Sashe 6
Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Na tashi na fito zuwa kicin na samu su Juma suna ta goge goge. Nace Juma ta min bayanin abinda ake buƙata na buɗa baki, sannan yara a tabbatar an ba su abinci da wuri tunda basa yin azumi. Ta ce "Dama yanzu nake faɗawa Laure ta ɗora musu Indomie zanje gunki in tambayi abinda za ayi,sai kuma in faɗa miki abinda ake buƙata. Nace babu damuwa ki sanar da ni yanzu. Kuma tace yau ranar kunun tsamiya ne da ƙosai sai farar shinkafa da kayan ciki, sai lemon zoɓo sannan akwai fura da kilishi." Nace to duka akwai su ko sai an nemo? Tace Nono ne za ayi waya a kawo. Nace to ina lambar? Tace bani da ita, sai dai ki kira Hajiya ta baki. Nace to na fita na koma falo na duba in da Hajiya ke zama akwai wani ɗan littafi da na fahimci tana rubuta lambobi. Na ɗauke shi ina dubawa, ɗauke ya ke da suna da kuma lambobin waya. Tabbas zan gani tunda ga sunayen masu kaji da nama. Boɗejo mai nono, take na kira lambar wani namiji ya ɗauka muka gaisa yace gidan Alhaji Baita ko? Nace e yace to zan faɗa mata za a kawo ne? Nace E .
Ƙwarya ɗaya aka kawo nace nawa take bayar wa? Suka ce dubu ishirin nace to ina lambar akawut ɗin su, sukace Hajiya na dashi a rubuce. Nace to ba damuwa. Sai lokacin na tuna ai ba amshi lambobin sirrin ba.
Na sake ɗakko ɗan littafi tabbas ga account ɗin su. Lambobin shirin sune matsala yanzu koda na saka direba ya kai ni banki ai babu su, sannan wani ƙalubalen ban taɓa zuwa banki ba tunda uwata ta haife ni.
Na shiga kai mari ina kai gauro, ina ganin dai Hajiya tana sane bata bani number ba. Na sake zuwa ɗaki na kira Umma na faɗa mata. Tace " Ki samu nutsuwa Baby duk lambobin sirri suna zama na musamman ne, haka kuma zasu kasance ɗayan biyu, kodai wasu daga cikin lambar waya ko kuma ya kasance ranar haihuwa. Zai iya kasance wa ranar haihuwar ɗa ko miji, wani abu dai da ba'a manta shi. Nace to, sai dai ya zanyi in gwada.
Nace wa Juma ta faɗawa direba zamu fita zuwa banki. Har na hau mota sai na tuna da Azima na sauka da sauri na cewa direba ina zuwa. Na je na shiga ɗakinta. Tana zaune tana kallo. Ta bini da kallo nace Azima zo muje banki mana. Tace Hajiya ta ce kar in sake in fita zuwa wani guri. Na zauna bakin gadon nace kin taɓa zuwa ciro kuɗi da Hajiya?
Ta dube ni. Ta sake mai da kanta ga kallon TV kamar ita ce Hajiyar sannan tace, ki duba jikin katin zaki gani. Na kalli katin da kyau banga wani rubutu ba, na miƙa mata nuna min. Ta amsa ta kalla tace wannan ba katin da na sani bane, kije ku duba gurin da take zama, ko kuma ki kira ta mana. Na fita na koma na duba bangani ba. Na kira Shamaki a Video call, ya ɗauka suna Madina yace min "Yi haƙuri Baby ina ta son in kira ki in na samu nutsuwa. To ya gidan ya kowa da kowa?" Nace duk muna lafiya . Kaga dama zan tambayi Hajiya ne bata bani lambobin sirri na katin ba, kuna tare ne? gashi masu nono sun kawo za ayi musu Transfer. Yace "Gaskiya ban sani ba,amma tana yawan amfani da 1950 ki gwada ki gani. Sai dai kuma kada ki ce mata ni na baki,domin tsawon shekara ɗaya ne bazan shiga wata magana da ke tsakanin ke da Hajiya ba, ƙa'idar shi ne in an cika shekara zata bani umarni." Nace Umarnin saki na ko? yace "Bana fatan haka. Ke dai kiyi ta ƙoƙari duk da bansan me take dubawa ba ina yi miki kyakkyawan zato. Nace direba zai kai ni banki zan tura kuɗi in ciro wasu in aje a gida saboda buƙatar gaggawa. Yace "To amma dai ki sani Hajiya ce zata karɓi alert. Nace Karka damu. Yace ki kula da Azima in tana bukatar wani abu ki mata. Nace ." To. Sannan ban taɓa zuwa banki ba yaya za ayi in gane yadda zanyi amfani da katin? Yace ki samu ma'aikacin gurin gurin guda ɗaya sai ya nuna miki, kar ki yarda da kowa fa." Nace to.
Cikin sa a da naje banki ashe ita ce lambar da na faɗawa ma'aikacin. Ya nuna min yadda zan tura kuɗi da yadda zan cire da kuma yadda zan duba ragowar kuɗin.
Da ya tafin na shiga gurin duba ragowar kuɗin ban gane ko nawa bane sai tarin ziro. Na ciri dubu ɗari na koma mota.
Washe gari Rahin ta same ni tace za a yi wa yara kitso." nace To ayi musu. Na je har lambu inda ake yi musu kitso na tambayi mai kitso kuɗinta ta faɗa min nace in an gama Rahin ta zo ta amsa, na ɗauki takarda na rubuta. Su kuma nace ta ba su cakuleti su daina rigima.
Haka nayi fama ina iya kacin ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai. Har kwanaki tara na gana duk ma'aikata da masu gadi jani albashin kowa kuma na biya su. Kuma ce ta sanar da ni cewa Hajiya tana ba su atamfar salla kala biyu maza shadda. A shagon Zeena na sa su Ahmad yaran shagon Shamaki suka kawo na biya su kuɗin. Yaran kuwa a mota na zuba su muka je Zeena Supar market na zaɓa musu 'yan kanti masu kyau. Azima kuma tace Jallabiya take so, ta faɗi tsayi da kala muka zo mata da shi. Ni kam ban sai wa kaina komai ba,sai kuɗin kitso ne a lissafina da kowa sunan shi na saka.
Sai kuma batun mama da kajin salla. "Shanu biyu raƙumi biyu kaji hamsin ake amfani da su." Inji Juma. Na zaro ido tare da faɗin wa zai je siyan waɗannan?
......
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 40*
Allah cikin ikon sa a na sauran kwana huɗu salla sai ga Shamaki ya kira ni yace sun sauka a Abuja zasu hau jirgi zuwa Kano, nace shine jiya fa mun yi waya amma baka faɗa min ba. Yace "Bazata ce." Don haka na tashi na shiga shirin tarbar mai gida. Ranar kuwa mai ƙunshi ta zo ta yi mana jan lalle, ita kuma mai kitso sai washe gari.
Nayi murna sosai da dawowar mijina, kasancewar Hajiya bata nan a gaban kowa na rungumi mijina ina murna. Shima ya ƙanƙame ni sannan yace "To ga yaranki bari suma in ba su runguma." Ya ɗauke su ɗaya bayan ɗaya, sannan ya miƙawa Rahin wata leda, yace a ba su chocolate kowa ya sha. Ko suna azumi?" Anisa tace bamayi Dady.Nace Kince min ki na yi fa Anisa Baby. Tace Mommy ai na karye shi fa. Muka sa dariya.
A ranar dai kam na tabbatar cewa na yi kewar shi na tsawo kwanakin,. ,amma shi ya fi kewata ya kasance kamar zai cinye ni.
Dawowar Shamaki ya taimake ni sosai domin sai dai naji an kawo shanu da raƙuma. Kaji kuwa haka aka yi ta rabon su, kamar in tambayar wa su Umma, amma sai nayi shiru tunda na san suna sane da su.
Juma ta same mi tace "Hajiya tana nemo wasu masu aikin su taya mu kamar uku sai kuma aikin cincin da duk kayan fulawa bamu ke yi ba Zeena ake kaiwa wanda suke cewa ko batiri ko me?." Nace ko dai Factory? Baba Juma tace "Yawwa haka." Muka yi 'yar dariya. Nace to zanyi masa magan. Sannan ina zani neman masu aiki ukun da ki ke magana? Tace "In kuma in samo su sai in samo, domin da akwai su."
Nace ki samo. Haka ta samo mata ta faɗi abinda za a ba su agaban su na sallama in an gama salla.
Ranar Idi na matsawa Shamaki don Allah zamu je sallar idi yace , "Ba wadda ta taɓa zuwa in tsoro kar Hajiya ta ga cewa an kawo wani abu daban." Nace amma wata ta taɓa cewa zataje Hajiya ta hana? Yace "A cikin su babu wadda ta ambaci zuwa Masallaci." Nace bana zaton Hajiya zata hana ibada. Yace Haka ne."
Haka dai ya kwashe ni da yara mukaje sallar Idi duk mun sha hijabai waɗan da na saya mana a kasuwa domin amfanin yau ɗin.