← Book details Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 14

Sashe 6

Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A tsaye suka tarar da Inna ta kasa zaune ta kasa tsaye,k'irjinta sai wani irin bugu yake.
"Har d'inki akai a goshin?"
Tana jin muryar Inna ta k'ara k'arfin kukanta. "Inna bana ganin komai sai duhu,shi kenan na daina ganinki Innata sai dai naji muryarki,na daina ganin komai,ji nake kamar zan mutu Inna,dan Allah kicewa Baba ya dawon da idona bazan k'ara masa musu ba,bazan k'ara rashin ji ba,zanje duk inda zan samo HANKALI DA NUTSUWAr da kuke so kuga nayi."
Innalillahi Inna ke ta ambata a zuciyarta kafin ta kalli Baba tace. "Yau dai hankalinka ya kwanta ka aikata abinda ka dade kana furtawa (furuci)ka nakasta Rahina,sai ka zuba ruwa dan Allah a k'asa kasha tsabar farin ciki."
Tana kawowa nan,ta share hawayen da ya biyo kuncinta,ta kamo hannun Rahin d'in suka nufi d'aki tana rarrashinta da cewar zaa gyara mata idanuwanta zata dawo tana gani kamar daa.
Baba baisan da wani baki zai wanke kansa gurin Inna da Malam ba,komai zaice komai zai dad'e yana gaya musu baza su yarda ba da niyya yai mata ba duba da furucinsa a kullum a kanta,anman zai nema mata magani matuk'ar zata warke dan goge laifinsa daga idanuwansu harma da na Rahin d'in.

Fad'a da sababi babu wanda bai sha a gurin Malam ba,ya tabbata da zai iya dukanshi babu abinda zai hana ya dakeshidon ransa yayi mugun b'aci aunun.
"Muddun kana son ganin farin ciki cikin rayuwarka yadda ka zamo silar nakasta Uwata ka zamo silar warkewarta,in ba haka ba ni kaina bazan yafe maka ba." Kalamin mahaifinshi ya k'ara masa k'aimi gurin ganin ya nemawa Rahin lafiya,asibitoci biyu suka je suka bashi shawarar ya kaita asibitin Makka da ke garin kano.
Da Inna Hajara ya so su tafi kanon tunda Innar Rahin d'in babu dama anman tace ba inda zata je dan haka suka tafi daga shi sai Rahin d'in.

Kasantuwar mota da ta dinga lalace musu ana sallar isha suka shiga garin kano,dan haka ya bari su kwana a tasha washe gari sai sui tambaya su isa asibitin Makan,cikin dare 'yan fashi suka yiwa tashar haure a lokacin Baba yana can ya zaga cikinsa ya rud'e,ya bar Rarhin tana barci,aikwa aka shiga gudun ceton rai kowa ta kansa yake Baba kuwa hankalinsa yana kan Rahin har zuwa lafawar komai ya koma inda take kwance wayam ba ta nan,hankalinsa yayi mugun tashi yadda alk'alami bazai iya rubutawa ba.Kwanansa biyu cikin tashar yana fita bilayin neman Rahin bai ganta ba,har police d'in da suka zo bayan barin 'yan fashin gurin ya sanarwa amman har yau babu wani information haka ya hak'ura ya koma cikin taraddadi da tashin hankali anman da niyar zai dawo yaci gaba da nemanta ko Allah zaisa a dace,fatanshi d'aya Allah yasa ba 'yan fashin ne suka saceta ba.Bai iya gayawa Malam da Inna gaskiyar Rahin d'in ta b'ata ba,musamman da yaga Innar ba dad'i take ji ba sai kawai yace da su anyi aikin,basa bukatar masu jiyya ne shiyasa ya taho anman kwana biyu kawai zai ya koma,a daren washe garin da ya dawo kuma 'yan bindiga suka dira a k'auyan,sun kashe na kashewa sun tafi da na tafiya wanda suka tsira Allah ya tseratar da su,a cikin wanda aka kashe harda Baba Malam da matarsa da Idi suka tafi da Bashir (Da yake Idi da Bashir d'in acan gidan Baba Malam d'in suke kwana)su kuma Baba da Inna,Inna Hajara,Sale,Kabiru,Mubarak suka b'uya a d'akin da Baba ke ajiyar dukiyarsa,kunsan mutumin k'auye ba kowa ya yadda da accaunt ba,k'ofa ya sakawa d'akin me kyau wacce duk dukan da za'a mata kuma datse kanta take ta nan Allah ya kub'utar da su wanda a cikin gumurzun Inna ta haihu ta haifi jaririyarta MACE,rungume 'yarta tayi ta fashe da kuka, ba ta sani ba ashe kukan rashin Malam take,ta rasa mahaifi,ta rasa mai sanyawa jaririyarta suna,ta kuma rasa mai tayata son jaririyarta a wannan karan.
Zata iya rantsuwa mutuwar Mallam tafi gigitata akan yadda ta gigita Baba,mutuwar ta kad'ata yadda ba kwa zato,addu'a zata yi ta bin bayansu da ita da itace take jin zata iya cike wani guri na soyayya da d'awainiyar da sukai da ita dan ba tace zata biyasu ba Allah ne kawai zai iya biyansu. An yiwa wa'yanda suka rasu sallah an binbinnesu,a ranar Baba ya harhad'a komai nasa suka bar garin dan da yuyuwar 'yan bindigan suka k'ara waiwayar garin nasu,wasu da dama ma sun bar garin,wanda kwa zaman garin ya zame musu dole haka suka zauna da kuma masu halin rik'au irin na Baba Malam.

Halima da d'an Audunta kamar wa'yanda aka sanarwa da abinda ya faru a k'auyansu gaba d'aya hankalinsu yayo gida,dama kuma Haliman na ta shirin zuwa d'aukar Rahin,sai kwa Audun yace tare kawai zasu huce shima hankalinsa ya yo gida,dan yana ta kiran wayar Magaji baya samu,kwana biyu da barin Baba garin su kuma suka dura anan ne suka tarar da bak'in labari dan shi Audu gaba d'aya gidansu babu wanda ya tsira sun kashe na kashewa sun tafi da na tafiya,Halima kuwa tashin hankalinta ba ta san ina su Innarta suka nufa ba,ga cikinsu babu wani mai waya,dama Kabiru ne me wayar kuma sun kasheshi,taji mutuwarsu shi da su Baba Malam ta kuma bi bayansu da addu'a ga kuma mutuwar ajalin mijinta,ta tayashi kukan fili da na zuciya sun taho da daddad'an labari a bakunansu (Halima na dauke da cikin watanni hudu)ashe babu wanda zasu fesawa cikin ahalin nasu,gara ita in da rabo zata ga nata iyayan shi kuwa sun tafi inda babu dawowa har abada,kwana sukayi cikin alhini da k'unar zuciya washe gari suka koma inda suka fito rayuka babu dad'i,kuzari ya tafi sai zuciya ke azabta...
[9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBEE'ARTH

HALITTAR
ZUCIYA.....

Watpad@Rashuna
Mama Jiddah
Heenah
Silar Soyayya
Masoya
Rabee'ah
Babbar Cuta
Muguwar Suruka
K'addarar Rayuwarmu
Cikin Duniyarmu500
Katanga500
Cin Amana500
Wadjda500
Halittar Zuciya500

Hak'k'in Mallaka.Rabee'ah Shu'ayb Nababa (Rashuna,Bebee'arth)Ban yadda a juya mini littafaina ba ko ta wata siga,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani.

(Oum Samha)
(DATA SERVICES)

(MTN)
>500 =150
>1Gb =250
>2Gb =580
>3Gb =900
>4Gb =1200
>5Gb =1500
>10Gb=3000

( AIRTEL)
>500mb =150
>1Gb. =300
>2Gb. =600
>3Gb. =900
>4Gb. =1,200
>5Gb. =1,500
>10Gb. =2,850

(GLO)
>1Gb. =350
>2Gb. =700
>3Gb. =1,050
>4Gb. =1,400
>5Gb. =1,750
>10Gb. =3,000

( 9MOBILE)
>1Gb. =450
>2Gb. =1,000
>3Gb. =1,400
>4Gb. =1,700
>5Gb. =2,150
>10Gb. =3,500
>11Gb. =3,800

✓All data plan valid for 30days.

Always available and reliable.

Account Details:
8167316776
Ummi Saidu
08167316776
.Thanks as u patronize🤝
(7)

Baba bai bari sunyi kwanan tasha ba,duk da kasancewar sai dare suka sauka cikin garin kano,gudin kar 'yan fashin su kuma yi musu haure,gashi tare da dukiyarshi yake tafe,duk da ba wanda zaiyi zatan kud'i ne don sun fi kama da tsummokara. Kwatancan gidan hamsin wani bawan Allah yayi musu,musamman da yake babu nisa gidan daga nan tashar sai suka nufi can d'in kai tsaye,suna zuwa ya biya kud'in kwanan da zasu yi kowa hamsin-hamsin.
Innar Rahin tafi kowa jigata musamman da yake gata da d'anyen jego,daga ita har jaririyar wanka suke buk'ata shine zasu samu yin bacci cikin nutsuwa,don jaririyar ma sai 'yan koke koke take mata,anan cikin gidan ta samu ta sayi ruwan zafi ta hayi bawo ta fara yiwa jaririyarta wanka ta shiryata kana taje ta yo nata wankan,sai da ta fara wanke band'akin tas kafin ta iya shigarsa don ya mugun k'azancewa babu kyahun gani,ga mamakinta shayi ta tarar me mugun kauri da gurasa a Baba ya ajiye mata,ba tace komai ba anman cikin ranta cike da mamaki har tasha shayin ta ci gurasar ta kwanta.
Washe gari ma ruwan zafin ta siya sukai wanka ita da jaririyarta,wainar shinkafa Baba ya siya musu a nan cikin gidan dan yadda ta fuskanta babu abinda ba'a sayarwa a gidan,anman ita har da shayi mai kauri ya siya mata yayin da lamarin nasa ke k'ara d'aure mata kai anman dai ta ja bakinta tayi shiru,ko sallama bai musu ba yasa kai ya fice dan tsoron kar Inna ta sako masa zancen Rahin.
Tashar ya fara zuwa don jin ko an samu wani information na b'atan Rahinan,anman bai samu labarin komi ba don haka ya fara bulum biton neman gida tare da wani Malam Habu da Allah ya had'a su a cikin tashar jininsu kuma ya had'u,ba su samu gidan ba duk inda suka je sai dai haya shi kuma yafi son ya siya gidan saboda,idan kana da muhalli komai da zai biyo baya mai sauk'i ne,ganin magariba tayi dole suka hak'ura sai zuwa gobe sa cigaba da bulumbiton neman gidan,haka ya nufo gida k'irjinsa na dukan tara tara da tunanin amsar da zai bawa Inna akan Rahin,ya ya zata d'auki lamarin,zata yadda da duk abinda zai gaya mata ko kuma zata zargeshi da saka hannunsa a b'atan Rahinan?Wannan tunanin kad'ai na dugunzuma zuciyarsa yana kuma sanyashin nadamar tsanar da ya nunawa Rahinan a sarari.

RAHINAH
Chapter 6 · 0% Book details