← Book details Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 14

Sashe 10

Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sallar la'asar Baba Malam(Mahaifin Madu,Rahina ce ta rad'a masa Baba Malam,dama Malam d'in ake kiransa,Innarta ce me ce masa Baba ita kuma sai ta had'e duka biyun take cewa Baba Malam)yayi sallama cikin gidan,Inna na jin sallamarsa ta fito da hanzari rik'e da tabarma ta shimfid'a masa a gurin da yakan zama a duk sailin da ya kawo musu ziyara,sannu take ta jera mishi har ya cire takalmansa ya nemi guri ya zauna da bismillah a bakinsa,yayin da Inna ta juya ta d'ebo masa ruwan randarta me sanyi a kofin silba ta kawo ta ajiye a gabansa kana ta durk'usa har k'asa ta gaisheshi ya amsa cike da kulawa da soyayya kana yace. "Hala uwata ba ta gidan nan?" "Taje nan gidan Hari ta anso awara,jiya da zazzab'i ta kwana ta kasa cin abinci,shine na bata hansin ta anso awara da kunu ko zata iya ci." "Haba ko da naji,tun da naga ba azo tarb'ata ba nasan ba ta nan,Ayya ashe ba taji dad'i ba?shiyasa Gwaggo (Matarsa da ya aura bayan rasuwar Inna Halima)tace mini yau ba ta biyo daga makaranta ba."
"Wallahi kuwa,anman dai da d'an sauk'i."
A dai dai nan Inna Hajara ta fito suka gaisa da Malam,ya amsa mata cikin kulawa had'e da tambayarta yara,sai ga Rahin ta shigo da hanzari ta k'araso gurin Malam ta kwanta a jikinsa had'e da fad'in. "Baba Malam" "Uhmmm,Uwata,ya jikin naki?" Ya fad'a yana shafa wuyanta yaji babu zafi. "Naji sauk'i Baba Malam." "To maza gyara zamanki ga gurasa da nama na kawo miki,har da fura." Baki ta washe cike da farin ciki ta gyara zamanta Inna ta d'auko kofi ta juye mata furar a ciki bisa Umarnin Malam,shi kuma ya bud'e mata ledar nama da gurasar ta hau danna lauma kamar ba mara lafiya ba,ta ma manta da ledar awara da kunun da ta ajiye a gefenta saboda taga masoyinta nama,Sale da Mubrak da Kabiru ne suka shigo,suka tisa Rahin d'in a gaba da kallo,Mallam ya d'ad'd'auka ya basu kafin Inna Hajara ta fito ta korasu d'aki tana zaginsu,ko d'aga kai Malam baiyi ya kalleta ba sai hirar su da suke ta yi da Inna Rahin na kora furarta bayan ta gama cin naman.
"Ina sonka Baba Malam,ina jin sonka sama da na Baba,ni dama kaine ka haifeni wallahi." Ta fad'i hakan bil hak'k'i da gaskiya har cikin ZUCIYARTA "Nima ina sonki Uwata sosai da sosai,Allah Ubangiji ya nuna mini auranki anan za'a ga soyayya." Rufe idanuwanta tayi alamun jin kunya kafin tace.
"Ai Inna tace ba za tamin aure da wuri kamar Yaya Halima ba sai nayi karatu sosai." Tana kai k'arshen maganarta Baba da Idi da Kabiru suka shigo,sun dawo daga gona,jin muryar Baban yana sallama su sale suka fito suna masa oyoyo yayin da Rahin ma ta shiga ayarin 'yan masa oyo yo anman haka ya tureta daga jikinsa alamun ba ya so tazo kusa da shi,gurin Malam ya nufa ya durk'usa yana gaisheshi,yayin da ya amsa masa a sake,kafin suka d'an tattauna game da aikin gona.

"Malam, 'yan bindiga fa sun kuma kawo hari k'auyen dake kusa da mu,kuma ana rad'e rad'en k'auyen nan zasu kawowa hari na gaba shiyasa nake k'ara rok'anka dan Allah mu tattara mu koma birni."
"Tun tuni na gaya maka,babu abinda zai saka na bar mahaifata,kuma kaima ban aminta ka bar garin nan ba sai dai idan har bana numfashi,ka saka a ranka duk wanda kaga ya mutu lokacinsa ne yayi."
Jinjina kai kawai Baba yayi,anman Allah na gani k'auyen gaba d'aya ya fita a kansa kawai dai dan ba yadda zaiyi da mahaifin nasa ne.
"Hajara kuje d'aki ke da yara zamui magana." Cewar Malam kafin ya kalli Rahina ma yace. "Uwata kema jeki d'aki kici gaba da shan furarki." Ran Inna Hajara babu dad'i ta shige d'aki yaran suka bi bayanta,dama dawowar Baba ce ta saka ta fitowa bacin haka tasan Mallam d'in ba ya maraba da ita ko kad'an. (A cewarta ba)

"Ahmadu ....

09037093702
[9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH

2023

Wattpad@Rashuna
Mama Jiddah
Heenah
Silar soyayya
Masoya
Rabee'ah
Babbar Cuta
Muguwar surika
K'addarar Rayuwarmu
Cikin Duniyarmu500
Katanga500
Cin Amana500
Wadjda500
Halittar ZUciya500
Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA.
Ban yadda a juya mini littafaina ko wata siga ba,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani.

HALITTAR
ZUCIYA

(4)
Malam ya kira sunansa,ya amsa yana me bawa Malam d'in dukkanin nutsiwarsa,dan da dukkan alamu magana ce zai masa mai muhimmanci,baiyi mamakin ganin bai cewa Inna ta bashi guri ba dan yasan akwai sirrikan Malan d'in da Innar ta sani wanda ko shi da ya haifa bai sansu ba.
"Wanene ni a gurinka." Malam ya jefo masa tambayar nan sai da ya numfasa kafin yace. "Mahaifina ne kai." "To a mtsayina na mahaifinka yau ina k'ara jaddada maka akan abinda muka sanar da kai ni da mahaifiyarka,ko bayan raina ka rabu da Mariya ko ka wulak'anta ta ban yafe maka ba,ina sane da har yau akwai nauyikan da baka sauke mata wannan kuma Allah ne zai tambayeka dalili,dan wallahi dalilinka ba dalili ba ne jahilci ne da jayayya da Ubangin,domin kuwa shine ya halicci ko wani jinsi,kuma shine nan ya bawa Mariya kyautar 'ya'ya matan da kake gudu ya kuma bawa Hajara mazan da kake so saboda haka yaso kuma haka yaga dama dukkaninsu ba zab'insu ba ne ba kuma son ransu ya zab'aba,sai dai dan hakan yayi niya kuma kyautar da yaga damar basu kenan.Bari na sanar da kai abinda baka sani ba,sanda Allah ya bamu cikinka fata muka dinga yi Allah yasa mace ce,anman da aka haifeka kazo a namiji haka muka nuna maka so da gata duk kwa tsanani da son da mukai na mace bai hana mun nuna maka k'auna ba,kuma daga kanka Innarka ba ta sake haihuwa ba har Allah ya bamu kyautar Mariya.
Dan haka abinda kake a tak'aice sunanshi jahilci,idan zaka gyara ka gyara dan wallahi abu d'aya nake jiye maka ranar da ZUCIYAR RAHEENA zata fara tsanarka,in bakai wasa ba kuwa sai kazo kana zub da hawayen ta soka wata rana a lokacin kuma bata da ikon yin hakan.Banga abin tsana a mace ba.Mahaifiyarka mace ce,kowa da ka gani a duniya silar zuwansa macece,idan ba macen za'a haifa ma mazan da kake so ne?
Mace na nufin k'warin guiwa.
Idan ba mace ba hayayyafa.
Idan ba mace ba rayuwar halitta.
Idan ba mace ba Zubin halitta.
Idan ba mace ba d'orewar gobe.
Idan ba mace babu ahali.
Idan ba mace babu gudanar da rayuwa.
Idan ba mace babu samun nutsuwar rayuwa.
idan ba mace ba ni'imar rayuwa.
Mace abar a tausayawa ce ba abar tsangwama da kyara ba. Idan maganganuna sun hankaltar da kai ruwanka,duk da ba yau na fara ba,idan kaci gaba da nunawa Raheena tsangwama da kyara ruwanka Allah yana gani."

Daga haka ya mik'e sukai sallama da Inna ya fice yabar Baba a durk'ushe ko karatun Malam ya shige shi?
(To wa ya sani sai mun bishi munji tukunna. )

Washe gari RAHENA ragas ta tashi,dan haka da su Bulki suka biyo mata makaranta a shirye suka tarar da ita,suna zuwa suka rankaya suka tafi Bulki rik'e da jakar Rahin d'in dan ita ke d'aukar mata ba kuma ta isa tace ta gaji baza ta d'auka ba.
"Rahin nima jiya fa banje makarantar ba Abun gidan Bawa me jakai na tsokana a burtsatse shekaran jiya shine na gudu tace sai a makaranta zata kama ni taci ubana."
"Me yasa ba ki gaya mata ubanki yayi mata kad'an ba sai dai taci Bawa me jakai dan shine dai dai da ita."
"Bari nayi sai yau ma gaya mata."
A dai dai nan suka shiga cikin ajinsu,Salima ce dake mugun son k'awance da Rahin ta taso ta tareta had'e da fad'in.
"Allah yasa kin tahon da wainar Inna ?"
"Na dai tawo da ita,idan an fita break in zamu ci sai na kirawoki ." "Me yasa jiya ba kizo ba?na tambayi Fad'ime ba ta kulani ba ." Dan haushinta suke ji yadda take likewa Rahinan ta k'arfin tsiya,yanzun ma tsaki sukai suka wucesu.
"Ban ji dad'i ba ne,nayi fama da zazzab'i."
"Ayya,Allah ya sawak'e,idan an fita break d'in sai mu fita tare yai d'ari Innata ta bani "
Washe baki Rahin tayi had'e da farin ciki,a ranta tana b'uyarwa su Bulki zasui wainar ma yau baza taci tare da su ba.
Bayan tashinsu daga makaranta ansha dambe tsakanin Abur wacce Bulki ta tsokano da Rahin,har sai da Rahin tayi mata k'ululu a goshi aikwa tayi rantsuwar baza ta yadda ba washe gari sai takai k'ara gurin Headmastee d'insu dan ba ma za ta kaiwa Innarsu k'arar ba da iyakacinta tace tayi hak'uri.
Chapter 10 · 0% Book details