← Book details Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(5)
Da gudu ta shigo cikin gidan nasu,wanda ba ta kula da redion Baba da ke tsakar gida ba tayi gaba da ita ta ragargaje a gurin dama redion ba ta kirki ba,gefe ta ja cike da tsoro tana shishshigar da idanuwanta ciki,kafin hantar cikinta ta kuma kad'awa jin muryar Baban daga d'akinsa yana. "Kai waye nan ya tab'an radio?"
Inna Hajara ce da ke durk'ushe gaban murhu tace. "Wa ka sani banda mahaukaciyar 'yarka" A harzik'e ya fito ya kalli radion dake yashe a k'asa a ragargaje ya d'ago ya kalleta tana ta raba idanuwa,kwalfa yayi ya koma d'aki ya zaro wayar radion ya fito,wayam ya tarar babu ita ba alamunta kallon Inna Hajara yayi had'e da tambayarta.
"Ina Rahin d'in take?" "Ta fice"
Ta bashi amsa,k'wafa yayi had'e da fad'in. "Zata dawo ta same ni ne"

"Idan ta dawo ta sameka dan Allah kada ka barta da ranta,ina ba Sale ne ya lalata radion ka zauna ka gyarata ba ko dunguri ba kai masa ba sai ita da yake tsintarta akayi ba haihuwarta akai ba?" Cewar Inna da fitowarta kenan daga band'aki takaici yasa ta yin magana ta yadda ko yaushe yake nuna yafi son 'ya'yansa maza a kan Rahin d'in. "Ke ni kike gayawa maganar banza,idanma na kasheta ai na kashe banza da ita da babu duk d'aya suke a gurina wallahi,ki bar tunk'aho da Malam,dan wallahi ba shi zai hana na ci miki mutumci ba." D'aki Inna tayi shigewarta ba ta saurareshi ba tana jinsa yana ta sababi a tsakar gidan,dama bata tanka mishi yau dinma kuskure aka,samu.

Har yamma Inna na zaman jiran shigowar Rahin shiru kike ji,ga babar Salima ta kaho k'arar Rahin d'in wai tana saka Salimar sato mata kud'i tazo makaranta su kashe,hak'uri ta bata anman da cewar ba musu tayi mata ba tunda ba'a shaidar 'ya'yan yanzu,in Rahin d'in ta dawo zata tisota suzo nan gidan duk inda matsalar take za'ai maganinta,to anman gashi har yamma Rahin d'in shiru ba ta dawo ba,duk inda take tsammaninta taje ba ta nan,gidan Halima ne hop dinta na karshe anman kuma ta rasa wani yaro zata aika.
Itakwa Rahin tana can gidan Halima,kamar yadda Innar take tsammani,tsoron dukan Baba take tunda har yau ba ta manta dukan da yayi mata shekaran jiya ba,shiyasa tayi zamanta gidan Haliman,idan taje gurin Innar Audu ta isheta da fitina ta koreta sai ta koma gurin matar wan Audun can ma in ta korota sai ta dawo gurin Haliman,to itama Haliman ba tsira tayi ba kawai itama dan ba yadda za tayi da ita ne,daga k'arshe dai cewa tayi ta tashi ta rakata gida,ita kuma ta botsare ba inda zata sai da ta bata naira ashirin kana ta yadda suka taho,uniform d'innan nata yaci k'aniyarsa ya fita daga hayyacinsa.

Halima gaisawa sukayi da Inna kawai ta juyo,dan ba ta k'aunar su had'u da Baba ya koreta ranta yana matuk'ar k'una da suya,sai da Inna taiwa Rahin wanka ta shiryata kana ta sakata gaba da tuhumar ita ke saka Salima na sato kud'in Innarta suna kashewa? Sai da tayi rau rau da ido kafin tace.
"Wallahi cewa take Innarta ce ta bata,ni kuma idan naje da waina sai muci tare mu kashe kudin tare."

"Ta Innarta ki gayan gaskiya,fain lam takun tarahu."
"Fa innahu yaraka" Tayi saurin k'arasa mata,haka Innar ke mata indai tana son gane gaskiyarta,a gaba ta sakata sukaje gidansu Salima,sai gashi da aka titseye Saliman ta fad'i gaskiyar Rahin din ba ta san sato kudin take ba,Innar Saliman kunya duk ta isheta ta bawa Innar Rahin din hak'uri.Kashedi sosai Inna taiwa Rahin akan babu ita babu Salimar,tace ai dama su Bulki basa son ta kulata,Salimar ce ta nane mata anman tawa Innar alkawarin ba ita ba ita. A haka kwanaki ke shud'ewa a hankali su koma watanni,watanni su rikide su koma shekaru cikin hikimomi da iyawar Ubangiji.Su Rahinah har an zana common entrance,ana ta tsalle da murnar jiran zuwan su Halima su tafi da ita Habujar.Audun ne ya fara yin gaba sai da yayi wata shida a can kana ya turowa wansa Magaji kud'i ya yiwa Halima shirin komai na tafiya ta bi bayanshi da alk'awarin idan Rahin ta kare primary Halima zata zo ta taho da ita,sai dai kuma murna da farin cikin Rahin ya koma ciki sabili da Baba da yace babu inda zata je makarantar ma ta gama aure zai mata,a can gidan mijin tayi hankali,Inna babu yadda ta iya tunda maganar aure ake anman ta so Rahin d'in tata tayi karatu sosai sai gashi ita tun tana shekara goma ma Baban zai mata aure ko shekarun Haliman ba ta cika ba sanda aka mata auran.Ihu kuka tumami Rahin baza ta auri Tanimu ba,anman Baba ya kafe sai ta aureshi dan ya karb'i komai na aladarsu yinin biki ya rage,kuma ya samu goyan baya gurin Baba Malam d'in nata tunda shima bai fiya son karatun bokon ba,kuma auran shi ya dace da Rahin d'in sai tayi hankali da nutsuwa.Rahin kuwa tayi rantsuwar baza ta auri Tanimu ba dan haka ta shiga neman hanyar kaucewa wannan aure.

Gidansu Tanimu sukaje da ita da su Bulki suka dinga yi musu ruwan duwatsu ko ta ina suna yi suna cusa musu zagi kala kala har da ambato sunan Innar Tanimu da cewa."Zulai idan har kin haifu cikin iyayanki kisa Tanimu ya fasa aurena,dan kwa in na shigo cikin gidianna sai na zame muku masifa da bala'i."
Daga nan kuma sai sukai gonar Malam Buba(Mahaifin Tanimu)sukai b'arnarsu san ransu suka sha mangoro sukai nak kana kowa yayi gida.
Aikwa a ranar Malam Buba yayi sallama da Baba ya anshi komai da suka kawo na aure,dan ya samu labarin su Rahin ne sukai masa b'arna a gona,ga ruwan duwatsun da sukai a gidansa har goshin Shafa(kanwar Tanimu)suka fasa shiyasa ma suka yanke shawarar fasa aurota dan in ta shigo ba su san wata illa zata yi musu ba,Tanimu dai yasha kuka dan yana mugun son Rahin dan ba yadda zai da mahaifansa ne,ya gaya musu k'uruciya ce nan gaba sai sunsha mamakinta anma sunk'i fahimtarsa bama su tsaya sun saurareshi ba. To dai fad'a k'arshe sai da ya kaure tsakanin Malam Buba da Baba,dan yace sai an biyashi b'arnar da su Rahin suka shiga gonarsa sukai,shikwa Baba yace bazai biya ba sai dai yaje ko wacce tsohuwarta ta biya shi,shikwa Malam Buba yace hukuma ce zata raba su,ai dama yasan 'yarsa bata da hankali da yake neman lik'awa d'ansa,shikwa Baba yace dad'in abin d'an nasa ne ya kawo kansa ba janyoshi yayi ba.

A harzuk'e Baba ya shiga cikj ya dank'i Rahin yana jibgarta kamar Allah ya aiko shi yana fad'in.
" 'Yar iskar yarinya mara mutumci mara hankali,haka kawai kin janyo mini masifa ina zaman zamana wallahi in baki wasa ba sai na nakasta ki,kuma aure dole ne ki rubuta ki ajiyeshi wallahi sadaka zan bada ke tunda ke annoba ce ga duk wanda ya rab'e ki ." Wani mari da yakai mata ta hantsila ta kifa kan dan damalin k'ofar d'akin Innarta goshinta ya dakin gurin da ta saki wata shegiyar k'ara ta azabar da takai mata ziyara har tsakiyar k'wak'walwarta.
"Waiyo Inna Baba zai kasheni,Innata kaina,innata goshina ,innata idona zafi,Innata jini,shi kenan Innata zan mutu ban cika miki burinki ba....
[9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBEE'ARTH

HALITTAR
ZUCIYA.....

Watpad@Rashuna
Mama Jiddah
Heenah
Silar Soyayya
Masoya
Rabee'ah
Babbar Cuta
Muguwar Suruka
K'addarar Rayuwarmu
Cikin Duniyarmu500
Katanga500
Cin Amana500
Wadjda500
Halittar Zuciya500

Hak'k'in Mallaka.Rabee'ah Shu'ayb Nababa (Rashuna,Bebee'arth)Ban yadda a juya mini littafaina ba ko ta wata siga,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani.

(Oum Samha)
(DATA SERVICES)

(MTN)
>500 =150
>1Gb =250
>2Gb =580
>3Gb =900
>4Gb =1200
>5Gb =1500
>10Gb=3000

( AIRTEL)
>500mb =150
>1Gb. =300
>2Gb. =600
>3Gb. =900
>4Gb. =1,200
>5Gb. =1,500
>10Gb. =2,850

(GLO)
>1Gb. =350
>2Gb. =700
>3Gb. =1,050
>4Gb. =1,400
>5Gb. =1,750
>10Gb. =3,000

( 9MOBILE)
>1Gb. =450
>2Gb. =1,000
>3Gb. =1,400
>4Gb. =1,700
>5Gb. =2,150
>10Gb. =3,500
>11Gb. =3,800

✓All data plan valid for 30days.

Always available and reliable.

Account Details:
8167316776
Ummi Saidu
08167316776
.Thanks as u patronize🤝
(6)
Ganin yadda jini ke wanke mata fuska yasa jikin Baba yin sanyi,Inna kuwa ta rasa wani taimako zata bawa Rahin d'in,ga tsohon ciki ne jikinta haihuwa ko yau ko gobe,ga kuma Rahin d'in ta runtse ido tana zunduma uban ihu sai Baba ne jiki a sanyaye ya d'auketa ya nufi camise da ita,treatment in goshin nata akai tana zunduma ihu tana kaiwa Baba duka ko ta ina sai da ya had'e hannuwan nata guri guda kana aka samu aka gama mata har d'inkin goshin nata da ya tsage a tsaye,sai kuma me? Tana bud'e idanuwanta taga babu abinda take gani banda duhu dumd'in ai da ta zunduma wani uban ihu sai da ta firgita mai camise d'in da Baba.
"Na shiga uku na lalace Inna Baba ya makanta ni,kizo kice ya maida mini da idanuwana." Hantar cikin Baba ce ta kad'a ya kalli mai camise d'in cike da tsoro.
"Ke Rahin nutsu ki gaya mini me kike ji?" Cewar Baba k'irjinsa na dakan lugude. "Wallahi bana ganin komai,ka taimaka mini ka dawo mini da idanuwana wallhi na maka alk'awarin zan auri ko mahaukaci ne ba ma Tanimu ba dan Allah Baba." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Cewar Baba yana kallon mai camise ko da wani taimako da zai musu. "Ai abinda yafi kamata kawai ku bari zuwa gobe da safe ka tafi da ita asibiti anan ne za'a binciki ko wata matsala ce."
"Tom shikenan na gode" Cewar Baba ya kamo hannun Rahin d'in suka taho yana ta zabga salati,wata iriyar nadama ce ta shige shi (NADAMA MARA AMFANI)itakwa Rahin kuka take bil hakki tana tausayawa rayuwarta tana fad'in shi kenan rayuwarta ta durkushe ta lalace tunda ta makance zata fara bara a titi,da ta sani da ba tayi jayayya da auran Tanimu ba,gashinan Baba ya makantata a banza makantar da bata jin akwai wanda zai iya auranta a haka,burin rayuwarta(karatu)ya ruguje raga raga.
Chapter 5 · 0% Book details