← Book details Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 14

Sashe 3

Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Inda Rahin d'in ke tsugune na alwala Sale ya nufa Inna ta dakatar da shi da fad'in. "Kada ka sake hannunka ya sauka a jikinta,in ba haka ba wallahi sai ranka yayi mugun b'aci,uban waye yace ka tsokaneta?da kaja girmanka zata bi ta taka shine?"
Jaa da baya yayi saboda yana shakkar Innar Rahin d'in,sam bata musu wasa shiyasa suka fi tsoranta ma akan Innarsu,k'wafa kawai yayi,had'e da cewa Rahin d'in. "Shegiya mummuna,duk fad'in garin nan kowa ya shaida Baba baya sonki,kuma wallahi zan kamaki a waje ne inda babu Innar taki sai naga me tare miki."
"Ka nad'a mata na jaki wallahi ni nan na tsaya maka,kuma mahaifinka ma ya tsaya maka,yarinya sai kace iblishiya kuma ana dad'a d'aure mata baya,kai nidai Allah na gode maka da ba ka bani 'ya mace ba,ashe ta bakin baban nasu 'ya mace tarin wahala ce."

"Shige d'aki,kiyi sallar magariba sannan ki isha." Inna tacewa Rahin,sai da taga shigewarta d'akin kana ta juyo kan Hajara dan mayar da martani. "A gurin kune 'ya mace tarin wahala,anman a gurina ni'ima ce kuma sanyin idaniya,da ace zan k'ara haihuwa dubu,kuma Allah du ya bani 'ya'ya mata da zanyi matuk'ar farin ciki,abinda Rahin kuwa keyi k'utuciya ce kuma kowa da kalar tasa k'uruciyar,wata rana baza kice tayi haka ba,kuma ina ji a jikina wata rana sai kin shiga inuwarta 'ya'ya mazan da kike ganin mafaka ne a gareki sai tawa macen ta zane miiki mafaka kafin su,da kina da hankali da tunani ko akan Halima zaki fahimci falala da ni'imar da yayi mini da ya azurta ni da samunta."
Tana kawowa nan tayi shigewarta d'aki ba ta tsaya saurarar kunfar bakin da Inna Hajara ke yi ba ta dai jiyota tana Allah ya sawak'e ta shiga inuwar Rahin d'in ba taga abinda zata tsinana mata ba ita da Allah ya azurtata da samun mazaje har guda biyar ba taga wani abu da wannan iblishiyar za tayi mata ba. A k'udun dine ta samu Rahin d'in tana ta rawar d'ari,alamun zazzab'i ne yake shigarta,paracetamol ta d'auko ta bata tasha,kana tace ta shige cikin gidan sauro ta kwanta ita kuma ta tayar da sallar isha'i. Rantsuwar Baba taci Rahin,dan kwa kwana tayi da azababban zazzab'i,gashi in tana zazzab'i sai tai ta firgita,washe gari da safe kuwa ko makaranta ba taje ba su Fad'ime da suka,biyo mata suka tarar bata da lafiya sai kwa bulki cewa tayi. "Alqur'anin Allah yau nima kwa baza ni ba,komawa zanyi nacewa Innata ba'a yi." cikin marai raita Fad'ime tace.
"Kekwa dan Allah Bulki kizo muje,yau ni kad'ai kuke so ku bari,makarantar baza tamini dad'i ba,gashi in naje na yiwa Innata k'arya baza ta yadda ba." "Ai yau ko me zaki Fad'ime ba zanje makarantar nan ba,kin manta jiya na tsokano kin manta jiya na tsokano Abun gidan Bawa me jakai,tace sai mun had'u a makaranta zata ci ubana,kuma me tare mini ba lafiya in ba so kike tayi k'uli k'ulin Kubra da ni ba." Ba yadda Fad'ime ta iya haka ta bar Bulki ta juya gida ita kuma ta nufi makarantar bokon nasu da ke da d'an tazara sosai da su,ajinsu uku a yanzu,kuma ajinsu d'aya duka su ukun,k'awaye ne tun daga yarinta,Bulki tsinanniyar tsokana ce da ita wacce ta dame ta Rahin ta shanye ga tsoro fal ciki,idan tayo tsokanar Rahin ke uwa ke makarb'iya,ita Rahin fitina tafi yawa a cikinta,Fad'ime ce me sanyin hali kawai a cikinsu anman itama idan ana fad'a da d'aya a cikinsu haka zata zage ayi da ita duk da ba ta kasance me son fad'a ba.

Bayan sallar la'asar Baba Malam(Mahaifin Madu,Rahina ce ta rad'a masa Baba Malam,dama Malam d'in ake kiransa,Innarta ce me ce masa Baba ita kuma sai ta had'e duka biyun take cewa Baba Malam)yayi sallama cikin gidan,Inna na jin sallamarsa ta fito da hanzari rik'e da tabarma ta shimfid'a masa a gurin da yakan zama a duk sailin da ya kawo musu ziyara,sannu take ta jera mishi har ya cire takalmansa ya nemi guri ya zauna da bismillah a bakinsa,yayin da Inna ta juya ta d'ebo masa ruwan randarta me sanyi a kofin silba ta kawo ta ajiye a gabansa kana ta durk'usa har k'asa ta gaisheshi ya amsa cike da kulawa da soyayya kana yace. "Hala uwata ba ta gidan nan?" "Taje nan gidan Hari ta anso awara,jiya da zazzab'i ta kwana ta kasa cin abinci,shine na bata hansin ta anso awara da kunu ko zata iya ci." "Haba ko da naji,tun da naga ba azo tarb'ata ba nasan ba ta nan,Ayya ashe ba taji dad'i ba?shiyasa Gwaggo (Matarsa da ya aura bayan rasuwar Inna Halima)tace mini yau ba ta biyo daga makaranta ba."
"Wallahi kuwa,anman dai da d'an sauk'i."
A dai dai nan Inna Hajara ta fito suka gaisa da Malam,ya amsa mata cikin kulawa had'e da tambayarta yara,sai ga Rahin ta shigo da hanzari ta k'araso gurin Malam ta kwanta a jikinsa had'e da fad'in. "Baba Malam" "Uhmmm,Uwata,ya jikin naki?" Ya fad'a yana shafa wuyanta yaji babu zafi. "Naji sauk'i Baba Malam." "To maza gyara zamanki ga gurasa da nama na kawo miki,har da fura." Baki ta washe cike da farin ciki ta gyara zamanta Inna ta d'auko kofi ta juye mata furar a ciki bisa Umarnin Malam,shi kuma ya bud'e mata ledar nama da gurasar ta hau danna lauma kamar ba mara lafiya ba,ta ma manta da ledar awara da kunun da ta ajiye a gefenta saboda taga masoyinta nama,Sale da Mubrak da Kabiru ne suka shigo,suka tisa Rahin d'in a gaba da kallo,Mallam ya d'ad'd'auka ya basu kafin Inna Hajara ta fito ta korasu d'aki tana zaginsu,ko d'aga kai Malam baiyi ya kalleta ba sai hirar su da suke ta yi da Inna Rahin na kora furarta bayan ta gama cin naman.
"Ina sonka Baba Malam,ina jin sonka sama da na Baba,ni dama kaine ka haifeni wallahi." Ta fad'i hakan bil hak'k'i da gaskiya har cikin ZUCIYARTA "Nima ina sonki Uwata sosai da sosai,Allah Ubangiji ya nuna mini auranki anan za'a ga soyayya." Rufe idanuwanta tayi alamun jin kunya kafin tace.
"Ai Inna tace ba za tamin aure da wuri kamar Yaya Halima ba sai nayi karatu sosai." Tana kai k'arshen maganarta Baba da Idi da Kabiru suka shigo,sun dawo daga gona,jin muryar Baban yana sallama su sale suka fito suna masa oyoyo yayin da Rahin ma ta shiga ayarin 'yan masa oyo yo anman haka ya tureta daga jikinsa alamun ba ya so tazo kusa da shi,gurin Malam ya nufa ya durk'usa yana gaisheshi,yayin da ya amsa masa a sake,kafin suka d'an tattauna game da aikin gona.

"Malam, 'yan bindiga fa sun kuma kawo hari k'auyen dake kusa da mu,kuma ana rad'e rad'en k'auyen nan zasu kawowa hari na gaba shiyasa nake k'ara rok'anka dan Allah mu tattara mu koma birni."
"Tun tuni na gaya maka,babu abinda zai saka na bar mahaifata,kuma kaima ban aminta ka bar garin nan ba sai dai idan har bana numfashi,ka saka a ranka duk wanda kaga ya mutu lokacinsa ne yayi."
Jinjina kai kawai Baba yayi,anman Allah na gani k'auyen gaba d'aya ya fita a kansa kawai dai dan ba yadda zaiyi da mahaifin nasa ne.
"Hajara kuje d'aki ke da yara zamui magana." Cewar Malam kafin ya kalli Rahina ma yace. "Uwata kema jeki d'aki kici gaba da shan furarki." Ran Inna Hajara babu dad'i ta shige d'aki yaran suka bi bayanta,dama dawowar Baba ce ta saka ta fitowa bacin haka tasan Mallam d'in ba ya maraba da ita ko kad'an. (A cewarta ba)

"Ahmadu ....

09037093702
[9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBE'ARTH

2023

Wattpad@Rashuna
Mama Jiddah
Heenah
Silar soyayya
Masoya
Rabee'ah
Babbar Cuta
Muguwar surika
K'addarar Rayuwarmu
Cikin Duniyarmu500
Katanga500
Cin Amana500
Wadjda500
Halittar ZUciya500
Compleet guda hud'unnan ga masu buk'ata zan iya baku a 1500 da kuma samun damar karanta HALITTAR ZUCIYA KTAUTA.
Ban yadda a juya mini littafaina ko wata siga ba,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani.

HALITTAR
ZUCIYA
Chapter 3 · 0% Book details