← Book details Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 24 OF 28

Chapter 31-32: The price of togetherness

Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read

Nanameera, YOTA/023.


General ya kalleta sai kuma ya mayar da kansa gurin Hashim, Hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarsa muryarsa a dake babu alamar wasa ya ce


“Where are they?”


Girgiza kai Hashim ya yi muryarsa na rawa ya ce“ban san inda suke ba, ban san su wane ku ke magana akai b...”


Maganar ta tsaya cak saboda yanda general ya daki bakinsa da kan bindigar hannunsa, Hashim ya durƙushe yana sakin ƙara, kuka Maryam ta saka tana ɗora hannu aka, General ya gyara tsaiwarsa hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗin jikinsa ya kalli Mukhtar ya ce“Are you sure?” gyaɗa masa kai ya yi ya ce“absolutely sure sir, jiya na gansu cikin gidan nan”


Furzar da iska general ya yi sai kuma ya juya a fusace ya damƙi maƙogaron Hashim fuskarsa a haɗe yana zaro idanu ya ce“Don't ever let me ask you again, Ina suke?”


Hashim da ke numfashi dakyar gumi sai keto masa yake ya sake girgiza kansa a karo na biyu muryarsa bata fita ya ce“ka yarda dani, ban sani ba yallabai”


Sakinsa general ya yi yana jinjina kansa ya ce“Okay, yayi ka yi ƙokari”


Daga haka ya juya yana kallon sojojin da suke tsaye, Da hannu ya yi musu alama dasu tawo dasu sannan ya juya ya fice daga gidan.


Salma ta dinga kallon ƙofar gidan dama wajen unguwar ganin yanda ta zama tamkar ƙaramin barikin sojoji. Ta rufe bakinta da hannunta ganin sanda general ya fito daga gidan, bayan mintunan da basu shige biyu ba sai ga Hashim da Maryam sojoji sun fito dasu, Tuni hawaye suka wanke fuskarta ta juya ta kalli Zayyad wanda tun da suka shigo siririn layin yake kallonsu. Cikin sa'a kuma idanunsa ya sauka akan general da ke ɗaga waya, ƙura masa idanu ya yi sai kuma ratsa ta gefenta yana shirin fita, Da sauri ta jawo shi murya can ƙasa ta ce“Ina zaka je?”


Da hannu ya yi mata nuni da su Hashim da ake ƙoƙarin shiga mota dasu, Khalil wanda dawowarsa daga makaranta kenan sai ihu yake yana riƙe da gefen rigar Maryam. Salma ta fashe da kuka ta riƙe shi sosai ta ce“Ba zamu iya taimakonsu ba, ka yi hakuri yaya Zayyad”


Fizge hannunsa ya yi ya sake nufar wajen layin, Da ƙarfi Salma ta jawo shi, ta rikeshi sosai tana kuka kamar ranta zai fita, tureta ya sake yi a karo na uku sai dai wannan karan ƙin yarda ta yi, ta rungumeshi sosai ganin yanda yake ƙoƙarin kwace mata ya sanya ta fashe da kuka, Ba tare da wani tunani ba kuma ta haɗe bakinsu guri ɗaya a kokarinta na son ganin ya bar wajen, kamar yanda ta yi tunani haka ne ya kasance, Zayyad ya juyo yana zaro idanu ganin bakinsa Salma cikin nasa, Ita kuwa ta rufe idanunta har sannan kuma bata cire bakinta daga cikin nasa ba.


After 2mins ta sake leƙa wajen layin sai taga wayam babu kowa sai wasu tsirarin sojoji da basu shige uku ba suna sintiri a bakin gidan, A hankali ta janye bakinta daga cikin nasa tana sauke numfashi, Zayyad kallonta kawai ya dinga yi sai kuma ya kwaɓe baki, Hannunsa ya sanya akan lips ɗinsa ya shafa sai kawai taga ya fashe da kuka.


Kallonsa ta shiga yi ganin ya yi zaman dirshan a ƙasa, ta tsuguna tana kallonsa sai dai ta kasa ce masa komai dan gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, koda wasa bata taɓa tunanin zata iya aikata irin haka ba, Sai dai ta riƙe irin wannan abun ne sakamakon kallon da take tashar zee world da mbc a finanin India, bata yi tunanin abun yana aiki da gaske a zahiri ba sai gashi ta gwada kuma ya yi a gaske. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce“Dan Allah Yaya Zayyad ka tashi mu tafi, har yanzu suna nan bana son su kama mu"


Kukansa ya ci gaba da yi babu alamar ma yana sauraronta, Ta dinga jan hannunsa daga tsayen da take tana kuka. Cizo ya kawo mata ta yi saurin janye hannunta tana cewa“Cizona zaka yi kuma?” Ya dinga kallonta ta ja baya tana gyaɗa kanta ta ce


“Shikenan ai sai ka yita zama, tun da duk abin da nake maka baka gani, ka tsaneni baka sona, baka tausayina, baka ganin yanda nake shan wahala. Tun da kafi son ka bi iyayenka kaje ka tafi dasu ɗin, nima zan haƙura na ci gaba da rayuwata ni kaɗai, zan manta da kai, daga yau kai ma ka manta dani...”


Ta kasa ƙarasawa saboda kukan da take, tsallake duk ledojin da suka zube ta yi ta juya ta yi tafiyarta. Zayyad ya dinga kallonta ganin da gaske tafiyar take kuma bata ko waiwaye, Ya ɗauke kansa yana ci gaba da kukansa.


Tafiya ta dinga yi tana kuka kamar zararriya, Daga ƙarshe ma ta nemi wani dakali ta zauna tana rusa ihu kamar sanda Abbanta ya rasu, Ko sharrin da aka mata akan Zayyad bai sakata cikin tashin hankali ba irin wannan, Ko wane hukunci za'a musu? Daga taimako General ya saka an tafi dasu, Allah ne kaɗai yasan irin halin da zasu shiga yanzu.


Salma ta sake fashewa da wani sabon kukan na rashin madafa da abin yi, ƙirjinta ya yi wani irin nauyi ta dinga sauke numfashi da kyar, tunani ta shiga yi na abin da zata yi yanzu. Cikin kuka ta ce


“Nashiga ukuna, yanzu ya zan yi? Wayyo Allahna...”


Ta sake fashewa da wani sabon kukan, tunanin ta je ta sanar da gidansu Maryam ta yi dan haka ta miƙe tsaye tana share hawayenta da mayafin hannunta sannan ta ci gaba da tafiya wasu hawayen na sake zubowa.


Tafiya ta dinga yi a ƙasa dan tama manta da cewa akwai kuɗi a jikinta, Har ta kai unguwar rigasa wajejen gefin magriba, Malam na tsugune ƙofar gida yana yin karatu ya hangota tsaye tana kallonsu, Sallamar ɗalibansa ya yi sannan ya ta ƙaraso, zama ta yi tana gaishe shi ya amsa yana cewa


“Babban mutum zauna mana”


Salma ta juya da sauri dan ganin wanda yake nufi,baki buɗe ta dinga kallon Zayyad wanda ke tsaye hannunsa riƙe da ledojin data zubar, bai ko kalleta ba ya nemi gefen malam ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa ya ajiye ledar hannunsa bisa cinyarsa. Malam ya dinga kallonsu can kuma ya ce“Ummusalma lafiya?”


Sai da ta ɗan yi jim kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce“Baba daman wani abu ne ya faru...”


Malam ya sauke numfashi bayan ta gama bashi labarin duk abin da ya faru, ya jinjina kansa fuskarsa babu alamun ɗimuwa ko tashin hankali ya ce“Allah alhakamu, ai na tabbata ba wani abun zasu yi musu ba, idan sun tambayesu ba'a samu biyan buƙata ba zasu sake su”


Salma ta girgiza kanta cike da ɗimbin damuwa ta ce“A'a Baba wallahi a tsorace nake, kar su cutar dasu aunty Maryam, hankalina ya kasa kwanciya”


Ɗan murmushin manya Malam ya yi kana ya ce“Ummusalma kenan, ai ita rayuwa mutum baya gujewa ƙaddararsa, tun da har kin san waɗanda suka ɗaukesu to ai shikenan. Dawo dasu ba abu bane mai wahala, yanzu kawai ke ku shiga gida sai ku zauna”


Salma ta dinga kallon malam tana jinjina halin kirki irin nasa, duk da yanda aka tafi da yarsa a kansu hakan bai sa yaji ba zai iya taimakonsu ba. Ta girgiza kanta muryarta na rawa ta ce“A'a malam wallahi ba zan iya zama a cikin gidanka ba, tsoro nake ji zasu ya dawowa a kowane irin lokaci, kawai na zo na sanar da kai halin da ake ciki ne amma tafiya zamu yi”


Malam ya girgiza kansa cikin dattako ya ce“ashsha! Ai ba wani abu bane dan kun zauna a gidana, daman gidan nan gidan baƙi ne. Sai ku yi zamanku babu damuwa ummulsalma amma yanzu idan ku ka tafi ina zaku je? Shin kin san wani gurin ne?”


Murya a sanyaye Salma ta ce“bamu san kowa ba Baba, kawai zamu tafi ne yanda Allah ya haɗa mu dasu Aunty Maryam haka zai sake haɗamu da mutanen kirki in sha Allah, amma duk sanda muka samu dama zamu zo domin duba su, zamu dawo watan wata rana”


Malam ya ɗan yi shiru can kuma ya ce“shikenan tun da kina ganin haka shi ne mafi kwanciyar hankali, amma ina da wata magana guda ɗaya”


“Ina jin ka Baba”


Ya ɗan numfasa kafin ya sake cewa “wato Ummulsalma kin san shi a rayuwa komai zaka yi kana duba addininka da kuma al'adarka, kuma kin san a addinan ce kasantuwarki da Zayyad a haka ba abu bane mai yiwuwa. Shi ba ɗan uwanki bane dan haka bai zama muharraminki ba, ba zai yiwu ku ci gaba da rayuwa a haka ba”


Salma ta kalli Malam sai kuma ta ce“Eh Baba amma ai ka ga babu yanda zamu yi ne, shi baya cikin hayyacinsa ba zan tafi na bar shi ba. Sannan ma ba shi da kowa ballantana na kai shi gurinsu, nima kuma banida dangi da zan je mu zauna a can, dole ta sanya nake tafiya ko ina da Yaya Zayyad na tabbata shi ɗin ƙaddarata ne”


“To idan haka ne meyasa ki ka ƙi bari ya bi mahaifinsa?!”


Tamkar saukar aradu haka taji tambayar ta Malam, ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce“saboda na riga da na saba dashi Malam, bana son na daina ganinsa, kuma na tabbata idan suka gan shi ba zasu bar ni dashi ba. Shiyasa ba zan iya barin su tafi dashi ba, shi kaɗai nake gani naji daɗi banida kowa sai shi malam”


Ta ƙare maganar tana kallon Zayyad wanda ya yi shiru abin sa. Malam ya yi shiru for some minutes yana nazarin kalamanta, har sai da ta ɗago ta kalleshi, ganin yanda ya yi shiru ya sanya ta sake sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta. Gyaran murya ya yi kafin ya fara cewa


“kenan baki son rabuwa dashi? Kuma kina ganin kin shirya rayuwa dashi a kowane irin hali?”


Gyada masa kai ta yi ta ce“eh, na yarda zan rayu dashi ko da daɗi koda wahala, idan har yaya Zayyad ya zame mini kaddara to nasan ba zan iya guje masa ba. Dan haka na yarda zan kasance a kusa dashi a kowane irin yanayi”


Malam ya jinjina kansa kana ya ce“Masha Allah, to idan haka ne mafita ɗaya ce ta rage muku daga ke har shi”


Salma ta ji gabanta ya faɗi ta dinga fargabar wata irin mafita ce wannan domin ba zata taɓa yarda a ce mafitar ita ce rabuwarta da Zayyad ba. Malam ya ce“Idan har kina son ki ci gaba da zama tare da Zayyad to mafita ɗaya ce ita ce ki aureshi...”


With so much shock Salma ke kallon malam bakinta ya kasa rufuwa sai zaro idanu take, bakinta na rawa ta ce


“a'a... a'a Malam, aure fa? Aure zan yi da yaya Zayyad? Ba zan iya ba Malam, wallahi ba zan taɓa iya aurensa ba!”


Malam ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce“kenan baki shirya rayuwa dashi ba, idan har da a ce kina son rayuwa dashi to ba zaki kasa aurensa ba, domin Allah bai haramta hakan ba, kina da damar da zaki iya aurenshi, idan har kin amince ni zan ɗaura muku aure a yau ba sai gobe ba”


Ban da girgiza kai ba abin da Salma ke yi, hawaye kuwa tamkar an buɗe famfo haka ya dinga zubowa kan fuskarta, ta kalli Zayyad wanda ke kallonta ganin yanda take kukan, sai kuma ta sake mai da Idanunta kan Malam a karo na biyu ta sake cewa


“Ba zan iya ba Malam, ina yiwa yaya Zayyad kallon yaya ne a gareni, ba zan taɓa iya aurensa ba, ba zan iya ba Malam dan Allah ka yi hakuri”


Malam shiru ya yi yana bin ta da kallo, ya juya ya kalli Zayyad wanda ya yi jigum sai kwaɓe fuska yake yana kallon Salma, wajen ya ɗauki shiru na wasu daƙiƙu kafin ya numfasa ya ce“Ba zan miki dole ba Ummulsalma, idan har kin ce baki son Zayyad to babu yanda za'a yi na tirsasaki, kina da damar zaɓar wanda ki ke son ki yi rayuwar aure dashi ko a yanzu ko kuma nan gaba. Amma ki sani idan har baki auri Zayyad ba to ba zaki sake tafiya wani gurin dashi ba! Sai idan ki yi tafiyarki ke kaɗai, shi kuma da kaina zan mayar dashi har gidansu domin ba zan bari ku yi zaman haramci ke dashi ba”


Fashewa da kuka ta yi ta kifa kanta kan cinyoyinta ta shiga rerashi tamkar karatu, Malam bai sake cewa komai ba ya kalli Zayyad jin an fara kiraye-kirayen sallar magriba ya ce“Babban mutum tashi mu je masallaci” babu musu Zayyad ya tashi har sannan yana riƙe da ledojinsu, Malam ya kalleshi ganin yana ƙoƙarin tafiya dasu ya ce“a'a ajiye kayan muje mu dawo” girgiza kansa ya yi ya sake ƙanƙame ledar, Malam ya ce“ajiye nace mana” tura baki ya yi sannan ya dire ledojin ya yi gaba Malam ya Girgiza kai sannan ya bi bayansa, Salma ta bisu da idanu tana zubar da wasu hawayen.


****

Mommah ta dinga kallon Nimra ganin yanda take faman kuka ta ce“kin yimin shiru ko sai ran ki ya ɓaci?” sake fashewa ta yi da kukan tana buga ƙafarta, Mommah ta girgiza kai Sai kawai ta tashi ta bar parlon, Nimra bin ta tayi da kallo, sai kuma ta tashi tabi bayanta da sauri tana ci gaba da kukan, tura ƙofar ɗakin ta yi ta hangi Mommah zaune gefen gadon ta yi tagumi, da sauri ta ƙarasa ta faɗa jikinta tana sake rushewa da wani sabon kukan, Mommah ta girgiza kanta ta ce


“Yanzu me ki ke so nayi Nimrah?”


Cikin kuka ta ce“dan Allah Mommah ki faɗawa Daddy, wallahi ba zan iya zama da kishiya ba Mommah, wallahi ba zan iya ba” ta ƙare maganar tana sake ruƙunƙumeta. Mommah kallonta ta dinga yi kafin ta ce“ Nimra kenan, shi zama da kishiyar mene a cikinsa? Mu duk ba haka muka zauna da kishiyar ba? Ke uwarki ma ita ce ta zo a kishiyar” ɗagowa Nimrah ta yi fuskarta ta yi caɓa-caɓa da hawaye ta kalli Mommah ta ce“Momma ai ke kina zaune lafiya da Mommy, wallahi ba zan iya rayuwa da kishiya ba, ba zan iya sharing mijina da wata ba mommah”


Janyeta daga jikinta ta yi ta ɗago kanta tana kallonta sosai ta ce“Na ce ki kwantar da hankalinki kin ƙi, tun ɗazu nake baki haƙuri amma kin ƙi, ya zan yi miki?” cikin shessheƙar kuka ta ce“to mommah ya zan yi?”


Gyara zama Mommah ta yi ta ce“Yawwa kina ji, ki kwantar da hankalin ki, idan har kin iya riƙe mijinki kin kuma san martabar kan ki to koda ya yi aure babu abin da zai sameki, just calm down, ki koyi yanda ake iya magana Nimrah,ki daina saurin fushi sannan ki daina gaddama, sannan ki koyi yanda ake wa miji biyayya. Idan har ki ka riƙe waɗannan abubuwan to babu abin da zai taba ƙimarki a gurin mijinki”


Nimrah ta sanya hannunta ta goge hawayenta sannan ta ce“tom amma Mommah idan suka yi aure daina son Uwar gidansu suke, shikenan na zama banza”


Ɗan murmushi Mommah ta yi sannan ta ce “Nimra kenan, Ni yanzu a gidan nan wa ake bawa girma?”


Shiru Nimrah ta yi Mommah ta ce“talk mana”


A sanyaye ta ce“Mommy mana” jinjina kai Mommah ta yi ta ce“good, yanzu kin gane abin da nake nufi ko? Idan har kin iya riƙe mutuncinki to babu yanda za'a yi a raina ki, saboda haka ki daina ɗaga hankalin ki akan wai Faruk zai ƙara aure, just leave him, ke dai ki ci gaba da kyautata masa”


Nimrah ta gyaɗa kanta wasu sabbin hawayen na sake sakko mata ta ce“tom Mommah zan yi yanda ki ka ce, amma zuciyata zafi take min” ta ƙare maganar tana sake faɗawa jikinta, rungumeta Mommah ta yi ta dinga shafa bayanta a hankali ta ce“ya isa haka, stop crying kin ji Nimrah, zan taya ki da addu'a in sha Allah”


Nimrah kasa daina kuka ta yi, har after 5mins kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya tana shessheƙar kuka a hankali, Mommah ta yi shiru tana jin kukan ɗiyar tata har cikin ranta.


****
A tare suka fito parlon, Mommah ta dinga kallon general ganin yanda yake safa da marwa cikin parlon, a sanyaye ta ce“lafiya dai Yallaɓai?” kallonta kawai ya yi amma bai ce mata komai ba, Ta mai da Idanunta kan Khalil wanda suka shigo tare ta ce“Ibrahim meya faru?”


Satar kallon general ya yi yaga hankalinsa baya kansu sannan ya ce“an je gidan dasu Yaya Zayyad suke ne...”


“an same shi?”


Mommah ta yi saurin katse shi, girgiza kansa ya yi a hankali ya ce“ba'a same shi ba, amma an tawo da mutanen da suka riƙe su, an yi an yi dasu su fadi in da suke amma sun ƙi” wani irin abu taji ya tsaya mata a ƙirji, ta ɗago idanunta wanda suka sauya kala ta kalli general, sai kawai ta fashe da kuka ta juya ta koma sama da sauri. Nimrah ta bita da idanu sai kuma ta kalli general, jiki babu kwari ta ƙarasa gabansa muryarta na rawa ta ce“daddy dan Allah a samu a dawo dashi, duk mun damu” general kallonta kawai ya yi sai kuma ya gyaɗa mata kai dan baya jin zai iya magana ma, ta juya ta nufi hanyar fita daga parlon ba tare da ta sake cewa komai ba..


Tura ƙofar ɗakin ya yi jin shessheƙar kukanta, zaune ya hangeta gefen sofa sai kuka take ya ƙarasa a hankali ya zauna gefen drawer yana kallonta. Above 5mins kafin ya furzar da numfashi cikin sanyin murya ya ce


“Kukan na mene ne? Baku son hankalina ya kwanta, dame zan ji?”


“Tambayata ka ke yallaɓai? Baka san dalilin kukana ba? Shikenan ai”


Kallonta ya yi sai kuma ya ce“i know but you have to calm down, Ina kan bincike akan yanda za'a samu yaron nan ya dawo, kin san yanda na damu? Kin san a irin tashin hankalin da nake ciki Khadijah? Ya kamata ki tausayamin”


“Ni ban ce baka kokari ba, nasan kana yin iya bakin ƙoƙarinka, but you have to put effort into it, Ina son naga Zayyad wallahi”


Mommah ta yi maganar hawaye na sakkowa kan fuskarta, Hannunta general ya kama ya riƙe cikin nasa cikin nutsuwa ya ce“shikenan, yanzu dai na saka an kamo min waɗanda suka zauna dasu, ina sha Allah nan bada jimawa ba za'a gan shi”


“To tun da ba'a gansu ba mene ne amfanin kamasun? Me zaka musu?”


General ya ce“i'll deal with them har sai sun faɗi in da suka kai su”


****
Salma na nan zaune har gari ya fara yin duhu, a wajen ta yi sallar magriba, ta dinga jiransu amma shiru ga wata yunwa da take ji kamar ta ci babu. Sai da aka idar da sallar isha'i sannan suka dawo, Malam ya dinga kallonta da mamaki har ya ƙaraso wajen,


“Shiga kaje gida yanzu zan shigo”


Ya ƙare maganar yana kallon Salma ya ce“au baki tafi ba?”


Ɗago jajayen idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta, ya sake kallon Zayyad dake tsaye har sannan ya ce“muje ciki”


“Idan har aurena da Yaya Zayyad shi ne zai bani damar ci gaba da rayuwa dashi to na aminci zan aureshi, na yarda Baba, amma dan girman Allah kar ka rabani dashi...”


# HCD
# Salma
# Yaya yad
# Nanameera
08106608363.

*HASKEN CIKIN DUHU*
Chapter 24 · 0% Book details