Chapter 35-36: When healing meant separation
Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read
Nanameera, YOTA/023.
“Tabbas Mama naga Zayyad, kuma na zauna tare dasu, amma yanzu ban san inda suke ba. Domin na tabbata Salma idan taji an ce an zo an tafi damu to baza bari su ci gaba da zama ba. Mama da gaske kina son Zayyad kuma? Domin ban ga alamun wannan soyyayar a tare dashi ba”
Mommah ta dinga kallon Maryam, can kuma ta ce“ina sonsa mana, shi ɗin ɗana ne, akan me ba zan so shi ba? Babu wanda ya kai ni son shi duk duniya” Maryam ta girgiza tana ɗan murmushi ta ce“amma kina son shi ki ka bari aka lalata rayuwarsa? Kina son shi ki ka bari aka koreshi daga gidan ubansa? Mama duk da ban san wasu abubuwan ba amma na tabbata akwai abin da ba daidai ba cikin rayuwarsa, wallahi Mama akwai sakaci cikin lalacewar rayuwarsa, akwai rashin kula daga wajen iyayensa. Domin naga hakan a tare dashi”
Mommah fashewa ta yi da kuka, Maryam ta dafata itama tana hawaye ta ce“amma ki yi haƙuri idan na ɓata miki rai Mama, a tare da Zayyad babu kulawa daga iyaye, musamman mahaifiya”
Tashi tsaye Mommah ta yi tana tafiya a hankali, muryarta cike da damuwa ta ce“nagaza! Ban kula dashi yanda ya kamata ba, ashe kowa nagane bani na haifeshi ba. Ya zan yi? Kaddara ta sanya na auri Idris da badan haka ba babu abin da zai samu rayuwarsa...”
Mami ce ta rufe mata baki tana girgiza mata kai, fashewa ta yi da kuka ta faɗa jikin Mami tana cewa“nagaza Mami, Yaya Jiddah ba zata yafe min ba. Ba haka ta rainemu ba Mami, bai dace a ce na bar ɗanta ya shiga wani hali ba a rayuwa. Amma na kasa tsawatarwa, ya zan yi Mami? Ya zan yi...”
Ta kasa ƙarasawa saboda kukan da yaci ƙarfinta, Maryam dake zaune ta kalli Hashim da mamaki dan bata gane inda zancen nasu ya dosa ba. Kenan ba ita ce mahaifiyarsa ba?, Ganin yanda take kuka ya sanya ta miƙe ta ƙarasa gabanta, Dafata ta yi tana jikin Mami ta ce
“Ki yi haƙuri, ban san haka ba da ba zan yi maganar ba, nayi tunanin kece ki ka haifeshi, ashe ba haka bane. Ki yi haƙuri dan Allah”
Mommah ta ɗago fuskarta wadda hawaye ya gama wanketa ta ce“babu abin bani haƙuri, kin faɗi gaskiya, gaskiyar dana daɗe ban ji an faɗa min ba, kin ganar dani abin da na daɗe ina tunaninsa, tabbas ban yi kama da mahaifiyarsa ba” ta maida idanunta kan Mami ta ci gaba da fad'in
“Da nasan haka zai faru, dana bari kin riƙe shi a lokacin da ki ka nema. Sai dai nayi tunanin idan muka haɗu dani da ƙanin mahaifinsa zamu fi kasance iyaye gare shi, ashe ba haka bane. General ya lalata komai, yayinda ni kuma na taya shi, mun yi tunanin nuna masa soyyaya shi ne abin da zai saka ya ɗauka mune iyayensa na asali, saboda haka muka fifitashi fiye da kowa, bama son ɓacin ransa. Sai dai ashe ba haka bane, ashe makamin tarwatsa rayuwarsa muka ɗauka, a lokacin dana fara gane haka nayi kokarin fahimtar da General sai dai sam yaƙi saurarata ya ci gaba da yi masa duk abin da yake so, koda a ce abun ba shine mafi dacewa dashi ba. Duk da nakasa sakawa a daidaita rayuwarsa amma ina taya shi da addu'a, wallahi ban so rayuwar Zayyad ta kasance a haka ba, ban so hakan ba!”
Ta ƙare maganar wasu zafafan hawaye na biyo fuskarta. Girgiza kai Mami ta yi ta ce“Baki da laifi Khadijah, kin yi iya bakin ƙoƙarinki, wannan abin da ya faru kaddara ce. Kuma idan da wanda yake da laifi to general ne bake ba, ki daina ɗaurawa kan ki abin da baki aikata ba. Kin so Zayyad ba kaɗan ba, kin kula dashi a lokacin da yake karkashin kulawarki. Duk abin da ya faru ya faru ne a sanda ya fara girma, dan haka ba laifinki bane”
Mommah ta sanya hannunta ta goge hawayen da yake ƙoƙarin sakkowa wuyanta ta ce“amma ai Mami kowa laifina yake gani, babu yanda za'a yi na goge wannan tunanin daga zuciyoyin mutane”
“Ko kaɗan babu wanda zai zargeki, wannan laifin namu ne duka, kowanenmu yana da alhaki akan abin da ya faru. Jiddah bata cancanci haka ba, soyyaya ta rufe mana idanu mun kasa fahimtar abin da ya kamata mu yiwa Zayyad, mun cutar da rayuwarsa ta hanyar da bamu fahimci hakan ba, ki daina cewa ke kaɗai ki ka yi Khadijah kowa yana da nasa laifin!”
Mommy ta ƙarasa maganar tana shigowa cikin ɗakin, da mamaki suka dinga kallonta dan babu wanda ya yi tsammanin shigowar Tata, ta ƙaraso gabansu ta dafa Mommah tana hawaye ta ce“wannan duk laifinmu ne, ba iya ke kaɗai ba, nima tamkar mahaifiyarsa ce, ina son Zayyad yanda ba'a tsammani, wallahi ko bacci bana iya yi” Kuka sosai suka dinga yi, dakyar Mami ta basu haƙuri suka yi shiru, Maryam ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Mommah ta ce
“Ki daina kuka Mama, nayi miki alƙawarin dawo miki da Zayyad gida, idan har Allah ya hukunta komawata gida. Na tabbata ba zasu yi nisa damu ba, ni kuma zan dawo dashi gareki a kowane irin hali”
Da sauri Mommah ta kalleta, ta kama hannunta bakinta na rawa ta ce“Da..da gaske za ki dawo min dashi? Da gaske Zayyad zai dawo gida? Ina son na ganshi”
Maryam ta ɗora nata hannun a saman nata ta gyada mata kai ta ce“Nayi miki wannan alƙawarin Mommah, zan dawo miki da Zayyad har gida”
Da sauri Mommah ta rungumeta ta ɗago sannan ta ce“Idan ki ka min haka ba ƙaramin daɗi zan ji ba. Dan Allah ki dawo min dashi”
Maryam ta ce“In sha Allah Mama, da zarar an sake mu zan dawo miki da Zayyad”
“Yanzu zan yiwa general magana a sake ku”
Mommy ce ta yi saurin cewa“Idan an gama bincike kenan”
Kallonta kawai Mommah ta yi amma bata ce komai ba. Mami ta ce“Muje to” dakyar Mommah ta saki hannn Maryam tana juyowa suka fice daga ɗakin, sojojin suka sake shigowa.
****
Ƙarfe 9:00 na dare suka shiga cikin gidan, Salma ta dinga kallon ko ina na gidan, parlon ne guda ɗaya a ciki da kitchen da banɗaki sai bedroom guda biyu a ciki, gidan da haske dan akwai wuta a unguwar. Ya kalleta ya ce“to ni zan koma, duk yanda ake ciki zaki jini” Toh kawai Salma ta ce, ya juya ya fita. Hannun Zayyad ta riƙe tana cewa “Yaya yad muje ciki” kallonta ya yi sai kuma ya kwace hannunsa ya shiga cikin parlon.
Zama ya yi kan kujera ya zuba uban tagumi, koda Salma ta shigo kallonsa ta dinga yi kafin ta ce“Ka tashi ka shiga ciki kaji, zan je na siyo mana abinci” ko kallonta bai yi ba ballantana ta saka ran da yaji abin da ta ce, Salma ta yi shiru sai kuma ta ajiye ledojin hannunta ta juya ta fita. Sai da ta saka key ya wajen gidan sannan ta nufi hanyar titin da suka biyo dan wajen akwai tarin kantina a wajen, koda ta zo babban titin tsayawa ta yi tana kallon tarin motocin dake shigewa, ta yi shiru tana tunanin abin da zata siya masu, juyawa ta yi ta hango wata mata tana suyar wainar masa, wajen an cika sosai da motoci. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta nufi wajen direct.
Ganin tarin maza a wajen ya sanya ta tsaya daga baya tana leƙensu, tana nan tsaye har bayan 5mins sai taga wani yaro ya zo gabanta yana miƙa mata ledar ya ce
“wai gashi”
Kallon ledar ta yi sai kuma ta kalli yaron ta ce“mene wannan ɗin?”
“wancan ne ya ce a kawo miki”
Ya faɗa yana nuna mata wajen wata mota glk white colour, matashin saurayi ne da ba zai shige 34yrs ba tsaye jikin wata glk white colour, yana sanye da wata dakkakiyar shadda milk colour ya ɗora hula akansa, idanunsa maƙale cikin shade glasses. Salma ta kalli wajen sai kuma ta kalleshi ta ce“to ai ni ban siya ba, ka mayar masa” daga haka ta matsa daga wajen, ganin mutanen sun ragu yasa ta ƙarasa wajen, matar tana ganinta ta amshi kuɗin ta zuba mata dan daman tun ɗazu take ganinta. A wata roba ta zuba mata sannan ta saka a leda ta miƙa mata, Salma ta amsa sannan ta juya ta bar wajen ba tare da ta sake kallon inda mutumin yake ba.
Tana ƙoƙarin buɗe ƙofar gidan taji an ce“da kin bani minti ɗaya domin nayi miki magana”
Da mamaki ta juyo tana kallon wanda ke mata maganar, wannan mutumin ne na wajen mai sai da waina, ta dinga kallonsa amma ba ta ce komai ba. Ya ɗan gyara tsaiwarsa yana murmushi ya ce“Sunana Dr Aliyu Ahmad, ko zan san naki sunan?”
Salma ta dinga kallonsa kamar ta samu tv sai kuma ta ce“Sannu amma ni matar aure ce” daga haka ta juya ta ƙarasa murɗa key ɗin ta shige gidan ta rufo ƙofar. Aliyu ya dinga kallon ƙofar sai kuma ya yi murmushi wanda ya fitar da asalin kyansa ya jinjina kai ya ce“okay”
Sannan ya juya ya shige motarsa. Koda Salma ta shiga tsayawa ta yi jikin ƙofar ra dinga sauke wani wahalallen numfashi dan ba ƙaramin tsorata ta yi ba. Above 2mins kafin ta ɗaga ƙafarta ta ci gaba da tafiya. Zaune ta sami Zayyad in da ta bar shi, ta ƙarasa ta ajiye ledar tana kallonsa ta ce“Har yanzu baka tashi ba Yaya?” ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya sake ɗauke kai, ta ɗan yi murmushi ta ce“sauko mu ci abinci”
Buɗe robar ta yi dan babu faranti a gidan, ta zauna tana kallonsa ganin ko motsi bai yi ba ta ce“ka sauko mana" ta ƙare maganar kamar zata fashe da kuka, saukowa ya yi ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa. Ta tura masa robar ta ce“kaci sai ka rage min” taɓe bakinsa ya yi sai kuma ya tura mata robar yana harararta, murmushi Salma ta yi ta ce“just eat, idan ka ƙoshi sai nima naci” Banza Zayyad ya yi mata bayan 2mins ta ce“to idan ba zaka ci ba sai na cinye na barka” daga haka ta yi bismillah ta fara gutsurar wainar ta dangwali miyar har ta kai wajen bakinta sai kuma ta miƙo masa tana cewa “ka ci” kallonta kawai ya yi sai kuma ya ture hannunta, ya sanya hannunsa ya dauki wainar ya saka a bakinsa ba tare da ya dangwali miyar ba. Kallonsa kawai ta yi sai kuma ta saka wadda ta gutsura a bakinta ta shiga taunawa a hankali. Haka ua dinga cin wainar ba tare da miya ba har suka cinye.
Salma ta ɗauke robar ta kai kitchen ɗin sannan ta fito tana kallonsa ta ce“tashi kaje ka kwanta Yaya Zayyad”
Ko musu bai yi mata ba ya tashi ya nufi inda yake ganin kamar ɗaki ne ya shiga, katifa ce kawai a dakin ya yi kwanciyarsa a kai ba tare da ya lura da wani abun ba. After 2mins Salma ta shigo ɗakin, kallonsa ta dinga yi ganin har bacci ya ɗaukeshi sai kawai ta yi murmushi ta juya ta fita. Ɗaya ɗakin ta shiga babu komai shi a ciki, ta shimfiɗa ɗankwalin kanta ta yi kwanciyarta sai dai sam bacci yaƙi zuwa idanunta, ta dinga tunanin irin rayuwar da zasu yi yanzu.
Washegari around 9am ta fito tsakar gidan ta hangeshi zaune ya yi tagumi, jiki a sanyaye ta ƙarasa wajen dan ta fuskanci kwana biyun nan gaba ɗaya ya sauya, baya magana, kuma ba zai yi abu irin na mahaukata ba sannan ba zai kula kowa ba. Salma ta dafashi ta ce“Yaya Zayyad” ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya sake ɗauke kansa, ta tsuguna gabansa fuskarta cike da damuwa ta ce“Ka faɗa min me aka yi maka Yaya yad ɗina? Ko ni ce?” taɓe baki ya yi, sai kuma ya ce“Mommah gida zani” Ji tayi jikinta ya yi wani irin sanyi, ta ɗan yi shiru ta haɗa nutsuwarta sannan ta ce“to zan kai ka, bari naje na siyo mana abinci”
“Zan biki”
Ya yi maganar kamar ƙaramin yaro, murmushi ta yi ta miƙo masa hannunta, kamawa ya yi ya miƙe ta ce“muje to” ya ɗan yi murmushi sannan suka fita daga gidan.
****
Sai kusan azahar sannan suka dawo gidan, ta kalli Zayyad wanda yake rike da ledoji ta ce“muje ka tayani aikin” bai ce komai ba ya ƙarasa parlon ya dire ledojin. Ajiye nata ta yi itama sannan ta ce“muje kitchen na zuba kayan sai mu dafa abinci”
“Ni nagaji”
Ya faɗa yana zama a ƙasa, murmushi kawai ta yi ta ce“tom bari nayi da kaina tunda ba zaka tayani ba” daga haka ta fara ɗiban ledojin tana shigewa dasu, ya dinga bin ta da kallo daga ƙarshe ya nemi waje ya kwanta..
Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin gidan har na tsawon wata guda, zuwa sannan abubuwan Zayyad sun yi sauƙi sosai, ko kaɗan baya Abu irin na mahaukata. Haka zalika kuma baya yin irin na masu hankali, babu abin da yake sai dai ya ci abinci ya kuma kwanta. Amma kullum cikin kiran Mommah yake, idan abun ya motsa sai ya daina kulata, ranar daya bushi iska kuma ya yi mata magana, kuma har zuwa sannan General bai saki su Maryam ba, sai dai sun yi sabo mai yawa dasu Mommah dan kusan kullum sai ta zo ta gansu.
Biyoshi ta yi ganin yana shirin fita ta ce“magana fa nake yi”
Juyowa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce“mene ne kuma? Me ki ke so yanzun?”
“so nake ka saki yaran nan daka kamosu, basu da wani laifi, kuma basu san inda Zayyad yake ba”
Wani kallo General ya yi mata sai kuma ya ce“kuma kawai dan sun ce haka sai na sake su ko? Wai Khadijah me ki ka ɗauki Zayyad ne? To bari ki ji ni ba zan bari wani abun ya sameshi a banza ba”
“Mene ne abun da zai same shin bayan wanda ya same shi? Kamata ya yi ka mayar da hankali akan nemansa ba wai ka tsaya kana kamo mutanen da aka ce maka sun ganshi ba. Dan Allah ka sake su, idan ya so sai a haɗa baki dasu idan sun sake zuwa inda suke a rike su har kazo” General ya yi shiru yana nazarin maganarta can kuma ya ce“ina da abun yi yanzu, idan na dawo sai muyi maganar” numfasawa ta yi dan taga alamar zai iya yarda ta ce“tom shikenan Allah ya dawo da kai lafiya” Ameen ya ce sannan ya sauka daga stairs ɗin, Momma ta ɗan yi shiru sai kuma ta girgiza kai a fili ta ce“Allah ka bayyana shi”
****
Salma ta dinga kallonsa ganin yanda yake shan rubutun ta ce“Yaya yau kuma ji ka ke da shan maganin?” harararta ya yi ya ce“Na kula ki?” murmushi ta yi tana ɗauraye kayan ta ce“ba ruwana” ko kallonta bai yi ba sai da ya shanye rubutun jarkar tas. Ya tashi ya koma ciki ba tare da ya ce mata komai, ita ma bata sake bi ta kansa ba ta ci gaba da wankin da take har ta kammala. Zaune ta sameshi kan kujera ya yi shiru kamar mai tunani, ta girgiza kanta sannan ta ce“tunanin me ka ke yi?” ta ƙare maganar tana zama a ƙasan kujerar da yake. Shiru ya yi mata, ta ɗago daradaran idanunta tana kallonsa ta ce
“Ka faɗa min abin da ya dameka, dan Allah Yaya Zayyad ka daina wannan damuwar. Bana son ganinka cikin damuwa kaji”
Ba zaka taɓa cewa da Zayyad take ba, Sai kawai ta fashe da kuka. Kallonta ya dinga yi amma bai ce mata komai ba, ta tashi ta nufi hanyar daƙinta.
Koda ta shiga ɗakin faɗawa kan katifa ta yi ta fashe da wani sabon kukan, da gaske Zayyad bai damu da ita ba, amma ita ta damu dashi fiye da komai a yanzun.
Sai da aka kira sallahr la'asar sannan ta fito daga ɗakin, bata same shi a parlon ba, kuma bata damu ta ganshi ba. Kawai ta nufi cikin kitchen, spaghetti ta ɗauko guda ɗaya ta ɗauko tukunya ƙarama ta fito tsakar gida, ɗan ƙaramin kurfotin dake tsakar gidan ta kunna sannan ta ɗora ruwa ta koma ciki. After 20mins ta fito ta samu ruwan ya tafasa ta kakkarya taliyar ta zuba sannan ta nemi waje ta zauna, sai da taliyar ta dahu sannan ta tace ta ɗauka ta koma kitchen. Taliyar ta zuba ta saka manja ta ɗauko robar yajin ta dawo parlon. Ko loma biyu bata yi ba y shigo ta kalleshi ta ce“Yaya na zubo maka abincin?”
Shiru yayi mata, ta tashi ta shige kitchen ɗin. Bata jima ba ta fito hannunta riƙe da wani plate ɗin ta ajiye a gabansa sannan ta koma ta zauna ta ci gaba da cin nata. Har ta gama ci bai ɗauki abincin ba, ta mai da plate ɗin kitchen sannan ta fito tana kallonsa ta ce“Ko baka son wannan?”
“Mommah zani”
Girgiza kanta ta yi ta ce“Ba nace zan kai ka ba? Ka zauna ka ci abincin amma” tashi ya yi ya shige ɗaki ba tare da ya ce komai ba. Salma ta bi shi da kallo hawaye na zubowa kan fuskarta. Ɗaki ta shiga ta ɗauko hijabinta ta saka ta fice daga gidan tana kuka.
Unguwar rigasa ta nufa, zaune ta hangi Malam kan ladduma da ɗalibai a gabansa suna ɗaukan karatu. Tsayawa ta yi ɗan nesa dasu ta rufe fuskarta da hijabinta tana kuka. Tasowa Malam ya yi dan ya ganeta ya kalleta ya ce“Ummulsalma lafiya?” cikin kuka ta ce“Yaya Zayyad ne Malam, ka zo muje ka gan shi dan Allah” ta ƙare maganar tana sake fashewa da wani kukan. Malam ya ce“subhanallahi, menene ya same shi?”
“Baba ka zo muje ka gani da kan ka dan Allah”
Shiru ya yi sai kuma ya ce“shikenan muje” daga haka ta yi gaba yana biye da ita.
Bakinsa dauke da sallama ya shigo parlon, ta kalleshi ta ce“yana cikin ɗaki malam” tom kawai ya ce sannan ya nufi ɗakin, ƙararin numfashinsa yaji ya sanya ya ƙarasa da sauri yana kallonsa ya ce
“Muhammad! Muhammad!”
Kasa magana Zayyad ya yi saboda yanda numfashinsa ke hawa da sauka, tsugunawa ya yi ya dafa shi ya ce“me yake damunka Muhammad?” muryarsa na rawa ya ce“Ba...Baba... Momma! Mommah Baba”
Salma dake tsaye bakin ƙofa ta fashe da kuka tana kallonsu ta ce“ka gani ko malam, kullum haka yake cemin. Kullum baya kulani, sai ya dinga cemin zai tafi ya bar ni, malam ka gani dai a gabanka, Yaya Zayyad baya son zama dani Baba, baya sona Baba...”
Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani kukan, ta sulale ƙasa kan siminti. Girgiza kai Malam ya yi cike da tausayinta, ya mayar da idanunsa kan Zayyad a hankali ya ce“Wajen Mommahn ka ke so ka koma?” gyaɗa masa kai Zayyad ya yi yana hawaye ya ce“zan ga Mommah malam, ina son naga momma dan Allah” jin yanda ya yi magana cike da hankali ya sanya Malam ya dafa shi ya ce“shikenan Zayyad zaka je gida in sha Allah, ni nayi maka wannan alƙawarin, amma yanzu ka zauna lafiya kaji”
Gyaɗa masa kai kawai ya yi, Malam ya sake cewa“kar ka sake ɗaga hankalinta kaji?” nan ma ya gyaɗa masa kai, Malam ya numfasa ya ce“bari naje gida, da safe in sha Allah zan zo” Zayyad ya lumshe idanunsa bai ce komai ba. Tashi Malam ya yi ya ƙarasa bakin ƙofar ya kalli Salma dake faman kuka ya ce“taso ki biyoni” daga haka ya fita daga dakin, tashi tayi tabi bayansa tana kuka kamar ranta zai fita.
A tsakar gida malam ya tsaya, Salma ta tsaya ɗan nesa dashi tana shassheƙar kuka, Malam ya kalleta sai kuma ya girgiza kansa ya ce“ki yi haƙuri ki daina wannan kukan Ummulsalma, ina son zan yi magana da ke ta fahimta”
Rage sautin kukan nata ta yi amma bata ce komai ba, Malam ya kalli sararin samaniya wadda gajimare ya rufeta ya ɗan yi jim sannan ya ce
“wato Ummusalma abin da na fahimta shi ne Zayyad ya fara dawowa natsuwarsa, saboda haka a yanzu babu abin da yake buƙata sama da danginsa, musamman mahaifiyarsa. Saboda haka akwai buƙatar a mayar dashi gareta, ko hakan ya saka ya dawo nutsuwarta hankalinsa ya dawo, sannan su Maryama ma su dawo gida, idan Allah ya kai mu gobe ni da kaina zan zo na ɗaukeshi na mayar dashi garinsu”
Durƙushewa ta yi akan gwiwoyinta ta haɗe hannayenta waje guda bakinta na rawa kuma cikin kuka ta ce“D...dan girman Allah, dan soyyayar da ka kewa Annabi Muhammadu(S.A.W) kar ka rabani da Yaya Zayyad malam, idan har ka mayar dashi ba zan sake ganinsa ba Malam, ba zan sake magana dashi ba. Ba zai dake kulani ba Malam, Amma ni ina son Yaya Zayyad, ina son zama dashi, ina ganinsa tamkar wani bangon wanda yake kareni. Ina ganinsa tamkar Abbana, kuma Yayana, domin shi ne wanda ya taimakeni a sanda na rasa kowa nawa, dan Allah dan Annabi malam kada ka rabani dashi, kada ka mayar dashi gida, wallahi ba zan sake kawo maka ƙararsa ba, ka yi hakuri ka barni dashi...”
Ta kasa ci gaba da maganar saboda yanda numfashinta ke sarkewa, Malam kallonta ya dinga yi yana jin wani irin tausayinta, duk da yarintar ta amma tana sonsa sosai. Ya gyara tsaiwarsa yana kallonta sosai ya ce“Ummulsalma kina son Zayyad har haka? Kin yarda zaki zauna dashi koda a ce shi baya son ki?”
“Na yarda malam, na yarda wallahi, zan zauna da Yaya Zayyad koda zai dinga yankar naman jikina na yarda zan zauna dashi, domin shi ne Haske dana daɗe ina nema a cikin duhu, Shi ne HASKEN CIKIN DUHU na Malam!”
_Book 1 ya kusa karewa fa, amma har yanzu baki yi payment, to ki yi maza maza ki yi payment via 7041901078 Hauwa lawan Adamu Opay evidence via my number 08106608363 Nanameera, a yi payment kafin lokaci ya ƙure_
# HCD
# Light within the darkness
# Nanameera
08106608363
*HASKEN CIKIN DUHU*