← Book details Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 31

Sashe 9

Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan masu aiki a lokacin nan mutum tara ne har ni goma, amma Hajiya Zeena ita ce ke yiwa Hajiya Gwamma gyaran ɗaki ta fidda mata kayan wankin ta shirya mata gogaggu a durowar ta. Komai Hajiya Gwamma ta ke so Zeena ta ke yi wa magana.
Zeena ga kyauta dangin Hajiya Gwamma kuwa duk wadda ta zo gidan tamkar ta bata ranta dan nuna ƙauna, ko daga ƙauye mace ta zo ba ruwan ta zata jata jika ta cika ta da alheri, sannan tana taimakawa mijinta da abinda ya shafi harkokin kasuwanci sa tunda ita ma layin tane. In taƙaice miki cikin hikima da basira da wayo dan tana da dan bazan wayo.
saida ta mallake zuciyar kowa na gidan da ƙauna da mutumci ta maida dangin shi tamkar nata. Ta ɗan yi shiru tana maida numfashi. Sannan ta ɗora. Rashin samun haihuwa shine ƙalubalen Ali da Zeena. Hajiya Gwamma ce ke kwantar musu da hankali tana faɗa musu tsawon shekarun da ta share kafin ta haifi shi Ali.
Cikin haka sai Allah ya amshi rayuwar mahaifin Zeena."
Nace tsohuwa ban katse ki ba,duk wannan labarin lokacin shi Alhaji Baita baya raye?
Tace "Yaushe rabon shi da Duniya a wannan lokacin? Ya rasu tuni Ali ya ci gado mai yawa, ance a yankin nan namu na baƙar fata in an samu na ɗaya to kuwa Ali ne na biyu a dukiya dai." Ta sake numfasawa tace "Kina jin wannan taɗi ko 'yannan Zeena ta rungumi gadon ta cancakat ta danƙawa Ali,shi kuma da ya tashi sai ya gina mata gidajan mai, ai duk gidan mai da kika ga ansaka Shinkafi to na Zeena ne a wancan lokacin ban san yanzu ba.

Sai kuma wani abin mamaki da zan faɗa Miki yanzu. Mutuwar mahaifin Zeena sai ya tona wani sirri wanda shi Ali da Zeena suke ɓoyewa . Ashe dai Zeena ba a Budurwa Ali Baita ya aure ta ba." Kuna jina jin wannan zance?" Na kasa magana saboda tsabar mamaki,yaya ma za a yi haka, ko dai tsohuwar nan takanta ya fara juye wa ne?. Hajiya ta ɗan faɗa min wani abu daga cikin daren farkonta. Amma sai na yi shiru domin inji ƙarshen zance.

Tace duk munsha mamaki a ranar da Ali Baita ya shigo da yara mata guda huɗu ya gabatar da su ga Hajiya Gwamma a matsayin yaran da Zeena ta haifa da wani miji kafin haɗuwar su da Ali.Wai ya ɓoye mata ne saboda kar ta hana shi auren Zeena a matsayin shi na saurayi.

Hajiya Gwamma ta girgiza da wannan baƙon lamari harta nuna fushin ta ga Ali da Zeena wadda ta ɓoye kanta tun daga ranar da Ali ya kwaso yaran daga Shinkafi.
Hajiya Gwamma ta daina cin abincin da Zeena ke dafa mata, ta faɗawa Uwar gandu da Tabawa tace su faɗawa Zeena ta daina yi mata girki domin ta daina ci.
Ina falon Zeena lokacin da Ali Baita ke lallashin Zeena wadda ta haɗa kayanta da kuma 'ya'yanta tana roƙon ya sawwaƙa mata auren shi zata koma Zamfara da yaranta."
Nice na je na faɗawa Hajiya Gwamma halin da a take ciki. Da kanta ta taso zuwa falon ta ce in tafi da yaran sasanta. Zeena ta zube a gaban Hajiya Gwamma tana kuka.
Hajiya Gwamma tace Zeena na yi fushi da ke fushi mai tsanani, ban taɓa tsammanin cewa ƙarya ne alaye ne baki ɗauke ni a matsayin Uwa ba, sai wannan karon. Kinsani Sunnar gidan nan ce ba a yin ƙarya, me yasa ke da Ali ku ka yimin ƙarya, me yasa da akayi auren baku zo kun fayyace min komai ba? Kenan ni muguwa ce kuka ɗauke ni wadda bansan ina yake min ciwo ba. Bansan ƙaddara ba,ko da ni bansan ràɗaɗin soyayya ba lokacin da aka aura ɗaura min ubanka amma ai ina jin labarin masoyan ko. Dan haka ni na karɓi yaran zan riƙe su, domin nasan cewa a can ɗin suna hannun masu aiki ne da mahaifin ki, kasancewar tun bayan rasuwar mahaifiyar ki bai sake aure ba. Ta girgiza kai, ina son kusani cewa ba ku kaɗai kuka iya shayar da mamaki ba, zan baku nawa kusha yanzu.

Ina son kusan wani abu,duk wata uwa Hamshaƙiya bata zama karabiti mai yara da yawa ma bare ni mai ɗara rak." Tsohuwa ta mufasa sannan tace,
Kunsan abinda yasa na nemi guri na zauna bayan na kai yaran sasan Hajiya na dawo? Nace a a. tsohuwa ta ci gaba da faɗin.

Kalaman Hajiya sun firgita ni lokacin da tace. Zeena kin auri Alhaji Uzairu wanda ya kasance shine mai kula da dukiyar mahaifin ki, kuma ya haɗa aure ne saboda yarda da yayi cewa ko bayan ransa zai kula da ku da kuma dukiyar ku.

Bayan ya ga cewa ya same ki, har kin haifa mishi yara sai ya fara shirya yadda zai ga bayan mahaifinki domin ya mallaki dukiyar sa. Asirin sa ya tonu ne lokacin da ɗaya daga cikin ma'aikatan da yake tunanin ya haɗa baki da su ya tona shi ya sanar da mahaifin ki abinda ke faruwa kuma ya roƙi kar yasha duk wata fura da wani zai bashi. Dan haka tuni Mahaifin ki ya sanar da jami'an tsaro suka zo cikin farin kaya suka kamashi dumu dumu da furar da ya kawo Office ɗin Alhajinki. Bayan bincike an gano cewa guba mai kisan mummƙe aka sawa mahaifin ki wanda zai ɗauki tsawon wata uku yana jinya kafin ya mutu.

An kashe auranku a kotu ne lokacin da alƙali ya iza ƙeyar shi zuwa gidan kaso.

Ta dubi Zeena wadda ta cika da mamaki tace, duk da ni banyi karatun zamani ba,na tabbata ni ba jahilan bace. Kuma in har Uwa takai uwa dole tasan duk wani shigi da fici na ɗanta. Sannan duk tsanani karki yi ƙarya tana zubar da kima kuma tana saka aji kunya kamar dai yanzu gashi ke da mijinki.
Hajiya Gwamma zata juya Zeena ta tashi da sauri ta zube a gaban Hajiya tana neman gafara. shima ya zo ya zube. Tace ku ki roƙi Allah gafara. Kunsan wani abu?

Ko masu aikin gidan su dai sunga yara amma basu san yaran Zeena bane ,sai ni da mai gidana wanda shima ni ce na sanar da shi.
Hajiya Gwamma ta yarda da ni matuƙa amma duk da haka sai da ta jamin kunne tace matsawar zancan ya fita to kuwa ni ce, dan haka na ja baki na nayi gum. Aka kai yara makaranta da sunan Ali Baita.

Gwamma ita ce ta riƙe yaran nan tamkar kakarsu.
An samu tsawon lokaci kafin aka samu cikin Shamaki. Faɗin gatan da Zeena ta samu kanta a ciki ma ai ƙauyanci ne a gurin Hajiya Gwamma .
Nace tsohuwa Kina nufin Aliyu Shamaki shine kadai ɗan Ali Baita?

Tace ƙwarai kuwa, duk wata dukiya ta shamaki ce, sai ta Zeena wadda bata fi cikin cokali ba in aka karata da ta Shamaki."

Nace to kuma kin ci gaba da zama da Zeena ne bayan Hajiya Gwamma ta rasu? Tsohuwa tace 'Ai Shamaki bai rufa wata uku ba ciwo suga ya tasarwa Hajiya Gwamma aka fita da ita ƙasar waje, ashe dai tafiyar kenan.
Sai gawa aka dawo da ita. Zeena ta yi kuka kamar zata yi me har sai da aka yo mata rubutun dangana tasha sannan ta haƙura. Ni kuma da suka gina sabon gida za su tashi sai suka saya mana wannan gidan,a wancan lokacin gida irin wannan sai wane da wane muka dawo. Sai saidai muje muyi aiki lokacin mai gidana ya fara tsufa sai aka kawo sabon direba kuma ta canza wasu masu girki domin nima lokacin girma ya fara shiga kuma ga yara amma dai ina zuwa in yini domin tana son ina zauna kusa da ita kasancewar tana da son labarai. Daga baya kuma sai larurar ido ta kamani, sun kashe min kuɗi amma haka na rasa idanun, sai na hakura da zuwa, Ali Baita shine ya budewa mai gidan nan kati a nan ƙofar gidan muka ci gaba da riƙe kanmu amma Zakka ta fidda kai da ta azumi baya wuce mu har ya rasu Hajiya Zeena bata dai na ba. Sai shekarun nan ne ma aka canza to Gara wannan karon an baku komai da ake bamu.
To kinji."
Nace Lallai Hajiya Zeena ita ma tana da kirki kamar surukar ta.. Tace "Ƙwarai banbanci su kaɗan ne, ita wannan Zeena tana da zafi sosai kuma tana da iko da yawa koda dai mako ance sun shafi sarauta acan garin na su."
Na ce me yasa ake kiran Shamaki da wannan sunan mai makon sunan su na gado wato Aliyu?
.......
*Assalamualaikum*

*Naga addu'o'inku game da sace man waya da akayi, nagode😍*

Tsohuwa Ta ce bani kofin can insha ruwa, ina Maryama ta zo ta kawo muku ruwan kuma."

Jamila ta ce yanzu muka sharuwa . Tsohuwa tace, , "Nima karambani ne 'yannan, nasani gidan Zeena ko masu aiki basa shan ruwa dan awo sai na roba." Ta daga ta sha sosai har ta dan kware, muka tsaya muna yo mata sannu. Tace "Me ki ke tambaya ne? "Nace game da sunan Shamaki.

Ta ce "Anyi haka. Yadda Zeena ta fada min tace Ya samu sunan ne daga asalin mahaifin su acan Sudan Wato shi Baita shine babban yaron sarki kuma duk babban dan sarki to Shamaki ne kuma yana dai dai da Hakimi. Sai Ana ganin shi taro ne bai dace a bashi Shamaki ba. Ya za a ce Sarki yana ji dashi harma ya kasa boye soyayyar sa, har taja aka fara neman rayuwar sa. Sarki ya kira malamai su yi masa istihara akan wannan matsalar,
baki uku ya hadu daga malamai daban daban akan cewa mafi alkhairi shine ya bar garin domin kuwa taurarinsai masu haske suna nesa. Sannan hadari yana kusa da shi.

Haka suka ba Sarki shawara ya nesanta shi daga garin, ya hada shi da amintattu suka kawo shi kasarnan suka juya suka barshi da guzurin shi." todai . Kinji inda ya samo sunan Shamaki. Ali Bauta da Zeena ai suje can kasar a wata shekara.

Kuma sunga dangin su dawo suna yaba karbar da suka samu haka kuma sun zo a rasuwar Ali Baita
Chapter 9 · 0% Book details