← Book details Haka Nake Sanki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 14

Sashe 11

Haka Nake Sanki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yawwa na kiraka ne inasan daga yau karka sake daukarmin diya xuwa koma inane xan sami maikaita hajiya sabida me sabida nace ka saketa kaki dan Allah hajiya kiyi hakuri akasi aka samu ada kasani bana mgn biyu dan haka indai har baxaka xo min da maganar sakin yarinyar nanbq inasa kadena min maganarta kaji ko.

Duk yadda jafar yaso sha kan hajiya abin yaci tura dan kamar kara tunxura ta ma yake gashi ta hanashi ganin khadijar inyaxo falon inxeyi awa nawa baxai ga khadijanba makarantarma besan lokqcin datake tafiya ba.

Yau kam ko aiki yace baxai jeba sai yaga khadija duk yadda xai seyai yasa tacema hajiya akaita gidanta duda itama yarinyar bata taba nuna masa shidin mijin tane ba

Yana farfajiyar gidan gindin bishiyar mangwaro ya hangota tana fitowa tai kyau sosai wani kishi ya rufeshi ace matarsa ce xata makaranta cikin wannan adon duda ba shigar banxa taiba yama manta da abinda yaxaunar dashi afusace ya mike yai inda take tana ganinsa ta fadada murmushinta yah jafar ina kwana be amsaba yahau fada yanxu wannan wane irin abu ne xaki sch kinsan da maxa anman xakiyi kwalliya haka yah maine aibin wannan shigar haka ma xakice dan kin rainani to wallahi inkinga kin fita to saikin sauya kayannan shigar tai murmushi batace komaiba ta koma ciki mama na kallonta ta shige daki bakar riga ta sako sai hijabinta iya gwiwa Golding kalar adon rigar sai takalminta shima golding tai kyau koda ta fito mama tace sekin makara ko wadancan ne naga sunmin wani iri koda yaganta gani yai ta kara kyau fiye da daxin yai tsaki kawai ko basuyi bane suna a'a sai kin dawo tana fita yashiga gidan yana kunbure kunbure kai kuna lpy dan Allah mama kina kallon yarinyar nan take kwalliya wajen xuwa sch eh lallai daman kai kasa taxo sauya kaya aida ta fadan wallahi baxata sauyaba.

Abin duniya duk ya ishi jafar dan haka ya yanke shawarar xuwa yasamu yayan babansu yasanar masa mai makon yace wani abu sai dariya kawai yai jafar kenan watakil basu gama shirinsu na mata bane tunda kaga ai auren ba shiri akai ka kara basu time.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Abu kamar wasa karamar mgn ta xama babba dan jafar ko aiki ya dena xuwa duk ya fada tun mama bata damuba harta yake shawar gwara tabashi matarsa karya cutu.

Iya shiri da gyara duda wanda khadijan tasha baya haka mama tai mata bilkisu da safiyya sai matan abokin jafar biyu da maxajensu bayan yayar mama taxo tadauki khadijan suka tadda agidan saida inna ta dawo sannan mama ta shiga bangaren jafar din yana xaune saman kujera idonsa arufe tadan tabashi ya bude ido mama kece eh nice takalli gebensa kwanukan abincin datasa akawo masane da'alama ko kallonsu beba balle yaci yanxu kai haka xaka xauna baxaka ci komaiba banajin yunwar ne ai shikenan xuwanai naga ganin kadija dakake ke kara hanaka yin abinda nace nasa duk kayanka an diya ankai gidanka na sultan inaso kai wanka kaxo kakoma can ko kasamu ka war ware yadan kalli mama baice komai ba be kuma motsaba wai badakai nakeba ne ya mike yashiga bayi jika jikarsa kawai yai yafito ko mai bai shafaba ya xura kayansa yarasa me yasa mama takasa fuskantarsa ko ganin halin dayake ciki batai sema korarsa daxatai har ya kai kofa dauke da jakarsa yaji tace kamanta vaka karbi mukullinba ta mike taxo dab dashi ta danka masa yakarba Allah ya karo sauki yace amin mama aransa yana cewar komai xa'ai wallahi baxai saki matarsaba.

Yajima a cikin mota koda ya shiga far fajiyar gidan nasa kafin yashiga gidan yana budewa salim da abbakar sukaxo tararsa yai mamaki to sukuma wadannan yaushe suka shigo wama ya bude musu tunda dai shi yasan mukulli nagunsa ango ango wato saima yanxu kaga damar xuwa ka shirgamu ko yadanyi tsaki wane ango anhashi amarya suka saka dariya salim ya jashi xuwa falon safiyya ta taso yaxaku shigo dashi ba vayani aiko da sauri tai dakin da dja ta shiya yanxunnan ta kullo ta dawo inda suke ai inkunga yaga amaryar nan to kuwa mun kayyade ciniki aikodai se an biya kudin baki inji matar salim anji nawa kuka mata kudi bilkisu tace kunsan amaryar tamu tadabance dan haka dole abiyamu da tsada kufa matsalane matannan kunfiya san kudi inji abbakar inbaku biyaba sai mudau abarmu mutafi hakadai kudi kudi to kaji ango ni kunga ko nawane kubasu kuhada matanku kubarmin gida iyye haka ma xakace wallahi kai wasa semu kwana nan what aiko da kare xan sanya yai waje daku suka saka dariya.

Yar karamar walima suka hadama ango da amarya ta kayatar sosai wajen takwas suka bar gidan yaxama daga ango sai amarya bayan ya rufo kofar gidanne ya tsaya yana godema Allah wai yaushine gida daya da khadijansa yasani mama ta gama masa komai baida kamarta.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Tana xaune kamar yadda ya xata yai sallama ta amsa masa asanyaye har ka dawo eh wallahi yadan xauna kusa da ita khadija ya fada ta dago ta kalleshi kafin ta dauke idonta bakiyi farin cikiba ko dame da aurena tai shiru nasani mamace ta takura miki ko tai shuru nasa me kike tunani me nake tunani tace ki tunanin an min auren dole ko an aura min ke bana sanki ko tai saurin kallonsa kamar yasan hakan take tunani yai murmushi na canka inasan kisa aranki kasan tuwar bamuyi soyayya va kasantuwar bansan da batun aurenmu ba kasantuwar ban taba cewa inasanki ba bashi yake nufin ban sanki ba tun bayan rasuwar kanina nake tausayinki ban gano na kamu da sanki ba saida na koma lokacin dana gano kedin mama ta auramin nai farin ciki farin cikin daban taba yiba arayuwata kisa aranki ni maisanki ne xankuma soki har rayuwata aduk tsanani karki sanya asalinki a matsalarmu hakan bai xama komai ba gare ni takalleshi dagaske kana sona inasanki nasan nan gaba xaki yadda da haka.

Khadija kam tasani tai sa'ar miji mai santa mai kula da ita duk inda ta motsa yana biye da ita makaranta adole yake barinta gun aiki dakyar yake iya fita itakam ba abinda xata ce sai alhamdilillah burinta ayanxu bai wuce dai daita ummanta da kakanta va fuskantar hakan yasanya jafar yadaiki aniyar tayata cimma burinta.

Tun bayan rasuwar matar malan tukur lokacin baxa wuce aji biyu a primary ba rabonta da unguwar yakasai yau ta gudiri niyyar xataje komai xa'a mata kuwa sai taje.

Adai dai kofar gidan ta parker motarta yana xaune kamar yadda yasaba xama bai kawo komaiba game da motar ta sauko ya bita da ido bai fiskance taba taxo gefen tabarmar da yame xaune taxauna abinda ya kara bashi mamaki kenan tagaishe shi ya amsa fuska ba yabo ba fallasa baba baka gane niba ko eh kimim karin haske tai murmushi kafin tace dan Allah baba kamin alkawarin komai baxo ma dashi vaxaka koreni ba yai dariya inbaifi karfin hankalina va nan tafara masa bayanin kanta kafin daga karshe tace nice khadijar jikarka ta wajen saliha da mamakinta taga ya fadada murmushinsa yarinya kifadan gaskiya wallahi baba da gaske nake yanxu to ina ita uwattaki ki tai maka kikaini gunta inasan naganka ta yafemin konasamu sassauci ga abinda nai mata ita da babarta itama ta mike kaya hakuri baba batasan baxo ba xan kawota ita yakamata taxo bakaiba yaja hannunta sukai cikin gidan daki daki ya nunata duk inda sukaje sai tamusu alkairi bayan sun fito tasa aka sauke kayan data yo musu tsaraba.

Umma kimin afuwa nai miki wani laifi kadija ta fada maisunan manya komai kikai min na yafe miki umma naje gun abbanki me kikaje gunsa mutumin daya koreni akan naki kaahe ki haba umma kiji tausayinsa mana mahaufine fa kema kin haifa inji abban khadijan da ya shigo yanxu kiyi tunanin halin daxaki shiga in akace yau khadija ko su mubaraka sun haifi da va aure shima fa haka yaji anji yai kuskure anman bakiga yadda yake san ganinki ba ba tun yauba duk inda yasan xai ganni xuwa yake kanna kawo shi inda kike naki kace kawai kana bin bayansa wato gori xaka min ko haba saliha aikinsan ko labari aka baki nayi miki gori kyace karyane ai gwanda sakace lbr ynx agaba na kayi fuuu tabar dakin khadija ta durgushe tana kuka.

Shiko tsohon tun xuwan khadijan yake xuba idon yaga dawowarta anman shiru gashi har andoshi sati har ya cire ran dawowarta katsam yana xaune adakinsa yaji talatu na buga salati saliha dagaske ke nake gani da hanxari ya fito ita dince aiko kan kace me wannan duk matan gidan an fito yajata daki khadijan ma anan yabarta sauran matan nata kallonta ita kuka shi kuka dakyar yai shiru yafara neman afuwarta haba baba nice da lefi ni ya kamata na rokeka afuwa nima ban kyauta ba na yanke xumuncinki da yan uwanki ni baba tuni na yafe maka fatana ka yafemin kadawo dani matsayina na da nadade da dawo dake nadade da gano kuskurena.

Kadija kam tafi kowa farin ciki ganin yadda ummanta taketa nishadinta cikin yan uwanta itama kanta datai shiru xa asata cikin hirar duk sansu nasasu farin ciki su harira da kuka suka dinga rokon umman gafara kan abinda sukai mata.

Kwanci tashi ba wuya yauce ranar farin ciki gun dja domin yau ake yayesu a sch dan sun gama service dinsu ta fita da result mai kyau wato first class su biyar ne a course dinsu duk maxa ita ce kawai mace se masu second class upper da yawa burinta ya cika duda kuwa ita ba abinda take so sama da akirata prop. Tasani inda rai wataran shima mai cikane.
Chapter 11 · 0% Book details