← Book details Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 23 OF 28

Chapter 29-30: In his absence

Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 16 min read

Nanameera, YOTA/23.


Mutumin da take iƙirari da boka ya bushe da wata dariyar mugunta, Ya kalli gefensa na hagu ya yi shiru can kuma ya yi gyaran murya yana kallonta ya ce“Ki ɗauka duk abin da ki ka nema an yi miki, Zaki sha mamakin abin da zai faru, Zaki yi dariya, Zaki ji daɗi...”


Jinjina kanta ta yi cike da jin daɗi ta ce“Nagode boka, Allah ya ƙara maka tsawon rai ya baka abin da ka ke buƙata, Allah ya...”


Wata razananniyar tsawa ya daka mata wadda ta sanya ta firgita, Ya haɗe mummunar fuskarsa mai ban tsoro kamar bai taɓa dariya ba ya ce“Kar ki sake kira mana Allah a nan, Muke yi ba Allah ba!”


Cike da gamsuwa ta gyaɗa kanta ta ce“Wannan haka yake, Ku ne masu taimakonmu”


Bokan ya sheƙe da wata dariya yana busa ƙahon hannunsa.


****
Washegari da safe Mommah ta shigo parlon, Zaune ta sami general kan sofa yana danna system ɗin gabansa, Sauke numfashi ta yi sannan ta ƙarasa ta zauna gefensa, Ɗago idanunsa wanda suka nuna zallar gajiya ya yi ya zuba mata yana kallonta, Mommah ta kalleshi sosai sai kuma ta ce


“Yallabai baka samun bacci ji idanunka, Kar fa wani ciwon ya sameka”


Lumshe idanu General ya yi ya buɗe sannan ya ce“Ya zan yi Khadijah? Bana iya baccin ne, Gaba ɗaya bana jin daɗi, Idan na rufe idanuna Zayyad nake gani, Tunaninsa ya hana ƙwaƙwalwata samun nutsuwa, Ba zan taɓa daina damuwa ba sai ranar dana sake saka shi cikin idanuna”


Mommah ta sauke numfashi tana jin damuwar na sake dawo mata sabuwa, a hankali ta ce“Ka yi haƙuri Yallaɓai, ni kaina bana iya bacci saboda tunanin Zayyad, ban san inda zamu same shi ba, Ban san halin da yake ciki ba. Ko yana cin abinci ko baya ci, ko yana samun inda zai kwana ko baya samu, hankalina a tashe yake, dan girman Allah General ku sake saka sabon bincike a samu a dawo da Zayyad, dan Allah ka yi haka, Wallahi ina jin kamar zan mutu idan na tuna baya kusa damu, ka taimaka mana dan girman Allah general, dan Allah...”


Rungumeta general ya yi abin da ya daɗe bai yi ba, Ta yi lamo akan ƙirjinsa tana shessheƙar kuka, Shafa kanta ya yi yana sauke numfashi a hankali. Sun ɗauki lokaci a haka har sai da ya ji ta yi shiru sannan ya a nutse ya ce


“shikenan ki kwantar da hankalinki, in sha Allah zan saka a sake sabon bincike, za'a baza securities da police in sha Allah za'a samo shi nan kusa, in dai yana cikin Nigeria to nayi miki alƙawarin dawowa dashi”


Mommah ta jinjina kanta har sannan bata ɗago ba ta ce”Tom Allah ya baka sa'a general”


General ya ce“Ameen”


Mommah ta yi shiru tana jin wani irin abu na yawo cikin ranta, maganganun Zayyad suka dinga dawo mata, yanda yake murmushi da yanda yake son taɓe baki, ranar da zai tafi London tafiyarsa ta farko, ranar ta kasance Monday ya shirya cikin kayansa ƙananu wanda suka masa kyau sosai duk da lokacin akwai yarinta a tare dashi, ya tsaya jikin corridor yana kallonta. Ta sakar masa murmushi ganin yanda ya kwaɓe fuska ta ce“Lafiya dai ɗan rigiman Daddy?” Zayyad ya taɓe bakinsa ya ce“Mommah bana son na tafi na bar ki, ina son ki Momma”


Mommah ta ja kumatunsa tana murmushi ta ce“nima ina son ka ɗan gidan Mommah, zan yi missing ɗinka, ko da zaka fasa zuwa ne?” Girgiza kansa ya yi “Ina son ki Momma, But ina son nayi karatu sosai, Daddy ya ce yana son ya ga na zama doctor” Mommah ta sake murmushi tana gyara masa gashin kansa ta ce“Ai shikenan tun da ka zaɓi karatu, Sai ka je ka zauna kai kaɗai baka ganina”


Daga haka ta sake shi ta juya, Sai da taje kofar ɗakinta sannan ta juyo ta kalleshi, Sosai ya ƙura mata idanu ta gyaɗa masa gira kana ta ce“Mene ne?” da gudu ya tawo ya rungumeta yana cewa


“Mommah bana son na bar ki, nafison kullum na dinga zama kusa da ke. Idan bana ganinki tsoro nake ji Mommah, dan Allah kar ki bar ni Mommah”.


Wani irin kuka ne ya kwace mata, General ya kalleta fuskarsa babu walwala ya ce“Khadijah ba nace zan saka a ci gaba da nemansa ba?” cikin kuka ta ce“Naji Yallaɓai, kawai na tuno shi ne, ranar daya fara tafiya London, Ya ce baya son ya ga baya ganina, Ban taɓa tunanin Zayyad zai yi nisa dani irin wannan ba. Domin a yanzu ban san in da yake, ban san wace irin rayuwa yake ba, Kuma duk wannan laifina ne, I'm the one behind everything”


Girgiza kai General ya yi idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, muryarsa bata fita ya ce“Ki daina cewa haka, Baki da laifi, Ni ne wanda yake da laifi cikin wannan lamarin, ni na jawo duk abin da ya faru. Da ban bar Zayyad ya tafi ba da yanzu haka bata faru ba, Ni ne na saka ya tafi kuma ni zan dawo dashi in sha Allahu”


Daddy ya ƙare maganar cike da ƙarfin gwuiwa.


****

Tsaki Mufeeda ta yi tana kallon Nayla wadda ke yafa mayafin abaya ta ce“To ke wane ya faɗa miki?” Ba tare da ta juyo ba ta ce“Yaya Khalil” Mufeeda ta yi shiru tana kallonta can kuma ta ce“Kuma da gaske yake?” Sai a sannan ta juyo ta zuba mata gajiyyun idanunta kamar zata yi kuka ta ce“Amma kin san ɗakin yaya khalil ai, So kindly go and ask him stop bothering me please” Nayla ta ƙare maganar tana ɗaukan school bag ɗinta, harararta Mufeeda ta yi ta ce“To kar Allah yasa ki faɗa ɗin, Kuma ba zan je na tambayar ba” Ko kallonta Nayla bata yi ba ta nufi hanyar kofa ta fice daga ɗakin, Mufeeda ta bita da wani banzan kallo sai kuma ta yi tsaki.


Koda Nayla ta sakko ƙasa bata samu kowa ba, Ta kalli dining area ɗinsu wanda yake wayam babu kowa saɓanin da, Da akoda yaushe yake so lively, Rabon da a taru a parlon aci abinci tun kafin tafiyar Zayyad. Ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta juya ta nufi ƙofa, Tana ƙoƙarin shiga motarta Khalil ya kira sunanta, Ta fasa bude handle ɗin ta juya tana kallonsa. Sanye yake da sport wear hannunsa riƙe da ƙaton ball, Nayla ta dinga kallonsa har ya ƙaraso gabanta.


“School ɗin za ki tafi?”


Khalil ya tambayeta, Gyaɗa masa kai ta yi dan yanzu ba wani magana take ba, Ya sake cewa“Ko zaki jirani sai na yi dropping ɗin ki daman akwai maganar da nakeson mu yi dake”


Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a Yaya sai dai idan nadawo muyi maganar kai fa baka shirya ba, ni kuma zan iya yin late idan na tsayaka kuma lecturern mu bashi da kirki”


Harararta Khalil ya yi ya ce“To tafin” Daga haka ya juya ya bar wajen, Buga ƙafarta ta yi a ƙasa sannan ta biyo bayansa tana tura baki.


****
Kaduna.
4:30pm
Maryam ta yi murmushi ta ce“To yanzu dai idan kin je kar ki zauna dan Allah” Salma dake tsaye sanye da hijabi ta ce“In sha Allah Auntie, Ina amso maganin zan dawo gida” Maryam ta ce“Kamar gaske ba, Kar ki zauna hira wajen Umma dan Allah kin ga dai jiranki nake” Toh kawai ta ce sannan ta fice daga parlon. Zaune ta hangeshi gefen flower ya yi shiru, Ta ƙarasa tana kallonsa ta ce“Yaya Yad” Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya ɗauke kai, Salma ta yi murmushi ta ce“Au ba zaka kulani ba?” Shiru ya yi mata, Ta rausayar da kanta kamar abin tausayi ta ce


“Shikenan na tafi na bar ka ba zan sake dawowa ba” Daga haka ta nufi gate shi kuma ya bita da idanu.


Ganin babu mai Napep a layin ya sanya ta yanke shawarar zuwa titi tafara tafiya a hankali kanta a ƙasa, Har ta kai bakin titi bata haɗu da Napep ɗin ba, Ta tsaida wani ta ce unguwar rigasa zai kai ta, Ya amsa sannan ta shiga, Juyowar da zata yi ta ga Zayyad yana ƙoƙarin shigowa shima. Da mamaki ta kalleshi sai kuma ta ce


“Kai meyasa ka biyoni?”


Ko kallonta bai yi ba ballantana ya bata amsa, Mai Napep ɗin ya ce“Hajiya tare ku ke ne?” gyaɗa masa kai ta yi ya sake cewa“To kuɗinki ɗari biyu da hamsim” Toh kawai Salma ta ce sannan ya ja napep ɗin suka fara tafiya. Har suka je unguwar Zayyad bai ce ƙala ba duk yanda ta dinga masa hira, Wata maganar idan ta yi ya kalleta wata kuma ko arzikin kallon bata samu. Bayan sun sauka daga Napep ɗin ta kalleshi ta ce“Yanzu daka biyoni na biya maka kuɗin mota da me zamu koma gida?” Kallonta kawai ya yi sai kuma ya ɗauke kansa, Ta haɗe rai ta ce


“Baka ji na ne?”


Yanda ta yi maganar cike da tsiwa ya sanya ya juyo ya sake kallonta, Bata yi aune ba kawai ta ga ya ɗauketa sama ya fara tafiya da ita, Zabura ta yi duk da layin ba mutane sosai ta dinga cewa ya sauketa amma ya yi mata banza. Har dukansa ta dinga yi tana mintsininsa amma kamar ba shi takewa ba, Bai sauketa ba sai da suka je kofar gidan Malam, Yana zaune kan tabarmarsa sai wasu maza guda biyu. Da mamaki ya dinga kallonsu Salma kuwa fashewa ta yi da kuka, Malam ya kalleta bayan ta zauna ya ce“Lafiya dai Ummusalma? Mene ne ya sanya ya ɗauko ki?”


Cikin shassheƙar kuka ta ce“Malam baya jin magana shi, Kawai dan nace meyasa ya biyoni shi ne ya ɗaukeni yana tafiya dani Na ce masa kuma ya daina min irin haka” Malam ya Girgiza kansa sai kuma ya mayar da idanunsa kan Zayyad wanda ke tsaye har sannan a sanyaye ya ce


“Babban mutum zo ka zauna mana, Muhammadu mai babban suna”


Kallonsa Zayyad ya yi sai kuma ya ƙaraso ya zauna gefen tabarmar ya juya musu baya, Malam ya Girgiza kansa kawai ya kalli Salma ya ce“Ki daina yi masa magana idan ki ka ga yana irin haka kin ji” Tom kawai ta ce, Malam ya sake cewa“Rubutun ki ka zo karɓa?” Gyaɗa masa kai ta yi kana ta ce“Eh Auntie ta ce ka gama”


“Eh na gama, Ki shiga ciki wajen Ralma ki amsa” Tom kawai ta ce sannan ta tashi ta shige gidan, Zayyad ya dinga bin ta da idanu. Koda ta shiga gidan bata wani daɗe ba ta amso rubutun ta fito, Zaune ta sameshi daga shi sai Malam yana masa karatu, Dan haka kawai ta nemi gefe ɗaya ta zauna tana jiransu. Sai da ya gama tsaf sannan ya kalleta ya ce“Kin karbo?” gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh na karbo Baba” Ya ce“Tom shikenan a tabbatar yana sha kuma ana yi masa turaren, Ki gaishe da Maryam ɗin”


“Tom Baba an gode Allah ya saka da Alkhairi zasu ji”


Daga haka ta mike tsaye tana kallon Zayyad ta ce“Ka taso mu tafi to" Babu musu ya mike ya zura takalmansa ta sake yiwa Malam Sallama sannan suka bar kofar gida.


Around 5:40pm suka shigo gidan saboda yanda ya dinga sakata magana a hanya, Ta shige ɗakinsa ita kuma ta yi cikin gidan. Zaune ta sami Maryam tana danna wayarta, Tana ganinta ta ajiye wayar tana cewa“Ai nace na ɗauka sai gobe zaki dawo” Dariya Salma ta yi ta ce”Kai Auntie gobe kuma, Ai ba mu daɗe ba, Umma nata yi mimi hira fa haka na taso dan naji kin ce kar ta dafa”


Maryam ta taɓe baki ta ce“Haka fa, Ina Zayyad ɗin?”


“Ya shiga ɗakinsa, Ni wallahi kar ya sake cewa zai bini wani waje" Salma ta ƙare maganar kamar zata zunduma ihu, Murmushi Maryam ta yi ta ce“Ai na leƙo naga baya nan nace to ke ya bi, Wani abin ya yi miki acan?”


Labari Salma ta bata Maryam ta yi dariya ta ce“Zayyad kenan, maganin ki, Ba ke na cewa ki dinga fita a sabgarsa ba, Amma kin ƙi yarda, Ai gashi nan kina shan wahala a banza”


Marairaice fuska Salma ta yi ta ce“To Auntie ya zan yi dan Allah, Kawai fa gani nayi ya biyoni”


Maryam ta ce“Ba wannan ba, Nasan daman dole zai iya bin ki Amma ki daina kula shi idan ki ka ga ya miki banza sau ɗaya”


Salma ta langwaɓar da kanta ta ce“To kuma sai ya dinga shareni”


“To mene ne dan ya share kin?”


Salma ta kalleta sai kuma ta yi shiru, Maryam ta yi murmushi ta ce“Ko dai akwai wani abun a ranki Salama?” Da sauri ta kalleta sai kuma ta ce “Auntie ban gane ba” harararta Maryam ta yi ta ce“Kin gane abin da nake nufi, Ko dai baki son Zayyad ya daina kula ki?”


Salma sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba, Maryam ta sake cewa“Ba zaki faɗa min ba?”


Muryarta na rawa ta ce“Ni fa babu komai Auntie”


“Tom Allah yasa, Tashi mu ƙarasa aikin nan ya ce ana idar da magriba zasu zo” Tom kawai ta ce sannan ta miƙe tsaye ta zare Hijabin da ke jikinta, Doguwar rigar atampa ce a jikinta ɗinkin A-shape ba mai kama jiki ba. Ta nufi kitchen ɗin bayan ta ajiye ledar rubutun.


Ana kiraye-kirayen sallar magriba ya buɗe gate ɗin ya shigo yana cewa“Bismillah shigo ciki”


Shigowa ya yi bakinsa ɗauke da sallama, Hashim ya mayar da gate ɗin ya rufe yana kallon abokin nasa ya ce“Finally dai ka zo gidana” Murmushi Mukhtar ya yi ya ce“Ai kam dai na huta da mita, ka shigo Kaduna baka ƙaraso gidana ba to yau dai gani” Dariya Hashim ya yi ya ce“Naji ɗin muje ciki”


Sun kai balcony Zayyad ya buɗe kofar ɗakinsa ya fito, Duka suka kalleshi Hashim ya ce“Babban yaya ina zuwa?” Da hannu ya yi masa nuni da waje sannan ya yi gaba, Mukhtar ya sake kallonsa Hashim ya ce“Muje mana” Okay ya ce sannan ya shiga parlon, Babu kowa a cikinsa amma komai na abinci an gama jera shi, Suka zauna Hashim ya fara zuba masa abincin.


Sun ɗan jima suna hira sannan Maryam ta fito suka gaisa, Ta nemi waje ɗaya ta zauna tana danna wayarta, Ana fara kiran sallar isha'i suka tashi kai tsaye kuma masallaci suka nufa, Koda suka dawo Zayyad na zaune jikin bishiya ya yi kamar koda yaushe, Suka kalleshi sai kuma suka shige.


Tunda suka shigo parlon yake bin ta da kallo tamkar idanunsa zasu faɗo, Salma data fito daga kitchen ke tana ƙoƙarin shigewa ta ga irin yanda yake kallonta ya sanya ta ɗan durƙusa murya can ƙasa ta ce


“Ina yini”


Da sauri Mukhtar ya amsa yana murmushi, Ta shige ɗakinta ya ci gaba da bin ta da kallo, Hashim ya ɗan yi murmushi sai kuma ya ce“Yallabai! Yallaɓai!!”


A ɗan firgice Mukhtar ya juyo sai kuma ya ɗan yi dariya yace“Afuwan na tafi tunani ne” Hashim ya jinjina kansa kawai dan ya lura da abin da yake wa.


****

Karfe 8pm ya bar gidan, Hashim ya raka shi sannan ya dawo gida, Zaune ya samu Maryam tana koyawa Khalil karatu, Ya zauna kan kujera yana kallonsu ya ce


“Oh my goodness, wallahi nagaji sosai”


Ɗago kanta ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce“Har ya tafi?”


“Eh mana, ai yau zai koma a Abuja shiyasa”


Hashim ya bata amsa, Gyaɗa kanta ta yi tana mayarwa da Khalil books ɗinsa cikin jaka dan sun gama aikin ta ce“Sai kallon Salma yake kamar ya samu tv” Hashim ya yi murmushi kana ya ce“Kema kin lura ashe”


Miƙawa Khalil jakar ta yi ta nuna masa hanyar bedroom sannan ta ce“Sosaima, Har sai da ya bani haushi ba'a son irin wannan kallon haramun ne” Hashim ya gyaɗa kansa ya ce“Tom Malamata ki yi haƙuri a maimakonsa” Taɓe baki ta yi ta ce“Tun da kai ka yi laifin” Girgiza kansa yayi ya ce“Ai ko bani nayi laifi ba dole ne na bada haƙuri dan kada ran Amminmu guda ya ɓaci”


Murmushin da bata yi niyya bane ya suɓuce mata, Ta kalleshi ta ce“Baka rabo da abin dariya Abu, Yanzu ba wannan ba ni ina son muyi magana da kai” Gyara zamansa ya yi yana kallonta sosai ya ce“Ina jin ki”


“Baka ganin ya kamata akai Salma makaranta, tunda ta gama secondary school ɗinta kawai sai a sama mata takardu ta ci gaba da zuwa University ɗinta kafin muga abin da hali zai yi”


Hashim ya jinjina kansa ya ce“ i think so fa, Ya kamata ta ci gaba da karatu cause she's to small bai kamata a ce karatunta ya yanke daga nan ba, Kuma daga dukkan alamu tana da ƙoƙari”


Maryam ta yi murmushi ta ce“Yawwa hakan ma za'a yi, in sha Allah gobe idan na fita zan iya Malama Rabi magana naji yanda za'a a samar mata takardun”


“Tom shikenan, Allah ya kai mu”


Ameen kawai ta ce sannan ta tashi tana hamma ta ce“Yau bacci nake ji, ni dai da wuri zan kwanta” Tashin shima ya yi ya ce“Nima ai hakan” Ta kalleshi sai kuma ta girgiza kanta bata sake cewa komai ba ta nufi bedroom ɗinta yana biye da ita.


Washegari da yamma Salma ta shirya domin karbo rubutun Zayyad, Har ta fita tsakar gida sai kuma ta dawo ta shige ɗakinta. Jakar da kuɗinta yake ta buɗe ta zari wrapper na yan dubu-dubu sannan ta yi waje, Maryam na kwashe shanya ta kalleta ta ce


“Salma karki dade dan Allah ki dawo da wuri da an gama masa”


To kawai ta ce sannan ta fice daga gidan, Tsaye ta sameshi kan dakali ya yi shiru kamar mai tunani, Ta ƙarasa gabansa tana murmushi ta ce“Yaya Zayyad” ɗago kansa ya yi ta ce“Zo ka rakani” maƙale mata kafada ya yi ta langwaɓar da kanta ta ce“Dan Allah mana, Jiya ba rakani ka yi ba”


“Ba zamu je ba ɗin”


Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Salma ta ce“Zan siya maka abun daɗi ba, har da riga zan siya maka”


Ya kalleta amma bai ce komai ba, Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Da gaske fa nake, Taso ka ji”


Ta mika masa tafin hannunta, Kallon farin hannun nata ya yi sai kuma ya ɗora nasa akan natan ya miƙe tsaye, Ta saki murmushi wanda ya fito da zallar kyanta ta ce“Ko kai fa Yaya Yad”.


****

Maryam na zaune a parlon taji ana bugun ƙofa, Ta tashi ta fito tana cewa waye, Jin ba'a yi magana ba ya sanya ta sake cewa waye, nan ma ba'a ce komai ba. Ta yi tsaki sannan ta ƙarasa ta buɗe kofar tana cewa


“Ana cewa wane kuna jin...”


Cak maganar ta tsaya a maƙogaronta sakamakon sojojin data gani kusan guda goma tsaye a bakin ƙofar, Baya taja da sauri suna danno kai cikin gidan without even ask for a permission. Zagaye gidan suka yi, Wasu a waje wasu kuma a ciki sai a sannan ta gane yawansu yafi yanda take tunani.


Muryarta na rawa ta ce“Yallaɓai lafiya?”


Babu wanda ya kulata a cikinsu, Suka shiga har cikin bedrooms ɗinta suka dudduba, Maryam ta dinga bin su da idanu tana jin gabanta na wani irin faɗuwa dan bata san laifin data aikata ba.


Hashim ne ya dawo hannunsa riƙe da ledar salad wanda daman shi ne ya fitar dashi, Ganin tarin jami'an tsaro a ƙofar gidansa ya sanya ya saki salad ɗin ba tare da ya sani ba, Ya ƙarasa cikin gidan da saurinsa sai dai ya yi turus ganin Maryam tsaye ta rufe fuskarta sojan ya sai ta mata bindiga a saitin kanta yana cewa


“Zaki faɗa ko ba zaki faɗa ba? Ina suke nace!”


Da gudu ya ƙarasa gabansu yana Girgiza kansa ya ce“Yallaɓai su wa ake nema? Mu ba masu laifi bane”


Wani soja ne ya fincikeshi ya durƙusar dashi ƙasa ya dasa masa bindiga a tsakiyar ka ya ce


“Kana motsawa sai na fasa kan ka da bindiga”


Fashewa da kuka Maryam ta yi tana girgiza kanta, Aka buɗe gate ɗin gidan suka shigo, General ne sanye cikin uniform sai kuma General Kabeer abokinsa shi ma sanye da uniform ɗin, Suka dinga bin gidan da kallo kafin general ya ƙaraso inda suke, sara masa suka yi duka, ya jinjina masu kai Sannan ya ƙurawa Hashim idanu..


Da hannu ya yi wa wani soja alama ya sara masa sannan ya juya ya fice ba'a fi 2mins ba suka shigo tare, Zabura Hashim ya yi ya dinga nuna shi da yatsa yana son kiran sunansa amma mamaki ya hana shi, Ya tako har in da suke ya rusunawa general, Murya a dake general ya ce


“Shi ne?”

Gyada masa kai ya yi kana ya ce“Eh Yallaɓai su ne, nan ne gidan”


“Mukhtar!”

Maryam ta faɗa tana zaro idanu waje..

_Book 1 ya kusa karewa and book 2 isn't free it's ₦700 via 7041901078 Hauwa lawan Adamu Opay evidence via 08106608363 Nanameera_

# HCD
# Nanameera
08106608363.

*HASKEN CIKIN DUHU*
Chapter 23 · 0% Book details