Chapter 27-28: “I will never forgive him”
Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read
Nanameera, YOTA/023.
Kallonsa Salma ta dinga yi ba tare da ta ce komai ba, Maryam ta kalleta sai kuma ta kalleshi a sanyaye ta ce“Abu ka kyaleta mana, Tun da kamar bata san ta faɗa” Girgiza kai Hashim ya yi yana mai da idanunsa kanta ya ce“But she have to, Ina son sanin gaskiya” Numfasawa Maryam ta yi sannan ta ce“Duk da haka kar a takura mata kaga...”
“Mu ba laifi muka yi ba, Kawai mun bar garin ne, Da gaske ne daga Abuja muke amma babu wanda muka yiwa laifi”
Salma ta faɗi maganar kanta a ƙasa. Hashim ne ya gyara zamansa ya ce“Idan haka ne meyasa ake nemanku a Abuja Salma? Har pictures ɗin ku suke yawo, Mene ne alaƙar da ke tsakaninki da Zayyad?”
Shiru ta yi na wasu mintuna sannan ta sauke ajiyar zuciya, Ta fara basu labarin abin da ya faru. Babu abin da ta ɓoye musu tun daga farko har ƙarshe.
Ba Maryam kaɗai ba har Hashim sai da ya yi hawaye, Salma ta sunkuyar da kanta tana shessheƙar kuka ta ce“Wallahi ban haukata shi ba, Ban san yanda ake haukata mutum ba, Kuma ko zan haukata kowa ba zan taɓa haukata wanda ya taimakeni ba. Amma sun kasa yarda dani, Sun ɗora min abin da ba zan iya ba, Rayuwa kawai nake amma ji nake daman na mutu na huta. Ta yaya zan iya ci gaba da rayuwa da Yaya Zayyad a irin wannan yanayin? Ya zan yi dashi? Sai abun nasa ya yi sauki sai ya dawo sabo, Wallahi na rasa yanda zan yi!”
Ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka, Tashi Maryam ta yi ta dawo kusa da ita ta kama hannunta tana hawaye ta ce
“Ki yi haƙuri Salma, Komai zai shige in sha Allah, Babu yanda za'a yi ku dawwama a haka, Tabbas an cutar da ke, Sun cutar da rayuwarki. Kin yi ƙarama da ɗaukan wannan nauyin, Ki yi haƙuri kin ji”
Rungume Maryam ta yi tana sakin wani kuka mai tsuma zuciya, Hashim ya girgiza kansa yana goge hawayen daya zubo masa. Shiru parlon ya yi kowa da abin da yake tunani cikin ransa.
Hashim ne ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin
“Ki yi haƙuri ki bar kukan nan haka, Duk da ban san Zayyad ba amma naji ya bani tausayi, Mutum kamar sa mai hankali wannan ba ƙaramin jarabawa bane, Amma akwai abin da ba daidai ba, Duk wanda ya yi masa haka ba ƙaramin maƙiyinsa bane, Kuma dole akwai shirin daya sanya aka yi haka. Amma in sha Allah komai zai zo da sauki”
Tana jikin Maryam ta ce“Na sani Yaya, Duk da ban san wanda ya aikata masa haka ba amma akwai abin da ya sanya aka yi hakan, So nake nafara nema masa magani ya samu ya dawo daidai, Wallahi tausayi Yaya Zayyad yake bani”
Hashim ya ce“Kar ki damu in sha Allah za'a fara nema masa magani, Abin da ban gane ba shi ne haukan nasa na asibiti ne ko kuma na gida ne”
“Ni a ganina tun da asiri ne mu je dashi gida wajen Malam mana, Sai ya duba shi ya dinga masa addu'a da taimako mu ga abin da hali zai yi”
Maryam ta yi maganar jiki a sanyaye, Jinjina kai Hashim yayi ya ce“Haka ne, Gobe idan Allah ya kai mu sai muje duka gidan”
“Allah ya kaimu lafiya”
Hashim ya kalli Salma ya ce“Sannan mene ne ya sameki ɗazu?”
Salma ta goge hawayen dake kwance kan fuskarta sannan ta ce
“Yaya Zayyad ne ya shaƙemin wuya, Saboda nayi masa magana”
Da mamaki Maryam ta ce“Shaƙe wuya kuma? Daman haka yake?”
Gyaɗa mata kai Salma ta yi kana ta ce“Eh, Idan nayi masa abu yana shaƙe min wuya kamar na mutu da kyar yake sakina. Kuma shi ne na bugu da jikin ƙarfe”
Hashim ya girgiza kansa ya ce“Ayyah ki yi haƙuri kin ji, In sha Allah zai samu lafiya”
Ɗan murmushi ta yi ta ce“Ameen Yaya, Nagode muku sosai Allah ya saka muku da Alkhairi, Yanda ku ka kula damu Allah ya bamu ikon biyan ku”
Hashim ya ce“Ameen Salma, Tashi ki je ki kwanta”
Toh kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta bar parlon, Sai da ta tafi sannan Hashim ya mai da hankalinsa kan Maryam ya ce“Allah sarki, wace irin rayuwa muke ciki ne yanzun?”
Maryam ta ce“Abu na tsorata sosai, Wallahi mutane basu tsoron Allah, Har a haukata mutum ba komai ba ne” Hashim ya ce“Haka ake yi, Akan abin duniya sai a raba mutum da ransa ma gaba ɗaya, Sai dai kawai Allah ya shirya mu”
“Amma Abu baka ganin akwai saka hannu cikin mutanen gidan nasu? Ni ban yarda dasu ba wallahi”
Maryam ta yi maganar a dame, Ɗan murmushi Hashim ya yi sannan ya ce“Ya za'a yi yan uwansa su masa asiri? Ai ba zai yiwu ba”
“Ba yan uwansa ba, Baka ganin wannan Mommy ɗin da ta ce matar ubansa, Wadda ta sanya aka koresu, Akwai alamun rashin gaskiya a tare da ita”
Hashim ya yi shiru yana tunani, Maryam ta sake cewa
“Saboda babu yanda za'a yi ta ce a koreshi idan har bata da mugun nufi akan sa, Kasan fa matan uban nan, Kwata kwata ba imani gare su ba, Wallahi ni ita nake tunanin ta yi wannan abun”
Girgiza kai Hashim ya yi ya ce“Kin ga wannan duk bashi da amfani a garemu, Koma wane ya yi masa haka ai zai je ya tarar da ubangijinsa koda a ce ba'a gane shi anan duniya ba, Abin da ya dame mu yanzu shi ne a sama masa lafiya ya dawo hayyacinsa” Maryam ta kwaɓe fuska ta ce“Duk da haka, Idan ya dawo daidai Wallahi sai na saka shi ya nemo wadda ta masa asiri an ɗaureta dan wannan rashin imani ne” ta ƙare maganar kamar zata yi kuka.
Murmushi Hashim ya yi sanin halinta ya ce“Daɗina da ke naci, Ki yi haƙuri dan Allah”
Tashi ta yi tana ƙoƙarin kwashe kayan abincin ta ce“To ba zan yi naci ba, Ka kai Khalil ɗaki dan Allah ka ga ya yi bacci” Okay Hashim ya ce sannan ya tashi ya ɗauki Khalil wanda yake kwance kan 3 seater ya nufi hanyar ɗakinsa dashi. Koda ya fito bai samu komai a parlon ba, Kawai ya nufi waje. Ɗakin Zayyad ya shiga, Ya hangeshi can ƙarshen gado ya cure jikinsa waje ɗaya sai faman rawar sanyi yake, Da sauri Hashim ya ƙarasa kan gadon yana kallonsa ya ce
“Zayyad lafiya? Zayyad!”
Ganin bai bashi amsa amsa ya sanya ya hau kan gadon ya riƙe shi, Wani irin zafi mai tsoratawa yaji a jikinsa hatta numfashinsa hucin zafi yake, Hankali tashe Hashim ya ce
“Baka da lafiya ne Zayyad? Meya sameka?”
Babu abin da Zayyad ya ce masa, Daga karshe ma janye jikinsa ya yi daga nasa ya tashi ya fice daga ɗakin yana tafiya kamar zai fadi, Cikin gidan ya nufa Hashim ya bi bayansa yana kiran sunansa, Tsaye ya samu Maryam bayan ta fito daga kitchen ta kalleshi ganin yanda jikinsa ke rawa ta ce
“Zayyad lafiya?”
Kafin ya yi magana Hashim ya shigo parlon yana kiran sunansa, Turus ya yi ganin Zayyad tsaye tsakiyar parlon yana kalle-kalle, Hashim ya ƙaraso gabansa ya riƙe shi yana cewa
“Meya sameka Zayyad? Mene ne?”
Ture shi ya yi ya zube ƙasa yana sakin wata ƙara, Salma na tsaye jikin press tana linke hijabi taji ƙara, Fitowa ta yi da sauri dan taji muryar Zayyad. Tsaye ta same su sunyi cirko-cirko suna kallonsa, Salma ta ƙaraso da sauri ganin yanda yake kuka kamar ƙaramin yaro, Bata san sanda ta tsuguna gabansa ba ta dafashi tana cewa
“Yaya mene ne? Me aka maka?”
Ɗago kansa ya yi da sauri ya kalleta sai kawai taga ya rungumeta yana kuka yana cewa
“Mommah! Mommah! Ba zan bi ki ba, Ba zan tafi ba, Ki bar ni anan ni, Tsoro nake ji”
Ya dinga maimaita maganar yana Girgiza kansa, Kallonsa suka dinga yi, Salma ta gyara zamansa ta rikeshi sosai duk da yanda ya yi mata nauyi, Ta dinga karanta masa duk addu'ar da ta zo bakinta tana tofa masa, Hashim ma ya durƙusa ya dafashi yana yi masa addu'a, Sun ɗauki mintuna sama da goma kafin ya fara daina maganar amma har sannan jikinsa bai bar ɓari ba, Salma ta dinga hawaye tana girgiza kanta. Maryam kuwa tsayawa ta yi jikin bango sai kuka take.
Sai da ya fara sauke numfashi Hashim ya kalleta a nutse ya ce“Bari na maida shi ɗaki”
Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin janyeshi daga jikinta, Zabura Zayyad ya yi ya sake ƙanƙameta yana magana ƙasa-ƙasa, Salma ta kalli Hashim cikin shessheƙar kuka ta ce
“Yaya ka bar min shi”
Hashim ya ce“Salma ya yi miki nauyi, Kuma na ai ba muharraminki bane”
Girgiza kanta ta yi tana sake rikeshi ita ma ta ce“Dan Allah ka bar shi, Ai Allah ya ga zuciyata, Bashi da lafiya ne”
Shiru Hashim ya yi yana kallonsu ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita, Neman kujera ya yi ya zauna yana kallon Maryam ya ce“Zauna mana” Fashewa ta yi da kuka shige ɗakinta da sauri, Hashim ya bita da idanu sai kuma ya sauke numfashi.
Bayan awa ɗaya Hashim ya kalleta ganin kamar bacci yake yasa ya ce“Ya yi bacci ne?”
Leƙa fuskarsa ta yi sai kuma ta gyaɗa masa kai, Hashim ya taso ya ce“To bari na mai da shi ɗakinsa”
Hashim ya dafa shi jin jikinsa ya yi sanyi kalau ya ce a hankali “Zayyad”
Shiru yaji alamun bacci yake sosai, Ya ɗago shi sai dai nauyin Zayyad ba ƙarami ba ne, Dole ya sake shi yana haki ya ce
“Tabarakallah, Salma na kasa ɗaukansa”
Salma ta ce“To yaya kawai ka bar shi a nan idan ya tashi sai ya tafi da kansa”
Hashim ya ce“To shikenan, Ke tashi ki je ki kwanta”
Langwaɓar da kai ta yi ta ce“A'a ka bar shi a nan”
Girgiza kai Hashim ya yi ya ce“Salma dare ya yi, Kuma kema baki jin daɗi ki je ki kwanta ni sai na zauna dashi anan ɗin”
“Dan Allah Yaya ka bar ni nima, Wallahi ba zan iya tafiya na bar shi ba, Ka bar ni anan”
Ta ƙare maganar hawaye na sauka kan fuskarta, Ganin ta dage ya sanya Hashim ya rabu da ita, Ya nemi kujera 3 seater ya kwanta ita kuma ta jingina da center table tana kallon Zayyad dake bacci a hankali, Sai kusan ƙarfe 2:00 na dare sannan bacci ya ɗauketa ita ma.
****
Abuja.
Cikin sanɗa ta tashi daga kan gadon tana kallonta. Bacci take hankali kwance, Ta ɗauki wayarta kan drawer sannan ta fice daga dakin tana tura ƙofar a hankali. Corridor ta fito tana ɗan kalle-kalle, Sai da ta tabbatar babu kowa sannan ta tsaya ta shiga danna wayarta, Number ta yi dialing ta fara ringing sai dai har ta katse ba'a ɗauka ba, Ta sake danna kiran ta mayar kunne, Sai da ta kusa tsinkewa sannan aka ɗaga ta yi ƙasa da murya ta ce
“Ina ki ka shiga ina kiranki?”
Daga ɗaya ɓangaren aka ce“Ke bacci nake yi, mene ne?”
Sai da ta ɗan kalli corridor ɗin gaba ɗaya sannan ta ce
“Ko za ki fito mu je yanzu?”
Daga ɗaya ɓangaren ta kalli screen ɗin wayarta sai kuma ta ce
“Kina ganin za ki iya fitowa yanzun?”
Jinjina kai ta yi ta ce“Daddy baya nan, Mummy Kuma bacci take, zan iya fitowa”
“What about Suhaila?”
“She already sleep fa, Babu wanda yake ido biyu, Ki zo muje yanzun”
Ta gyaɗa kai bayan ta tashi daga kan royal bed ɗin ta ce“Shikenan ki fito gani nan”
Okay ta ce tana ƙoƙarin katse kiran ta ce
“Oh wait, Ki zo ki ɗaukeni ba zan iya fitowa da mota ba”
Okay ta ce mata sannan ta yi cutting kiran ta ajiye wayar, Jidda ta sauke wayar tana kallon screen ɗin. Dare ya yi sosai amma hakan ba zai hana ta aiwatar da abin da take so ba, Ta juya ta koma ɗakinta da sauri domin shiryawa.
Ko da ta fito cire takalmanta ta yi gudun kada su yi ƙara ta sauka daga benan tana tafiya cikin sanɗa, Koda tazo main parlon na gidan duhu ta gani domin duk an kashe light ɗin wajen, Ta samu ta buɗe ƙofa ta fice da sauri, Ta ƙofar baya inda babu securities da yawa ta bi, A bakin gate ɗin ta samu sojoji guda biyu suna tsaye riƙe da bindigu, Suna ganinta suka washe baki suna faɗin
“Madam kin fito?”
Gyaɗa musu kai ta yi ta ce“Zan je na dawo ba zan daɗe ba bana son magana” Sara mata suka yi a tare suka ce
“Yes Mah!”
Jidda ta yi murmushi sannan suka buɗe mata gate ɗin ta fice da sauri.
Bata fi 2mins a tsaye ba wata Accord black colour ta yi parking a gabanta, Ta sauke glasses ɗin motar tana kallonta. Sai da ta kalli both right and left side nata sannan ta nufi motar ta buɗe ta shiga, Sauke ajiyar zuciya ta yi ta kalleta ta ce
“You Are not serious Bibi, mene ne abin fargabar?”
Tsaki Jidda ta yi ta ce“You won't understand Meema, Idan Mummy ta ganni ban san me zance ba, I can't explain anything to her”
Taɓe baki Meema ta yi ta ce“Ashe baki shirya ba” Daga haka ta yi reverse suka bar titin.
****
Around 4:45 na asuba ta yi parking motar, Ta kalli Jidda dake gefe ɗaya ta yi shiru ta ce
“Kin dai ji abin da aka ce ba? You have to calm down, Komai na tafiya yanda aka tsara”
A matukar dame Jiddah ta ce“But how? Ba zan iya ba Meema, Wallahi hankalina bai taɓa tashi irin na yau ba, Ni ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba idan har ban aiwatar da abin da nakeso ba, i can't get peace Meema”
Meema ta girgiza kai ta ce“To shikenan za ki ci gaba da cutar da kan ki kenan? Jiddah idan ciwonki ya tashi kin san ba daɗi za ki ji ba ko? Kuma zaki ɗaga hankalin duk wani mai son ki, Ki bi komai a sannu, Za ki yi nasara in sha Allah”
“Zuciyata ba zata taɓa daina min ciwo ba har sai sanda naga bayan Zayyad wallahi, Ba zan taɓa kwantar da hankalina ba har sai na ganshi a tagayyare a rayuwa, Ba zan samu sukuni ba sai har na wulaƙanta rayuwarsa ta inda duk wanda ya san shi zai daina mu'amala dashi, Duk wanda yake son sa zai tsaneshi, So nake ya rasa zaman lafiya, So nake ya zama tamkar kare Meema! So nake rayuwarsa ta zama abun kyama, Ya rasa jin daɗin rayuwa ya gwammace mutuwa akan rayuwa!”
Ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, Dafata Meema ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta ce“Ki daina irin wannan tsanar Jiddah, Ki yi haƙuri dan Allah, Duk abin da ya shige ki bar shi kawai. Na sani kina da buƙatar ki ɗauki fansa amma duk da haka ki daina irin waɗannan kalaman, Ki yi hakuri”
“Na yi haƙuri fa ki ka ce Meema! Na yi haƙuri? Wallahi ba zan iya ba, Sai na ɗauki fansar abin da ya yimin,Yanda ya tozarta rayuwarta sai na tozarta tasa. Yanda ya mayar dani abar tausayi sai na mayar dashi abin tsana, Wallahi ba zan taɓa yafe masa ba Meema, Ba zan iya ba”
Rungumeta Meema ta yi itama tana kukan ta ce“Duk da haka ba zan bar baki haƙuri ba, Na sani akwai buƙatar ki ɗau fansa kuma nima ina bayanki amma ki cire damuwa daga cikin ranki, Tun da duk abin da ki ka shirya yana kasancewa”
Dakyar ta samu Jiddah ta daina kukan, Ta ce“Ki je kada Mummy ta tashi” Toh kawai ta ce sannan ta sauka daga motar ta nufi gidansu. Koda ta shigo parlon bata samu kowa ba ta haye sama tana tafiya a hankali, Tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakinta taji saukar Muryar Mummy
“Jiddah!”
Sai da gabanta ya faɗi amma ta dake ba tare da ta juyo ba ta ce“Na'am Mummy”
“Ina ki ka je? Ya jikin naki?”
“Na ɗan sauka ne, Na je kitchen”
Mummy ta yi shiru tana kallonta can kuma ta ce“Naji muryarki a haka ko dai jikin ne?” Girgiza mata kai Jiddah ta yi ta ce“A'a Mummy na ji sauki, I just need to rest”
Numfasawa Mummy ta yi ta ce“Okay ki je ki kwanta but make sure you perform ur salat” Gyada mata kai kawai ta yi sannan ta buɗe ɗakin ta shige, Mummy ta tsaya tana kallon wajen can kuma ta girgiza kai ta nufi hanyar downstairs.
Jiddah na shiga ɗakin ta mayar da ƙofar ta rufe ta jingina da jikin kofar tana sauke wani irin wahalallen numfashi, ta fi 2mins a wajen kafin ta ƙarasa cikin bedroom ɗin, kwance ta sami Suhaila har sannan baccinta take, Ta zame mayafin abayar da ke jikinta ta nufi hanyar toilet, Alwala ta yi sannan ta fito ta sanya ladduma ta gabatar da sallar asuba sannan ta zauna ta yi addu'o'in data saba ta yi azkar sannan ta koma ta kwanta.
****
Washegari da sassafe Mummy ta shigo ɗakin, kwance ta samesu har sannan, Ta girgiza kanta sannan ta tashe su. Mummy ta kallesu ta ce
“Daddynku ya dawo kuma fita zai sake yi ya ce a kira ku”
Suhaila ce ta fara tashi tana mitsitsika idanunta ta ce“Daman ina son magana dashi”
Daga haka ta tashi ta shige toilet dan ko sallar asuba bata yi ba, Mummy ta ƙurawa Jiddah idanu ganin yanda take numfashi da kyar ta ce
“Jiddah jikin ne?”
Girgiza kanta ta yi ta ce“Babu komai fa Mummy, Kawai ban samu bacci bane sosai”
Mummy ta dinga kallonta wanda ya sanya ta sunkuyar da kanta, Mummy ta ce“Tashi ki je wajen Daddynki”
Gyaɗa kanta ta yi sannan ta sauko ƙafafunta daga kan gadon tana cewa“Mummy ina zai je ne?” Ta yi maganar kamar zata yi kuka, Mummy ta harareta ta ce“Ba kina da baki ba? Je ki tambayeshi” tura baki Jiddah ta yi sannan ta ƙarasa sauka daga gadon ta zura slippers ɗinta ta nufi hanyar waje tana tafiya kamar iska zata hureta.
A hankali ta tura kofar parlon bakinta ɗauke da sallama, Zaune ta hangeshi kan sofa ya naɗe ƙafafunsa idanunsa maƙale da glasses, Yana ganinta ya saki murmushi ya wara mata hannayensa. Da gudu ta tafi ta rungumeshi tana dariya ta ce
“Daddy!”
Ta yi maganar ya shagwaɓe, Shafa kanta ya yi ya ce“Hauwa'u, Ya jikin naki?”
Ɗora kanta ta yi a ƙirjinsa tana cewa“Babu sauki Daddy, Duk nagaji”
Ɗago kanta ya yi ya ce“Mene ne yake miki ciwo yanzu? Ina ne?”
Ganin yanda ya ruɗe ya sanya ta yi murmushi har sai da beauty point ɗinta suka loma ta ce“Daddy baka san wasa ba, I'm just kidding fa, Naji sauki sosai”
Jan kumatunta ya yi ya ce“But you scared me Jiddah, Kar ki sake haka kin ji”
Ta gyaɗa masa kai ta ce“I'll not Daddy, Ina zaka je?”
Murmushi ya yi ya ce“Yawwa Baby, Fita zamu yi da General”
Shiru ta yi tana kallonsa da idanunta masu girma, Ya kalleta ya ce“Ki daina damun kan ki in sha Allah za'a gan shi nan kusa, muna ta ƙoƙari a kai”
Cikin shessheƙar kuka ta ce“Daddy bana iya bacci, Hankalina ya kasa kwanciya, Dan Allah a nemo shi Daddy, Wallahi zan aure shi ko a haukan”
Shafa kanta ya yi ya ce“Ki daina kukan nan, Daman za ki aure shi in sha Allah, Amma ki bar damun kan ki kar wani abun na daban ya sameki”
Gyaɗa masa kai ta yi still crying ta ce“But Daddy...”
Hannunsa ya ɗauka kan bakinsa ya ce“Shiiii...”
Shiru ta yi tana goge hawayen fuskarta, Suhaila ta buɗe ɗakin ta shigo da gudu ta ƙaraso ta ce“Daddy welcome back” Zama ta yi gefensa ta riƙe hannunsa tana murmushi, Juyo da fuskarsa ya yi ya shafa kanta ya ce“Auta”
“Daddyna, I dey missed you alot”
Murmushi ya yi ya ce“Same dear, Ya school ɗin”
“Not too bad, Amma nagaji”
Girgiza kai General ya yi sannan ya ci gaba da musu hira..
****
6 days later, Kaduna..
5:00pm
Fitowa Salma ta yi daga kitchen tana kallon Maryam ta ce“Auntie nagama fa”
Maryam da ke Ƙoƙarin cirewa Khalil uniform ta ce“Tom Salma je ki duba Zayyad ko ya sha rubutun”
Salma ta nufi ƙofa tana cewa“Ni na san bai ma sha ba wallahi” Maryam ta yi murmushi tana cewa“Duk da haka duba dai”
Tura ƙofar dakin ta yi ta same shi zaune kan tile ya yi tsit yana tunani, Ƙarasawa ta yi ta zauna kusa da shi tana cewa
“Yaya Yad ɗina”
Ɗago kansa ya yi ya kalleta, Ta janyo ledar rubutun nasa ta buɗe, waro idonta ta yi tana kallonsa ta ce“Yanzu shi ne baka sha ba?”
Ɗago kansa ya yi ya harareta sai kuma ya ɗauke kansa, Dauko ledar rubutun ta yi ta fasa bata ce masa komai ba riƙe fuskarsa ta buɗe bakinsa ta fara bashi, Sai da ya shanye tas sannan ya juyo ya kalleta, Murmushi ya ga ta yi masa ya ɗauke kansa yana kallon gefe. Tashi Salma ta yi ta fice daga ɗakin dan daman kwana biyun nan ba magana yake ba.
****
Girgiza kai mutumin ya yi ya ce“Yanzu me ki ke so a yi?” Matar da ke zaune gabansa ta ce“Kawai A yi abin da ya dace boka, Ni bana son ya samu salama, Bana son ya dawo da hankalinsa, So nake ya yi haukan da za'a dinga kama shi ana ɗaurewa, So nake ya yi haukan da zai kai shi ga halaka, Bana son ko da wasa ya dawo hayyacinsa, Wanda yake tare dashi ma bana son ya samu nutsuwa a rayuwarsa. So nake a ɗaiɗaita rayuwarsa, A kwance masa ragowar tunaninsa, Ya manta da rayuwarsa ta da, Ya ƙare rayuwarsa akan bola, Ko kuma ya yi hatsari mota ta markaɗeshi akan titi, Bana son ko labarinsa na sake ji, Kawai a kashe shi ta kowace hanya, Ita kan ta yarinyar da ke tare dashi ina son a ɗaiɗaita rayuwarta a sanya mata tsanarsa cikin ransa, Idan kuma baka ba zai yiwu ba to kawai a kasheta ita ma!”
_An kusa gama book 1 and book 2 isn't free it's ₦700 via 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay evidence via 08106608363, Ki biya domin ki karanta cikin kwanciyar hankali_
# HCD
# Yaya Yad
# Salma
# Nanameera
08106608363..
*HASKEN CIKIN DUHU*