← Book details Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yakai k'arshen maganar yana hankad'a Rahin d'in gaban Inna,saurin tareta Innar tayi bacin haka da sai tayi muguwar fad'uwa.
"Hankalinki ya kwanta ko Rahina,kin fi son ki ganni cikin tashin hankali ko yaushe?."
"Innarmu wallahi ita ta fara tsokanata,ni kuma ban san ya ajiye k'wai ba da bazan turata gurin ba."
Innar ba tace komai ba sai hannunta da ta jaa suka shiga ciki,suna shiga ciki sai ga Halima tayi sallama da gudu Rahin taje ta tarota,duk da a rana takan je mata sau kusan uku,anman idan taga Haliman a cikin gidansu ba k'aramin dad'i take ji ba,ko don ba ta fiya ganinta cikin gidan nasu ba ne oho?tunda ba kasafai takan zo ba,saboda Baba ba ya barinta,da tazo yake korarta indai yana cikin gidan.
Rungume k'anwarta Halima tayi cike da so da k'auna,anman da sun zauna guri d'aya sai sun raba gari saboda k'iriniyar Rahin d'in.
"Inna ina yini?"
"Lafiya lau Mamana,ya kuke ya Abdullahin?"
"Lfy lau wallahi yana gaisheki,lafiya naganki wani iri?"
"Ina amsawa "Kafin ta numfasa ta kuma cewa.
"Ta Innarta ce ta tura wata yarinya kan k'wan Muhammadai suka fashe,yanzun nan yabar k'ofar gidannan yace sai na biyashi kud'inshi ko ya kira mini 'yan sanda."
"Innalillahi,kud'in har nawa ne?"
"8000 yace,wai akan ma yadda ya saro"
Duka ta kaiwa Rahin d'in da ke kusa da ita tana danna wayar Haliman,duk da ba ta san inda take shiga ba,wani wawan ihu ta saki saboda yadda dukan ya shigeta ba zato ba tsammani,aikwa ba shiri tayi jifa da wayar Haliman inda tayi gefe tai fisis fisis.
A fusace Haliman tayi kanta ita kuma tayi bayan Inna tana zunduma ihu.
"Yi hak'uri Mamana,kinji,sau nawa zan gaya miki ki dinga hak'uri da k'anwar nan taki,idan kowa ya kasa hak'uri da ita ke ya zamar miki dolen doliya ki hak'uri da ita,wata rana idan ba na raye ke zata rab'a taji sanyi domin ke zaki zame mata gurbina."
Cike da takaicin Innar ta hanata dukan Rahin d'in take had'a wayar tata,dama wayar ba wata wayar kirki ba,sam ba ma ta saurari me Innar ke fad'i ba saboda ranta da yayi mugub b'aci."
"Amman Inna har da d'aurin bayanki Rahin ke samu tana wani iskancin wallahi"
"Haba Mamana,yau ke kike gaya mini wannan maganar,maganar da in an jefeni da ita kin fini jin d'acinta?Nonon da kika sha shi Rahina ta sha,tarbiyar da na baki ita na bata ba kuma hakanne zai hana halayyarku bam bamta ba,ba zab'ina bane ba kuma son raina ba ne Rahina ta zamo a haka,duka zagi hantara ba shi zai sauyata ba illa addu'a ina kuma fatan Allah ya tsayar mata iya k'uruciya."
"Ba ina nufin ba ki bata tarbiya ba,ba kuma ina nufin ke kike sakata yi ba,ina ganin kamar soyayyar da kike mata ce ta saka hakan saboda tasan baza ki tab'a iya dukanta ba."
"Ke kanki shaida ce,da duka yana gyara mutum da ko dukan da Babanku kewa Rahina yasa ta gyaru,so kike Babanku ya daka yayyanta su daka 'yan waje su daka,nima na daka,babu inda zata rab'a taji sanyi kenan?Itama ba zab'inta bane Allah ne yayi ta haka,kuma ko wani yaro da kalar k'uruciyarsa duk me kallon ni na sangarta Rahina Allah ne zai mana sakayya."
"Allah ya huci zuciyarki Innarmu" Halima ta fad'a cike da dana sanin furucinta.Sallama aka rafka daga k'war gida,Inna na jin sallamar tace.
"Ina to Muhammadai ne ya dawo."
"Inna ke a gurinki nawa za'a samu? mu had'a mu bashi kud'insa,ni bana son harka da 'yan sanda"
"Ai ina jin kud'in hannuna idan na had'esu gaba d'aya baza su huce dubu hud'u ba."
"Kawo na bashi,anjima idan na koma na fasa bankina na cikasa masa sauran."
"Yaa Halima zaki bani biyar in kin fasa bankin?"
Wata shegiyar harara ta zabga mata kana ta anshi kud'in gurin Inna ta fita kai masa,anci sa'a ya karb'a,da sharad'in anjima tana komawa zai biyo bayanta ya ansa.

"Inna sati mai zuwa Abdullahi zai tafi habuja cirani."
"Ke dan Allah."
"Wallahi kuwa,nima yace idan yaje yaga yanayin garin zai turowa D'ahiru k'aninsa kud'i na bi bayansa,dan yace in ya tafi zai jima bai zo ba,zai dai dingawa su Innarsa aike,saboda matsa masan da suke sai ya k'ara aure wai tunda ni nak'i haihuwa,shiyasa ma ya tsiri tafiyar."
"Hmmmm,Allah ya kyautawa wasu mutanen wallahi,da yake ke zaki bawa kanki shiyasa kika k'i haihuwa kenan,in banda jahilci na mutane sun san Allah ke bada haihuwar nan anman da mutum ya kwana biyu bai samu ba za'a jingina masa laifi,dudu auran naku da ko shekara biyu bai rufa ba har an sanya muku idanu,banda ma haihuwar ta zama ta zamani yanzu wata tara cif zaki ji mace ta haihu,da kwa da sai a 'yebi shekaru kafin kiji ance wance ta haihu."
"Wallahi kuwa Inna,shiyasa ma bana damuwa,saboda ban isa na bawa kaina abinda Allah bai bani ba,shima kuma bai damu ba,ko nayi zancen sai dai kiji yace"To ke zaki bawa kanki,ba sai sanda Allah yaso ba"
Dai dai k'arshen maganarta Hajara tayi sallama ta shigo,taje yinin biki a can mak'otan gidansu,sai yanzun ta dawo,sallamarta kawai suka amsa suka cigaba da hirarsu dama Halima ba kulata take ba,tun wani fad'a da akai tun kafin bikin Haliman,babu yadda Inna ba tai da ita ba akan taci gaba da gaisheta anman fir tak'i,tace gaisuwa kam tsakaninsu da ita har abada,Halima akwai zuciya ban bancinta da Rahina kenan,ita Rahina yanzu zaki mata abu kuma anjima ta komo gurinki.

Bayan sallar magariba Inna na cikin zubowa Halima d'anwaken da tayi dominta sai ga sallamar Baba ya shigo cikin gidan,idansa akan Haliman ya fara sauka ya wani had'e fuska,ko gaisuwar da take mik'o masa bai amsa ba yace tazo ta shige ta koma inda ta fito,tsam ta mik'e tana saka hijabinta a ranta fad'i take."Banda arzik'in mahaifiyarta dake cikin gidan da ko fuskarta baza su k'ara gani ba,har sai sun manta ya kalar fuskar tata take.A kwano mai murfi Inna ta juye mata d'an waken ta k'ulle a leda ta bata."To Inna na gode,idan da sauran canji zan bayar a kawo miki sai ki sayi sauran abinda babu a kayan wainar."
"To na gode Mamana,Allah ya yiwa rayuwa albarka,ki gaishe da mutan gidan."
"Amin Innarmu,zasu ji in sha Allah"

"Yauwa Babansu ga Mubarak can a kwance mashashshara ta kwantar da shi sakamakon dukan da Rahin tayi masa."
Cewar Hajara,bud'ar bakin Inna sai cewa tayi.
"Ke Hajara kiji tsoron Allah,yanzu Mubarak d'in da ke sa'an Rahina,shi za tayiwa dukan da har zai sakashi zazzab'i,bayan ke kanki kinsan k'arfin mace da namiji ba d'aya ba ne,idan har bai saka mata zazzab'i ba ai ba ta saka masa ba."
"To zan mata k'arya,sai an magana ba ke ke daure mata baya ba ki kawowa mutum k'auli da ba'adi."
Baba kuwa inda Rahin ke kwance na sharar bacci ya nufa,tun bayan gama cin abincinta ta b'ingire a gurin,saboda anyi fitina har an gaji...
[9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH

2023

Wattpad@Rashuna
Mama Jiddah
Heenah
Silar soyayya
Masoya
Rabee'ah
Babbar Cuta
Muguwar surika
K'addarar Rayuwarmu
Cikin Duniyarmu500
Katanga500
Cin Amana500
Wadjda500
Halittar ZUciya500
Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA.
Ban yadda a juya mini littafaina ko wata siga ba,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani.

HALITTAR
ZUCIYA

(3)

Sa k'amshi sa dad'i,hana gafi k'arni no,spices da curry kenan gangariya gurin k'awata girki.
09037093702
Ina macen da girkinta ke k'arni idan tayi amfani da nama,ina macen da ke son amfani karafish tana tsoron k'arni,ina kuma macen da rashin albasa ke hanata soya k'wai,ina macen da take son girkinta ya k'ara dad'i da d'and'ano da kuma k'amshi?maza hanzarta ki nemi spices d'in Rashuna domin kuwa nata ba irin nasu ba ne.09037093702
Mata da dama idan suka soya kifi zubar da man suke saboda gudun k'arni,abinda kuma ba ku sani ba kun zubar da sinadarin ki kelaya abinki Hajiyata,ki kawo curry da spices d'in Rashuna ki zuba,Hmmm na rantse miki da Allah mityarki ba za tayi k'arni ba.

K'afa yasa yakai mata wani irin dukan da ya sanyata farkawar ba shiri had'e da tsanyara wani uban ihu,dukanta ya shiga yi ko ta ina tana ihu tana kwararato shikwa yana fad'in.
"Ai yadda kika saka shi yau zai kwana da zazzab'i wallahi yau kema sai kin kwana da shi,shegiya me siffar aljanu,in baki wasa ba wata rana sai na nakasta ki wallahi."

Ko kallon inda yake dukanta Inna ba tayi ba tai shigewarta d'aki,duk da zuciyarta dake mata suya bama akan dukan nata da yake ba,a'a irin furucin da yake jifanta da shi,duk wanda ya zauna da su na wuni d'aya sai ya fuskanci irin tsanar da yayiwa Rahina wacce ba ya iya b'oyeta ko a gaban waye,ita kuma zuciyarsa na matuk'ar sonsa da k'aunarsa,abu d'aya take jiye masa shine ranar da ZUCIYAR RAHINAN zata fara tsanarsa wacce kuma ta tabbata wannan tsanar mai iya cireta daga zuciyarta sai Allah kuma.

Sai da ya tabbatar ta daku kana ya k'yaleta,band'aki ya shiga ya fito ya d'aura alwala ya fice saboda kiraye kirayen sallar isha da aka fara.Tana zaune tana rusa kuka Sale ya shigo,irin kukan da take ya fara kwaikwaya,aikwa da ta d'auki farantin silbar dake kusa da ita ta lailaya shi ta jefa masa sai kuwa akan goshinsa,wata gigitacciyar k'ara ya saki da ta sanya Hajara saurin fitowa,nufo inda take a zaune yayi yana."Wallahi bazan yadda ba sai na rama." Mik'ewa tayi tana huci tana jiran yazo ayi duk wacce za'ayi,janyeta Inna tayi had'e da fad'in. "Shige kiyi alwala kibar nan gun."

Hajara ce a k'ufule tace."Wannan wani irin zalinci ne?Kibar yaro mana ya rama abinda ta masa zaki wani janyeta tsabar rashin gaskiya." Ci kanki Inna ba tace da ita sai tsaiwarta ta gyara tana jiran Rahin d'in ta fito daga band'akin,tana fitowa kuwa Hajara ta hankad'a Sale had'e da fad'in jeka ka rama dukanka,in kuwa ba haka ba wallahi Babanku ya dawo sai na gaya masa tunda ita aljana ce duka ba ya shiga jikinta,ko kuma nace jaka"
Chapter 2 · 0% Book details