← Book details Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 28

Chapter 21-22: The mask of generosity

Hasken Cikin Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 22 min read

Nanameera, YOTA/23.


Girgiza kai Salma ta yi ta kalli Zayyad wanda ke kalle-kallensa ta sauke nunfashi sai kuma ta kalli mai Napep ɗin ta ce“Baba sauka zamu yi” Ba tare da ya juyo ba ya ce“Haba yarinya da kin ɗan jira, Yanzu zasu gama aikinsu, Ƙarshe wani mai laifin suke nema” Salma bata saurareshi ba ta kalli Zayyad ta ce“Sauka muje Yaya Yad” Kallonta ya yi sai kuma ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce“Ki bar ni anan Mommah, asibiti fa zan je”


“Idan mun sauka zan kai ka asibitin sauka na ce”


Daga haka ta kama hannunsa suka sauka daga Napep ɗin, Ta cikin motoci suka ratsa suka bar titin. Tafiya kawai suke Zayyad na bin ta amma fuskarsa a haɗe babu wata walwala.


Sun yi nisa da titi yaja ya tsaya, Juyowa ta yi ta kalleshi ta ce“Muje mana” Ɗauke kansa ya yi yana kallon gefe, Ta dawo gabansa ta ce“Muje mana yamma nayi” Banza ya yi mata, Ta ja hannunsa ya fizge, Baki buɗe take kallonsa sai kuma ta ce“Yaya Zayyad kana son mu kwana anan ne? Common let's go mana” Ba zaka taɓa ɗauka da Zayyad take magana ba dan ko kallonta bai yi ba. Gajiya ta yi ta dawo bayansa ta dinga tura shi kamar mota yana turjewa, Daga ƙarshe ta sake shi tana haki. Neman waje ya yi ya zauna, Salma ta kalli Hanya ganin jama'a na shigewa sosai ta tsuguna gabansa muryarta na rawa ta ce


“Dan girman Allah Yaya ka zo mu tafi kaji, Zan siya maka chocolate fa”.


Kallonta kawai ya yi, Ta gyaɗa masa kai ya sake ɗauke kansa alamar zancen sam bai masa ba, Furzar da numfashi ta yi sannan ta sake cewa


“To zan siya maka biscuit da alawa”


Wannan karon ko arzikin kallon bata samu ba, A karo na barkatai ta sake cewa “Okay zan kai ka wajen Mommah” Da sauri ya kalleta ta gyaɗa masa kai, murmushi ya yi ya tashi har da kaɗe jikinsa ya yi gaba ya bar ta a tsugune. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta tashi ta bi bayansa.


****Sojoji biyu ne suka tsaya gaban Napep ɗin, Ɗayan ya ɗora hannunsa samanta yana kallon drivern ya ce“Baba tambaya muke” Mai Napep ɗin ya ce“To Yallaɓai Allah yasa na sani” Wani hoto ya zaro ya nuna masa ya ce“Kaga ɗaya daga cikin waɗannan?” Sake wara idanunsa ya yi kan hoton Zayyad da Salma wanda aka haɗe waje ɗaya. Ya ɗago ya kalli sojan sai kuma ya sake sunkuyar da kansa, Kenan dalilin daya sanya yarinyar ta ce sauka zasu yi kenan? To laifin me suka yi? Kamar mahaukaci ne ɗayan ai.


“Baba kana ji”

Maganar sojan ta dawo dashi daga tunanin daya tafi, Ya ɗago kansa yana kallonsa.


“Ka gansu ne?”


Sai kawai ya girgiza kansa a sanyaye ya ce“Ban gansu ba Yallaɓai, Ni babu wanda na ɗauko ma” Sojan suka kalli juna sai kuma ya gyaɗa kai ya ce“Alright” Daga haka ya yi gaba yana yi wa ɗayan signal da hannu. Sojan ya kalli mai Napep ɗin sai kuma ya ce“Get down Baba” Mai Napep ɗin ya sauko ƙasa jikinsa na rawa ya ce“Wani abun ya faru Yallaɓai? Wallahi ban gansu ba” cakumeshi ya yi ya fara tafiya dashi, Ya dinga magiya yana cewa bai gansu ba amma bai saurareshi ba, A gaban wata Hilux white colour ya tsaya, Ɗaya daga sojojin dake tsaye jikin motar ya buɗe ƙofar, General ne zaune kan kujera sanye da uniform na sojoji idanunsa maƙale cikin glasses black, Sojan ya sara masa sannan ya ce


“Sir gashi, An ce an gansu a Napep ɗinsa amma ya ce basu shiga ba”


General ya ɗago kansa ya kalleshi, Ajiye wayar hannunsa ya yi ya fito daga motar ya ja kwalar rigar mai Napep ɗin duk da shekarunsa, Fuskarsa a haɗe babu alamar annuri ya ce


“Hey mr man! Ina suke?”


Jikinsa na wata irin tsuma muryarsa na rawa ya ce“Wallahi wallahi ban gansu ba, Ban san su ba. Ni babu wanda na ɗauko”


Jinjina kai General ya yi sai kuma ya sake shi, Ya kalli sojan ya ce


“Ku je dashi duk abin da ya kamata a yi masa har sai sanda ya faɗi in da suke”


Sake sara masa ya yi ya ce“Okay Sir!”


Sannan ya ja wuyan mutumin, Kuka ya fara yi yana cewa“Dan Allah Yallaɓai ku rabu dani wallahi ban san su ba” Babu wanda ya sauraresa a cikinsu a haka aka shige dashi mota.


****

Around 6:00pm suka iso tashar, Zayyad ya kalleta kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, Ƙarasawa ta yi tana tambaya motar Kaduna, Dakyar ta samu shima drivern ya ce ba zai tafi ba sai bayan sallar magriba, Haka kuwa aka yi suka zauna suna jiransa, Ta siyawa Zayyad abinci ya cinye tas dan ita ta ci abinci gidan Hajiya Turai. Ana idar da sallar kuwa motarsu ta tashi zuwa Kaduna, Basu yi nisa ba Zayyad ya fara jin bacci, Kasancewar a kusa da ita yake ya sanya ya ɗora kansa gefen kafaɗarta nan da nan bacci ya ɗaukeshi, Ita kuma ta ci gaba da kallon hanya tana jin kamar tafiya ce wadda ba zata sake dawowa Mararaba. Tana jin kamar wata sabuwar ƙaddarar ce take shirin kai ta Kaduna, Sai dai ta yarda kowace kaddara ce zata iya jureta muddin zata zauna tare da Zayyad.


****Ana idar da sallahr Isha'i suka shigo gidan, Mami na zaune kan sofa tana danna wayarta. Ganin jikinsu a sanyaye ya sanya ta ce


“Ya ake ciki? An same su?”


Zama Ahmad ya yi kan sofa ya lumshe idanunsa yana cewa“A'a Ba'a same su ba, Amma an samu wanda suka hau napep ɗinsa” Shiru Mami ta yi can kuma ta ce“Ina yake to?”


Al-ameen dake tsaye ya ce“General ya saka an tafi dasu, But you know what Mami ba lallai bane a samesu wallahi”


Wani banzan kallo Mami ta watsa masa wanda ya sanya shi sunkuyar da kai, Sannan ta ce“A saboda kai ne ka ke nemansu ko kuma ka san inda suke ba”


Girgiza kansa ya yi ya ce“Allah ya huci zuciyarki Mami, Ni fa kawai faɗa nayi”


“Eh shi faɗar, Get out from my side Malam!”


Al-ameen bai sake cewa komai ba ya nufi stairs yana tafiya da sauri, Kai tsaye ɗakinsa ya shige ya zauna gefen drawer yana tunani, Can ya zaro wayarsa a aljihu ya ɗan juyata sai kuma ya shiga phone, Wasu lambobi ya rubuta ya tsaya yana kallon screen ɗin wayar above 2mins kafin ya danna kiran ya saka a speaker. Ringing ta dinga yi har ta gama ba'a ɗaga ba, Ya sake kallon screen ɗin yana mamakin rashin ɗagawar tata. Sake kira ya yi nan ma har ta katse ba'a ɗauka ba kawai ya haƙura ya yi cilli da wayar kan gado sannan ya tashi ya shige toilet.


A can ɓangaren Mami tabi Al-ameen da kallo sai kuma ta numfasa ta ce


“Na something wrong with this boy, Akwai abin da yake ɓoyewa”


Jinjina kai Ahmad ya yi ya ce“I think so Mami, Dan ma baki ga yanda ya dinga behaving ba a wajen, Gaba ɗaya ma fa ba son a gansu yake ba”


Girgiza kai Mami ta yi ta ce“Duk abin da yake ɓoyewa ma zai bayyana ne sai dai idan ba Al-ameen bane”


Ɗan murmushi Ahmad ya yi ya ce“Mr talkative kenan, Wallahi Mami hankalina ba a kwance yake ba, Ko wane hali Zayyad yake, I dey missed him a lot”


Jiki a sanyaye Mami ta ce“In sha Allah yana nan lafiya a duk in da yake”


“Allah ya yarda”


Ahmad replied.


****

Iskar damina ta dinga tashi a hankali, tana ɗauke da ƙanshin ƙasa mai ɗumi da busasshiyar ƙura. Gajimare sun mamaye sararin samaniya, sun ɓoye komai sai ɗan ƙyalli daga fitilun motar da ke yanke duhun da gajimare suka lullube. Motar da suke ciki tana tafe a hankali kamar ta san cewa akwai wani sirrin da ke boye a gaba.

Salma na zaune a gefen taga, hannayenta rungume a kirjinta, idanuwanta na kallon wajen amma ba ta ganin komai. Ruwa kadan-kadan yana soma bugu a gilashin taga, Ta ɗan kai dubanta wajen. Hankalinta ba a kan tafiyar bane, sai akan abin da ke gabanta a Kaduna. A inda rayuwarta za ta canza, ko dai da alheri… ko kuma ta faɗa cikin duhun da ba ta san yadda za ta fito ba.

Ta juya kallonta ta kalli Zayyad wanda ke gefenta, Wanda a duniya kewa kallon mahaukaci, Sai dai ita a gurinta ba haka bane, Shi ɗin ƙaddararta ne yanzu, Shi ne kadai wanda ke da ikon kareta, ko halaka ta. Tunanin hakan ya haifar mata da wani irin yanayi a lokaci guda. Zuciyarta na bugawa da ƙarfi, tana tambayar kanta: "Me zai faru idan suka gane cewa muna tare? A kan me suke nemansa bayan su ne suka koreshi? Me ke shirin faruwa ne?.


Wata iska mai ƙarfi ta buso, ta ɗan jijjiga motar kaɗan. Ta runtse idonta, tana jin kamar ana kiranta da wata murya daga cikin duhu. “Ki dawo,” zuciyarta ta furta, “ki koma inda kika fito.” Sai dai hakan ba mai yiwuwa bane, Babu koma baya. Domin suna gab da shigowa Kaduna Kaduna, Kamar mafarkin da ba za ta iya farkawa daga cikinsa ba.

“Kin yi shiru,”


Ta tsinkayi muryar Zayyad wanda ya tashi ɗan mintuna da suka shige.


“Kina tsoron inda zamu je ne?, Mommah fa zamu gani”

Ta kalli fuskarsa, wadda take a kwaɓe Sai dai akwai wata shaida ta ciwo da ɓoyayyen gaskiya. Sai ta ɗaga kai a hankali, ta ce da ƙasa-ƙasa,

“Ban san abin da ke jiranmu a can ba.”

Ya yi murmushi mara annuri, yana cigaba da kallon titi.


“Mommah na can tana jirana Allah sarki, Ko ta sha paracetamol ɗin?”

Wata forked lightning ta fito a sararin sama, tana haska hanya na ɗan lokaci. Wani karan tsuntsu da ba a san ko daga ina ya fito ba ya kara. Motar ta ci gaba da tafiya, kamar zuciyarsu biyu na ɗanɗana wani abu iri ɗaya: Tsoro, fata, da tambayoyin da babu amsa a yanzu.


Ana kiraye-kirayen sallar asuba suka isa tashar a Kaduna, Tsayawa motar ke da wuya kuma passenger suka fara sauka, Salma ta kalli Zayyad wanda yake bacci gefen kafaɗarta, Ta kai hannu ta taɓa Fuskarsa. Buɗe idanunsa ya yi yana mitsitsika fuska, In a very cool voice ta ce


“Mun zo Yaya yad”


Kalle-kallen motar ya yi sai kuma ya fara ƙoƙarin sauka daga motar, Ganin yana shirin tureta ya sanya ta ce


“Bari na ce maka!”


Yanda ta yi maganar in a serious tone ya sanya ya tsaya yana kallonta, Salma ta ce“Daman haka ake fita waje?” Shiru ya yi ta sauka daga motar ba tare da ta ce masa komai ba, Sauka shima ya yi yana kalle kalle.


Gefe ta samu ta tsaya, Zayyad ya kalleta sai kuma ya ce“Mommah kawo na riƙe miki jakar”


Kyakkyawan murmushi ta yi sai kuma ta ce“Ka bar shi na gode”


Harararta ya yi ya ce“Dan ma zan riƙe miki, To sai ki yi ta yi”


Girgiza kai kawai Salma ta yi dan ta gane abun nasa ne ya motsa.


Ganin kowa na kama gabansa ya sanya ta yi shiru tana kallon mutane ɗaya bayan ɗaya, Wani benci ta hanga daga gefe, Ta kalli Zayyad sai kuma ta ce


“Zo mu zauna”


Wani banzan kallo ya yi mata kafin ya ce“Ba zan zauna ɗin ba, Ko an faɗa miki ni zama nake yi, Ni soja ne to”


Ko saurarensa Salma bata yi ba, Ta ja hannunsa suka ƙarasa wajen, Zama ta yi ta zauna dashi kusa da ita, Ya dinga kallonta amma bai ce komai ba. Ta zuba uban tagumi tana jiran gari ya fara wayewa ta sanda inda suka yi.


Suna nan zaune har gari ya fara wayewa, Haske ya game ko ina, Rana ta fito sosai dan da alama Kaduna na da zafi fiye da Abuja. Tashi ta yi tana kallon Zayyad wanda ya yi zaman dirshan a ƙasa yana haɗe haɗen shirgi. Wasu mutane ta hango zaune kusa da wani kanti da mai shayi a wajen ta ƙarasa tana tafe a hankali, Sai da tayi sallama suka amsa sannan ta ce


“Dan Allah a ina zan samu dillalan gidaje, Ina son kama haya ne?”


Mutanen suka kalli juna kafin na tsakiyarsu ya ce“Wallahi nan dai bamu sani ba yarinya sai dai ko ki yi gaba” Ta yi shiru sai kuma ta ce“Tom Nagode” Ta juya ta fara tafiya.


“Baki ji ba”


Salma ta juya ta kalli mutumin dake mata magana, Wani ɗan magidancin mutum ne, Fuskarsa sai sheƙi take yana murmushi ya ce“Naga kamar kina neman taimakone ko?”


Kamar jira take ta ce“E, Baba wallahi daman ni baƙuwa ce a garin nan na zo da ɗan uwana to ina nema mana gidan da zamu zauna ne”


Ya jinjina kai sannan ya ce


“Allah sarki, Daman naji kin yi magana acan ne shi ne nace bari na taimakeki, Akwai wani ɗan uwana da yake harkar idan babu damuwa sai na haɗa ki dashi”


Ajiyar zuciya Salma ta sauke cike da fara'a ta ce


“Ai ko Nagode sosai Baba, Wallahi ka taimakeni dan daman tunanin yanda zan yi nake”


Mutumin ya ce


“Allah sarki, Babu komai ai yiwa kai ne, Ana son taimako ai. Mu je sai na kira miki shi” Toh Salma ta ce sannan ta koma inda Zayyad yake, Dakyar ya tashi suka dawo wajen mutumin tana murmushi ta ce“Yi haƙuri Baba na tsayar da kai” Girgiza kansa ya yi ya ce“Assha yarinya, Babu komai muje” Daga haka ya yi gaba suka dinga bin sa a baya. Suna fitowa daga cikin tashar Zayyad ya ja ya tsaya, Ta kalleshi sai kuma ta ce


“Muje mana Yaya yad, Kana ganin za'a rakamu”


Banza ya yi mata ya ɗauke kansa, Mutumin ya juyo ganin ya ɗan yi nesa dasu, Dawowa ya yi yana kallonta ya ce“Lafiya dai yarinya?” Jiki a sanyaye ta ce“Babu komai Baba daman ya ƙi tafiya ne” Kallon Zayyad ya yi sai kuma ya ce“Bawan Allah muje mana” Ko kallo bai ishi Zayyad ba dan bai juyo ba. Salma ta kalleshi murya can ƙasa ta ce


“Mu tafi mana ko baka son ganin Mommah?”


Juyowa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce


“To abinci zan ci fa”


Salma ta ce“To ba sai ka faɗa min ba, Bari na samu kanti na siya maka”


Da sauri mutumin ya ce“A'a yarinya ba sai kin kashe kuɗinki ba, Gidana nan kusa ne mu je sai mai ɗakina ta dafa muku”


Girgiza kai Salma ta yi ta ce“Baba kar na saka ka wahala, Gara dai na siya masa”


Ya ce“Babu wata wahala ai yiwa kai ne”


Murmushi ta yi ta ce“Tom An gode Allah ya saka da Alkhairi” Daga haka ta kalli Zayyad wanda ke bin su da kallo ta ce“Muje gida sai a baka” Bai musu ba ya yi gaba abin sa, Salma ta sauke ajiyar zuciya sannan tabi bayansa.


Ƙarfe 6:56am suka isa ƙofar gidan, Wani gida na ƙasa mai ɗan faɗi, Ya kalleta ya ce“To yarinya bismillah” Murmushi Salma ta yi sannan ta yi gaba ya bita a baya. Da sallama suka shiga gidan, Salma ta tsaya a tsakar gida tana riƙe da hannun Zayyad gudun kada ya yi wani abun, Mutumin ya shiga cikin ɗaki yana kiran sunan Abu. Bai daɗe ba ya fito tana biye dashi, Wata farar mata mai ɗan jiki, Da murmushi ta kalli Salma sai kuma ta ce


“Sannu Yarinya shigo mana”

Durƙusawa Salma ta yi ta gaisheta, Ta amsa da fara'arta sannan ta ce“Shigo ciki kin ji” Salma ta kalli Zayyad sai kuma ta ce“A'a Mama zamu zauna a nan bani kaɗai ba ce” Matar ta ce“A'a shi ya je ɗakin Malam ya zauna mana” Mugun kallo Zayyad ya mata kafin a tsawace ya ce


“Ke ɗin banza! Baran je ba ɗin”


Saurin rufe masa baki ta yi da hannunta tana girgiza kanta, Ya doke hannunta ya ci gaba da fad'in


“Ke wace to, Ba zan je ba nace! Nonsense kawai, Haba”


Kallon kallo aka dinga yi a wajen, Salma da kunya ta isheta ta sunkuyar da kanta. Matar ta kalli mijin nata ta ce a hankali “Malam lafiya kuwa?” Kafin ya yi magana Salma ta ce


“Ku yi haƙuri dan Allah, Baya jin daɗi ne shiyasa yake haka”


Numfasawa Mijin ya yi ya ce“Bakomai Allah ya bashi lafiya” Salma ta ce“Ameen” Ɗaki matar ta shiga ta ɗauko musu tabarma ta ce“Tun da ba zai yarda ba ga waje ku zauna” Murmushi Salma ta yi ta ce“Tom Mama mun gode” Daga haka ta kalli Zayyad ta ce“Muje to” Daga haka tayi gaba, Da harara ya bita sannan yabi bayanta. Can gefen tabarmar ya zauna ya dinga wasa da zaren tabarmar.


****

Wajejen ƙarfe 10am ya shigo gidan, Zaune suke kan tabarmar bayan sun yi wanka, Zayyad yana sanye da wata t-shirt onion colour ya yi tsaf dashi, Ya ƙaraso gabanta yana murmushi ya ce“Yawwa nazo dashi taso muje ku yi magana” Tashi Salma ta yi tana gyara hijabinta ta ce“Tom muje” Daga haka ta kalli Zayyad wanda shima ya miƙe tsaye, A hankali ta ce


“Ka zauna yanzu zan dawo”


Ko saurarenta bai yi ba ya riga su nufar hanyar fita daga gidan, Mutumin mai suna malam Habu ya yi murmushi ya ce“Amma ya kamata a nema masa magani, Babban mutum kamar wannan” Jiki a saluɓe Salma ta ce“Eh In sha Allah Baba za'a yi” Toh ya ce sannan ya nufi wajen shima.


Tsaye suka samu Zayyad ya riƙe ƙugu kamar mace sai zagaye mutumin yake, Salma ta yi shiru tana kallon ikon Allah da alama kwana biyun nan haukan nasa gaba yaƙe ƙarawa. Malam Habu ne yace“To gata nan ita take neman gidan” Mutumin mai suna Malam Sammani ya kalli Salma fuskarsa cike da fara'a ya ce“Allah sarki Barka da zuwa yarinya” Murmushi ta yi ta ce“Yawwa Baba fatan mun same ku lafiya”


“Alhamdulilah, Ya yimin bayanin komai, kuma akwai gidaje a ƙasa yanzu. Idan ba zaki damu ba muna iya zuwa dake mu ga gidan dan tun da ya faɗa min irin wanda ki ke so na ce to tabbas zai miki”


Cike da murna Salma ta ce“Ai ko naji daɗi sosai Baba, Mu je dan Allah”


Tom ya ce sannan ya kalli Malam Habu ya ce“Ai tare zamu je ko?" Jinjina masa kai ya yi ya ce“Eh mana tare zamu je, Idan ta kama zasu dawo nan ai kaga basu san hanya ba” Murmushi kawai Salma ta yi tana jinjina halin kirki irin na Malam Habu. Napep suka tsayar ita da Zayyad suka shiga ciki, Malam Habu da Malam Sammani suka yi zaman gefe, Zayyad kallonsu kawai yake time to time yana zubar da yawu, Salma ta dinga kallonsa amma bata ce masa komai ba gudun abin da zai yi a haka har suka ƙarasa unguwar.


Koda suka sauka daga Napep ɗin sai da suka ɗan yi tafiya kafin su ƙaraso ƙofar wani gida, Gida ne mai kyau na bolon siminti ya sha fenti ash colour, Ginin zamani wanda ya tsaru sosai. Salma ta dinga kallon gidan haka ma Zayyad, Malam Sammani ya kalleta yana murmushi ya ce


“To ga gidan fa nan Hajiya, Wannan gidan yana da kyau sosai kuma na zamani ne ga kwari”


Salma ta jinjina kanta still smiling ta ce“Eh kam gashi nan Baba, Kuma ɗakuna biyu ne?”


“Eh mana ai buɗe miki za'a yi ki gani”


Cewar Malam Habu, Salma ta ce“Tom Baba Kuma nawa?”


Kallon kallo suka yi sai kuma ya ce“Ai tun da kece kuma kin ga ina ganin ƙimar wanda ya kawo ki to kawai ki bada Naira dubu ɗari uku, Sannan na shekara biyu ake biya saboda tsaro”


Shiru Salma ta yi tana kallonsa, Sai kuma ta kalli Malam Habu ta ce a sanyaye “Baba wannan kuɗin yayi yawa ai, Ni wanda bai kai wannan kuɗi ba nake so”


Girgiza kai Malam Habu yayi ya ce“Ai kin san yanzu yarinya gidajen ne suna wuta, Kuma kin ga nan babbar unguwa ce, Amma tun da an yi haka Malam Sammani ka bar mata a dubu ɗari biyu da hamsim kaga sai ta baka duba ɗari biyar na shekara biyun”


Girgiza kai Malam Sammani ya yi ya ce“Ai fa sauƙi na muku saboda kai, Amma wallahi har naira dubu ɗari huɗu na bada hayar gidan nan, Saboda haka mai gidan ya bani”


Malam Habu ya dafa shi cikin kwantar da murya ya ce“Duk da haka ka daure ka rage mata, Kaga baƙuwa ce”


“Ai hakan ba zai yiwu bane, Saboda ka san gurin nan ajiya aka bani nake dillanci yanda aka masa kuɗi haka zan bayar nima ba kayana bane, Idan kawai kun ga bai yi to ku je ku sami wani”


Shiru wajen ya ɗauka na wasu sakwanni kafin Malam Habu ya kalli Salma ya ce“Kawai haƙuri Salama mu koma gidana a samo wani”


Girgiza kanta ta yi jiki a sanyaye ta ce


“A'a Baba ba za'a yi haka ba kawai zan bashi kuɗin”


Cike da damuwa Malam Habu ya ce“A'a kamar ya yi miki yawa”


Ɗan murmushi ta yi ta ce“Kar ka damu Baba, Tun da na samu ragowar kuɗin da zan siya abinci ai shikenan”


Daga haka ta sauke jakar hannunta, wrapper shida na yan dubu-dubu ta ciro sannan ta miƙa masu, Malam Sammani ya amsa ya jujjuya ya ce“Ai ba ma sai na ƙirga ba tun da a manne suke”


Malam Habu ya ce“Tom yanzu sai a buɗe mata gidan ai”


Jinjina kai Malam Sammani ya yi ya ce“Ai tun da an biya kuɗi kuma to kamar ta shiga gida ta gama ne”


Ya ƙare maganar yana lalube a aljihunsa, Above 2mins kafin ya ce“Subhanallahi ai ko na baro wallet ɗin mukullayen nawa a gida”


Girgiza kai Malam Habu ya yi ya ce“Kash, Yanzu sai kaje ka ɗauko kenan?” Gyaɗa masa kai ya yi, Salma ta ce“To ai babu komai sai mu jiraka a nan” Sosai ya ji dadi ya ce“To to shikenan, Kaga Malam riƙe kuɗin nan idan na dawo da maƙulli sai a ƙarasa ciniki”


Kafin Malam Habu ya yi magana Salma ta yi saurin cewa“Ai ba sai ka bada riƙon kuɗin ba kawai ka tafi dashi ka ga ma ai ka ajiye a gida”


Girgiza kai ya yi ya ce“A''a yar nan kuɗi ba abun yarda bane, Ƙara naje na zo da makulli a buɗe miki gida ki shiga sannan na amsa”


Salma ta yi murmushi ta ce“Ni ai na yarda daki Baba, Babu komai wallahi ka je dashi kawai”


Malam Habu ya ce“Tun da ta yarda kawai kaje muna nan zamu jiraka” Tom kawai ya ce sannan ya mayar da kuɗin aljihu ya juya ya nufi titi. Malam Habu ya kalli Salma dake tsaye ya ce“To ki samu gefe ki ɗan zauna kafin ya dawo” Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Tom Baba” Daga haka ta koma kan dakali ta zauna tana kallon Zayyad wanda ke zaune can nesa da ita yana maganganu shi kaɗai.


Malam Habu ya kalleta ya ce“Amma ya kamata ki nema masa magani, Ba'a barin mutum irin haka”

Ya ƙare maganar idanunsa zube akan Zayyad cike da tausayawa. Numfasawa Salma ta yi sannan ta ce“Daman ina son mu nutsu ne sai na fara neman maganin, Ai zai dawo daidai ko Baba?” Malam Habu ya ce“Eh mana in sha Allah zai warke tas, Idan kun huta akwai wani malami dana sani yana bada maganin irin wannan lalurar sai na raka ku can” Salma ta ce“Ai ko da naji sosai Baba. An gode Allah ya saka maka da Alkhairi yanda ka mana” Girgiza kansa ya yi ya ce“Babu komai Salama ai yiwa kai ne”. Murmushi kawai ta yi sannan ta maida idanunta kan Zayyad tana kallon duk abin da yake.


Sama da awa ɗaya suna jiran Malam Sammani amma shiru bai dawo ba, Gaba ɗaya sun gaji, Malam Habu ya miƙe daga zaunen da ya yi kan takalmansa ya ce“Ko wani abun ya tsare shi?” Salma dake zaune a gajiye ta ce“Ina ga amma ya daɗe sosai” Wayarsa ya zaro ya danna sai kuma ya sake kallonta ya ce“Kin ga har an fi awa ɗaya da tafiyarsa, Ko dai na bi shi ne?” Saurin gyaɗa masa kai ta yi dan bata da burin daya shige ta ji ta a zaune a gida. Ta ce“Eh Baba, Kawai sai ka amso mana muƙullin ma”


Gyara zaman wular kansa ya yi ya ce“Gashi rana tafara yi sosai, Bari na yi sauri na dawo ku samu ki shiga gidan. Ki kula dashi sosai dan Allah” Ya ƙare maganar yana kallon Zayyad, Salma ta ce“In sha Allah Baba sai ka dawo” Tom ya ce sannan ya bar wajen. Salma ta kalli Zayyad wanda ke zaune ya takure waje ɗaya, Tashi ta yi ta koma inda yake ta zauna kan takalmanta tana kallonsa ta ce


“Ka gaji ko?”


Gyaɗa mata kai ya yi da sauri ta ce“Yi haƙuri yanzu zai dawo kaji” Zayyad bai ce mata komai ba ya kifa kansa bisa gwuiwoyinsa Ita kuma ta dinga kallonsa.


Suna nan zaune har kusan azahar babu Malam Habu babu Malam Sammani, Ta gaji da zama ta tashi tsaye, Har sannan Zayyad na zaune ko ɗagowa bai yi ba. Zafin rana duk ya dameta dan lokacin rana ta gama buɗewa.


“Mommah ruwa”


Zayyad ya faɗa bayan ya ɗago fuskarsa, Tsugunawa ta yi gabansa ta ce a sanyaye “Yunwa ka ke ji?” Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Ni zan sha ruwa kuma zan ci abinci” Numfasawa Salma ta yi sai kuma ta tashi tsaye tana kalle-kallen unguwar, Wani provision ta hango yana opposite gidan, Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli Zayyad ta ce“Bari naje can na siyo maka ko biscuit ne kaji...”


Bai bari ta gama maganar ba ya miƙe tsaye, Ta girgiza kanta kawai dan ta gane nufinsa ta yi gaba yana biye da ita. Da sallama ta shiga kantin, Mutumin ciki wanda ya kasance matashi dan Zayyad zai girmeshi ya amsa, Naira dubu ɗaya ta miƙa masa ta ce ya bata biscuit da ruwa, Ya zuba mata a leda ya miƙo mata. Amsa ta yi tana shirin juyawa ya ce


“Hajiya na ce idan jiran matar gidan nan ki ke ai ba yanzu zata dawo ba”


Da mamaki Salma ke kallonsa kafin ta ce“Matar gida kuma? Ni ai babu wadda nake jira, Wane gidan?”


Mai kantin ya ce

“Wancen gidan mana da naga kuna zaune a ƙofarsa”


Salma ta yi murmushi sai kuma ta ce“Au ho, Ai gidan da muka kama haya ne”


Shiru ya yi yana kallonta, Ganin haka ya sanya ta ce“Ko baka gane ba? Wancan gidan fa, Jira ma nake a kawon maƙullin gidan na shiga”


Mai kantin ya ce“Kuma shi wancan gidan ɗin?” Gyada masa kai Salma ta yi ya ce“Ikon Allah, Ɗazu fa matar gidan ta fita taje unguwa kin ga nan ta bada maƙullin gidan ta ce idan mijin ya dawo a bashi”


Da wani irin mamaki Salma ke kallonsa kafin ta sake cewa“Amma ai bata nan, Ni wani mutum ne ya bani shi haya fa”


Kafin mutumin ya yi magana wani ya shigo cikin shagon yana kallonsa ya ce


“Yawwa Auwal bani maƙullin”


Da sauri mai kantin ya ce“Yawwa to Kinga mai gidan nan”


Ya faɗa yana nuna mata mutumin dake tsaye, Salma kallonsa ta dinga yi kamar idanunta zasu faɗo. Shi ko mutumin ya ce“Lafiya dai Auwal?”


“Wai wasu ne suka bata hayar gidanka yanzu sun je kawo mata maƙulli tun wajejen 10:30am take zauna a ƙofar gidan”


Auwal ya faɗa.


Da mamaki mutumin ya ce“Haya? Kuma gidana?”


Jinjina masa kai Auwal ya yi, Mutumin ya juyo ya kalli Salma wadda ta kasa gane inda suka dosa ya ce“Su wane ne? Sannan kuɗi ki ka basu?” gyaɗa masa kai ta yi a sanyaye ta ce


“Eh, Mutumin ya ce Naira dubu ɗari uku ne kuɗin hayar shekara kuma sai dai na bada na shekara biyu, Kuma na bada”


“Danƙari! Ke ya aka yi ki ka basu kuɗin ki kin san su ne?”


Salma ta kwashe labarin duk abin da ya faru ta basu, Mai gidan ya Girgiza kansa cike da damuwa ya ce


“Ai ko sun damfareki, Ƙarya suke miki, Sun ga ke yarinya ce shi ne suka cuceki. Wannan ba gidan haya bane, Gidana ne muke zaune da matata”


Silalewa ƙasa ta yi ta faɗi kan tiles, Tuni hawaye suka wanke fuskarta, Ta dinga Girgiza kanta kamar zararriya, Magana take son ta yi amma sam ta ƙi zuwa bakinta. Kawai ta sanya hannayenta duk biyun ta toshe bakinta tana sakin wani raunataccen kuka.


# HCD
# Ya Yad
# Salma
# Nanameera
08106608363.

*HASKEN CIKIN DUHU*
Chapter 19 · 0% Book details