← Book details Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 28

Chapter 3: Behind Her Silent Tears

Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 19 min read

Nanameera, YOTA/023.


Maitama, Abuja.


Zaune take kan royal bed ɗinta, tana sanye da wata sleeping dress doguwa wadda ta tsaya iya gwuiwarta, hannunta na dama riƙe da bubble tea tana sipping a hankali, idanunta zube cikin system ɗin gabanta inda take kallon dramar Lee jae wook ta dear hongrang, sosai take jin daɗin kallon tana ɗan murmushi. Turo ƙofar ɗakin a kayi, ya shigo yana sanye da wasu pyjames White colour idanunsa sanye da glasses wanda ya kasance medicate ne, harɗe hannayensa ya yi a ƙirji ya zuba mata idanu, sarai Nimra taji shigowarsa amma ta share, ganin bata ɗago ba ya sanya Farooq takowa har inda take zaune, zama ya yi gefen gadon ya janye system ɗin gabanta. Sai a sannan ta ɗago ta kalleshi fuskarta babu walwala


“Madam ina kika je babu tambaya?”


Ya faɗa fuskarsa a sake, shiru Nimra ta yi, can kuma ta ce“Naje gidanmu ne, ko sai na tambayeka dan zan je gida?” ɗan murmushin takaici Farooq ya yi ya ce“A'a, tunda baki saba da hakan ba” taɓe baki tayi, ta sanya hannu zata ɗauki system nata. Sake janyewa ya yi ya ce“Yunwa nakeji madam, I need food”


“But akwai maid, why not kace ta dafa maka abinci?”


Farooq kallonta kawai ya yi, sai kuma ya girgiza kansa bai ce komai ba. Tashi tayi daga zaunen da take ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ya bita da idanu yana jin wani irin zafi can ƙasan zuciyarsa. Yana nan zaune har ta buɗe ƙofar ta shigo after 20mins, maid ɗin bayanta ta bawa hanya ta dire ɗan ƙaramin tray ɗin kan table sannan ta juya ta fita. Kallon tray ɗin ya yi, tea flask ne sai kayan shayi, milk, Milo, bounvita, da kuma sugar. Daya plate ɗin kuma slices sponge cake ne acikin sai kwalbar Nutella a gefe. Zama tayi ta ja bargo tana cewa“you can manage this, coz it's already late, good night” daga haka ta rufe jikinta da lallausan duvet ɗin. Kallonta Farooq ya yi sai kuma ya kalli tray ɗin, wannan zai ci matsayin abinci sunan yanada mata? Haka zai cigaba da rayuwata da ita? Tayaya?...


Washegari da sassafe ta tashi ta shirya cikin Abaya wadda ita ce kayanta koda yaushe, tayi rolling mayafin rigar sannan ta fito parlon. Zaune ta sameshi kan sofa yana karatun Alqur'ani, ta kalleshi sau ɗaya ta ɗauke kai


“Zan tafi”


Tafaɗa tana shafa lip gloss a bakinta, ajiye Alkur'anin ya yi ya tashi yana kallonta ya ce“lemme drop u” ta ɗan kalleshi sai kuma ta ce“then idan ka kai ne, zaka dawo ka ɗaukeni ne?” gyaɗa mata kai ya yi sannan ya shige ciki, taɓe baki ta yi a ranta ta ce“kamar na saka shi” tana nan tsaye har ya fito cikin wani yadi blue black wanda ya yi masa kyau sosai, ya kalleta ganin yanda take kallonsa ya ce“ko dai nayi miki kyau ne?” kallonsa ta yi da lulu eyes ɗinta amma bata ce komai ba, da hannu ya nuna mata hanyar waje ya ce“muje” ta ɗauki jakarta dake kan kujera tayi waje tana tafiya a hankali.


**** Cikin hanzari yake taka stairs ɗin benan yana sakkowa idanunsa kan rollex ɗin hannunsa, a dining area ya hangesu kasancewar safiya ce kowa yana cin abinci. Ƙarasawa ya yi ya ɗan yi hugging Dad yana murmushi ya ce“Morning Dad” shafa kansa Dad ya yi ya ce“Ɗan gidan soja ka tashi lafiya?” jinjina kansa ya yi ya ce“Alhamdulillah” daga haka ya gaida Mommy da Mommah. Kallonsa Mufeeda ta yi ta ce“Big bro jiya ban ganka ba” harararta ya yi ya ce“to yanzu kin ganni sai ki cinyeni” murmushi ta yi ta ce“Ni na isa na cinye Favourite ɗin Daddy, da an ciremin subsidy a gidan nan” Dariya duk suka yi, ya kalli Daddy ya ce“Dad I'm off”


“To where?”


Cewar Momma, langwaɓar da kai ya yi yana kallonta ya ce“My own Momma, nifa ba yaro bane, ko Nayla ce zata fita da safe ai ba'a tambayeta ina zata je ba, asibiti zan je fa” taɓe baki ta yi ta ce“to sannu Babba, irin wannan daɗewa da aka yi da haifarka” Dad ne ya katseta ta hanyar faɗin “leave ur Mom je ka kawai, kuma idan kana buƙatar wani abu ka sanar dani, duk da dai nasan kuɗi ba matsalarka bane, coz kama fini” sake hugging nasa ya yi ya ce“ni na isa nafi Dad kuɗi, bayan shi yake bani” dariya duk suka yi ya yi hanyar fita daga gidan. Tashi shima Dad ya yi yana kallon Nayla ya ce“kiyi sauri ki gama, Khalil zai kara ki makaranta” murmushi ta yi ta ce“Daddy nafa ƙoshi, so nake kawai na ganni a school”


"Su Nayla a University”


Mufeeda tafaɗa tana dariya, kallonta ta yi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce“Mommy kin ganta ko, sai kace wani girmana tayi” riƙe baki Mufeeda ta yi ta ce"sannu yarinya, au ni sa'arki ce?” tsaki Mommy ta yi ta ce“Mufeeda ranki zai ɓaci fa, ki fita hanyar yarinyar nan” girgiza kai tayi bata ce komai ba ta tashi ta bar wajen. Mommah ta ce“sauran idan kin je ki tsaya shashanci, karki mai da hankali akan karatun ki” gyaɗa mata kai Nayla ta yi ta ce“Zan yi Mommah, kuma ban faɗawa Yaya Zayyad zan fara zuwa school ba”


“Idan kin faɗa masa me zai yi miki?”


“Sai ya ƙaramin kuɗi Momma, yana da kuɗi dayawa wlh, kuma ma nasan Aunty zata bani kuɗi”


Shiru Momma ta yi sai kuma ta ce“with Aunty?” cike da son surutu Nayla ta ce“wata ce, mun taɓa zuwa wajenta tare da Yaya daya kai ni Magic land, she's so beautiful wlh, kuma tana da kirki fa” murmushi Mommy ta yi ta ce“Ki ce In-lawa ɗinmu ce” gyaɗa mata kai Nayla ta yi sai kuma ta ce“Allah yasa ya aureta Mom, zaku ganta, ta burgeni”


“Zaki shige ki tafi ko kuma zancen zaki ci gaba dayi?”


Mommah tafada tana kallonta, turo baki ta yi, ta ɗauki slice ɗin cake ta saka a baki sannan ta bar wajen tana cewa


“Goodbye Mommy, Goodbye Momma”


Girgiza kai Mommy tayi tana murmushi ta ce“Nayla kenan” murmushin itama Momma ta yi ta tashi tana cewa“Bari naje na shirya dan kar Hajiya A'isha tazo tana jirana” jinjina kai Mommy ta yi ta ce“Aikuwa dai, ya kamata ace ma kun je da wuri, Allah ya sanya Alkhairi, ya nuna mana ranar auren yaran nan haka. Musamman Zayyad” Murmushi Momma ta yi ta ce“Aikuwa, daman Inason magana dake akan haka, bari dai naje na dawo”


“Tom, a dawo lafiya” cewar Mommy.


****Zaune yake cikin office ɗin nasa, ya kishingiɗa da kujerar da yake kai, idanunsa a lumshe. Gabaɗaya ya gaji da surutun nata, dafe kansa ya yi ya buɗe idanunsa yana kallonta ya ce a hankali “Angel” murmushi ta yi tana kallonsa ta ce“Na'am Bae” yanda tayi maganar ya sanya shi tashi zaune sosai ya zuba mata idanu yana kallonta. Fara ce tas kuma kyakkyawa, tana da siririyar fuska da pointed nose bakinta ɗan ƙarami yasha Avon lipstick, sanye take da wata t-shirt fara sai tomy skirt baby pink, kanta ɗaure da jersey veil pink, babu kwalliya a fuskarta amma tayi wani irin siritaccen kyau. Hannunta ya riƙe cikin nasa yana murmushi ya ce“baki gajiya da surutu ne?” waro idanunta ta yi ta ce“in dai kai nake yiwa bana gajiya Bae”


“Saboda me?”


Ya yi maganar fuskarsa a sake, murmushi ta yi ta ce“Just because I love you, i can't do without you Bae” jinjina kansa ya yi ya ce“my cute Angel, she don love me” dariya tayi ta kai hannunta fuskarsa ta shafa cute beard ɗinsa, ɗayan hannun nasa ya sanya ya janye nata daga fuskarsa ya ce“tashi muje na mayar dake gida” langwaɓar da kai ta yi sai kuma ta ce“har ka gaji dani?” girgiza kansa ya yi ya ce“Idan baki so zauna till down” yanda ya yi maganar ya sanyata dariya ta girgiza kanta ta ce“Ni ba yanzu zan tafi ba to, ina nan har sai ka tashi” jinjina kansa ya yi, daidai lokacin aka buɗe ƙofar office ɗin, kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai, ya juya ya fita. Taɓe bakinta ta yi sai kuma ta ce“Wai mene matsalar Ahmad ɗin nan ne? Ni wlh bana son shi”


"Nima bakya sona kenan!”


Ya faɗa yana janye hannunsa daga nata, girgiza kanta tayi ganin yanda ya haɗe rai lokaci guda ta ce“A'a fa, ina sonka mana, kai ma kasani ina sonka”


“Idan har zaki ce baki son jinina ai nima baki sona, ko kin manta Ahmad cousin ɗina ne? Koma ba haka ba he's a friend of mine so you have to respect him, but in front of me ki ke cewa bakya son shi” ya ƙare maganar yana harararta. Shiru tayi for some seconds sai kuma ta ce“I'm sorry to” Ya ɗauke kansa, ta sake maimatawa. Sai da faɗa sau uku sannan ya juyo ya kalleta.


“Tashi na maida ki gida”


“Ni tare zamu kwana fa”


Taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“Look, I'm not in that mood today, I can't! I Just can't” girgiza kai tayi ta ce a shagwaɓe “Amma ni ai ina so” ɗauke kansa ya yi zata sake magana ya ce


“Aneeserh”


Jin yanda ya kira sunan nata ya sanyata yin shiru, ta tashi tana kallonsa ta ce“Sai anjima”


“lemme drop you”


Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a ka barshi aiki ka ke ai, zan tafi da kaina” taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“daman kin fito da mota ne?” Aneeserh ta ce“A'a I'll call my driver don't worry” jinjina mata kai ya yi ya ce“Okay then, bye” gyaɗa masa kai tayi kawai ta juya ta fice daga office ɗin yabi bayanta da kallo. Tana fita Ahmad ya shigo fuskarsa a haɗe ya zauna bai ce komai ba, kallonsa Zayyad ya yi sai kuma ya taɓe baki ya ɗauki wayarsa yana dannawa.


“Wai yanzu haka zaku ci gaba da wannan yarinyar?”


Ɗago kansa ya yi ya ajiye wayar kan table in a serious tone ya ce“Me kuma tayi maka?”


“Kwata-kwata babu tarbiyya a tare da yarinyar nan, ba kuma tada kamun kai, a haka zaka aureta ka kai ta gidanka matsayin mata?” ɗan murmushi Zayyad ya yi ya dafashi ya ce“Mr man, calm down, mene laifin Aneeserh? Mene tarbiyyar da ita bata da? Me tayi ba daidai ba?” a ɗan fusace Ahmad ya ce


“Oh, you're questioning me? Duk abubuwan da take baka gani kenan? Kalli irin shigar da take yi tana fita” ɗaga masa hannu ya yi ya ce “Heyy! Calm down mana, me shigar ta tayi? Ina ruwanka da life style ɗinta? Ni nakesonta kuma zan zauna da ita a haka so you don't need to be worry” jinjina kai Ahmad ya yi ya ce“Haka ne, babu abin da ya dameni, ka aureta, amma ai kaje islamiyya kuma kasan abin da yake dai dai daba dai dai ba, duk da kai ma takewar kake, sai hali yazo ɗaya daman ake iya zama waje ɗaya, da kai da ita duk ɗaya” a fusace Zayyad ya tashi tsaye yana harararsa ya ce“Na take gaskiyar ina ruwanka? Mene naka a ciki? Ahmad! Ahmad! Ka bar ganin ina raga maka wlh idan ka ƙureni ba zaka ji da daɗi ba” tashi shima Ahmad ɗin ya yi yana kallonsa ya ce“Ai ba sabon abu bane, ka wulaƙantani, kayi duk abin da kake ganin zaka yi Zayyad, wlh bazan fasa faɗa maka gaskiya ba!”


Zayyad haɗe hannayensa ya yi alamar roƙo ya ce“To malam Ahmad wanda yasan gaskiya, Zayyad baya buƙatar gaskiyarka, ka riƙe a barka dan Allah” murmushin takaici Ahmad ya yi ya ce“Haka kace?”


“Eh, haka nace”


Ahmad bai sake cewa komai ba ya juya ya bar office ɗin, tsaki Zayyad ya yi sannan ya koma ya zauna. After two minutes ya tashi ya ƙarasa inda fridge ɗin office ɗin yake ya buɗe, wata bottle ɗin Red snow wine ya ɗauko ya dawo ya dire kan table ɗin, ya koma ya ɗauko wani ɗan ƙaramin glass cup. Zama ya yi kan kujera ya tsiyaya giyar ya kai bakinsa yana sipping a hankali, sai da ya sha cup 2 kafin ya ajiye ya jingina da jikin kujerar ya lumshe idanu yana jin komai na saukar masa.


Kabayi, Nassarawa state.

4:50pm


Durƙushe take gaban kurfotin time to time take jan tsaki, tun ɗazu take abu ɗaya gawayin yaƙi kamawa, gashi ita kaɗai ce a gidan, tashi tayi tana tunanin inda zata samo ledoji dan yanzu duk ledar da mutum ya taɓa a jiƙe zai jita. Da sallama ya shigo gidan hannunsa riƙe da wata leda, ciki ciki ta amsa ya ajiye ledar hannunsa yana kallonta ya ce“Lafiya ki ke zarya?” cikin kunfar baki ta ce“To ba dole nayi zarya ba, tunda ni ce baiwa da komai zan yi, nafi awa ɗaya ina tsugune gurin wuta taƙi kamawa, ko yaron da zan aika ya samon garwashi ko leda babu, ita kuma waccen sarkin iyayin ta shige ta tafi makaranta” girgiza kai ya yi cikin sanyin murya ya ce“Yarinyar data tafi neman ilimi ita kike cewa mai iyayi? Daman neman ilimi iyayi ne?”


“To menene idan ba iyayi ba? Tunda bata da halin yin karatun? Sai ana buga buga” Umma Rahmatu ta bashi amsa, ɗan murmushi ya yi ya ce“Allah ya fito dake daga wannan duhun da ki ke ciki, Allah ya kawo haske” Umma ta ce“Ameen, Allah ya kawo mana Hasken cikin duhu dan nima nagaji da wannan masifar”...


Zaune suke cikin makarantar tasu, kowa hannunsa riƙe da Alkur'ani mai girma, dan lokacin angama ƙari. Addu'a malamin ya yi musu ya tashe su dan lokacin gefen magriba ne, sai da kowa ya tashi daga kan tabarmar sannan ta tsuguna ta naɗeta dan daman kullum ita take wannan aikin, bayan tagama ta shiga gidan da suke arowa ta mayar musu. Tana fitowa ta ganshi tsaye hannunsa riƙe da jakarsa, ta kalleshi ta ce“Sai da safe Malam”


“Ummusalma”


Taji ya yi kiran sunanta. Juyowa ta yi ta kalleshi ta ce“na'am malam” takowa ya yi inda take yana kallonta ya ce“Daman inason magana dake ne” shiru tayi sai kuma ta ce“Malam lafiya?” murmushi ya yi ya ce“bakomai Ummusalma, kawai daman Inason nafaɗa miki wata magana ne” gyara tsaiwarta ta yi ta ce“Tom, ina ji malam” shiru Malam Yusuf yayi na ɗan lokaci kafin ya ce“Wato Ummusalma na daɗe da wani abu a cikin raina, tun kina yar ƙaramarki halayenki suke burgeni, kuma naji ina da kwaɗayin ki zama matata idan har babu damuwa. Ina son ki yarda dani Salma, ki karbi soyayyata saboda Allah” wani irin abu Salma taji ya tsaya mata a ƙirji, so kuma? Malam Yusuf? Tuni hawaye suka wanke fuskarta, tabbas lokacin da zata daina zuwa makarantar nan ya yi, domin Abbanta ba zai taɓa lamuntar haka ba. Bata ce masa komai ba ta juya ta bar wajen tana tafiya kamar zata faɗi saboda sauri. Da idanu Malam Yusuf ya bita sai kuma ya yi murmushi


“Sai na mallakeki matsayin mata in sha Allah”...


Ana kiran sallahr Magrib ta shigo gidan, tsugune ta samu Abbanta yana alwala Umma kuma durƙushe inda take girki, cikin ladabi ta ce“Sannu da hutawa Abba” sai da ya idar da alwalar sannan ya kalleta ya ce“Ummusalma ina kika tsaya sai yanzu?” da sauri ta ce“Yau ba'a tashemu da wuri bane Abba shiyasa” ƙare mata kallo yayi ta sunkuyar da kanta.


“To shiga ki je ki ajiye jakar ki zo kiyi alwala” to kawai ta ce sannan ta shige ɗakinta, ita kuwa Umma Rahmatu ta bisu da kallo tana taɓe baki.


Bayan sallar isha'i yana zaune a ɗakinsa ta buɗe labule ta shigo, kallonta ya yi har ta ƙaraso gabansa ta zauna ta ce“Abba gani” ajiye Qur'anin hannunsa ya yi yana kallonta sosai cikin natsuwa ya ce“Meke damunki Salma? Faɗamin?” girgiza kanta tayi ta ce“Babu komai Abba” ɗan murmushi ya yi ya ce“karki damu faɗa min, ni mahaifinki ne, sannan kuma abokinki, duk abin da yake damunki ni za ki faɗawa, to karki ji nauyi na faɗamin ”


Ɗora kanta tayi akan cinyarsa ta fashe da wani raunataccen kuka, shiru Malam Habu ya yi yana jin hawayenta na sauka akan wandon yadin jikinsa, shafa kanta kawai ya yi bai hanata kukan ba, dan bai san dalilinta nayi ba. Sai da tayi mai isarta sannan tafara sauke ajiyar zuciya, tana jin zuciyarta wasai. Ganin na nutsu ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce“To yanzu faɗamin mene ne?” goge hawayen fuskarta ta yi ta ce“Abba Inason naga Ammina, Inason ganinta Abba” ɗan murmushi ya yi ya ce“Kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo Salma?” girgiza masa kai ta yi ya ce“To Amminki ta bar duniya Salma, kinga baki da damar ganinta, amma kina da damar yi mata addu'a” wasu tagwayen hawayen suka sake biyo kuncinta, da kansa ya goge mata yana murmushi ya ce“Kin girma amma kina kuka ko? Ki daina to. Ki nutsu ki cigaba da karatunki Allah ya yi miki albarka” jinjina kanta ta yi ta ce“Ameen Abba” shafa kanta ya yi ya ce“tashi ki je ki ci abinci ki kwanta” gyaɗa masa kai ta yi sannan ta tashi ta fice daga ɗakin. A tsakar gida ta hangi kwanon abincin nata ta ƙarasa ta buɗe, shinkafa da wake ce da manja, ta ɗauka ta shiga ɗakinta.


“Ummusalma! Ummusalma”


Fitowa ta yi daga ɗakin da sauri tana faɗin “Na'am Abba” baƙar leda ya miƙa mata yana cewa“Na manta ban baki ba” hannu biyu ta sanya ta karɓa sannan ta juya ta koma ɗakin. Tana shiga ta buɗe ledar, gunduwar kifi sukunbiya ce a ciki, ta yi murmushi tana jinjina ƙarfin hali irin na Abbanta, koda ba shida kuɗi amma yana da zuciyar faranta masu.


****Rahmatu ta kalleshi ganin ya yi shiru bai ce komai ba, ta sake cewa“Malam kayi shiru” tashi ya yi daga kashingiɗan da yake ya kalleta sosai ya ce“Rahmatu kin san me ki ke faɗa kuwa? Na cire Ummusalma daga makaranta ta koma talla akan titi haka ki ke so?” girgiza kanta ta yi ta ce“A'a, A'a fa Malam, baka gane abin da nake nufi bane. Ba wai nace Salma ta daina zuwa makaranta ba, amma ta daina zuwa ɗaya, ko bokon ce tunda ba wani amfanin zuwan yake mata ba” girgiza kansa ya yi ya ce“Shekarar ƙarshe take, kuma cikin zangon ƙarshe shine ki ke so ta bar makarantar? Saboda wani ƙuduri naki?” shiru ta yi ya sake cewa


“Rahmatu na tambayeki shin akwai abin da bana yi muku ne? Duk abin da yake na dole ina ƙoƙarin ganin nayi muku daidai ƙarfina, meyasa ki ke saka son zuciya cikin al'amuranki?”


“Amma Malam...”


Ya katseta ta hanyar ɗaga mata hannu. Shiru tayi tana kallonsa ya ce“Dan Allah Rahmatu ki rabu dani, gobe inada aikin gini da wuri Inason na kwanta” takaici ne ya isheta ta tashi ta fice daga ɗakin.


“Allah ya kyauta” Malam ya faɗa yana girgiza kai...


Daren ranar rabi da rabin bacci Salma ta yi, maganar Malam Yusuf ta tsaye mata arai, tunanin yanda gobe zata shirya taje makarantar take. Tana jin an fara kiran sallar asuba ta tashi ta fito tsakar gida, da hasken farin kwai kasancewar akwai wutar NEPA a lokacin, ta ɗauki buta ta shige banɗaki. Tana fitowa ta tsuguna nan wajen tayi alwala sannan ta koma ɗaki, tana ji Abbanta ya fito ya yi alwalar shima amma ban da Rahmatu. Tana idar da sallar asuba ta zauna tana bitar karatunta har wajen ƙarfe 6:30am. Bayan ta gama ta tashi ta gyara ɗakinta sannan ta fito tsakar gida, tsintacciya ta ɗauka ta hau shara gudun kada ta makara a makaranta. Tana gamawa ta haɗa wanke-wanke tafara, tana cikin yi ya fito daga ɗakin, ta tashi ta je har inda yake ta gaishes shi. Da fara'a ya amsa ya kalleta ya ce“baki jin sanyi Ummusalma?” ɗan murmushi ta yi ta ce“Ai Abba banason na makara ne shiyasa” jinjina kai ya yi ta tashi ta koma ta cigaba da abin da take, gani tayi ya ɗebo kayan gininsa ta kalleshi ta ce“Abba da wuri zaka fita aikin?” gyaɗa mata kai ya yi yana zaro wuƙar siminti ya ce“Eh, aikin yini zan yi, to gara naje da wuri. In sha Allah zan samu na baki kuɗin jarrabawar idan na dawo” Salma ta ce“Tom Abba, Allah yasa” takalmin ya zura ya ce“Idan babarki ta tashi ki ce mata na ajiye kuɗi a gefenta ta sarrafa ayi abinci, sai na dawo”


“Allah ya tsare Abba” ta ce masa, ya amsa da Ameen sannan ya fita ya bar gidan.


Ƙarfe 7:40am tagama shiryawa, ta fito tana kallon Umma dake dama kunu ta ce“Umma zan tafi” a fusace ta ce“To Al huda huda, sai kin dawo, tun da makarantar ta ubanki ce da bazaki tsaya ki karya ba” sunkuyar da kai Salma ta yi sai kuma ta ce“Umma ai zan makara, ki ajiyemin sai nadawo zan sha” taɓe baki ta yi ta ce“Allah ya taimaka” Salma ta fita daga gidan, da idanu Umma ta bita ta ce


“Kinibabbiya”


A ƙofar gidansu suka haɗu da Fateema yar ajinsu, murmushi ta yi tana kallonta ta ce“Candy tamu” murmushi Salma tayi har sai da beauty point ɗinta ya Loma ta ce“Fatima kin tashi lpy?” Fatima ta ce“Lafiya klao beauty, mu tafi kar mu makara” to Salma ta ce sannan suka jera suna tafiya suna hira gwanin sha'awa. Suna shiga aji Malam Dawood ya shigo hannunsa riƙe da wata takarda, tsit ajin ya ɗauka ya fara kiran sunaye, sai da ya gama tas sannan ya ce wanda duk bai ji sunansa ba ya koma gida ya karbo kuɗin da ake binsa” tashi Salma ta yi tana kallon Fatima ta ce“na tafi, duk abin da aka yi ki biyo ki faɗamin kinji ” murmushi Fatima ta yi ta ce“Tom shikenan”.


Sallama ta yi ta shigo gidan, zaune ta hangi Umma ta zuba uban kunu a kofi tana haɗawa da ƙosan dake gabanta. Da mamaki take kallonta har ta ƙaraso ta zauna kan ƙofar ɗakinta, Umma ta ce“ke kuma lafiya?”


“Umma korarmu aka yi fa”


Dariya ta yi ta ce“Allah shi ƙara, maganinki ai kenan, kuma in sha Allahu kin bar makarantar nan kenan” haɗe rai Salma ta yi sai kuma ta ce“To fa Abba ya ce idan ya dawo anjima zai bani kuɗin daman” harararta Umma ta yi ta ce“Idan ya samo ba, ke ko tausayin uban naki ma bakya yi, ya yi ta fama yana buga buga yana magiya a bashi aiki, amma ke ba zaki yi zuciya ki dinga neman kuɗi ba” tura baki ta yi tana cewa“Kuma ai idan nagama makaranta nafara aiki zan gina masa gida, zan kuma kai shi makkah” ta yi maganar cike da wawta da yarinta. Taɓe baki Umma ta yi ta ce“To ayi mugani idan tusa zata hura wuta, kuma in sha Allah ba zai samo ba, naga ta tsiya” shiru Salma tayi hawaye na biyo fuskarta.


“Sai ki tashi ki cire kayan ki zo na aike ki gidan Hajiya Jinjin” tashi Salma ta yi daidai lokacin aka yi sallama daga waje, amsawa ta yi wasu maza suka shigo. Tashi tsaye Umma tayi, Salma ta dinga gwalalo idanu tana ganin yanda aka ɗauko Abbanta ɗaukan yara. Akan tabarmar da Umma ke zaune aka shinfiɗeshi, da gudu Salma ta ƙarasa gabansa tana kuka ta ce“Abba meya sameka? Me ya samu ƙafarka?”


“Yana cikin aiki ne a sama ya faɗo shine ƙafarsa ta karye”


Fashewa da kuka Salma tayi, Umma Rahmatu ta ɗora hannunta aka tana faɗin “Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, mun shiga uku” girgiza kai ɗaya daga cikin mazan ya yi ya ce“sai haƙuri, amma an kira mai ɗori an ɗora shi, sai fatan Allah ya bashi lafiya” daga haka suka juya suka fice daga gidan. Salma Kuka kawai take tana kallon Abbanta wanda idanunsa suke a lumshe da alama an yi masa har da allura ne, ta kalli Umma ta ce“Umma kin ga ko? Kalli Abbana Umma, mun shiga uku” harararta Umma ta yi ta ce“Ai duk kece sanadi, domin da badan shegiyar makarantar da ki ke ba da bai fita da safen nan ba, kin cucemu wlh” ta ƙare maganar tana sharar hawaye, girgiza kai Salma ta yi tana kuka ta ce“.


HCD#
08106608363,
Nanameera.

*HASKEN CIKIN DUHU💋*
Chapter 3 · 0% Book details