← Book details Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 31

Sashe 11

Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma ke jiya na san baki samu komai ba kila ma sai zunubi amma na yafe miki. Jikina ya yi sanyi nace to ai kaine baka gaya min ba. Ya harare ni, in fada miki me bayan kina ta hauka, kuma zaki ce duk baki san komai ba kinyi makaranta fa. Na turo baki, nace dan nayi makaranta ta gwamnati ce ina cikin lokon mu ni ba kallon TV ba ba jin radio ba, garama ina dan karance karance. NI ban san me ake ciki ba. Yace to yanzu jeki kiyi salla dai." Na shige bandaki, na kalli ko ina gwanin shi shi'awa, na kalli kaina a madubi nace ni Baby a Hotel yau. Nayi wanka na yi alwalla na fito. Na saka siket na daga rigata nace to ni yanzu sai ka biyani rigata. Ya daga rigar tayi kaca kaca, ya yi murmushin mugunta yace, ni ma dai jiya na yi wa wata yarinya fyade, kuma fa naji dadin hakan. Kinsan namiji yana son style kala kala. " nace Ni baruwa na yanzu kasan yadda zakayi da ni. Ya cire janfar da ke jikinsa sai singiletin shi yace "Sa wannan ni sai inje da malun-malun tana mota."

Na dauka na saka a jikina. Ya kalle ni ya yi murmushi ya kuma Hajiya ba a yi mata karya. Na tashi na ja baya da sauri gaskiya kai zaka fada mata. Cikin shagabar da bansan na hi ba na yi maganar.
Yace "In ba haka ba fa? " Na soma kuka nace sai dai ka kaini gida. Ya tashi ya fara daura agogonshi yana fadin can gidan sai kice musu munje Hotel kin ki bani hakkina na yi miki fyade mun kwana gashi Hajiya bata sani ba." Shikenan said Umma ta raka ki gida. Ya karasa maganar cikin dariyar da yake ta kunshewa. Nace kenan dariya ma ka ke yi ko? Yace "Kowa tashi ta fisshe shi." Ya fada yana hada kan wayoyin shi. Na zauna bakin gadon nace In kuwa haka ne gara in zauna a nan. Yace "Shabiyu tana cika zasu kore ki ne, su gyara dakin su. Ya zura takalmi ya dauki yagaggiyar rigata ya ce shike nan ni na tafi....
🖊️🖊️🖊️
Da gudu na tashi na bi bayansa har ya shiga mota ya tada, ban damu da rigarsa da ke jiki na ba. Koda dai mutum biyu ne a Reception din, na nufi motar yana kallo na sai ya yi hanyar waje.

Na kwasa da gudu na nufi gunsa, na bude gaban motar na shiga, da alamu dariyarsa ya sha domin har lokacin ita yake kunshewa. Nace da gaske da tafiya zaka yi?
Yace "To me zai hanani tafiya tunda kince ke bazaki tafiba. "
Nace tsoro nake ji Hajiya zata yi fada, da wane ido zan kalli Hajiya, sannan kuma dubi yadda ka maidani kayan ka ne a jikina fa..
Ya ce "Ki dai shirya bayaninki tun a nan kafin aje ki kasa magana. Ki fara shirya fada mata inda ki ka kwana da kuma dalilinki ". Nace mu fara biyawa ka saya min ko doguwar riga ce in baka taka ka saka mu fara zuwa gida a mutuce. Ya ce ba inda zani.

"Ki barni inji da me zan fadawa Hajiya kema ki tanadi abinda zaki kare kanki." Nace kai ne zaka fada mata tunda kai ka ja komai, ni ban taba zuwa Hotel ba. Ya sake fafin kowa tashi ta fisshe shi. " Na kifa kaina a cinya takaici ya ishe ni. Ga tsoro ga kunyar Hajiya da zanji, ko yaya zata kalli abin? Nasan bazata ji haushin danta ba, abin akai na zai kare.

Muna shiga kan ya gama fakin na kama kiciniyar bude kofa. Yace ki tsaya in fada miki wata magana, na kalle shi ya daure fuska, in har ki ka yarda na rigaki zuwa gaban Hajiya ke ce zakiyi yi mata bayani." Nace Allah ni ba zaka dora min laifi ba. Na soma kawo ruwan hawaye. Yace Au kuka zaki yi to shikenan ki yi. Daga nan zata fara gane cewa baki da gaskiya. "

Ya bude mota ya fita. Nima na fita na bi bayan shi da sauri a falon daf dana Hajiya muka hadu. Ya kalle ni, "Gabana faduwa yake. " Ya fada yana kallona. Na tsoro ya kara kamani, in shi yana jin tsoro ni kuma yaya kenan? Ya sake fadin "In har na riga ki shiga ke ce wadda zaki yi wa Hajiya bayani.
Da sauri na tura kofa na shige kafin ya rufe baki.

Kamar yadda na zata Hajiya tana zaune a inda take salla da carbi a hannunta na shiga da sauri, na zauna a gefen ta. Ta waiwayo da sauri kamar ta firgita da ganina, ta kuma kafe ni da ido. Nace sannu Hajiya. Ta dauke fuskarta ba tare da ta amsa min ba.

Jikina ya yi sanyi ko ba a fada min ba nasani dole ne in dauki Wannan Zunubin lokacin Ya yi sallama kamar wani salihi, ga mamakina sai Hajiya ta amsa sallamar harma ta kara da fadin an shigo. Ya iso ya zauna daf da ita ya yi kasa da kai yana gaishe ta. Ta amsa cikin fara 'a. Ya kalle ni ya yi wani murmushin mugunta, sannan ya dora min yagaggiyar rigata akan jikina ga rigar ki je ki cire min tawa. Na yi zaton Hajiya zata tambaya dan in samu in wanke kaina amma sai naga ta kalli rigar sannan ta sake kallon ta jikina. Sai kuma tace masa, in ka shiga ina bukatar takardun filin nan da aka siya a Fandanka? Yace suna jakata a kawo su ne? Tace ka fito da su domin a kwai wata magana akan gurin jiya lauya ya kira ni nace ya same ni a gida in kuma zaka fita kasuwa yau sai ku karasa can. Shamaki Yace zamu fita kasuwa sai dai kuma yau ina da meeting kashi uku ki hadu da lauya kawai. Akwai wadannan 'yan China da suke son stor dinmu na Sharada a nawa ganin gara mu saida musu tunda kinga bama komai a gurin, kuma zai yi daraja saboda su suke bukata. Ni dai na mike na nufi dakina a sabule.

Na shiga ban daki na dan gasa jikina da ruwan dumi sannan na canza kayan jikina na hau gado na kwanta, ina tunanin wannan zama namu. Ina ta fadi tashin ganin cewa na samu zama na har abada amma wani lokacin sai inji jikina ya yi sanyi. Kamar dai yanzu da muka yi laifi amma sai ta wanke danta fes.

Na fita lokacin karin kummalon su ya yi, Na samu Juma tana jere abinci, na shiga cikin dari dari, Hajiya tana zaune a kan kujerarta Shamaki a gefe ga takadu kusa da shi yana sanye da Jallabiyya. Na yi wa Hajiya sannu. Ta amsa ba tare da ta kalleni ba. Na fara da goge teburin ta na jikin kujerar ta wanda da shi take cin abinci. Nace me za a saka? Tace kunu zata sha na gyada. Na san abubuwan da zan hada mata in kunu zata sha. Na hada mata komai. Tace wa Shamaki "Ya kamata gobe a tashi da azumi a gidan nan tunda bikini salla ya kare sai a yi sitta shawwal ko? "

Shamaki ya ce wannan tsuntsuwar data sani a gaba tin washe garin salla na fara, in nayi yau da gobe na gama". Na kale shi ya zuba min ido. Na yi kasa da murya nace na ci maka bashi ne da zaka zura min ido?
Wai da Hajiya ta ji mu sai ya daga murya. Me ki ka ce? Na kalli Hajiya ta maido hankalinta garemu kuwa. Nace me zakaci in zuba maka? Yace ina azumi fa kin sani. "
Nace Baka yi sahur yau ba, gaskiya bazaka yi dore ba, ka bari sai gobe tunda ka ga ai ba wai farilla bane. Yace "Baki tashe ni ba ne ai." Na harare shi, haka ma zaka ce? Ya yi murmushin mugunta, yace ashe fa gurin maulidi muka kwana. Hajiya ta kalle ni, ni kuma na kalle shi ya kauda kai. Azuciya ta nace karyar da ya yi kenan to wane maulidi kuma a salla.

Ya katse ni, "Dama ke ki ka takura inyi in gama amma yanzu zaki zo da zamiya. Na soma zubo masa kunu, sai na tuna da wayon da nake yi wa Jafar din mu in ya ki cin abinci a ramadan ya ce wai shi yana azumi. Sai in zuba masa kunu in ce ya sha baya karya azumi..
Na mika wa Shamaki kunu cikin tsokana na ce kasha wannan baya karya azumi. Ya karba ya kurba, nace Allah ya yafe maka. Ya ce "Ameen amma alhaki a kanki.
Ke ki ka sa na karya azumi. Ya dauki kosai daya da na zuba na tura masa. Ya gutsira yace na sani fa bakya son insha wahala ne ko? "Nace ta yaya zan so ka sha wahala, amma kai kana son insha ai tunda kai da kanka ne ka shayar... Ya nuna min Hajiya da ido, ya gane maganar jiya zanyi. Na rasa wani lokacin in muna tare da Shamaki gaba daya sai in manta da akwai wani a gurin.

Juma ta sake shigowa tana fadawa Hajiya cewa man shanu ya kare tace za a kawo shi yau kuwa domin miyar danyar kubewa nake son ci. Tace to sai an kawo naman rago shima ya kare.

Hajiya tace a yi ta kaza.
Na tuna da irin yadda Tsohuwa ta bani labarin yadda Hajiya Zeena ta ke yi wa Hajiya Gwamma abinci da kanta, sai naji ina shi'awar in aikata hakan. Na ce Hajiya ina son in roki wata alfarma don Allah. Ba Hajiya ba hatta Shamaki ya dakata dan ya ji me zance. Ita kuma Hajiya da alamu yadda na yi maganar cike da kwarin gwiwa shine ya sa ta dakata, ko da dai na lura Hajiya tana son jin magana ko tsegumi amma bata nuna cewa ta damu da hakan.
Chapter 11 · 0% Book details