← Book details Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 28

Chapter 4: When Hope Fades

Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 18 min read

Nanameera, YOTA/23.


“A'a Umma, wannan ƙaddarace, haka Allah ya rubuta, da ace nasan idan Abba ya fita zai gamu da wannan masifar wlh dana haƙura da zuwa makarantar, dana hana shi fita, sai dai ban isa na hana abin da Allah ya rubuta faruwa ba, kuma...” Salma ta sake fashewa da wani kukan, harararta Umma ta yi ta ce“Rufa min baki anan, munafuka, ai yanzu kin ji daɗi, naga da uban da zaki koma makarantar, nagani” Komawa kusada Abbanta ta yi ta zauna tana kallonsa hawaye na biyo fuskarta, ita kuwa Umma ɗaki ta shige tana cigaba da masifa kamar Salma ce wadda ta sanya ya karye.


Abacha road, Mararaba.

5:45pm.

Compound ne mai kyau sosai, Yana ɗauke da flats biyu, dukkansu neat and modern. Gidan yana da spacious compound, akwai parking space sosai. Fence ɗinsa high ne da strong gate, yana bada security and prestige. Flowers da small trees sun zagaye gidan suna ƙara masa kyau da fresh look. Gidan ya haɗu, perfect for comfort and peace of mind. Zaune take kan veranda idanunta maƙale cikin glasses gabanta system ne na companyn Apple, tana dannawa a hankali, gefenta wani glass cup ne mai ɗauke da milk shake a ciki tana sipping a hankali. Horn ɗin motar ya sanyata ɗagowa, babbar mace ce ba zata shige shekaru 50 ba, tana da haske, bafulatana mai tsagu a gefen fuskarta, sai kana ganinta kaga kuɗi da kuma arziki. Ɗauke idanunta ta yi ta cigaba da kallon abin da take yi, a parking space ɗin gidan ya yi parking sannan ya fito, matashin namiji wanda ba zai haura shekaru 34yrs ba, shima kyakkyawan bafulatani ko ba'a faɗa maka ba kasan wannan matar ita ce Mahaifiyarsa. Yana zuwa veranda ɗin ya nemi kujerar dake facing nata ya zauna.


“Mami”

Ya faɗa kamar zai yi kuka, ɗago kanta tayi tana kallonsa sai kuma ta ce“Al-ameen ka dawo?” gyaɗa mata kai ya yi yana ƙoƙarin ɗaukan cup ɗin gabanta, harararsa ta yi ta ce“Oh daman kai ka ajiye?” langwaɓar da kai ya yi bayan ya ɗauki cup ɗin, ya kai bakinsa ya sha sannan ya ajiye yana murmushi ya ce“nagaji ne wlh” ɗan taɓe baki ta yi tana kallonsa ta ce“Tashi ka bar nan ni sai warin magani kake” tuntsirewa ya yi da dariya yana kallonta, wanda hakan ya sanya ita ma ta yi dariyar ta miƙe tsaye yana cewa


“Daman magani wari yake Mami?”


Banza tayi masa ta cigaba da abin da take, shima bai jira amsarta ba ya nufi entrance na gidan. Kai tsaye ɗakinsa ya shige yana duba agogon hannunsa


“Oh god!”


Ya faɗa yana girgiza kai. A gefen luxury bed ɗin nasa ya zare suit ɗin jikinsa sannan ya yi hanyar toilet. Ana kiran sallar magrib ya sakko daga upstairs, tsaye ya samu Mami tana jera warmers a dinning table. Kallonsa ta yi ta ce“Ina kuma zaka je?” murmushi ya yi ya ce“Mami masallaci zan je, daga nan kuma zan biya gidansu Mubarak”


“Sai ka dawo” tafaɗa ba tare da ta kalleshi ba. Kusan karo suka yi tana ƙoƙarin shigowa, baya ya yi yana cewa“wai yaushe zaki yi hankali ne?”


“Gobe”

Tafaɗa cike da tsiwa, Al-ameen bai sake bi ta kanta ba ya yi gaba abinsa, da harara ta bishi sannan ta shiga parlon tana kiran sunan Mami.


Asokoro, Abuja.


Da daddare around 8pm Momma ta shigo ɗakin, zaune ta samu Mommy tana magana da Mufeeda, tana ganinta ta ce“Ai nayi tunanin ma kin manta ne” girgiza kai Mommah tayi tana zama kan sofar ta ce“A'a wlh, na tsaya ƙarasa aiki ne kafin na fito” jinjina kai Mommy ta yi, tana kallon Mufeeda ta ce“Tashi ki je zamu yi magana” to ta ce sannan ta tashi ta fice daga parlon. Gyara zama Mommy tayi tana kallonta ta ce“Ina jin ki Khadijah” numfasawa Mommah ta yi sai kuma ta ce“Daman akan maganar Zayyad ne, naga ya girma yanzu, ya kamata ace an fara maganar aurensa ko hakan zai saka ya yi hankali” jinjina kai Mommy ta yi ta ce“Nima nayi wannan tunanin Allah ne bai nufeni da yi miki maganar ba, to amma yanzu ya ki ke ganin za'a yi?” shiru Momma ta yi na wasu sakwanni kafin ta ce“Ni da nace ko Fatiha ya nema, yarinyar Adda Maryam” shiru Mommy ta yi sai kuma ta ce“Hajiya Maryam taku?” gyaɗa mata kai Mommah ta yi, Mommy ta yi murmushi ta ce“Hakan ma ya yi sosai, yanzu tayaya za'a haɗasu?” murmushi Mommah ta yi ta ce“Wannan ba zai gagara ba, idan nace Zayyad yaje ya ganta tabbas zai je” jinjina kai Mommy ta yi ta ce“To shikenan, ayi hakan, ki samu kiyi magana dashi” tashi Mommah ta yi tana cewa“Tom Shikenan, bari naje na sameshi tun yanzu”


“To, Allah ya jisshemu Alkhairi”.


Da Ameen Mommah ta amsa sannan ta fice daga ɗakin. Tashi Mommy ta yi ta shige bedroom nata, wayarta ta ɗauka ta shiga danna kira, sai da tayi ringing sau uku sannan aka ɗaga, Mommy da ranta ya gama ɓaci ta ce


“Ina ki ka shige ne?”


Daga ɗaya ɓangaren wata mata ta ce“Kaga uwar gida a gidan Colonel Idris, matar soja, wlh ina can gurin Yallaɓai ne” shiru Mommy ta yi tana ayyana abin da zata ce, matar ta sake faɗin “Hello, Hajiya kina jina kuwa?” numfashi Mommy ta sauke sannan ta ce“Akwai matsala Hajiya, abubuwa na gab da lalacewa” cikin tashin hankali matar ta ce“Subhanallahi, me kuma ya sake faruwa?” girgiza kai Mommy ta yi ta ce“Maganar bata waya bace, gobe idan Allah ya kaimu zan zo gidan naki sai kiji abin da ake ciki” shiru matar ta yi can kuma ta ce“To Allah ya kaimu, ina nan ina jiranki” To Mommy ta ce sannan suka yi sallama ta kashe wayar. Zama tayi gefen gadonta tana saƙe-saƙe a ranta.


Momma na fita ta samu Nayla na ƙoƙarin shiga ɗakin Zayyad.


“Zaki je takura masa ɗin?”


Langwaɓar da kai ta yi tana cewa“Wlh Mommah ba takura masa zan yi, assignment ɗina nakeson ya yimin”


“Ku kuka sani dai” cewar Momma tana barin wajen. Tura ƙofar ɗakin ta yi ta shiga, shiru taji parlon babu alamar mutum sai tv dake kunne tana faman aikinta. Taɓe baki Nayla tayi sai kuma tayi hanyar bedroom ɗinsa, turus Nayla tayi, tayi baya tana toshe hancinta. Zaune yake kan kujera idanunsa zube kan marble Coffee table wanda yake ɗauke da bottle na wine da kuma cigarette kwali guda, sai shisha wadda yake zuƙa a hankali, hayaƙi sai tashi yake. Shigowar Nayla ya sanya shi ɗago idanunsa yana kallon inda yarinyar ke tsaye, tuni hawaye suka wanke fuskarta, sai girgiza kanta take hannunta bisa bakinta. Zare shishan ya yi daga bakinsa ya kashe, sannan ya tashi daga zaunen da yake, da gudu Nayla ta juya ta bar ɗakin, ya bita da idanu sai kuma ya yi hanyar toilet kawai. Wanka ya yi sannan ya fito ya gyara gashinsa sai sheƙi yake, ya shirya cikin wasu Burberry dark blue, ya sanya Gucci vandaner akansa ya feshe jikinsa da mayataccen turaren Clive Christian No.1 nan da nan ɗakin ya ɗumame da ƙamshi, ƙarasawa yayi ya kwashe komai dake kan table ɗin ya mayar dasu inda ya saba ajiyewa, sannan ya ɗauki car key ɗinsa da wayarsa ya fito kai ba zaka ce shine wanda ya gama shaye-shaye ba, he look quite and gently man. A corridor ya tsaya ya yi ɗan jim sai kuma ya yi hanyar ɗakin matan gidan. Tura ƙofar parlon ya yi bayan ya yi sallama wadda ba lallai a ji ba. Zaune take kan sofa idanunta zube kan system ɗin gabanta tana game, sanye take da wata Gucci oversized sweatshirt sai Celine wide pants, gashin kanta wanda yake ƙyalli ta yi parking ɗinsa a tsakiya, she looks elegant. Tana ganinsa ta rufe system ɗin tana murmushi ta ce“Welcome Yaya” kallo ɗaya ya yi mata ya yi hanyar bedroom ɗin Nayla yana faɗin “How are you doing”


“Fine Yaya” Mufeeda tafaɗa tana mai da hankalinta kan kallon da take. Can ƙarshen gadon ya hangeta ta cure jikinta waje ɗaya fuskanta cikin tsakiyar ƙafafunta tana shassheƙar kuka a hankali. Kasa ƙarasowa ya yi ya tsaya daga bakin ƙofar idanunsa harɗe a ƙirji yana kallonta. Above 5mins yana nan tsaye kafin ya ƙarasa cikin ɗakin yana tafiya a hankali, a gefen bedside drawer ya zauna yana kallonta, Hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta. Zabura Nayla tayi ta sauka daga gadon tana girgiza kanta, tashi Zayyad ya yi yana kallonta ya ce“Lil sis”


“A'a Yaya, banaso, ni ka tafi, ka tafi dan Allah” tayi maganar tana sake rushewa da kuka, ɗan murmushi ya yi ya ƙarasa gabanta tana ƙoƙarin barin wajen ya riko hannunta, hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen daya cika mata fuska yana murmushi ya ce“Guduna kike yi? Kina cewa na tafi Nayla?” girgiza kanta tayi tana cigaba da kukanta. Sakin hannunta ya yi yana murmushi ya ce“anyway, sai anjima” daga haka ya juya ya bar ɗakin, durƙushewa tayi a inda take tsaye tana cigaba da kuka. Ashe daman abun nasa har ya kai haka? Yayanta kuma a cikin gidansu?.


Zayyad na fita ɗakin Daddy ya nufa, zaune ya sameshi a parlon suna magana da wani Soja a waya, zama yayi kusada shi ya ɗauki remote ya can ja tasha zuwa Bollywood inda suke haska film ɗin Mohenjodaro. After some minutes Dad ya kalleshi yana ajiye wayar hannunsa ya ce“Har ka fito?” gyaɗa masa kai Zayyad ya yi, ya ajiye remote ɗin hannunsa ya juyo yana kallon Daddy ya ce“Dad inason zan yi tafiya ne” shiru Dad ya yi sai kuma ya ce“Ina kenan?” murmushi ya yi ya ce“Maybe London zan je, nagaji da zaman nan wlh, kwata-kwata bana jin daɗi” dafashi Daddy ya yi ya ce“Duk yanda kake so haka zaka yi Zayyad, ni ba zan takura maka ba, idan ka tsayar da ranar tafiyar sai ka min magana” sosai yaji daɗi a ransa shiyasa yafi son magana da Dad fiye da kowa, dan koda yaushe yana goyon bayansa, babu yanda za'a yi ya ce ga abin da yakeso ba'a yi masa shi ba. Tashi ya yi ya ce“Tom, duk yanda ake ciki I'll let you know, zan ɗan fita” jinjina kai Daddy ya yi yana kallonsa cike da so da ƙauna ya ce“Tom a dawo lafiya”. Zayyad ya fice daga sashin yana tafiya cike da isa da kuma taƙama.


Wuse 2, Abuja.


Kwance take akan gado tana danna wayar hannunta taji ana knocking ƙofar ɗakin


“Yes, coming”

Tafaɗa ba tare data ɗago ba. Buɗe ƙofar ɗakin aka yi wasu yan mata guda biyu suna shigo, muryar waɗanda taji ya sanyata tashi zaune tana kallonsu baki buɗe, sanye take da wata riga Dior blouse sai chanel tweed skirt, ta ɗaure gashin kanta da hermès scarf, sosai tayi kyau abin ta, duk da babu makeup a fuskarta amma ta saka eyeliner a idanunta ta kuma saka lip gloss a bakinta. Harararta Khairiyya tana cewa “why are you staring at us?” ɗan murmushi Aneeserh ta yi tana kallon Hibba dake tsaye ta ce“Have a sit mana Beb” wani banzan kallo Hibba ta watsa mata tana cewa“Sai kin ce min na zauna zan zauna?” tuntsirewa tayi da dariya ta ce“To sai kiyi ta tsaiwa ai” ta juya tana kallon Khairiyya ta ce“I thought ai da wasa kike fa” Khairiyya ta ce“A'a da gaske muke fa, mun je transcorp tun jiya da tuni mun shigo sai muka fasa kuma tunanin ko Dad yana nan” murmushi ta yi ta ce“sarkin tsoro to me zai yi muku? Bayanan ma” girgiza kai Khairiyya tayi ta ce“A'a kamarya mai zai yi mana? Kin san dai halinsa ai” Tashi tayi tana cewa “Ke dai kin fiye tsoro kawai” daga haka ta nufi inda fridge yake, coke mai sanyi ta ɗauko musu guda biyu ta haɗo da cups. A ƙasa ta ajiye sannan ta koma kan gadon ta tankwashe ƙafafunta tana kallon Hibba ta ce“Manyan mata, Hibba naga kina wani ƙara jiki mene sirrin ne?” ɗan murmushi ta yi ta ce“Ke matsalata dake kenan, kamar ya ina ƙara jiki”


“Tana nufin taga kin sauya” cewar Khairiyya tana ƙoƙarin buɗe coke ɗin hannunta. Harararta Hibba ta yi ta ce“To nima ban sani ba” dariya Aneeserh ta yi ta ce“Shikenan, idan tayi tsami ma ji”


“Ba ma zata yi ba. Wai kuwa Aneeserh ina Zayyad?” Hibba ta tambaya tana kallonta. Aneeserh dake danna wayarta ta ce“Yana nan wlh” Hibba ta sake cewa “Ɗan girman kai da jin kai” Aneeserh ajiye wayar hannunta tayi tana kallon Hibba ta ce“To bari kuma. Girman kan me ya yi miki? Kinga Hibba banason ana taɓa min miji rai zai ɓaci” tuntsirewa da dariya suka yi a tare Khairiyya ta ce“Wai miji, abokin rayuwarki dai kawai” Aneeserh ta ce“Like how? Bangane ba”


“Aneeserh mene baki gane ba? Cewa nayi abokin rayuwarki ne shi ba mijinki ba, domin ba lallai bane ya aureki” wani mugun kallo Aneeserh ta watsa mata tana cewa“Haka yace miki ai ko? To bari kiji Zayyad shine mijin aurena, in har na tashi aure to Zayyad zan aura” jinjina kai Hibba tayi ta ce“Muma shine fatanmu, Allah yasa ya aureki”


“Ai ma kamar ya aureni ne” Khairiyya ta buɗi baki zatayi magana wayar Aneeserh ta shiga ringing, ɗaukan wayar tayi sai kuma ta saki wani murmushi tana kai wayar kunne


“I'm outside, ina jiranki”


Taji muryasa. Numfasawa ta yi ta ce“Tom gani nan” daga haka ta kashe wayar, kallonsu Khairiyya ta yi ta tashi daga kan gadon tana faɗin “To ni dai saurayina yazo kuma zan bi shi, idan anan zaku kwana ne to” harararta Hibba ta yi ta ce“Tunda ke kaɗai ce mai saurayi wanda zai zo ya ɗaukeki ko?” ɗaga kafaɗa Aneeserh tayi tana cewa “Ni na sani”. Cikin mintuna kaɗan tagama shiryawa cikin wata riga doguwa wadda ta tsaya iya gwiuwarta, ta gyara gashin kanta sai sheƙi yake, wayarta ta ɗauka tana kallonsu ta ce“Ya kuka ganni” tafaɗa tana juyawa. Murmushi Hibba ta yi tana cewa“Kin yi kyau yarinya kamar bake ba” sosai Aneeserh taji daɗi jin sun yabeta ta tabbata haka Zayyad ɗinta zai yabeta idan ta fita. Koda suka sakko ƙasa babu kowa a ƙaton parlon hakan yasa suka yi waje a bin su. A bakin gate ɗin gidan ta hangi motarsa Lexus jeep, ta ƙarasa tana tafiya cike da kwarkwasa. Front seat ta buɗe ta shiga tana kallonsa ta ce“Sorry Bae I keep u waiting” tayi maganar a shagwaɓe. Murmushi ya yi ya ce“Kin yi kyau” dariya Aneeserh tayi tana cewa “Thank You, ina zamu je?”


“Transcorp” ya faɗa yana yiwa motar key.


****Ranar Saturday da yamma suna zaune a parlon suna hira ya shigo, Tashi Nayla ta yi ta bar parlon ba tare da ta kalleshi ba. Murmushi Mommy tayi tana kallonsa ta ce“Wai meya haɗaka da mutuniyar?” girgiza kansa ya yi yana zama kan sofa ya ce“nothing kawai shirmenta ne” Mommy ta ce“Nayla uwar rigima ita har yanzu autar bata barta ba” Mufeeda dake zaune kan kujera tana danna waya ta ce“Wlh Yaya Nayla taba da kai, kullum fa sai tayi kuka har can dare bata yin bacci” shiru Zayyad ya yi bai ce komai ba, Mommy ta kalleshi sai kuma ta kalli Mufeeda ta ce“But kin tambayeta me aka yi mata? Ko a school ne ake ɓata mata rai?” girgiza kai Mufeeda tayi ta ce“Babu wani a school da ake ɓata mata rai fa Ita dai tasan abin da ya dameta, kuma nafaɗa mata zan faɗawa Daddy idan ya dawo daga Paris” Tashi Zayyad ya yi ya bar parlon suka bi shi da kallo. Kai tsaye apartment ɗin su Naylan ya shiga, ya buɗe ɗakinta amma bata ciki, fitowa ya yi ya shiga apartment ɗin Mommah. Zaune ya hangeta kan kujera hannunta riƙe da handout tana karatu, ajiyar zuciya ya sauke sai kuma ya ƙarasa ciki, Zama ya yi kan sofa tayi saurin tashi tsaye ta haɗe takardunta tana shirin barin wajen


“Nayla” Zayyad ya kirata da kakkausar murya. Cak ta tsaya amma bata juyo ba, ya tashi ya ƙarasa gabanta, juyo da fuskarta ya yi yana kallonta saurin shigewa jikinsa tayi tana sakin kuka. Tsaf ya rungumeta jikinsa yana shafa kanta, sai da yaji tayi shiru sannan ya ɗago kanta yana goge mata hawayen ya ce“I'm sorry” cikin shassheƙar kuka ta ce“Dan Allah Yaya kadaina, wlh it's totally haram, ka daina kaji” numfashi ya furzar still looking at her ya ce“shikenan, muje ki rakani” hannunta ta miƙa tana cewa“then promise me you won't do it again” Lulu eyes ɗinsa ya zuba mata sai kuma ya ce“Then u didn't trust me?” girgiza kanta tayi ya ce“Alright muje”.


“Maganar me kuke yi naji ana ba'a yarda ba?” Suka ji maganar Mommah akansu, juyowa Nayla ta yi tana cewa“Chocolate nace ya siyomin shine ya manta fa Mommah” taɓe baki Momma tayi tana faɗin “I see” daga haka ta kalli Zayyad wanda ke tsaye ta ce“Zayyad Inason magana da kai”


“Tom Mommah bari naje nadawo”


“Kaje Ina?” tafaɗa tana tsare shi da idanu, komawa ya yi ya zauna yana murmushi ya ce“Na tuba” harararsa ta yi sannan ta zauna tana kallon Nayla ta ce“Madam yi tafiyarki” tura baki Nayla tayi sannan ta fice daga ɗakin. Gyara zama Mommah tayi tana kallonsa ta ce“Daman Inason nayi maka magana ne akan batun aurenka domin naga kamar kai hakan baya gabanka ma” langwaɓar da kai ya yi ya ce“Mommah aure kuma? Har yaushe nayi girman da zan bar gabanku?” baki buɗe Mommah ke kallonsa kafin ta ce“Zayyad ka fita a idona, idan baka yi aure yanzu ba sai yaushe ka shirya yi kenan? Sa'anninka duk sun ajiye iyali amma kai ka zauna kana faman shashanci. To bari kaji kafin mahaifinka ya dawo ka fitar da matar aure, idan kuma babu to ni na fitar maka” shiru Zayyad ya yi yana kallonta ganin how serious she's. Ta ce“Sannan kana sane da Adda Maryam batada lafiya ban ji kace zaka je dubata ba” Zayyad ya ce“Eh mun yi maganar da Ahmad, maybe gobe zan je in sha Allah, bana son shiga garin nan traffic ya yi yawa wlh” harararsa ta yi ta ce“To ka fasa zuwa kaji, shi Ahmad ɗin da kullum yake tawowa daga can bai ce komai ba sai kai”


“But Mommah shi ya saba da zaman can daman, garin gabaɗaya mutane sun yi masa yawa, tafiyar mintuna ashirin amma idan baka yi sa'a ba sai ka yi awa, suna fama” tashi Mommah tayi tana cewa“Sannu wanda baya fama” dariya Zayyad ya yi sannan shima ya miƙe yana cewa“Zamu je tare ne?” girgiza kai tayi ta ce“A'a ni naje, amma idan zaka tafi ku tafi da Nayla taga Fatiha” okay ya ce sannan ya juya ya fita, ita kuma ta koma kitchen dan cigaba da abin da take.


Kabayi, Mararaba.


Da salamma ta shigo gidan hannunta riƙe da wata ƙatuwar cooler, sanye take da hijabi yadin ɗan Abba coffee colour wanda ya tsaya iya gwuiwarta sai wata doguwar rigar yadi baƙa a jikinta, zaune ta hangeshi kan tabarma ta ƙaraso gabansa tana kallonsa ta ce“Sannu Abba ya ƙafar taka?” madadin ya bata amsa sai taga hawaye na zuba akan idanunsa, rikicewa Salma tayi cikin tashin hankali take faɗin“Abba meya faru? Kafar ce? Kayi hakuri Abba” ta ƙarashe maganar hawaye na biyo fuskarta. Malam Habu kallonta kawai yake har sannan hawaye bai daina zuba daga idanunsa ba, girgiza kanta tayi tana cewa“Dan Allah Abba kayi hakuri Allah zai yaye maka” yatsansa ya sanya ya goge hawayen dake idanunsa cikin sanyin murya ya ce“Ummusalma ba wai ina kuka bane saboda Allah ya jarrabeni, A'a ina kuka ne saboda nagaza a matsayina na mahaifi, na gaza. Na kasa kare rayuwarki, har yau ta kai kina fita talla domin sama mana abin da zamu ci, Ummusalma wane irin ubane ne? Sam ban cancanci zama mahaifi ba, nagaza!” girgiza kai Salma ta shiga yi tana kuka ta ce“Dan Allah ka daina faɗar irin haka Abba, tabbas ka ubane wanda kowace ƴa ke fatan samun kamarsa. Ka tsaya kai da fata wajen ganin ka kare mutuncina, duk da bakada hali hakan bai sa nayi kuka akan wani abu ba, Abba ka cancanci yabo, wlh ban taɓa ɗaukar dan nafara fita sana'a gazawarka bane, ƙaddarace. Haka Allah ya tsara mana, kuma malam ya faɗa mana ba'a iya gujewa ƙaddara, saboda haka ka daina damun kanka Abba, fatanmu Allah ya baka lafiya”


Malam Habu kallonta kawai yake yana sake godewa Allah cikin ransa daya bashi Ummusalma a matsayin Ƴa, jinjina mata kai ya yi ya ce“Allah ya yi miki albarka, ya kula da rayuwarki, ya haɗaki da masu sonki tsakani da Allah” da Ameen ta amsa sannan ta tashi ta shige ɗakinta. Gab da Magriba ta shigo gidan hannunta riƙe da leda, zaune ta sameshi inda yake ta zauna gefen tabarmar tana cewa


“Wash Allah!”

Kallonta ya yi amma bai ce mata komai ba, ganin coolern da tayi yasa ta ce“Allah dai yasa Salma kin siyar da lemon nan kafin ki ka dawo” Salma dake kunna wuta ta ce“Eh Umma na siyar sauran leda biyu ne ya rage, to kuma inason na dawo wajen Abba tunda ke bakya nan shiyasa ban siyar ba” taɓe baki Umma tayi ganin idon Malam Habu ta ce“Da kin tsaya kin siyar ɗin me zai cijeshi a gida, ke wai uwar kinibibi” shiru Salma tayi bata ce komai ba, Umma ta tashi ta buɗe cooler, lemon tsamiya ne mai sanyi guda biyu ta ɗauko ta dawo ta zauna, miƙa masa leda ɗaya tayi tana cewa“Gashi kai ma ka jiƙa maƙoshinka” kallon ledar lemon ya yi sai kuma ya kalleta, amsa ya yi ya ajiye gefensa, ita kuwa tafasa na hannunta tafara sha. Around 8pm tana zaune kusada Abbanta yana mata ƙari wani yaro ya shigo yana cewa


“Salama alaikum wai Salma tazo”


Wata irin faɗuwar gaba Salma ta ji, ta saci kallon Abbanta taga ya ɗago yana kallon yaron ya ce“In ji wa?” komawa ɗan ya yi, bayan minti ɗaya ya shigo ya ce“Wai in ji wani” shiru Abba ya yi Umma da fitowarta kenan daga banɗaki ta kalli yaron ta ce“kai je kace masa to, gatanan” juyawa ɗan ya yi ya fita, Salma ta ɗago tana kallonta. Fuska a hade ta ce“Kin bar mutum a tsaye ba zaki je kiga kowane ba” Salma marairaice fuska tayi ta ɗago ta kalli Abbanta taga ba ita yake kallo, sake kallon Umma ta yi ta ce“To ai ni ban san wane ba Umma” a fusace Umma ta ce“To zauna sai kin san wane sannan ki tashi” Jiki a sanyaye Salma ta tashi ta shige ɗakinta, Hijabinta na ɗazu ta ɗauko ta saka, ta zura slippers ɗinta dake Kofar ɗakin tayi waje tana waigen Abbanta. Turus tayi a ƙofar gidan nasu ta dinga kallonsa kamar idanunta zasu faɗo.


“Ummusalma”.

# HCD
Nanameera,
08106608363.

*HASKEN CIKIN DUHU 💋*
Chapter 4 · 0% Book details