← Book details Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 31

Sashe 2

Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace to bata, suka gaida shima dai ya bada haƙuri akan cewa su yi haƙuri da ni in har na yi ba daidai ba. Suka yi sallama yace da Umma ta gaishe ni, kuma ta taho domin gashi nan zai koma gidan yanzu.

To haka dai muka sake fitowa gaba ɗaya,domin Hajiya bata da niyyar bamu guri, muka dawo Falon Hajiya. Umma ta miƙo leda mai layi layi tace ga tafarnuwa da kayan ƙamahi Hajiya, tsarabar ce sai na rasa me zan kawo muku tunda Allah ya sa kuna da komai.

Hajiya tace "To muna godiya Allah ya saka da alkhari. Hajiya ta dube ni, "Shiga ciki kan gado ki ɗakko mata Envelope ta sayawa yara alawa a hanya. Ta dubi Juma da ke kwashe kayan abinci tace "Je ki faɗawa direba zai maida baƙuwa gida.

Har mota na raka Umma sai da naga motar ta bar harabar gidan sannan na dawo ciki. Hajiya ta kalle ni, ke ce "'yar fari ko?" Nace E. Hajiya. Tace. "Naga itama yarinya ce mahaifiyar ta ki. Nayi Murmushi tace "Gurinta ki ka samo wannan shegen baƙin wayon ko?" Nayi 'yar dariya nace bari in shiga ciki.

Na yi wanka na yi salla naji daɗin zuwan Ummana duk da Hajiya ta hana mu sakewa. To wai ita Hajiya domin kar in faɗawa Umma cewa Shamaki zai ƙara aure shine ko kuwa dai tana zaton zan faɗawa Umma cewa bata min yadda kamata ne?

Bani da amsa don haka sai na tashi na ce bari in kira Umma inji ko sun isa gida.

Na faɗa kan gado na, na ɗauki wayata na kira layin Umma, ta ɗaga tace "Yanzu fa na ke shirin kiran ki in faɗa Miki cewa
Dubu Hamsin ne a 'yar takarda nan da Hajiya ta bani."

Na ja dogon numfashi nace amma angode Allah ya saka da khairan. Gashi bamu samu minti hira ba. Tace "To wace hirar ma zamuyi ko kina da wata matsala ne?" Nace "To ba dai wata ƙatuwar matsala bace amma dai an saka mishi ranar aure da wata yarinya 'yar uwarshi, tana nan a gidan ko da kika zo tana ciki bata fita ne hatta makaranta ta daina zuwa. Umma tace "Tofa! Amma kin san abinda nake so da ke?" Na ce A a,Tace ki kama kanki ba ruwanki da auran sa. Sannan hanyar da da maganar gidan malami da Hajiya ke yi duk yadda aka yi so take ta gwada ki, ko dai wani abu mai kama da haka. Nima baki ga ta latsa min basira ba, kar nake kallon ta. Wata uwa ce zata ce a kai ɗanta gidan malami ki kiyaye sosai wata kitimirmira take haɗawa. Kuma ki ke nazari ko magana zaki furta domin na lura cewa 'yar shan loga ce, ga ta da alaye. Sannan karki taɓa damuwa da abinsu. Baki gani ba,naman nan ina son inci shi amma ina jin tsoro kar in bar miki abin faɗa dan haka na kauda kai daga gare shi na haɗiye kwaɗa yi na.

Nayi dariya nace zan kiyaye Umma, tunda ga kuɗi nan kin samu sai ki siyo muku mama ku dafa.

Tace wannan kuɗin zan ciri jari a ciki in ba Abbanku dubu goma shima. In sai wa Jamila tukwane, ba zan bari in maimaita kuskuren da nayi a baya ba a bikin ki. Nace haka ne Allah ya rufa asiri. Tace "Ameen dan Allah kar ki saka maganar aurannan ya dame ki, ke dai kiyi ƙoƙari ki iya allonki. Nace Insha Allahu.

Muka ɗanyi shiru can tace ina ganin fa kamar kin ƙara ramewa, anya babu wata matsala bayan wannan?" Nace babu, ai nayi zazzaɓi ne kwanaki harna kwanta a asibiti amma nayi ƙiba, sosai. Tace Allah ya ƙara lafiya, yanzu dai ki kwantar da hankalinki. Nace to Umma.

Bayan mun yi sallama na yi shiru ina tunani, yaushe kuwa zanyi wata ƙiba a gidan nan tunda nayi kuskuren duba wayar mijina.

Kuma gashi abin ya zame min masifa ko na ce bazan duba ba sai na duba. Gashi dole in haɗiye duk abinda na gani a cikinta tunda bani da damar fadawa wani domin in samu salama. Duk da cewa ina bukatar shawara amma bansan wa ya kamata in nema shawara ba, wanda asirina zai rufu. Zan ci gaba da miƙawa Allah kuka na shine mafi girman wanda zai bani mafita.

Azumi ya gabato bai fi sauran kwana tara ba, Shamaki baya samun zama yawanci sai na jima da bacci ya ke shigowa. Suna ta fama da lissafi za su cire Zakka. Za su tafi Umara,ita Hajiya acan zata yi Idi shine zai dawo kafin lokacin salla, amma sai an fara azumi da sati biyu zasu tafi.

Sun fara rabon zakka ina zaune ina jin su ana lissafin, masallatai da za'a kai miliyoyin kuɗi. Sai kuma wasu marasa ƙarfi, sai dangin su da za a baiwa dubu ɗari ɗari a Envelope da kayan abinci. Yayinsa kowa ta zo ta kawo list na mutanen da take son a taimaka. Ni kuwa matar gida ko oho,ina zaune bana maganin ahu, ko kitso da ƙunshi ko wanke kai saidai direban ya kai ni in turawa Hajiya account ta turo musu kuɗin.

Ɗinki kuwa da yace in bada kayan cikin lefena duka a ɗinka da na faɗa mata zan kai ɗinki Unguwar mu sai tace a a,ta sa Maman Iman ta kawo tela har gida ya gwadani ya kwashi kaya, sai dai ɗinki na gani bani da wata hanya da kwabo zai shigo min duk wani abu da nake buƙata za a kawo min.

To irin wannan uƙuba ta rashin kuɗi dan ma dai dama can ban saba riƙewa ba bare in damu sosai.

Ina kwance sai ga Juma wai inzo inji Hajiya. Na same ta a hakimce kamar kullum da carbi tana ja, ta bini da kallo har na fara tunanin ko nayi wani abu ba daidai ba. Na tsugunna nace Hajiya gani. Ta nuna gefen ta da yatsanta, "Ki ƙirga min wannan Envelope ɗin guda nawa ne." Na ce To. Na ƙirga guda ashirin ne. Tace "Dubu ɗari ɗari ne a ciki ina son ki rabawa mutum irishin ma su buƙata ciki harda su Juma, sannan yanzu zan saka Juma ta je ta rakaki can baya inda kayan abincin zakka su ke, na azumi , ki raba su ga masu buƙata. Na zaro idanu ina faɗin Hajiya bazan iya ba." Ta ɗago ta dube ni cikin gimtsewar fuska,tace kina auren Shamaki amma baki san yadda ake raba taimako ba? Na kalli Juma wadda ta min alamar inyi shiru da ido. Na maida dubana ga Hajiya wadda ta kuma tattara hankalinta ga carbin da take ja. Na miƙe na ce Juma muje ki nuna min.....
....
Muka fita can wata haraba ta bayan gidan ina ta tunani yadda zan bigi cikin Juma.

Nace wai kuwa Baba Juma a ina ake rabon kuma suwa da wa ake baiwa.? Tace "To kowace mace dai da yadda ta ke rabon ta wata ta yi a cikin gida wata kuma a waje amma can da dai a cikin gida ake yi kuma ba a taruwa, yanzu dai naki sai yadda ki ka yi da shi."

Nace kina nufin duk sauran matan sun yi irin wannan rabo? Juma ta ja baya ta riƙe ƙugu sannan Tace "Babu wadda ba ta yi irin wannan rabon ba." Nace ni damuwar ban san su wa zan baiwa ba. Kuma yaushe zan bayar? Tace "wannan duk yadda ki ka yi Hajiya bata da matsala da haka, in kina so ma zaki iya bari sai sun tafi Ummara sai ki yi yadda ki ke so." Na kalli Baba Juma tabbas tana min wani irin kallo mai kama da shurin jeki ki mutu.

Muka ƙarasa wani ƙaton store narke da shinkafa 'yar gwamnatin ga taliya da makaroni Suger Indomie da sauran kayan abinci na azumi.

Na kalla nace taɓɗi gaskiya in wannan aikin yana cikin jarabawar Hajiya ba shakka dole a faɗi.

Muka dawo ni dai ranar haka na yini ina nazari
Na ɗauki waya na kira mijina Shamaki ya ɗaga cikin sauri yace "Menene yi magana meeting zan shiga yanzu." Nace to dan Allah ina son magana da kai in ka fito. "Ki kira ni ƙarfe Shidda na yamma." Bai jira amsa ta ba ya kashe wayar.

Na ce kai nima fa ina da uwa,duk Duniya ita ce take min son da ba wanda ya ke min makamancin shi, dan haka ita ce zata bani mafita kamar yadda ya ke tutuyar ta shi uwar tana sama mishi mafita.

Na ɗaga waya na kira Umma, Muka gaisa nace Umma dama wani yanayi na samu kaina ina buƙatar wanda zai tsaya min har komai ya yi kyau "To kuwa wake gare ki bayan mu Baby?" Ta katse ni. "Menene faɗa min. Na kwashe komai na sanar wa Umma sannan na tsaya sauraron ta. Tace abu na farko yanzun ki je ki samu Hajiya ki ce abaki list na mutanen da za su amfana da wannan zakkar in ta baki sai mu sake yin magana."

Na zo bayan la'asar na samu Hajiya tana kallo na zauna na gaishe ta,sannan nace Hajiya dama list za a bani na waɗanda aka saba baiwa wannan taimakon. Hajiya ta ɗago ta dune ni kamar zata yi magana sai kuma ta kauda kai, sannan ta ɗaga wani fayal ta ciro wata doguwar takarda mai ɗauke da sunaye a jere tace "Gashi." Na amsa,nannan na nace yawwa Hajiya dama su waɗannan kuɗin na cikin... Ta ɗaga min hannu duk yadda ki ke buƙata haka zaki yi abida ya sa na baki list ɗinnan saboda kin tambaya ne,da baki tambaya ba bazan baki ba."

Na ce To na gane. Na koma ɗaki ina me alfahari da uwata na zauna na duba list mutum ɗari harda uku. Na kalli kuɗin aka durowar gefen gado na, nace gashi kuɗin na mutum ishirin ne.
Naira miliyan biyu ne ta riga ta raba kuɗin bare ince a rage su yadda kowa zai samu. Na sake duba takardar sosai ko a kwai sunayen da zanga anyi musu alama amma bangani ba,na kuma kiran Umma na faɗa mata ga halin da ake ciki.
Chapter 2 · 0% Book details