, inason na san inda matsalar take. Karka damu, an jima Nimrah zata dawo nd duk abin da ta sake yi maka just tell me. And one thing kar ka fasa ƙara aure, ka samu wata ka aura” murmushin jin daɗi Farooq ya yi ya ce“Tom na gode sosai Allah ya ƙara girma” Zayyad ya miƙe yana ɗaukan car key ɗinsa ya ce“Shikenan see you later” Farooq ya bashi hannu suka gaisa kafin ya bar transcorp ɗin. Tun da ya fito yake kallonta har ya ƙaraso inda ya yi parking Lexus ɗinsa, sanye take da wata riga wadda ta tsaya iya gwuiwarta gashin kanta a buɗe ta gyara shi, fuskarta ta ci ka da kwalliya, kwata kwata bata gansa ba, dan hankalinta yana wajen ƙawayenta wadanda suma suka ci uwar kwalliya, taɓe baki Zayyad ya yi ya shige motarsa ba tare da ya kulata ba, ya daɗe a motar kafin ya yi mata key ya bar wajen. Ana kiraye-kirayen sallar magriba ya shigo gidan, zaune ya same su duk a parlon suna hira, kallo ɗaya ya yi musu ya mai da hankalinsa kan Nimra wadda tana ganinsa ta sake riƙe Mommy, a fusace ya ce“ke zo nan” kallon Mommy ta yi sai kuma ta kalli Mommah ganin ba ma ita take kallo ba. Tashi tayi ta ƙarasa in da yake tsaye, Zayyad ya ƙare mata kallo kafin ya ce


“Wato ke baki da hankali ko? Ke mahaukaciya ko? Yaushe ki ka koyi irin wannan halin na dabbobi? Yaushe ki ka lalace har haka Nimrah? Who's behind all of this? Who changed you? Da suwa ki ke mu'amala? Me ki ka ɗauki aure! Tell me!”


Tuni hawaye suka fara wanke mata fuska cikin kuka ta ce“Yaya cewa fa yake zai ƙara aure, na rantse da Allah in dai ina numfashi Farooq bai isa ya auri wata ba idan ba haka ba wallahi tallahi sai na...”


Ta ji saukar maruka har biyu a both checks nata, suman tsaye Nimrah ta yi, tun da uwarta ta haifeta ba'a taɓa mata irin wannan dukan ba, infact ma bata san mene ne duka ba. Da dafe kuncinta tana sauke ajiyar zuciya dan kukan ma ya gagareta, shiru Parlon ya ɗauka ganin yanda idanun Zayyad suka kaɗa, yana dadewa bai yi faɗa irin haka ba, ana dadewa bai shiga sabgar shirmen ya'yan gidan ba. Ya gyara tsaiwarsa yana ci gaba da kallonta ya ce


“And this is the first nd the last warning da zan yi miki, ki koma gidan mijinki kuma ki zauna lafiya, tun da ba wani ya ce ki yarda ki aure shin ba, ba dole aka miki ba! Duk ranar dana sake jin kin dawo gidan nan saboda wai wani abun ya haɗaku wallahi sai kin gane baki da wayo, sai kin san wane Zayyad! Shashasha kawai mara hankali”


Ya juya ya fice daga parlon kamar zai tashi sama. Sai da ta ga ya fita sannan ta zube a ƙasa ta fasa ihu tana sake shafa check ɗinta ko ya fashe. Mommy ce ta taso ta zo inda take ta kamo hannunta cikin rarrashi ta ce“Ya isa haka Nimra, tashi” Sake fashewa tayi da kukan ta rungume Mommy tana cewa


“Mommy ba'a sona a gidan nan, ki kalla fa Yaya marina ya yi a kan Farooq, he slapped mommy, kuma ya ce sai na koma gidan Farooq, wayyo Allahna, ni wlh gara na mutu” Mommah ce ta taso tana kallonta ta ce“Tashi ki shige ki shirya! Kar ki bari na sake miki magana, idan kin so ki bari ya dawo ya tarar dake a gidan nan” daga haka ya yi hanyar upstairs kamar zata tashi sama, da idanu Mommy ta bita sai kuma ta kama hannun Nimra ta ce“tashi mu je kin ji” Nimra ta mike tsaye har sannan hannayenta na kan fuskarta tana kuka.


Mararaba, Nassarawa.


Tafiya take a hankali tana ɗan shassheƙar kuka, idanunta har sun gaji da kumburi saboda irin kukan da ta yi, maganganun likitan ne suka shiga dawo mata daya bayan ɗaya


“Tabbas sai dai a yanke ƙafarsa, domin gaba ɗaya ta riga da ta ruɓe, wannan shine dalilin daya sanye ake cewa a kawo mutum asibiti idan karaya ta same shi. Dole yanzu sai an yi masa aiki, sannan domin yin wannan aikin ana buƙatar kuɗi kimanin Naira dubu ɗari huɗu, zaku je ku biya zuwa gobe in sha Allah za'a yi masa aikin, idan ba haka ba gaba ɗaya ƙafar zata ruɓe ne”


Salma ta ja dogon numfashi, bata san sanda ta zauna gefen titin ba ta kifa kanta tana sake rushewa da kuka, a ina zasu sami waɗannan kuɗaɗe? Ko dubu hamshi basu da ita ballantana wadannan kudaden da tun da take a rayuwarta bata taɓa ganinsu ba. Ta ina zata fara? Ya za'a yi ta bar Abbanta a haka?. Waɗannan tunanin sune suka sanya ta kasa daina kuka tun safe take yawo daga nan taje nan, babu inda bata zaga ya ba daga Orange market zuwa cikin Kabayi ba tare da tasan inda ta nufa ba, yunwa, ƙishiwa, gajiya duk sun haɗe mata, she wish a ce ita ce wadda ƙafarta ta samu matsala ba Abbanta ba, ina ma ranar bai fita ba, ina ma ranar bata zo ba, sai dai ƙaddara ta riga fata, tana nan zaune har wajejen ƙarfe 11 na dare, sahun mutane ya fara ɗaukewa, daman tun mutanen kasuwar Orange market kowa ya kama gabansa, kasa ci-gaba da zaman tayi hakan yasa ta kwanta a wajen tana cure jikinta waje guda, duk sanyi da kumar raɓar damunar data gama sauka a wajen. Around 11:43 na daren wata mota ta yi parking daidai gabanta, hasken da taji an dallareta dashi ya sanya ta runtse idanunta ta sanya hannunta ta rufe fuskarta, mutumin dake cikin motar ya ƙura mata idanu, a ransa ya ce


“what a beautiful girl” a fili kuma ya yi murmushi ya kashe motar ya sakko ƙasa. Karasowa gabanta ya yi ya tsuguna dai dai tsayinta, numfashin mutum da taji kusa da ita sosai ya sanya ta buɗe idanun, zabura ta yi sai kuma ta yi baya tana girgiza kanta, daga gani a tsorace take. Ɗan murmushi mutumin ya yi a ƙalla zai kai shekaru kusan 40 ya ce a nutse


“Nutsu kin ji yarinya, ba cutar da ke zan yi ba”


Salma kallonsa kawai take, ƙoƙarin tashi take sai dai yunwar da take ji ta hanata yin kwakwaran motsi, ya tashi tsaye har sannan idanunsa akanta ya ce


“Me ki ke yi cikin daren nan?”


A sanyaye ta ce


“Abbana ne yake asibiti shi ne aka ce na je na samo kuɗin da za'a yi masa aiki, shi ne Ummana ta ce na je na samo” ta kare maganar tana shassheƙar kuka, ɗan murmushi ya yi kafin ya ce


“Allah sarki, shikenan zo mu je sai na baki kuɗin” shiru Salma ta yi tana kallonsa sai kuma ta girgiza kanta ta ce


“A'a ni”


Hannunsa ya sanya a aljihu ya zaro wata id card ya ce


“I'm Barrister Tareek Mohd, ki yarda dani ba zan cutar dake ba” Salma kallonsa kawai ta yi, a lokacin bata da wata buƙata wadda ta shige ta samo kuɗin da za'a yi wa Abbanta aiki, hakan ya sa ta gyaɗa masa kai a hankali ta ce


“Duka zaka bani kuɗin?”


Ta yi maganar cike da yarinta, murmushi ya yi ya ce


“Har ma na ƙara miki wani kin ji” tashi tayi a hankali ta ƙaraso inda yake tsaye ta ce“To sai ka dawo dani?” nan ma ya gyaɗa mata kai, jin jina kanta ta yi ta ce“To mu je ka bani” ajiyar zuciya ya sauke sai kuma ya buɗe mata back seat yana kallonta ya ce“Zauna” ta sake duban cikin motar kafin ta shiga ta zauna tana kallonsa, rufewa ya yi ya buɗe driver seat ya shiga ya tada motar da wani irin Speed ya bar wajen..


# HCD
# Nanameera
08106608363.

https://chat.whatsapp.com/GSEDyyyzuMm3woohSiin9W?mode=ac_t


HASKEN CIKIN DUHU
Chapter 8 · 0% Book details