Sashe 17
Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Na zauna tare da fadin gani. Tace "Me ki ka fada masa game da kwana da ya zo ku yi magana a kai? " Nace ya je ya kwana can na hakura. Hajiya ta yi dan murmushi, wannan hakkin ki ne in kin sarayar musu ba zance komai ba, amma ba zai taba yiwuwa ya zauna a can gidan ba, zai zo nan duk kwana biyu ya je can kwana biyu. " Nace Ai na fada masa dama ni bansan ya ake yi ba da yace wai zamuyi shawara nace yasan da ku ake yin shawara kune kula san abinda y kamata ayi, shine ya zo gurina. Hajiya ta ce ni dai na gama magana." Nace to amma Hajiya yanzu dai ai sati daya zai yi tukunna ko,? Tunda dai budurwa ce. Suka kalli juna da Hajiya ni kuma na kauda kai ina murmushi nasan dai sunsan magana na yi nima. Hajiya ta ce "Haka ne." Nace Hajiya zan iya tafiya? Ta daga kai. Na wuce a raina nace na dai aje muku magana.
Haka dai ya cika sati a gidan amarya. Ranar da zai da wo gidan
Tun safe da naje gaida Hajiya tace min yau mijinki zai kwana a nan, "Me ki ke shiryawa? " Nace bana shirya komai. Tace kina ganin kuma hakan dabara ce a gurin ki? Na sunkuyar da kai, na san nufin ta in zubar da duk wani haushina in rugumi danta kar in bata masa rai. Ta katse ni. "Kar ki taya fushin kishi kin san dai namiji shi kamar yaro yake, inda ake lasa masa zuma can ya ke zuwa yawo." Nace bana fushi da shi. Tace to kamata ya yi kije yau ki yi kunshi ki gyara kanki duk da cewa na lura sosai bakya zama da rashin tsabta. "
Nace to zanje. Ina zuba mata abin karin ya shigo. Na gaida shi kafin na tashi, duk da kokarin da nake yi na kar in kalle shi sai da ya yi yadda ya yi muka hada ido. Na daure fusaka sannan na mike na nufi dakina. Da gudu na karasa na kullo kofa na sai zai biyoni. Ya gaji da kwankwashen shi ya tafi. Sai da na tabbatar ya bar gidan sannan na fito da shiri tafiya unguwar su Maman Iman dama na mata waya.
A gidan aka samin lallen muna ta labari. Tace min Baby wai kuwa ni kullum ina son in tambaye ki amma ina jin tsoro kar Hajiya ta san na tambayi wani abu game da cikin gidanta, kinsan bata son maganar gidanta na fita waje harmu sai iya abinda ta ke son mu sani muke iya sani. " Nace To Anty dan munyi magana tsakanin mu wa zai fada mata.? Tace
"Bansani ba, amma na lura kin karbu a gurin Hajiya duk da bata da korafi da yanzu ko so daya ne munji ta yi maganar ki ko da yaya ne. In kika fahimci Hajiya zakiga saukin kanta sosai, Soyayyar Hajiya daban ce ba lallai kiyi saurin fuskanta ba,. Wanda Hajiya ta ke so yana da wahala ya gane ta na son shi lokaci guda. Son mutum daya ne bata iya boye shi ko a gaban waye, son Shamaki shike sa Hajiya ta yi ba dai dai ba, kullum cikin uzri take masa. Kunsan Allah mun sha yin tunani akan wace mace ce zata iya zama da Shamaki saboda irin yadda Hajiya ta ke matukar son shi da boye laifin shi, shi kanshi ya na son Hajiya fiye da kowa a rayuwar shi kafin ya yi aure lokacin Hajiya take gudanar da harkokin kasuwanci, shi lokacin yana dan makaranta da ya taso daga makaranta office din ta zai wuce, lokacin da aka kai shi China karatu ya dawo kusan so uku, sai da Hajiya ta aje komai ta je can ta yi wata uku tare da shi kafin ya zauna. Dan haka duk matarshi sai ta yi hakuri ta kauda kai. "
Nace na lura da haka, amma ko hakan yana da alaka da rabuwar sa da matansa? Maman Iman ta ce duk da Hajiya bata bari a san dalilin ke inaga ko shi kanshi Shamaki ba zai ce miki ga cikakken dalilin sa na rabuwa da matansa ba. Hajiya ce ke sa ya sake su, amma tana da wani dalili da ita ce ta bar wa kanta sani. " Nace shiyasa kullum a fargaba na ke, in Shamaki ya sake ni Anty na shiga uku, son sa nake har bana iya boyewa a gaban kowa, kuma ga shi yana min abinda ya kamata in nuna masa jin haushina amma bana iya wa. Maman Iman ta yi dariya. Tace "Shimaki yana son ki fa, na sani in Hajiya tace ya sake ki zai iya, amma za a sha fama. Sai dai kuma kamar bana zaton Hajiya zata ce din duk da ita kadai ta san dalilin ta." Nace ina ta fadawa Allah ya zaba min abinda ya fi zama alkhari a rayuwa ta. "Kin gama magana, ni ma abinda ya sa na kawo wannan maganar saboda na ga bakya kiba sam, har yanzu kina nan firit sai dai fatar ki ta goge kin murje alamu hutu." Nace haka kowa ke cewa, Ummana har cewa ta yi wai ko zan dinga yin madarar waken suya tana saurin gina jiki. Nace mata muna cin abubuwan gina jiki sosai, kila dai ni haka nake. Amma shi fa bai damu da kibar ba, domin bai taba min maganar ba. Tace zan baki wasu kwayoyi na gargajiya ne 'yan waje za su fidda miki shef ki yi kyau. Nace ta bani. Ranar na yini munsha hira irin wadda bamu taba yi ba, na kuma sake fahimtar wasu abubuwa game da su.
Sai karfe hudu na dawo ga turaruka ga kayan gyara na mata duk ta hada ni da su.
Hajiya ta sa anyi girki na musamman ana kiran sallar magriba sai ga Azima ta kwankwaso tare da sallama na gyarawa Hajiya gurin salla. Na amsa Hajiya ta shiga alwala. Azima ta min wani kallo sannan ta kama kujera ta zauna. Hajiya ta fito sai naga ta bi Azima da kallo cikin mamaki . Azima ta sakko ta rusuna ta gaida Hajiya. Ta amsa, sannan tace "Me ki ka zo yi? " Azima Tace shine ya ce wai mutaho bazai iya barina ni kadai a can ba. Hajiya ta kalle ni. Da wutsiyar ido na lura Hajiya ta kalle ni, kila tana son ta ga ya na dauki abin, ni kuwa na yi kamar banji su ba, na kalli Hajiya nace, bari in shiga inyi salla. Hajiya tace "Azima kin gaida 'yar uwar taking? " Azima ta ce mun gaisa. Na yi murmushi lallai yarinyar nan makira ce ko a ina muka gaisa.
Na shiga daki ina tambayar kai na me yasa zai ce ta zo nan? Tsabar ya raina min wayo, dan tsabar sone ko me? Bayan da yana gidan ta hatta Hajiya sai daya daga mata kafa, amma bari muga ikon Allah.