Sashe 5
Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abin ya birge ni banya da muka gama sallar asham na koma ɗaki dan in yiwa su Umma sannu da shan ruwa.
Cikin satin Shamaki ya zama cikin yi musu shirin tafiya.
Ana jibi za su tafi Hajiya ta kira ni. Tace min nauyi ya hau kanki na kwanakin da zanyi kafin in dawo, duk wani abu da ake bukata ke zaki samar da shi a gidan nan. Ta ciro ATM kati ta bani,ga wannan katin duk wata hidima ta gidan nan a cikin wannan asusun ake yin sa, yau sha biyar ga watan bature zaki biya dukkan ma'aikatan gidannan kuɗin su a ranar ashirin da biyar ga wata. Hidimar salla da abincin salla duk ke zaki samar, haka duk wanda ake ba goron salla zaki bashi, 'yan uwan Shamaki wadda duk bataje Ummara ba,nan zata yini da yaranta. Dan haka ki kula sosai ki mu'amalanci kowa da kyau bana son in dawo in samu wani ƙorafi ko da na mutum ɗaya ne. Nace To Hajiya insha Allahu zan yi bakin ƙoƙarina.
Tashin magariba za su yi ranar Shamaki bai fita kasuwa ba, na gama shirya masa komai na tafiya. Yace "Na so ace tare zamu tafi Baby." Nace Allah bai kawo lokacina a yanzu ba, in kaje ka saka ni cikin addu'o'in ka, Allah ya amince inje wata shekarar. Yace haba Baby ai ya amince insha Allahu. Ni addu'a zanyi ina dawo wa in samu in baki cikin Zeena 'yar mitsila." Nace wai kuwa in tambaye ka mana. Yace "Ina jin ki." Nace meyasa duk yaran sunansu ɗaya ko Hajiya ce ke zaɓa musu? Ya kama kunne na ya riƙe da ƙarfi har sai da na yi ɗan ƙara yace, bansan ko so nawa zan baki wannan amsar ba, amma in na kama kunanki zaki fi riƙewa, ni na zaɓa musu wannan sunan in zan haifi yara mata guda ɗari duk sunan su Zeena in kuma maza ne duk sunan su Aliyu." Na ƙwace kunne na daƙyar, nace na haddace amma fa ka handame da yawa. Kenan bani da damar saka sunan Umma da Abbanmu? Yace baki da hurumin haka, wannan hurumin su Jafar ne." Yin hakan laifi ne? Na jefa masa tambaya cikin harar wasa. Yace Babba ma kuwa amma fa a gurin Shamaki." Nace To Allah ya bamu masu albarka." Yace kinji batu.
Haka dai suka tafi har ina kuka ranar lokacin da zasu wuce. Hajiya tace, "Ba kuka zaki yi masa ba, addu'a zaki yi masa dan ga su Anisa nan bye bye suke yi masa ." Nace Hajiya kewa ce harda ta ku nake yi. Tace "Au to muna godiya. Ashe abin harda mu."
Na dai koma cikin gida bayan sun suka wuce. Ni sabo ne da ni,ko ina naje in zan tafi sai na yi kuka.
Na shiga ɗaki na zauna nace ni Baby wai gidan nan a hannu na yake sai yadda na yi da shi. Gashi babu wani cikakken bayani na sosai da Hajiya ta yi min bada kuɗin albashin ma'aikata. To kayan sallar ya zan samar da su,? Na miƙe. bari dai in kira Umma inji shawara sannan in samu Ba Juma in kallaɓa ta.
Lokacin da zan kwanta na kira Juma na faɗa mata cewa ayi duk yadda aka saba,a bawa kowa abincin asbahi in ba wani abu a yimin magana.
Tace "To Hajiya." Na kalle ta da sauri nace Kul Hajiya ɗaya ce a gidan nan bana son in kuma ji...
......
Da safe na kira Umma na ke faɗa mata hali da ake ciki game da gida da aka bar min, tace to ki yi komai tsakanin ki ga Allah sannan wannan katin na kuɗi kar ki kuskura ki taɓa ko ficika, duk abinda zakiyi ki ke rubuta an ciri kaza an sai kaza, ko naira hamsin ce ki tabbatar kin rubuta da kwanan wata da komai, domin in ta dawo zata buƙaci kiyi mata bayani, sai kawai ki ɗako ki karanta. Sannan duk wani mai aikin gidan ki keɓe da su ɗaya bayan ɗaya ki yi masu tambayoyi game da albashin su da kuma abinda ake masu a salla. Yaran nan nashi ki yi musu kayan salla da duk wanda ake yi wa." Nace to Umma sai dai abinda ke damuna wata magana da Juma tamin kwanan baya,tace wai Hajiya zata tambaye ni wanene Shamaki wai kuma in har ban sani ba,na faɗi gwajin ta, to ni da ba Allah musu su gare ni ba,yaya za'a yi in san wani sirri na su na ɓoye. Sai dai akwai wata mata a cikin waɗanda ake bawa sadaka da tace sunyi wa kakar Shamaki aiki wato uwar Alhaji Ali Baita, sai naji ina son inda tarihin asalin su,shine na tambayi kwatance sai kuma Juma ta yi min wannan maganar. Umma tace "Iko sai Allah, ni lamarin na ku kamar almara, to ai kuma akwai wata shekara da wani marubuci ya rubuta tarihin Alhaji Ali Baita har aka yi taron lancin na littafin a gidajan Radio aka yi ta sanar wa,me zai hana ki nemi littafin ki karanta,ba za a rasa shi a wannan gidan na ku ba." Amma ki bincika maganar kafin ki nemi littafin amma ba shakka na ji wannan da kunnen na.
Na yi wa Umma godiya sannan na fita domin in tabbatar da komai na tafiya daidai. Kasancewar azumi ne kowa na bacci kuma yaran dama an basu hutu dan haka na ɗakko makullin ɗakin Mijina na nufi can na tabbatar in har an buga littafin nan to dashi a gidan, in kuma tabbas akwai shi a gidan to ɗakin Shamaki yana ɗaya daga cikin ɗakunan da ya kamata a ganshi.
Ban wani wahala ba na ganshi a cikin wasu littattafai a durowar gefen gadonsa.
WANENE ALHAJI ALI BAITA?
Wannan shine sunan da ke manne a bangon littafin. Na kalli sunan marubucin Aminu Sani Takai.
Na rufe durowar na dawo bakin gado na zauna na buɗa shafin farko an rubuta Babi
na ɗaya.
Na fara karanta wa kamar haka..
Alhaji Baita wanda Asalin sunan shi Aliyu ɗan asalin ƙasar Sudan ne ya shigo Nigeria a lokacin yana matashi ɗan ƙasa da shekara ashirin,ya zauna a gidan wani malami inda yake karatun ƙur'ani,daga nan sai wani attajiri mai suna Alhaji Sani Aliyu ɗan kasuwar kwari maƙocin Malam ya ɗauke shi a matsayin yaron shago bayan Malamin ya nemi alfarmar hakan saboda shi Aliyu ya faɗawa Malam cewa ya na sha'awar kasuwanci.
Alhaji Sani shine ya sawa Aliyu suna Baita saboda irin sunan mahaifin shi ne ba zai iya faɗin sunan sa ba.
Biyayya da gaskiya da amana ita ta sa Alhaji ya maida Baita babban yaron shi wanda ya san dukkan sirrikan shi kasancewar shi duk 'yayan shi mutuwa suke yi sai guda ɗaya tak Amina suna kiranta da Gwamma . Saboda ya ƙara ƙarfafa zumunci sai ya wanke 'yar shi Gwamma ya bai wa Baita auren ta ya ci gaba da gudanar masa da kasuwanci har tsawon shekaru goma sannan ya fitar da shi ya yi masa sallama wato ya yi masa nasa Katin.
Cikin ikon Allah sai kuma Allah ya sa masa albarka kafin shekaru biyar sunan Baita ke yawo a sassan Najeriya da maƙwafta. Sai dai Allah bai bashi haihuwa ba, ya yi ta neman aure yana yi amma ba wadda ta haihu sai a shekarar su ta sha takwas da aure sai Gwamma ta samu ciki, ta haifi yaro na miji wanda ya ci sunan Aliyu ana kiranshi Ali. Haka ya taso a cikin gata. Allah ya yi wa Alhaji Sani rasuwa mahaifin Gwamma inda ta samu gado mai yawa da ƙadarori da kuɗi tsaba sai ta bi ta sa sunan ɗan ta Ali a matsayin mamallaki dukiyar ta. Shima Ali ya taso da cikin son kasuwanci shima tun kafin ya kai wani mata har sunan Ali ya doke na mahaifinsa Baita sunan Ali Baita ake ji domin shi ya yi karatun zamani.
Wannan ya sa Hajiya Gwamma ta fara tunanin matar da ya kamata Ali ya aure ta saboda mutane sai kyautar 'ya'yansu suke bashi yana cewa baya so.haka kuma Hajiya Gwamma tana bincike a hankali, sannan ta baza malamai suna mata addu'a Allah ya haɗa shi da mata tagari. Ganin yanda idon matan birni ya tsayu aka Ali Baita kuma ya gane dan kuɗinsa ne sai ya koma in yaga Yarinyar da yake so sai yaje gidansu da shiga irin ta talakawa, amma sai yarinyar ta wulaƙanta shi, washegari kuma sai ya yi shiga ciki ƙasaita yaje a Ali Baitan sa, sai ka ga yarinya ita da iyayen ta sun hau rawar jiki. Shi kuma sai ya zo ya faɗawa Hajiya cewa ya fasa, anyi haka ba bu adadi dan haka ya haƙura. Wannan ya sa ya ja lokaci bai yi aure ba abin yana damun Hajiya Gwamma har ta hakura kan cewa zuwa yanzu duk wadda ya samo ita ce alkhairi.
A Shekarar 1950 yaje wani taro na 'yan kasuwa na ƙasa wanda aka gudanar a jihar Lagos da yaje ya haɗu da wata 'yar kasuwa da ta zo daga jihar Zamfara. Ali Baita ya kamu da son wannan mata bayan sun tattauna hira akan kasuwanci kuma ya fahimci tana da basira da kuma nasibi a harkar kasuwanci sai kawai ya yi mata ta yin soyayya kuma ta amince ya dawo ya faɗa wa mahaifiyar shi Hajiya Gwamma, ta yi murna amma tace sai ta saka anyi mata binciken wacece Zeena Amadu Shinkafi.
Na ɗago kai tare da sauke ajiyar zuciya. Babi na ɗaya ya ƙare na miƙe naje na ja durowar na maida littafin na nufi ɗaki na. Na hau gado na kwanta lamo. Kafin in ci gaba da karatun ina buƙatar in yi nazarin abinda na karanta domin in rike shi kuma in haddace..Yanzu dai naji tushen Shamaki tun daga Kakansa labarin ya faɗo kan mahaifinsa wanda shine dama ake bada tarihinsa ko ince aka rubuta littafin domin minsa. Zai zama dole akwai iya inda labarin zai ƙare ba bu cikakken bayani akan Shamaki. Sai dai zanbi labarin a hankali har zuwa inda ya ƙare sanna in nemo sauran labarin in ɗora.