← Book details Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 31

Sashe 15

Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace na daina Hajiya wallahi naji kunya da yawa, ina yin dana sani sosai.
Ni ina can bansani ba, ya fice. Lokacin da na fito tamkar wani abu bai faru ba domin banga komai ba. Hajiya tana mazau nin ta na yi mata sannu na shiga kicin domin gabatar da abincin rana.

Juma tace "Uwar dakina me yake faruwa a gidan ne? "Nace wani abu ki ka gani? Tace Uban dakina Shamaki yaudai ya fusata Hajiya da rana suka rufe kofa suna tattaunawa, sannan wannan yarinyar Azima sai gata da kuka. Nace Juma bansan komai ba, suda basa gidan? Juma tace "To sundawo nace amma bai shigo gurinmu ba. Tace to bandai sani ba, amma Allah yasa inga Annabi haka yadda na ganshi." Na tsaya ina kallon Juma ta ce, "Hajiya dai cin zarafin su ta yi, domin yadda na ga yarinyar nan kamar ma kuka ta ke yi.
Na sauke ajiyar zuciya kila maganata ta yi tasiri na ayyana a zuciya. Nace ke to ina ruwan ki Juma, kince bakya gulma amma dai kina sa ido. Tace "A a "yannan karki yi min mummunar fahimta.
Bayan an idar da la'asar sai naga kawu ya shigo da wasu maza, da goro da kuma dabino. Na tashi na basu guri ina zaton an saka rana ne.

Da dare na samu Hajiya da Shamaki kamar yadda na saba amma shi kamar yana ta dan dari-dari. Yau Ni kai na ya kasa kallo na. Hajiya tace in shafa mata magani da wuri yau zata sha magani ta kwanta. Nace Hajiya bakijin dadi
ne? Tace yau kam jikina ya yi nauyi zan kwanata da wuri. shima ya yi mata sannu kafin ya dauki carbinta ya bi bayan ta. Na koma dakinsa ina jiran zuwan shi.

Suna shiga Hajiya ta hau gado ta zauna ya dakko mata magani ya mika mata, ta amsa ya bata ruwa ta sha. Ta kalle shi, "Yinin yau da bakin cikin ka na yi shi. Amma na yafe maka, ina son ka roki Allah ya yafe maka. Yace na gode Hajiya insha Allahu zan roke shi kuma har abada na daina.
Tace Allah ya sa haka. Tun lokacin da na fahimci cewa kana bin mata na baka dama ka yi mata hudu kuma bani da zabi ka zabo mace ba ta shi'awa ba wadda ka ke so kuma ka ke kauna. Ka auri yarinyar nan domin kana son ta na tabbatar kana son ta amma me yasa ka ke fita waje neman mata? "

Yace ki yafe ni Hajiya amma ba kamar yadda ki ka zata ba ne. Bani da sauran abin cewa dai amma ina neman yafiyar ki insha Allahu, ban taba jan kunya kamar yau ba a duniya.
Hajiya tace ya wuce, gata can a daki yanzu kam matarka ce duk abinda ku ka ga dama kuje ku yi, sannan ka gyara inda zaka sakara ba wani taron biki da za ayi, na baka sati daya ku tare bana bukatar zama da Azima a gidan nan. Sannan ka sani yin adalci a tsakanin matanka shine abu mafi mahimmaci da ya kamata ka maida hankali a kai.
Yace insha Allahu. Yanzu dai bansan yaya zan fuskaci Baby da maganar auren nan ba. Hajiya tace wannan ya rage na ka, duk a baya ni ce nike fada mata wannan karon sai ka fada mata.

Ta bishi da kallo, banda soyayyar da da uwa wadda Allah ne ya dora min da tuni na fita a sabgarka.
Ka tafi zanyi bacci.

Ya shigo dakin jiki ba karfi Ina kwance ina kallon TV, na bishi da kallo ya cire kayan jikinsa ya fada bandaki. Ya yi wanka ya fito, ina ta share shi wai ni irin ya tambayi dalili sai mu zauna a zube magana, amma sai naga shi bama ta ni yake yi ba. Ya hau gado ta kwanata kamar dai nima share ni ya ke yi. Na kalle shi ina mamaki. Nace ka tashi zamu yi magana dama kai nake jira. Yace a yau ba wata magana da zan yi da zai yiwu da sai kawai ki tafi dakin ki. "
Gaba ya fadi, nace ni kake Kira? " Ya ce to kwanata amma ki min shiru ina son inyi wani nazari ne. Ban kuma magana ba, na tashi na fice daga dakin na nufi daki na.
Na sha kuka a daren naga bazai kaini ba na dauro alwala. Akan sallayar na kwan bayan nayi ta salla na gaji na zame na kama bacci.

Washe gari na nufi gaida Hajiya amma bata falo, lallai akwai damuwa jiya ta kwanta bata jin dadi. Na nufi dakinta. Tana cikin bargo sai fuskar Shamaki yana zaune a bakin gadon yana waya da likita. Na isa na durkusa a bakin gadon nace Hajiya ya jikin tace da sauki bacci na kasa yi a jiya gashi dai har yanzu.. " Nace Allah ya baki lafiya Hajiya. Tace ameen. Likita ya zo jinin Hajiya ya hau da yawa, ya zuba mata allurai a cikin ruwan da ya sa mata. Ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita.

Shamaki ya kalle ni fuska ta a daura yace Baby jiya kin yi fushi ko? Na zura mishi ido ya ci gaba. Kiyi hakuri ni kaina ina da magana amma Hajiya bata jin dadi shine dalili. Bari ta samu sauki sai mu y maganar.
🖊️🖊️
A ranar dai Hajiya daki ta yini Shamaki ma sai azahar ya fita kasuwa, ni kuma na yini da Hajiya a daki saboda baccin bai yi tsawo ba ta farka. Na bata fura ta sha, sai kayan marmari da na matsa mata ta ci. Har zuciya ta ji nake kamar in baiwa Hajiya lafiya.

Lokacin shan magani ya yi na bata. Lokacin salla na yi mata alwala ta yi salla tana daga kan gado.
Shamaki kunsan duk minti goma sai ya kira waya ya ji batun jikin.

Yace min ko ya fadawa su maman Umar ne. Nace a a karya daga masu hankali ka barsu. Hajiya da ke kwance tana jin mu sai ta daga. Nace ya fada musu, ta girgiza kai alamun a a.

Umma ta kira ni, nake fada mata jikin Hajiya tace Allah ya sawake, sannan tace akwai wani magani da Abbanmu ya siyo mata lokacin da ta yi wannan haihuwar na hawan mini ne ana sha da zuma taji dadin sa ko ta aiki Jamila ta kawo mana. Nace bari dai in fara tambayarta domin nasan su basu cika bawa maganin gargajiya muhimmanci.
Na fadawa Hajiya tace a kawo mata.
Kwanan Hajiya biyu tana jinya ta murmure ta samu sauki.

Duk bansan an daura auren Azima da Shamaki ba. Sai a rana ta uku. Wadda ta kama juma'a. Shamaki yaje daurin auren wani abokinsu daga can ya dawo gida, nace ai na yi tsammanin
Kasuwa zaka wuce, yace kayan jikina zan canza bana son fita kasuwa da babban riga musamman ta shadda.

Na amshi rigar da hular na nufi dakin shi. Ya shigo dai dai lokacin da nake saka hular a mazauninta. Ban ankaraba sai naji ya cakulkuli a gefen cikina na saki hukar nayi zillo nace wayyo, na fara dariya. Yace kwana biyu dai kin share ni, har wani shakkar taba ki nake yi." Nace ni din ka ke shakka babban bako, ni a suwa zakaji shakkata?
Ya zauna ya janyo ni ya zaunar da ni a cinyar sa. Yace Baby dan Allah kifahimce ni akan abinda zan fada miki yanzu. Na ce ina jinka, kaima ka san cewa zan fahimce ka. Yace "Wallahi an daura auren mu da Azima shekaran jiya Waccan. ' Yawun baki na ya kafe, kirjina ya buga, sai naji cinyarsa ta zame min kamar na zauna a kan kaya. Dan haka sai na zame na zauna a bakin gado. Ya zuba min ido, ni kuma na kasa magana domin bani da yawun da zan sarrafa. Kallon shi kawai nake yi.

Yace "Ban yi domin cin fuska ba, Hajiya ta yanke hukunci itama bisa wani dalilinta wanda bata fada min ba. Kuma ta bani sati daya in tare da Azima a wani gidan, ko da dai tace ta baki zabi ko? "
Har lokacin ban furta komai ba, na dai mike ina dan kai kawo a gaban gadon so nake indan samu makoshi na ya yi danshin da zan yi magana.

Na isa karamin fridge na dakin na bude na dauka ruwa na bude ina kwankwada kamar wadda ta kai azumi a cikin sahara. Sai da na shaye tas na aje robar, na kalle shi kamar zanyi magana, amma sai na fasa, na sa kai na nufi dakina domn bana son in masa kuka.
Ina son inyi tunani kafin in yi masa magana, sannan ina son in sauka daga giyar kishin da ya danne ni ya duramin ita babu zato ba tsammanin.
Na fuskaci kuka rahma ne duk lokacin da ma ace in yi shi don in samun salama a cikin duk wata damuwa da na samu kaina, amma yau kukan ya ki zuwa ko zuciyata zata rage radadin azaba. Na fada bandaki nayi alwala na fito duk da ba lokacin yin salla bane sai na zuba sujja ina kiran sunayen Allah. Kar ku ga laifina ina da mugun kishi, wanda ba ni nayi wa kaina halittar shi a zuciyata ba, Allah ne ya dasa min.
Chapter 15 · 0% Book details