Sashe 11
Halittar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A k'aida kullum aka tashesu daga makaranta sai ta biya ta gidan Ya Halima,a k'ofar gidan suke rabuwa da su Bulki,su huce ita ta shiga ciki,to yauma hakance ta kasance,da gudu ta manna tayi cikin gidan kawa wacce aka biyo a guje,da ta daki wata buta dake babban tsakar gidan ba ta sauka a ko ina ba sai a gadon bayan Innar Audu (Surukar Halima)da ta tsuguna tana hura hutar iccen da ke ta bata wuya,a fusace ta d'ago dan ganin wanda ya jefo mata butar sukai ido hud'u da Rahin tana shishshigar da ido ciki sai kuma tayi murmushi ta bagarar kafin tace.
"Innar Audu me kike dafa mana ne." Dan haushi da takaici ba ta san sanda bakinta ya bata amsa da "Innarki Mariya nake dafa muku,dan tsabar rashin kunya ki jefon buta,sannan ki tsareni da k'ananun idanuwanki kina tambayata me nake dafa muku,to uwarki Mariya na had'a da yayarki Halima nake dafawa."
Turo baki gaba tayi kafin k'asa k'asa tace."Wannan mitsitsiyar tukunyar taki ai tawa Innata kad'an sai dai wannan tsililin mijin naki me kama da sandar rake,dan shi kam cif tukunyar zata amsheshi har da sarari" "Me kike cewa?" Innar Audu ta tambaya dan ganni bakinta yana motsi,sai kwa Rahin cewa tayi. "Ca nayi da kwa kin samu tsoka ba kamar k'yamushashen mijinki ba da motsatstsiyar Zuwairarki "(Itace Autar Innar daga Audu sai ita)
A harzuk'e Innar Audu ta d'auki muciya tayi kanta,da ta manna a guje tayi sashen Halima.
Halima kuwa tana can da d'an Audunta,fad'a suka yi da faccalarta ta mata gorin haihuwa shine take ta kuka shi kwa ya saka kayarsa a d'aki yace yau ba inda zashi sai sunyi cikin a yau yau d'innan.(To Malam Audu zafin nema ai baya kawo samu da yana kawo wa da mutane da yawa ba su jiggata ba,samu da rashi duka na Allah,Allah ka bamu zuri'a tsarkakakkiya.)
Jin yadda aka banko k'ofarsu aka shigo da mugun gudu yasa Audu hantsilawa gefen gadon yana k'ok'arin shigewa k'ark'ashin gadon,Halima kuwa cikin sif take k'ok'arin shigewa tsabar razana da kad'uwar da sukai babu wanda ya tsaya suturta jikinsa,duk a tunaninsu 'yan bindigar da aka ce suna harin k'auyansu ne suka shigo,a tsakar gidan ta tsaya tana rarraba idanu ,dan Inna ta hana ta afkawa mutane d'aki kai tsaye.
"Yaya Halima" Ta shiga rattaba mata kira,jin muryar Rahina yasa Halima sauke ajiyar zuciya da fasa shiga cikin sif din da take ta k'ok'arin yi,zani ta janyo ta d'aura,tana kallo Audu ma ya ja rigarsa yana maidawa,kallon Rahinan take cike da takaici kafin ta hauta da fad'an shigowa a gujen da tayi,sai cewa tayi." To ba Innar Audu ce ta biyoni da muciya ba" "Hala b'arnar da kika saba yi mata kikai mata?" "To ba ita bace daga tambayarta me take dafa mana tace Inna da ke take dafawa ba shine nace..." Saurin katseta Halima tayi,sanin cewar Audu yana jinsu,kuma tasan ba abu me dad'i Rahinan zata fad'a ba.
Fitowa Audun yayi yana.
"Kaga k'anwar matas,tafi matas kyau,duk da ba haka naso ba,amman haka dai nake maleji,dama can rufa ido aka mini"
Wani dad'i ne ya kasheta dan daga Baba Malam sai Innarta sai Audun ne kawai suke cewa tafi Halima kyahu,kowa sai dai kiji yace Halima ta fita kyau, Inna kwa cewa take a jira aga girman Rahinan tata musamman idan ta nutsu guri d'aya.
"Allah ya bar mini Yaya Auduna,anman da ni zaka tafi Habujar ko?"
"Ai k'afata k'afarki matas,dole naje da ke na sanya ki a makaranta mai kyau da inganci,Allah dai yasa Inna ta bamu ke."
Wani ihu da tsalle ta daka tana murna kafin tace.
"Zata baku mana,ai Inna tana so nayi karatu sosai,tace baza tamin aure da wuri kamar Yaya Halima ba."
"To ya zaki da saurayinki Tanimu?" Ya fad'a cike da tsokana. "
Cif wa zai auri wannan k'azamin gaja da shi? Nidai na tafi gayawa Inna da ni za'a Habuja."
Ba ta jirayi cewarsu ba ta manna a guje,tayi ball da tukunyar Innar Audu ta kife akan murhun ta kashe hutar da ta bata huya kafin ta kama anman ko waiwaye Rahin ba tayi ba ta fice,Innar Audu ta shiga sababi da masifa har sai da Halima ta kuma hura mata wutar ta mai da mata da tukunyar a ranta tana ta adduar Allah ya shirya musu RAHEENAH.
09037093702
Sa k'amshi sa dad'i,hana gafi k'arni no,spices da curry kenan gangariya gurin k'awata girki.
09037093702
Ina macen da girkinta ke k'arni idan tayi amfani da nama,ina macen da ke son amfani karafish tana tsoron k'arni,ina kuma macen da rashin albasa ke hanata soya k'wai,ina macen da take son girkinta ya k'ara dad'i da d'and'ano da kuma k'amshi?maza hanzarta ki nemi spices d'in Rashuna domin kuwa nata ba irin nasu ba ne.09037093702
Mata da dama idan suka soya kifi zubar da man suke saboda gudun k'arni,abinda kuma ba ku sani ba kun zubar da sinadarin ki kelaya abinki Hajiyata,ki kawo curry da spices d'in Rashuna ki zuba,Hmmm na rantse miki da Allah mityarki ba za tayi k'arni ba.
[9/18, 2:59 PM] Mtn Number: BEBEE'ARTH
HALITTAR
ZUCIYA.....
Watpad@Rashuna
Mama Jiddah
Heenah
Silar Soyayya
Masoya
Rabee'ah
Babbar Cuta
Muguwar Suruka
K'addarar Rayuwarmu
Cikin Duniyarmu500
Katanga500
Cin Amana500
Wadjda500
Halittar Zuciya500
Hak'k'in Mallaka.Rabee'ah Shu'ayb Nababa (Rashuna,Bebee'arth)Ban yadda a juya mini littafaina ba ko ta wata siga,duk wanda yaci da gumina idan ban gani ba Allah yana gani.
(5)
Da gudu ta shigo cikin gidan nasu,wanda ba ta kula da redion Baba da ke tsakar gida ba tayi gaba da ita ta ragargaje a gurin dama redion ba ta kirki ba,gefe ta ja cike da tsoro tana shishshigar da idanuwanta ciki,kafin hantar cikinta ta kuma kad'awa jin muryar Baban daga d'akinsa yana. "Kai waye nan ya tab'an radio?"
Inna Hajara ce da ke durk'ushe gaban murhu tace. "Wa ka sani banda mahaukaciyar 'yarka" A harzik'e ya fito ya kalli radion dake yashe a k'asa a ragargaje ya d'ago ya kalleta tana ta raba idanuwa,kwalfa yayi ya koma d'aki ya zaro wayar radion ya fito,wayam ya tarar babu ita ba alamunta kallon Inna Hajara yayi had'e da tambayarta.
"Ina Rahin d'in take?" "Ta fice"
Ta bashi amsa,k'wafa yayi had'e da fad'in. "Zata dawo ta same ni ne"
"Idan ta dawo ta sameka dan Allah kada ka barta da ranta,ina ba Sale ne ya lalata radion ka zauna ka gyarata ba ko dunguri ba kai masa ba sai ita da yake tsintarta akayi ba haihuwarta akai ba?" Cewar Inna da fitowarta kenan daga band'aki takaici yasa ta yin magana ta yadda ko yaushe yake nuna yafi son 'ya'yansa maza a kan Rahin d'in. "Ke ni kike gayawa maganar banza,idanma na kasheta ai na kashe banza da ita da babu duk d'aya suke a gurina wallahi,ki bar tunk'aho da Malam,dan wallahi ba shi zai hana na ci miki mutumci ba." D'aki Inna tayi shigewarta ba ta saurareshi ba tana jinsa yana ta sababi a tsakar gidan,dama bata tanka mishi yau dinma kuskure aka,samu.
Har yamma Inna na zaman jiran shigowar Rahin shiru kike ji,ga babar Salima ta kaho k'arar Rahin d'in wai tana saka Salimar sato mata kud'i tazo makaranta su kashe,hak'uri ta bata anman da cewar ba musu tayi mata ba tunda ba'a shaidar 'ya'yan yanzu,in Rahin d'in ta dawo zata tisota suzo nan gidan duk inda matsalar take za'ai maganinta,to anman gashi har yamma Rahin d'in shiru ba ta dawo ba,duk inda take tsammaninta taje ba ta nan,gidan Halima ne hop dinta na karshe anman kuma ta rasa wani yaro zata aika.
Itakwa Rahin tana can gidan Halima,kamar yadda Innar take tsammani,tsoron dukan Baba take tunda har yau ba ta manta dukan da yayi mata shekaran jiya ba,shiyasa tayi zamanta gidan Haliman,idan taje gurin Innar Audu ta isheta da fitina ta koreta sai ta koma gurin matar wan Audun can ma in ta korota sai ta dawo gurin Haliman,to itama Haliman ba tsira tayi ba kawai itama dan ba yadda za tayi da ita ne,daga k'arshe dai cewa tayi ta tashi ta rakata gida,ita kuma ta botsare ba inda zata sai da ta bata naira ashirin kana ta yadda suka taho,uniform d'innan nata yaci k'aniyarsa ya fita daga hayyacinsa.
Halima gaisawa sukayi da Inna kawai ta juyo,dan ba ta k'aunar su had'u da Baba ya koreta ranta yana matuk'ar k'una da suya,sai da Inna taiwa Rahin wanka ta shiryata kana ta sakata gaba da tuhumar ita ke saka Salima na sato kud'in Innarta suna kashewa? Sai da tayi rau rau da ido kafin tace.
"Wallahi cewa take Innarta ce ta bata,ni kuma idan naje da waina sai muci tare mu kashe kudin tare."