← Book details Haka Nake Sanki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Haka Nake Sanki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rahma mutunce mai surutu ga jaye jayen kawaye hakan yasa tai suna sosai tasan mutane suma sun santa anacewa sai hali yaxo daya ake abota tanan dai xan iya cewa ba hakaba dan jininsu kawai ya hadu da khadija anman ta ko ina sun banbanta.

Yanxu dan Allah kin kyauta kenan kawai kinsa naxama makaryaciyar dole kinsa nace bansan gidanku ba yanxu kuma sai kice nace masa ba'akafe dakeba inya ganki fa baxai ganniba xanyi duk yadda xanyi karya ganni haba kadija aikece sai kace mayya nace kidaina xuwa Aminu kano kinki harsaida kuka hadu naji yawwa ya batun jamb din haryanxu kinasan yi eh kuma inkikayi xakibar nan indai nasamu abinda nake so gaskiya xanbar nan wayyo xanyi missing dinki tai dariya suka cigaba da hirarsu...

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Af Rahma ban fada miki ba Allah ya amsa addu'ata ranar asabar xanyi jamb kinga baxanyi fashi ba kai anman natayaki murna ina suka kaiki cas ai bama sukaiki da nisaba eh wallah kinga da kina da waya ai da sai ki fadan result kan muxo sch uhum banni da batun wayar nan.

Kinga yunwa nakeji dan xoki rakani na sayo rake wa to inbake ba da waxance gaskiya baxani ba kina kallo anjima mai family health xatai test ban iyaba karkije din ta fada tai ficewarta.

Yawwa na sittin xaka yankan mai xaki ba tsoloba yai dariya kai gashi banida canji bata kudinta xan baka gaba daya suka juya inda sukajiyo muryar shikenan asirina ya tonu wannan mayen yagano ina makarantar nan yasakar mata murmushi tadan dauke idonta daga kallonsa a'ah nagode kabarshi Allah baxan baeshiba ba kyau maida hannun kyauta baya inji tsohuwar datake saida gurasa to shikenan iya xan karba danke tajuya nagode bata kara uffanba tai ciki.

Tansan fadawa rahma but tasan intafada mata ta banu dan haka tai gum da bakinta malama ki aje karatunnan musha rake nace miki xan shane to kinsan baxakisha ba aida daxan tafi saiki fadanko yi hakuri duk na rikice ne Allah ban iya komai a wannan topic dinba nidai kixo musha bansan bayani nace banasha kawai inje ana test indinga tunowa da xakin rake nakasa rubutu Allah yashiryeki rahma in ana neman sarkin shirme anai meki eh naji ni yimin shuru kisha rakenki karta shigo.

Hajiya kadija yau kuma kasuwar rake aka bude umar kenan insha xakai ai gwara kafada tunkan yajare waki banxa xansha saidai in va'abanba ni na isa inma rowa harkiyi yawa wai kuwa ina abba uhum abba yana nan ko jiya saida yace na gaidaki shine baka fadanba wato saidana ma tambayake ko ai yanxu xuwanda nai da niyar sanarki nai eh mana haka xaka ce am serious fa to naji kace ina amsawa yanxu kuwa yana ina abban shakali yana Germany kace abba anwaye lallaifa abvah anwaye aikece kinki rike waya da kina da ita ko dan charting dinnan akeyi ana gaisawa kayya barni da chart dinnan bata lokacine ke komai bata lokacine nura da yaxo wucewa inbakai sa'ama tace hirar da kukema bata lokaci bane tai dariya yanxu nura harda kai ko yai mamaki ashe tasan sunansa yatsaya suka dan taba hira kafin ya bar gun.

Nayi xuciya da gorinnan naku xan dauko wayata haba ko kefa rahma ta dago ta fadi eyye yar gari wato daman kina jinmu inji umar tai dariya kudinne in akace xa'a biyemuku sai kubar mutun kubaro kuje ku hadidiyo littattafai mukuma ku hanamu namu yai dariya haka kika ce ko eh xan rama ne.

Karubutan number din abba innaje gida nadauko wayar xan kirashi in hado datawa ya fada kajika kaida kullum ina ganinka eh anman sekin ga dama kike kulani ba sha'afa nake eh haka dama xaki ce.

Abba shine mutun na farko cikin maxan sch din data saba dashi haka kawai takejin yaron aranta baxai wuce sa'anta ba inma tagirmeshi ko ya girmeta baifi taxarar shekara guda ba abba yarone mai faran faran da san jama'a ada bata shiga sabgarsa duda yakanxo susha shirmensu da rahma salonda yadauka yasa take shiga sabgarsa ita mutunce maisan xaman gaba sannan bata san kujera mai babararren baya dan haka take xuwa da wuri ta dau kujera ta sa'agaba in an fita break saita dawo taga gu wayam duda ta aje littattafai ahankula tagane mai daukewa ashe abbane ta fiskanta shi kuma salon nasa tsokanar a haka yake tun tana xuwa da muxurai ta karbo abarta harsuka saba yaxama kafin taxoma ya tarar musu ita da rahma danshi ba gwanin xaman gaba
bane saboda baidan sch din waje yake dan fita. Lokacin da exam ta fito ma watansa guda a German duda kuwa hardashi awadanda suka ci.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Sannunku ta fada gami da tayar da sallarta Amina ce kawai tasamu damar cewa da ita yawwa yayinda yusra tace ni narasa me mutane sukeji insunyi girman kai zainab tace shi mutun badan kowan kowaba anman saiji daikai waishi mutum takamarsa yanada kokari da kyau kyan banxa kyan daba asali inji maryam Allahko ehmana ku vanda abinku kuntabajin inda mutu mai asali yake bearing sunan mum dinsa kumafa hakane da uba ake ado ahtoo kudaina damuwa dan anai muku girman kai mutum mai kashi a gindin suka saka dariya gaba daya tanajinsu tabidar da sallah dinta tashafa add'a tabar masallacin yawwa mujeko rahma suka bar sch din.

Towo yau kuma bayero aka tuno kenan me kagani gani nai jaxo nan kai xamanka yaushe rabonda naganka anan ai tun muna bayero inmuxo practical kai dai barni inacikin tension name fa walkahi wata yarinya na hadu da ita cikin daliban nurses tayi mugun tafiya da tunani gashi duk yadda xanyi inyi taki fuskanta ta kai ko gidansu taki bani dama naje to saita baka dama kawai kaje watakil ma ganin bakaje ba yasanya take ganin wasa kake innasamu fuskar sanin gidan nasuba kawatta xaka samu tama kwatance itama kawar taki lallai naka wasane sai kace ba mubarak din dana saniba kaga malan inxaka ban shawara kawai kaban tobama nanba kana ganin maryam xata yarda kamata kishiya ka cika shirme wallahi karma ta yadda aini nake aurenta ba ita take aurena ba hakane fa maxa kasan me xakai ka aro mashin dan karka dauki motarka su bace maka kaje bakin gate din dasuke fita insun hau abin hawa kabusu ka gano gidansu give her a surprise visit nasanka ka iya love a hankula saidai kaga tana ni imba mubarak ba se rijiya suka sanya dariya.

Shawarar nan takafa tayi malan wai maiyasa tun farko banyi wannan tunaninba hhhhh so ya tushe maka tunani kaifa kafiya shirme kaga nasan yanxu sun kusa fitowa toma mashin din waxan ara ka ari na masinjan ka kakuma kawo shawara.

Yaiko sa'a bayan ansauke rahma har kofar gida aka sauke khadija yaji dadi sosai saida yadan jima a kofar gidan kafin yatafi dan vayasan ko banan ne gidanba tunda yasan yan makaranta kan biya aike saida ya cikawa haruwa tankinsa da mai kafin ya koma.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Wayyo gaskiya natayaki murna sosai wallahi nagode sosai nima yanxu yaushe xa'afara admission kai da saura kedai ki tayani addu'a Allah yasa subani to shikenan karki samu damuwa suka koma wata hirar yawwa na dauko wayata gata ki rubutan number dinki wow daman haka wayar take anman kike yawo kamar baki da ita uhum kedai bari inna dauketa ne ina tunawa da abubuwa da dama shiyasa ma ta fita a raina nidai gaskiya wayar nan taki tagama tafiya dani Allah ko eh mana kona bar mikine hhh khadija kenan wannan ta manyan yara ce dake ta dace ke manyan yara fa na nifin yan iskan jami'a ke kuma da fassara abu ba haka nake nufiba.

Wai khadija taxo jeka kace tana xuwa wayyo umma dan Allah ni basai najeba kinga khadija bawai shawaraeki na nemaba umarni ne in kuma ban isaba to batasan batama ummanta rai dole tai abinda tace haka ta xari hijabi ta fice.

Yana ganin fitowarta yaji wani dadi ransa dan yadauka baxata fitoba dake yana cikin mota bata kaiga fiskanto ko wayeba saida yaga tadan tsaya sannan ya bude ya fito aiko tana ganinsa ta hade rai yadan saki murmushi khadija ina yini akasan makoshi ta amsa kafin yafara bayani adan takaice ya mata bayanin kansa sunana mubarak mahfux gami da abinda ya kawoshi tadan kalleshi nagode sosai da nuna soyayyarka gareni saidan inaso kataimaka ka fiskanceni ada nataba soyayya saidai ayanxu babu ita atsarina dan Allah kabarni nagode ta juya xatai gida taku daya biyu taji muryarsa na fadin kitaimaka kiban dama xan xame miki farin cikin daxakiyi alfahari dashi xan goge miki dacin bakin cikin dawanda kikaso din yasanyaki tajuyo gamida murmusawa da'alama na bakin cikine uhum bakin ciki innace naxir yasanyani bakin ciki banma kaina adalciba soyayyace nace banai tai shigewarta gida oppp yafadai gami da dafe goshi dakyar yabar gurin yarasa meke damunsa.

Lafiya kuwa naganki yau duk rai abace tadan dago ta kalleta ta cigaba da rubutunta batace komaiba haba kadija in wani abin nai miki basai ki fadanba anman ai baidace ba kixo kina ta wani kunbura nanma batace uffanba bakuma ta dagoba ta cigaba da abinda take haushi ya ishi rahma tako kwace biron kinga malama bansanfa wulakanci taya inai miki magana xakimun banxa au ke garkinsan wulakanci ba dadi kikaimun me nai miki ta koma ta xauna sai hawaye ganin haka yasa rahma komawa itama taxauna kifadan me naimiki xaman tare bashine karike mutun ranka dan yai maka laifiba.

Yanxi rahma kin kyauta kenan da kika fadama wannan mutumin gidanmu ta dafe girji ni khadija wallahi bani bace to waye inbakeba ke kadai kikasan gidanmu haba khadija ki yarda dani mana wallahi bani bace ki taya xandinga rantse miki kan karya dan kawai inasan xama dake kijedai kiyi bin cike ta mike tabar gurin.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u
Chapter 8 · 0% Book details