← Book details Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 14

Sashe 14

Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

hayaniya da iho ihon mutane yasa ta farkawa a firgice tana kiran Baba,jin babu alamun Baban kusa da ita sai ihun mutane da take ji yasa ta fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi,kukanta ne yasa Hadi da ya lab'e daga bayan katangar da take lek'owa idonsa ya sauka a kanta,wani irin sanyi yaji a ransa,yana ganin kamar wahalarsa ce tazo k'arshe idan ya samu damar k'wamushe wannan yarinyar,da azama ya fito ya ja hannunta ya koma inda ya lab'e,ganin yadda take a firgice tana kiran Baba yasa shi janyo wani hankici daga aljihunsa ya shek'a mata,ba tayi baccin da yake so ba anman jikinta ya saki gaba d'aya ta zube a jikinsa,bayan komai ya lafa ya faki idanuwan mutane ya sakata a bayan motarsa,Allah Allah yake gari ya waye ya fice daga cikin tashar dan ko lodi bazai yi ba tunda ga babban lodi ya samu.
K'arfe bakwai ya fice daga cikin tashar ya fara sharara gudu akan titi Allah Allah yake yaga ya d'auki hanyar barin gari dan yana hango yawan kud'in da zai samu idan ya kaiwa oga wannan yarinyar sai dai kuma kana naka ne Allah yana na shi,nashi kuma shine gaskiya domin kuwa wani k'aton ice da bai kula da shi ba motarshi ta daka a take sitiyarin motar ya kubfce mishi motar ta kife akan titi,mai ya fara zuba a take ta fara hayak'i alamun tana gab da kamawa da huta,mutum biyu Allah ya jeho zasu huce,su suka taimaka suka ciro Rahina daga cikin motar ba su kai ga fito da Hadi ba motar ta kama da huta.
Ko k'warzane babu jikin Rahina,anman a mugun tsorace take,rashin gani babbar illa ce a rayuwa tana jin komai anman bata ganin abinda ke faruwa,kuka take sosai tana kiran sunan Innarta ba ta san ina Baba ya kawota ya ajiye ba ko kuma da had'in bakinsa wannan mutumin yake k'ok'arin sayar da ita,dan taji wayar da yakeyi abinda ya shek'a mata baiyi nasarar sakata bacci ba jininta yana da mugun k'arfi,hankulan mutane na can kan motar da ta kama da huta da kuma k'ok'arin kiran police ta d'auki wata hanya da ban tana tik'ar gudu a ganinta Allah ne ya kub'utar da ita daga hannun azzalumin can dake k'ok'arin sayar da ita,bata da tabbas d'in wanda suka cirota daga motar suma ba azzaluman ba ne,gudu take sosai akan titi wanda ita ba ta san titin bane tunda ba gani take ba,aikam wata mota da ta yanko a guje tai sama da ita ta watsar babu alamun rai a tattare da ita,kifa kai mamallakiyar motar tayi jikin siyiyarin cike da takaici da bak'in cikin wannan mahaukaciyar yarinyar,ba komai take tsoro ba sai azumin da zata janyo mata ba taji ba ba ta gani ba,na Ramadan ma da yaya take sauke shi bare kuma wannan da ya ninka shi,tsaki ta ja kafin ta fito daga motar a ranta tana addu'ar Allah yasa ba ta mutu ba,ko k'warzane babu a jikinta anman da alamun wuya ta saka numfashinta d'aukewa.
D'aukarta tayi ta sanya cikin motarta ta juya zuwa asibitin da ta fito,tana jan tsaki akai akai da addu'ar Allah sa ba ta mutu ba,tsabar zafin da kanta ya d'auka baccin da ke cikin idanuwanta ji tayi ya wartsake gaba d'aya. Sai da aka tabbatar mata yarinyar na da rai ta samu karaya a k'afa da hannu kana ta samu nutsuwar tafiya gida bayan ta bar sallahun a yiwa yarinyar duk abinda ya dace idan taje gida zata turo wanda zai kula da ita.
Sai takwas da rabi ta baro asibitin zuwa gida,tana parking d'in motarta ta hango Fadwa ta nufi sashen FASIHUL LISAN a ranta tace "Wahalalliya." Tana shiga falon,Fadwan ta shigo da tray a hannunta fuskarta d'auke da damuwa,dining ta nufa kai tsaye ta ajiye tray d'in hannunta tana fad'in.
"Ammi sai yanzu?"
"Hmm wata yarinya ta jamin musifa wallahi,ta hau kan tsakiyar titi tana gudu ban aune ba na kad'eta,inda Allah ya tak'aita ba ta mutu ba,kicema Talatu ta shirya Bala ya kaita asibitin ta kula da yarinyar kafin a samu kanta."
"Ayya Allah ya kiyaye gaba,nima zan bisu na duba yarinyar."
Kamar yadda ta tsammata Ammin baza ta tanka ba,ba kwa ta tanka d'in ba sai shigewarta part d'inta tayi dan wanka take buk'ata kafin ta kwanta bacci,kwana tayi ba ta rintsa ba saboda yawaitar marasa lafiya duk rashin kirkinta tsakaninta da Allah take aikinta.

Murmushi Fadwa ta saki,ta d'auko kwaandon saka abinci ta jere break fast d'in da ta hana idonta bacci ta tashi ta tsantsarawa Yaa Fasee duk don ta burgeshi ta kuma karkato da hankalinsa kanta a bisa shawarar aminiyarta Siyama,sai dai kuma da yake Namijin duniya ne haka ya tsallake break d'in ko tab'awa bai yi ba ya fice ya bar mata,yanzu kuwa dole ya ci tunda ta samu hanyar zuwa asibitin sai ta bishi da shi har office d'insa wahalarta baza ta zama a banza ba in sha Allah.

Sai da ta gama jera abincin kana taje ta sanarwa da Talatu sak'on Ammi,ta d'auki d'an abinda zata d'auka suka fito Bala ya jasu zuwa asibitin...

Zan iya cewa a nan free page ya k'are masu buk'atar cigabansa zasu iya samuna kai tsaye a wannan layin 09037093702 na gode.

BEBEE'ARTH RASHUNA
Chapter 14 · 0% Book details