← Book details Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 31

Sashe 26

Hamshakiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shiga falon Hajiya sai ya ji gabanshi ya yanke ya fadi, falon ya yi masa duhu domin ga mazaunin Hajiya amma bata nan. Juma ta fito tana yi masa sannu da zuwa, ya amsa sannan yace "Baba Juma gidan wayam. " Juma tace har ka tuna min da Uwar dakina takance Baba Juma. Yace ashe sun tafi India. " Juma tace ah dama Hindiyar ne kasar waje? Shamaki yace "E canne kasar waje mana.,, " Tace Allah ya dawo da su lafiya. Yace "Ameen. " Ya nufi dakinsa kewar Baby ya ke yi a kalla ko muryarta ya ji, amma wannan bazata da Hajiya ke son yi masa tana azabtar da shi, ba Hajiya ba Baby, gaskiya dai ba Mutum. Ya furta yana cire kaya. Ya fito falonsa ya zauna yana ta kiran yayunsa yana fadin Hajiya zata yi mishi ba zata, suma suna tsokanar cewa ya gudu domin kar ya rabu da Baby.

Juma ta shigo ta same shi. Uban daki me za a dafa maka ne? Yace "Baku dafa komai ba? "Tace mun dafa taliya kai kuma ba layinka bace sosai. Yace inda a kwai kayan ciki ko wani dai farfesun a dumamamin shi. Tace akwai na kaza. Yace to shima zai iya yi. Har ta juya sai yace mata, wai Ina Azima ne? Tace tana ciki bari a kira ta.

Har ya manta da cewa za a kirata, sai gata ta shigo, ya bita da kallo, duk ta kumbura, Ta yi masa samnu da zuwa ta zauna. Yace kin koma Asibitin kuwa? " Tace Ni banje ko Ina ba, ta turo baki, bayan duk kun tafi ba mai kula da ni Hajiya ma ta dauki wannan matar sun barmi. Shamaki ya bata rai, in basu barki ba ina zasu da ke?" Ko kuwa wani zai tsaya gadinki ne, sannan kuma baki motsa jiki sam kamar yadda likita ya fada. Ta bata rai kamar zata fa she da kuka, tana fadin shi likitan da zaice haka dan ba a jikin shi cikin yake ba, Ina zan iya wani motsa jiki! Shamaki yace to naji yanzu dai tashi kije bana son ki kai ga hasalani karki bata min farin cikina." Ta taba baki sannan ta tashi ta wuce.

Haka dai Shamaki yaji gidan babu dadi sam. Fatanshi yasamu visa da wuri ya bisu.

A dai dai wannan lokacin Hajiya ta kalli Baby bayan likitan ya gama daura mata ruwa tare da zuba magungunan a ciki, yace zata samu bacci kar a tashe ta. Baby tace to. Ta zauna kan kujera wadda ke daf da gadon ta shimfida tafin hannunta cikin na Hajiya, tace Hajiyata Allah ya baki lafiya. Ta bude ido ta kalle ni, ta cije lebenta da alamu wani guri yana mata ciwo. Nace Hajiya me yake miki ciwo? Ta bude ido, ta kalle ni, ko ina ma ciwo yake min. Nace sannu insha Allah zaki samu sauki. Can tace Amanar me na baki? Nace Amanar duk wani wanda ke karkashin ki insha Allah amanata ne Hajiya. Ta bude ido, sunyi jajir. Tace ina jin Bacci ne amma na kasa hamma tun jiya, kila har hammata ta kare." Nace zaki yi insha Allah. Ta lumshe ido, ki ci abinci fa Rabi'a ki sa a kawo miki abinci kinji?"

Nace to. Amma ina wani cin abinci ni ko yunwar ma banaji. Ta bude ido ta rufe tana dan cije lebe sannan ta na motsi da baki kamar salati ta ke yi, can kuma bacci ya kwashe ta. Likita ya shigo ya ce kar inyi wani motsi mai karfi domin ta samu bacci mai kyau. Na fada masa tace ta kasa yin hamma, yace kar ki damu komai zai yi dai dai.
Na idar da salla ina zaune ina addu'a sai naji motsinta.
Da saurin na tashi na tafi gurinta. Ta bude ido tace zanyi salla. Nace to zata iya zuwa bandaki? Tace bari ta gwada. Mukaje na rike ta domin jikin ba karfi. Gani nake kamar ma su ne suka dora mata ciwon domin lafiya muka zo. Na zaunar da ita tayi fitsari na yi mata tsarki na yi mata alwalla na maida ta kan gado ta kasa zama, tace duk ji take yi ta gaji. Dan haka a kwance ta yi sallar. Haka dai har bacci ya kuma daukarta.

Shamaki ya kasa bacci ya mike ya shiga falon Hajiya yaje yana shafa kujerar zamanta. Har yanzu kamshin turarenta kujerar ke yi, ya zauna kasa ya dora kansa a saman kujerar yana fadin ina kaunara ki Hajiya Allah ya dawo min da ke lafiya. Can kuma ya tashi har ya nufi dakinsa sai kuma ya fasa ya nufi nata dakin, da duhu fitilar dakin a kashe. Bai kunna ba ya nufi gadon ya laluba ya kwanta.

Cikin bacci yake mafarkin ana biki a gidan gida ya yi cikar kwari ba masaka tsinke ga Hajiya ta caba ado cikin kaya na alfarma amma kuma shi da ''yan uwansa duk suna cikin damuwa.

Ya farka ya ji ana kiran sallar farko ya tashi ya lalubi makunna ya kunna haske ya gauraye dakin ya shiga bandaki ya dauro alwalla bai san me ya sa zuciyar shi duk yaji babu dadi ba. Ya tafi kan dardumar Hajiya da ta ke yin sallar dare ya tada sallar raka a ta 'i nil fijir. Ya, na zaune yana tasbihi ya jiyo za a tada salla, ya mike ya nufi fita zuwa masallaci. Kamar ance ya kalli kan madubin Hajiya. Wayoyinta guda ukun duk suna kan madubi. Gabanshi ya fadi, yace wai Hajiya manta wayoyinta ta yi ko ya abin yake? Ya sa hannu ya dauka ya kunna duk suka kunnu, amma abin alajabi duk ba komai an goge komai, sannan kuma babu layikan a ciki. Kamar dai ba a taba amfani da su ba.
Jikin sa ya hau rawa ya aje su ya nufi masallaci jin ana sujjada. Suka idar ya fito da sauri sam baiji maganar da liman ke masa ba. Ya nufi dakin Hajiya ya kuma daukan wayoyin, me kuma haka ke nufi. Ya nufi dakin shi ya dauki waya ya kuma kiran duk layikan su Hajiya a kashe. Sannan ya nufi dakin Baby ko ita ma ta bar wayarta. Ya duba bai ga komai ba, ya fito ya nufi falo yana kiran wayar Maman Umar. Ta daga a firgice domin ta rasa abinda ya sa bata da kwanciyar hankali a ciki kwanakin nan. Ko sallama baiyi ya yace Maman Umar wayoyin Hajiya na gani duka ukun an share komai na ciki kuma babu layukan. Gabanta ya fadi, tace to me hakan ke nufi? Yace bani da wata basirar da zan gane haka. Tace Kaje ka duba ko zakaga sim din, in zanje kai yara makarantar sai in biyo.

Ya je yana duba kan gado. Yana daga bargo sai ga wasu takardu guda biyar. Ya kai hannu jikin shi yana bari ya dauki guda daya. Ya ga an rubuta Aisha. Ya kuma dakko wata ya duba yaga Maryam. Kanshi ya kulle, waye kuma masu sunan nan? Ya manta da batun sunan 'yan 'uwansa kenan. Sai da ya kuma dakko wadda aka rubuta Aliyuna. Sannan ya fuskanta.

Ya zauna a bakin gadon ya warware takardar cikin sauri da rawar jiki ya soma karantawa kamar haka....

Dana Aliyu nasan lokacin da zaka samu wannan takardar kasa ta jima da rufe idona, ko kuma numfashina ya jima da tsayawa. Ka yafe ni Aliyu na zabi in nesanta kaina daga gareku, ina auna yadda zakuji in kuka ga na mutu a gabanku, na tabbatar baza ku manta da wannan ranar ba. Ina son ka rike Baby da amana duk wata damuwarka ka sameta kubtattauna, na yaba da halayenta, itace matar da na sa ka saki mataye uku saboda sa ran zuwanta. Ina fata zakaci gaba da yin dukkan wani taimako domin dauka a taskar Allah. Na yafe maka dukkan wani laifi wanda ka yi min a cikin sani ko akasin haka. Ina son ka yafe min kuma ka ci gaba da yi mini addu'a domin ita na fi bukata. In kunga wayoyin na to ku saka su a gadon ku na goge komai na ciki na kuma zubar da layukan, duk wata mamba mai amfani na kwashe muku su a cikin wani karamin littafi yana durowa. Sauran bayani zaka samu a gurin matar ka. Sai mun hadu a darrussalam!!! Yasa hannu a wani jirwaye wanda ya tabbatar jirwayen hawayen Hajiya ne.

Ya mike da sauri yana fadin Innalillahi wa inna ilaihirraji un.!! Maganar nan ba gaskiya bane! ! Juma!!! Ya shiga kwala mata kira da karfi.
Da gudu Juma ta fito daga kicin ya kama hannuwan ta da karfi ya jijjiga ya ce, "Wai Hajiyata ce tabar wasiyyar mutuwa! Ina Wayata. Ya koma dakin Hajiya da gudu ya dakko wayar shi numfashin sa na fita da karfi. Ya danna lambar wayar Maman Umar. Tana dagawa sai kawai ya fa she da kuka. A razane ta ce Menene! Yace Hajiya ta! ta! sai ya saki wayar kawai ya zube gwiwoyinsa a kasa ba zai iya furta cewa Hajiya ta mutu ba. Juma wadda tafita da gudu tana kiran masu aikin gidan maza tana cewa su zo ba lafiya sun samu Shamaki yana kuka sosai ya durkushe a kasa.

Kafin minti talatin Gidan Hajiya ya cika da ahalinta, ba wanda ke iya rarrshin wani a cikin 'ya'yanta, kowa yana rike da takardar wasiyyar da ta bar musu. Maman Umar itace mai karfin halin bin hanyoyin da za su sami tabbacin halin da ake ciki.
Chapter 26 · 0% Book details