← Book details Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 31

Sashe 4

Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina sako ƙafa falon Hajiya naji tana waya dan haka na dawo na tsaya tsam ji nayi tana faɗin. "Saurara kiji Aminiyata, ni dai na gama yanke nawa hukunci kuma dai kinsan dole duk yadda na dama a gidannan dole kowa ya sha shi haka,har yanzu ina kan bakana in yarinyar nan ta faɗi jarabawar nan ba zan ji nauyin sawa a sake ta ba. Duk ba wanda ya san dalilina. Taɗan yi shiru tana sauraron wancan ɓangaren sai ta yi murmushi mai sauti. Tace "Ya za 'ayi in daɓawa cikina wuƙa to kinsan halin kishi watarana ai gora mata zata yi,ban bari ta san maganar Azima ba,ita ma Juma na ja mata kunne shikuwa ai ba yadda zai yi duk da bashi bane ai dole ya aureta a haka. Ina ba so nake kimata ta ragu ba na gama cika baki ta baɗan ƙasa a ido ai ba yadda za a yi in fidda wannan zancan. Yanzu tunanin da nake kar inyi tafiyar nan ta ke sa ƙafa tana fita ta ƙara ɗakko min wata maganar ko iyayen ta fa banbari sun ji maganar ba, na cika baki akanta da yawa sai gashi ta kunyata ni. Abin ya min ciwo da yawa." Ta yi shiru tana sauraro sai tace "Haba Hajiya Zaliha ki na yi kamar baki sanni ba ne, ai ba batun jarabawa akan Azima me zan jaraba kuma baya ta riga ta faɗi warwas na faɗa masa dai ya zauna da ita 'yar uwarsa kuma matar sa, banda a gidana take abinnan ya faru wallahi ke kinsan ni sarai bazan taɓa bari ya aureta ba."
Ta kuma yin shiru can tace Ke kinsan itama akwai maatuƙar wahala ta tsallake ta wannan jarabawar ko ta tsallake komai ba zata iya tsallake ta ƙarshe ba, har zuwa yau ni kaɗai na san dalilin jarabawar, shi kuma dole ya sake ta, domin dai shekara guda in suka kwashe kinsan lokacin namiji ya fara gajiya da mace, yadda ya saki sauran ko a jikin sa haka ita ma zai mata. Daɗi na ɗaya ita ko cikin har yanzu shiru. Amma na kula ita wannan har yanzu bai kawo min ƙarar ta ba,duk da hakan baya cikin sharuddan jarabawa ta amma dole in bata makin su." Sai ƙaran ɗaya wayar ya shigo na ji tace Hajiya Zaliha sai mun sake magana bari in ɗaga wata wayar.

Nayi tsam jikina duk ya yi sanyi ba shakka ba zan tsallake tarkon Hajiya ba, gashi ina son mijina tunda shi har zuwa yanzu banda maganar neman matan shi bani da wata matsala da shi. Ba dama in wuce, dole in bari ta ɗanyi nisa a wannan wayar, sai in fito kar ta gane cewa ni ɗin nayi mata laɓe.

Da alamu suna magana da Shamaki ne aka batun tafiyar su,dan haka sai kawai na fito sai da na zo kusa da ita sannan nayi mata sannu, da kai ta amsa na wuce ɗakina.

Sukuti na yi a kan gado yanzu zamu rabu da Shamaki da gaske! A fili na furta gaskiya bazan iya ba, ya yi min alƙawari ba so ɗaya ba, amma ya kamata inke tuna masa da wannan alkawarin da ya ɗaukar min akai akai.

Kamar awa ɗaya da shigowa ta ɗaki na kira shi,ya ɗaga na soma ɗan kukan shagwaɓa yace "Wai me akayi ne kuma zaki ɗaga min hankali?" Nace Dan Allah wai zaka sake ni? Yace "Injiwa kuma?"

Nace bacci na yi yanzu sai na yi mafarki wai Hajiya tace sai ka sake ni.

Yace "To na sake ki ɗin a cikin mafarkin na ki?" Nace 'a 'a kana ta bata haƙuri ne sai tace me yasa zaka yi mata gardama shine kace ka ɗaukar min alƙawari tun kafin aurenmu har ka fara tuna mata girman alƙawari, shine ta ce ta janye. Sai naji ya sauke ajiyar zuciya,yace ba abinda zai sa in sake ki Baby." Nace Alƙawari yace "Alƙawari."

Sai kusan ƙarfe biyar Juma ta zo tace sun gama na fito naje na gani yadda nace haka suka yi, abin al ajab sai gashi wani abu guda ɗaya bai rage ba, wannan ya tabbatar min haka rabon nan ya ke. Nace dube su nace ku menene sallamar ku? Suka ce sai abinda aka bamu. Nace to ku zagaya mu haɗu a gurin Hajiya. Na tsugunna agabanta nace sun gama menene sallamar su? Hajiya ta dube ni, wannan baya cikin huruminki in dai sun gama miki aiki to ki turo min sunan.

Namiƙe dai-dai lokacin da suke shigowa.
Su Juma su uku ne mata masu aiki a gida da haka na basu kuɗin su sannan na nuna musu kashin da za su ɗauka wato mai suga buhu ɗaya. Juma tace 'yannan kin gaji Hajiya, wannan shine rabon da Hajiya ta ke bamu kafin zuwan matan Shamaki, insha Allahu zaki lashe jarabawar ki, ke ce mandiya matar gida, jinki ya fi ganin ki,ga ki ƙarama sai tarin basira. Ta yi ƙasa da murya 'yata saboda jin daɗi zan miki wani taimako guda ɗaya,kina jina?" Na tattara hankali na gare ta. Tace" ranar ƙarshe ta jarabawar ki da baki Hajiya zata yi muku tambayoyi anan duk wata ƙullaliya ta ke, ina son ki tabbatar kin san waye Shamaki kafin wannan rana."

Wannan gudunmawa ta ce nima zuwa gare ki,amma karki tambaye ni waye Shamaki domin bansani ba, kar ki kar ki tambaye ni wanda zai sanar da ke." Na yi shiru ina mamakin irin wannan abu, ni ko lokacin da na yi karance karance ban taɓa dubo irin wannan almarar ba. Tace kin ji mamaki ko? To kar ki tsaya mamaki kiyi ƙoƙari ki samu wannan bayani. Ta wuce na bita da kallo a fili nace kai jama'a Ni kuma irin tawa ƙaddarar ke nan.
Washe gari tun bakwai na fito bayan mun gaisa da Hajiya nace zan fita gurin rabon nan in sake bin sunayen in tabbatar kowa ya samu kashin sa. Tace min, hakan yana da kyau, Juma ta faɗa min abinda aka basu Allah ya saka da alkhari. Na sunkuyar da kai nace Hajiya ku za a yi wa godiya, Allah ya sa a ɗauka a gidan Aljanna. Tace "Ameen, amma me yasa ki ka haɗawa su Juma da kuɗi? Nace to ni dai a ganina su makusanta ne,kuma duk da ana biyan su hidimar da suke mana an so ka fara zakka da makusantan ka,sannan ka kyutata musu shine kawai dalilina. Tace "Allah ya amsa." Nace Ameen.

Haka mutane suka yi ta zuwa kujera na saka na zauna duk wanda ya kira waya sai ince ya shigo ya faɗi suna da lambar waya,kafin ya ɗauka kuma zaije ya yi wa Hajiya godiya a falo wannan shima tsari na ne.Direba kuwa ya kai na bashi na Liman da na Kawu, kuma bayan ya dawo na kirasu su suka tabbatar min da cewa an basu wannan kuɗi. Na ce to su kira Hajiya su yi mata godiya.

Rabo dai bai tashi ba sai ranar Litinin muka gama, matar da tsohuwar nan ta turo tace min dan Allah tana son ganin matar Shamaki, sai na tuna ni nace ta neme ni. Na tambaye ta unguwar su tace min a Fage suke ta min kwatance na yi godiya muka yi sallama. Bayan ta kwashi kayan ta.

Bayan an gama komai kashi uku ya rage biyu masu kuɗi ɗaya mara kuɗi na samu Hajiya na sanar mata cewa ga kashi uku ya rage kashi ɗari kuma kowa ya ɗauka ga jerin sunayen su da lambobin su da kuma saka hannun su cewa sun amsa.
Na bata tsohon list ɗin da ta bani da sabon da na yi da sauran kuɗin dubu ɗari biyu. Tace "Iyayen ki fa kin ba su?" Nace ai ba sunan su a list. Tunda kuwa basu ai maganar ba su bata taso ba. Hajiya tace to wannan uku sai ki ba su shine dama na su. Na sake durƙusawa ina godiya,nace to sai a baiwa Ya'yan Abban mu ɗaya shima Abban mu ɗaya,ɗaya sai a baiwa dangin Umma su raba hakan ya yi?" Tace duk yadda kika yi dai dai ne ni bansan 'yan uwanku ba.

Na kira Umma ina murna na faɗa mata.nace Umma an gama rabo lafiya,ga naku ya za ayi rabon na faɗa mata niyya ta. Tace ba haka za a yi ba, shi Abbanku ya hi ɗau ɗaya,ɗayan Abban zuhra ya ɗauki kayan abinci kuɗin kai Annan ku ya rabawa sauran ƙanan sa, maza da mata kowa ya sheda ya shi albarka, sauran kayan abincin suma 'yan Kurna su sheda. Nace to zan aiko direba gobe duk yadda ku ka yi dai dai ne.

Ranar azumin farko a falon Hajiya muka sha ruwa duk gidan domin a nan muka bi salla dan haka kawai nace Juma ta barmin abinci na a nan,haka su Anisa sun kasance da mu duk da su ba azumin suka yi ba. Azima ana idar da salla ta koma ciki.
Chapter 4 · 0% Book details