← Book details Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 14

Sashe 1

Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH

2023

Wattpad@Rashuna
Mama Jiddah
Heenah
Silar soyayya
Masoya
Rabee'ah
Babbar Cuta
Muguwar surika
K'addarar Rayuwarmu
Cikin Duniyarmu500
Katanga500
Cin Amana500
Wadjda500
Halittar ZUciya500
Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KYAUTA.

HALITTAR
ZUCIYA

(1)

Shimfid'a

Jajare garin jajaye in kaga bak'i to bak'o ne ya ka zo,wannan inkiya ce ta garin Jajere.Jajere gari ne na fulanin damaturu,Malam Madu yana d'aya daga cikin mutanen garin,haifaffan garinne shi tun iyaye da kakanni,mahaifansa ne suka wanke Mariya suka bashi,Mariya kamar 'ya take a gurinsu saboda su sukayi rik'onta tun tana yarinya,sun tsinceta ne a wani kango da ake gini suka rik'eta ba tare da k'yamata ba,suka kuma d'auketa suka bawa d'ansu duk saboda soyayya,anman Madu sam ba ya k'aunar Mariya,ya karb'i auranta ne saboda biyayya ga iyayansa,suna zaune,lafiya ba mai jin kansu duk da Mariya tana matuk'ar hak'uri da wasu halayen na Madu dan baza ta iya fitowa ta fad'a ba ne ana haka ta samu ciki inda ta haifi 'ya mace,zo kuga ruwan tijara gurin Madu shi ba ya son mace,mace ai k'arin wahala ce babu abinda za ta tsinana maka yak'i yin komai na haihuwa sai iyayansa ne suka yi mata,sunama babansa ne ya rad'a mata Halima,(Sunan mahaifiyar Madun kenan)a haka rayuwa ta gangara Mariya na matuk'ar hak'uri da halayen Madu duk saboda darajar iyayansa wanda su take kallo a matsayin nata iyayan da Allah ya bata sama ta ka,gashi yanzu k'asa ta rufewa Inna Halima idanu wacce ta kasance tana tausayinta da taimaka mata da wasu abubuwan,a haka rayuwa take ta juyawa Madu ya sake auran Hajara, haihuwar fari ta haifo masa namiji zo kuga murna gurin Madu sai a wannan haihuwar Mariya ta san mijin nata ba k'aramin arzik'i ne da shi ba dan sosai ya saki bakin aljihu yana wa Hajara da d'anta hidima har zuwa ranar suna inda yaro yaci sunan mahaifin Madu Idris.

Tun daga haihuwar Halima,Mariya ba ta sake haihuwa ba har sai da Hajara tayi haihuwa uku a jere duk maza wanda suke ganin so da k'auna da gata gurin Madu,Halima kuwa ko kallo ba ta isheshi ba a cewarsa bazai wahalta mata ba,dan su mata sai dai ka wahalta musu a banza ba tare da kaci moriyarsu ba,inda Allah ya taimaki Halima sai ya yota mai sanyin hali,ko kad'an ba ta dosar mahaifin nasu saboda ta san halinsa,abu kad'an za tayi ya mangareta har yanzu kuwa da take da shekaru takwas a duniya.
Hajara da Mariya a lokaci guda suka haihu inda Mariya macen dai ta kuma haifa,inda Hajara ta dinga yadar mata da maganganu shi kwa Madu ba ta isheshi kallo ba daga ita har jinjirar da ta haifa,inda Allah ya taimaketa ta tanadi komai na haihuwarta saboda tana sana'arta ta kayan miya bushashe da kuma wainar gero da k'uli da safe,tunda mai taimakon nata babu ita yanzu a doron k'asa,kamar haihuwar Halima wannan ma mahaifin Madu shi ya nad'awa jaririya suna RAHEENA.

Akwai bam-bamcin halaye k'ara k'ara tsakanin Halima da Raheena,Halima mai shiru shiru ce da sanyin hali,duk inda aka nuna ba'a sonta ba ta dosar gurin,yayin da Raheena ta kasance mai kwaraf niya ga tsokanar tsiya a cikinta kamar me,inda kuma Allah ya d'ora mata k'aunar mahaifinsu Madu duk da kasancewar shi yafi tsanarta ma akan Halima,dan dukan da take sha gurinsa bai daki Halima haka ba ga kyararta da yake anman ba shi zai hana ta koma gurinsa ba,zasu had'u ita da Mubarak tsarar haihuwarta d'an wajan Hajara suyi k'iriniya anman idan Madu ya tashi ko dunguri ba zaiwa Mubarak ba anman in ya kama Raheena da duka kamar Allah ya aikoshi.
Halayen Raheena suna mugun ciwa Mariya tuwo a k'warya anman babu yadda za tayi sai addu'a ta san k'uruciya ce ko wani yaro da kalar k'uruciyarsa nan gaba idan ta san ciwon kanta ba za tayi ba,gashi yanzu ta aurar da Halima tana cikin shekarunta na sha hud'u kenan Raheena kuma shida,komai na auran Halima Baffa Idris mahaifin Malam Madu shi yayi,har yau yana nisar da d'an nasa anma ya kasa ganewa shiyasa ya d'au ido ya zuba masa ya tabbata akwai ranar da zai gane kad'an daga cikin ni'imar da Allah ya yi maka idan ya azurtaka da samun 'ya mace.

Wannan kenan

……

Da gudu ta yanko layin gidansu k'afafuwanta fututu hakama kayan jikinta,kafin fitarta sai da Innarta tayi mata wanka tas anman yanzu wani ya ganta zaiyi zaton tafi sati rabonta da wanka,tana gab da shiga soron gidansu suka ci karo da Babansu wanda ya doso kai zai fita,k'afafuwanta ya tad'e ta zube a gurin had'e da sakin k'arar dake nuni da ba k'aramin buguwa tayi ba,kuma taji zafin fad'uwar ainun,ko sauraranta baiyi ba yasa kai ya fice daga soron gidan,yayin da kuma Innarta ta yo soron gidan dan jin ihunta da ya karad'e cikin gidan gaba d'aya,da sassarfa ta isa gareta ta d'agota tana kallon yadda bakinta ya fashe,ba ta kai ga tambayarta abinda ya faru ba sai ga Ramatu ta shigo zauran rik'e da hannun k'aninta jikinsa kwata ce gaba d'aya.
‘’Lafiya?‘’
Inna ta tambayi Ramatu,bayan ta mik'ar da Rahina tsaye har lokacin tana kuka sai dai kuma ta rage sautin kukan nata.
‘’ Rahin ce ta jefashi cikin kwatar gidan Ade,shine Innarmu tace na kawoshi ki wanke masa,ita baza ta iya saka hannunta cikin kwatar ba.‘’
Ba tace komai ba bayan ta gama saurarar Ramatu sai hanun k'anin nata da ta kama bayan ta saki na Rahin tayi ciki da shi,k'ilama sakayyar yaron ce ta saka Rahin d'in fad'uwa har ta fasa bakinta,ba manaki kuma kwatar da ta jefashin ce ta sakata nufo gida da gudu har ta fad'in ta fasa baki .
Kowa yasan kwatar gidan Ade da tsinannan d'oyi,k'azamai ne na k'in k'arawa,wani zubin a rariya suke kashi su koroshi waje,shiyasa kowa yake k'ank'yamin kwatar,anman haka Inna ta wankewa yaron kwatar tas,tayi masa wanka had'e da wanke kayan tas,to ya za tayi?D'an kuka ai shi ke janyowa uwarsa jifa.

Bayan ta gama wanke kayan ne ta nufi d'aki zata d'an zauna ta huta,dan Rahin ta faki idonta ta kuma ficewa,addu'ar shiriya kawai take nemawa Rahin d'in cikin ranta,har ta tsuguna zata zauna aka rafka sallama daga soron gidan,d'an dakatawa tayi da zaman gabanta na fad'uwa kafin ta amsa sallamar.
"Ina magana da Innar Rahin"
Cewar Muhammadai mai kanti dake tsaye a soran gidan,fuskarsa a murtuke babu sassauci a cikinta karma ayi tunanin zai d'aga k'afa,dan wallahi bazai d'auki asara ba.
Jin abinda akace ya sanyata sanyo hijabi ta nufo soron jikinta a matuk'ar sanyaye da tunanin wata maganar kuma ta innarta ta kuma d'auko mata?
[9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH

2023

Wattpad@Rashuna
Mama Jiddah
Heenah
Silar soyayya
Masoya
Rabee'ah
Babbar Cuta
Muguwar surika
K'addarar Rayuwarmu
Cikin Duniyarmu500
Katanga500
Cin Amana500
Wadjda500
Halittar ZUciya500
Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA.

HALITTAR
ZUCIYA
(2)

Idonta akan Ta innarta ya fara sauka wacce ke rik'e da hannun Muhammadai,d'aya hannun nasa kuma rik'e yake da wata yarinya wacce kayan jikinta duk ya b'aci da wani abu mai yauk'i wanda baza ta tantance meye shi ba,sanyi jikinta ya kuma yi don ta tabbatar wata maga Ta innarta ta kuma d'auko mata,don a rana in ba'a kawo k'ararta sau goma ba za'a kawo sau biyar.

"Na ajiye k'waina a bakin shago,kafin na bud'e shagon na shiga da shi ciki,shine ta hankad'o wannan yarinyar kai,gaba d'aya sun fashe."
Cewar Muhammadai yana kuma d'aure fuskarsa karma tayi tunanin zai yafe.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,yanzu Mhumadai k'wan har na nawa ne?"

"Kiret biyar ne"

"Nawa kenan ya kama?" Inna ta kuma tambaya.

"8000 a ma yadda na saro"Muhammadai ya fad'a yana k'ara tamke fuska,karma tayi tunananin zai iya ragin ko ficika"

Jinjina kai Inna tayi,tana shiga tunanin yadda zata lalibo wannan kud'i,don ko jarin wainarta bai kai haka ba,bare kuma d'an kud'in kayan miyan da sai lokaci zuwa lokaci ake cinikinsa."Dan Allah Muhammadai kayi hak'uri zuwa k'arshen watan nan idan na d'au dashina zan baka."
"A'a wallahi,ni yanzu nake son kud'ina don wani zan koma na saro kinsan d'an jarin nawa ba wani taka kara ya karya yayi ba."

"Yanzu yanzu kuwa ai sai Allah,don ni ko zuwa gobe ma kace ban san inda zan samo maka kud'innan ba,idan baza ka jirayi zuwa k'arshen watan ba,bansan kuma ya zan maka ba."

"Zaki san yadda zaki mini idan naje na d'ebo miki 'yan sanda,dan wallahi yau duk masifar da za'ayi sai an biyani kid'ina."
Chapter 1 · 0% Book details