← Book details Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 31

Sashe 21

Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shamaki ya shigo dakin Asibitin da dare, ya same mu muna hira da Mubina tana bani labarin Antynta yace wacece Antinta. " Nace wai Maman ta, yace to mu hada kaya mutafi an sallame mu". Nace to. Mubina ashe tana rike da maganar sai cewa ta yi, Mommy ba kince zaki tunawa Daddy a kaini gidan Anty ba. " Shamaki yace "Wacece kuma Anty? Nace Mamanta, mana meyasa yanzu aka daina kai su hutu ne? Yace "Uwar Meema ta ja musu, tana fadawa yarinyar abubuwan da basu kamata ba, kuma tana yi mata tambayoyi yarinyar ta zo tana min tambaya a gaban Hajiya Wai Maman ta tace Hajiya tana yi musu wasa ko sai fada. Sannan wai in an basu kudi tana boyewa in za a kawo ta sai ta saka a kayanta ta kaiwa maman. Shine Hajiya tace baza a kara kai su ba." Nace gaskiya bata kyauta ba gashi ta sa an shiga hakkin saura, domin su baruwan su, amma ba zai yiwu a kai su sukadai ba. Dakatarwar dai shine abinda ya dace a yanzu ha na har abada ba. .

Muka isa gida Hajiya tana kwance a gurin da take salla, ban taba ganin ta kwanta a gurin ba, na isa na zauna kusa da its nace Hajiya lafiya kuwa naga kin kwanta. Ta tashi zaune fuskar ta ta fada. Nace bakya jin dadi ko? Tace bana jin dadi amma da sauki. Shamaki ya iso shima ya tsugunna, yace Hajiya tun jiya nace baki da lafiya kin ce a a. Ta yi dan murmushi zazzabi ne kuma na samu sauki, karfine kawai bani da shi. Muka yi mata sannu, ya zauna ni kuma na shiga ciki dan in watsa ruwa.

Satin da Zan cika shekara Shamaki ya sanar da ni cewa zai tafi China daga can zashi Dubai. Kuma gaba daya tafiyar sati biyu zai yi. Nace to in ka tafi gashi saura kwana shida in cika shekara to kuma in banci jarabawa ba, yaya za ayi baka nan? Yace "Yadda za ayi ke nan ta yi hakuri domin haka na kirkiri wannan tafiyar sai dai na yi mamaki da ya kasance bata hana ni ba, kila hakan yana nufin cewa bazata raba mu ba. " Nace kar ka saki jiki akan haka kuma sai ka tafi tace ka turo sakin ta waya. Yace "Wai ke baza ki taba fadi alkhari ba saboda Allah?" Nace to ai bana son in yaudari kai na ne, saboda ko zan tafi dai dama na dangana. Ya rungume ni insha Allahu muna tare har abada, sai naji dumin hawaye a kafatata. Nace dago dasauri, kuka kuma Shamaki? Na fada cikin mamaki. Yace Tunda shekara ta gabato sai ina samun kaina cikin yawan kuka da damuwa, wanda nasan cewa tsoron rabuwa da ke ne. Na sa hannu a fuskar shi ina shafo hawayen nima sai naji nawa sun soma sauka.

Ya tafi ya barni cikin jimami. Ranar da ya tafi da dare wayar cikin gida ta bugs misalin Karfe biyu na tashi na fita. Nasan cewa munyi sallama da Hajiya na kuma shafa mata man zafi.
Na fito
ba kowa a falon Hajiya na nufi dakinta, Tana zaune a tsakiyar gado, na shiga da sauri ina fadin Hajiya lafiya? Tace lafiya kalau zauna. " Na zauna jikina sai kyarma ya ke yi. duk na firgita. Ta kalle ni sosai tace "Me ya ke baki tsoro? " Nace Ba komai na yi tsammanin baki da lafiya ne. Tace lafiya ta kalau kwantar da hankali. Ta kara matsowa, kin kuwa san dalilin da yasa na bar mijinki ya yi tafiya? " Gabana ya yanke ya yi wata muguwar faduwa, nace a a. Tace "Saboda in har yana nan bazai taba barina in yi hukuncin da ya dace ba, saboda son da ku ke yi wa juna wanda ni kadai na san dalilin son. Ina fata kina aje da lissafin kayan azumi wanda ki ka raba, shine zaki gabatar min da lissafin."
Na tashi cikin fargaba naje na dakko takardar na dawo. Nace gata nan. Tace to kowanne zaki fada min dalilin da yasa ki ka bashi abinda ki ka bashi. " Na kalle ta cikin rashin fahimta, naji zuciya ta ta fara zuwa wuya, tana fadin wai gidan nan na Aljanna ne da nake ta fuskantar damuwa da wasu ka idoji? Wata zuciyar ta bani amsa da cewa ba gidan Aljanna bane amma na neman Aljanna ne. Dan haka sai lallashi zuciyata sannan nace ban gane abinda ku ke nufi ba Hajiya.

Tace misali ai kin ba kanina kayan abinci da kudi ko?" Nace E, Tace to fada min dalilin da yasa ki ka bashi. " Nace To gaskiyar magana ni dai na yi la'akari da kusanci, domin musulunci ya nuna mana muhimmanci fara taimako daga kusa kafin kaje nesa. Tace "su Juma fa? " Nace ai na fada muku kwanaki, suma kusancin ne sannan suna yi mana hidima duk da muna biyansu kyautatawa yana da dadi.

Sannan taimako ne. Na numfasa, don Allah Hajiya kar ku tambaye ni dalilin da yasa na baiwa sauran domin ban san su ba. Tace 'To ya akayi kika basu? " Nace nabi layin sunayen ne har zuwa adadin kudin daga nan na fara da wadan da ba kudi, su kuma daya zan iya fada miki wani abu akan su ba, saboda suma layin na bi, sai guda daya wadda itama ta fada min ne da kanta.

Tace "Wa kenan? Nace Wata tsohuwa makauniya. Ta zuba min ido da alamun mamaki a tare da ita, a hankali ta ce "Kinje Fage kenan? "
Gabana ya yanke ya fadi, ba shakka bazan yi wata karya ba, ko da banci jarabawa ba na san dai bazan zargi kai na da kar ya ba. Nace naje Fage Hajiya gurin tsohuwar nan.
Hajiya ta yi shiru tana kallon gefe daya, kamar tana tunanin wani abu. Can ta numfasa sannan tace, "Ban tsammaci cewa kema irin wannan hanyar zaki bi ba, amma dai zan yanke hukunci ne kawai daga abinda kika fada. Ta sakko daga kan gadon ta yi dan tattaki a hankali, ta kai kan wata kujera dake manne a jikin gadon ta zauna, sannan ta ce.
"Jikina ya yi sanyi domin na gama yanke shawara cewa ke ce matar gidan nan, amma sai gashi kuma kin kama hanyar neman jin sirrin da da kin yi hakuri da na fada miki shi daga bakina kuma sahihin labari. Amma zan yi miki uzrin na sauraronki sannan in auna, zan kuma baki makin ki cikin adalci.
Kafin inji abinda ya kai ki gidan tsohuwa da kuma abinda ki ka jiyo da sauran abubuwan da suka biyo baya ina son ki taya ni kallon wannan. "
Ta kunna TV da Remote din hannun ta. Cikin sauri na maida kai na ga kallon TV.

Ba kamar fimba da za a nuna can da can ko sunaye, Hotona ne ya bayyana. Gani lokacin da ake shigo da ni, babu magana hoton ne kawai, ga lokacin da za a kaini daki na, sai kuma ga ni ina neman dakin Shamaki, Sai kuma aga Juma ta nufi dakina da kayan abinci. Sai kuma lafon Shamaki, duk ga shinan lokatan da muka zauna ko muka ci abinci ko wasu dai 'yan wasanni ba masu yawa ba. Haka kuma ga lokacin da Azima ta shigo falon kuma ga lokacin da ta shiga dakin Shamaki. Zuciya ta dauki zafin takaici kamar a lokacin abin yake faruwa. Har na tambayi kai na ina ina a wannan lokacini.
Sannan ga lokacin data fito.
Haka dai muka yi ta kallo, akwai gurare da na yi ta fargabar kar a gani gurin duba wayar Shamaki amma sai da wani guri daya ya fito da na dauka a falon. Sai anan Hajiya ta yi magana idanunta suna kan TV din, tace 'Wannan ba wayar Shamaki bace? " Nima ba tare da na dauke kai ba, nace ita ce. Me kika yi a ciki? Nace duba masa sakwanni na yi. Sai lokacin ta waigo ta kalleni, kina zarginsa ne a lokacin? " Nace kwarai kuwa. Tace me yasa ki ke zargin sa? " Nace akwai wani guri da aka wuce, inda zan shiga dakin na dawo baya har nayi karo da fulawa ya zo yana kirana ban dawo ba, shine dalilin da yasa na binciki wayar sa.
Ta tsada TV din,

Me ya faru a lokacin? " Nace samu yana waya da wata mace wadda ta turo masa hotuna na sassan jikinta, yana yabawa da hotunan, yana fadin wasu kalamai da suke nuna jin dadin kasancewar su da ita. Na juyo da sauri domin bana son ya ganni bare yaji kunya tunda ya san na yarda da shi kuma in wani ya fada min cewa Mijina yana neman mata bazan yarda ba. Kuma sai Allah ya kaddara na ji da kunne na. Garin in gudu karya ganni sai fulawa ta fado shine ya biyoni. Hajiya ta sauke ajiyar zuciya. Tace "sai me ya faru daga nan? " Nace kawai naje nayi kuka ne a daki ban fada masa abinda ya faru ba har zuwa yau? "Me yasa baki fada masa ba? "Hajiya ta katse ni da tambaya. Kila ya musa, domin ban kamashi ido da ido ba, ko ya fusata ya dauki matakin da bai dace ba a cikin borin kunya. Na san cewa ta hanyar tattaunawa ne kadai ake iya warfare matsala.
Chapter 21 · 0% Book details