← Book details Haka Nake Sanki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 14

Sashe 10

Haka Nake Sanki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar daga sama taji ana tashinta tadan bude ido taga rahma ce tsaye da katon cikinta tai tsaki ta juya taji ankara tabata taga bilkisu towo yau kuma mafarkin kawaye nake taja bargo wai danta kara jin dadin baccin aiko bilki ta janyo bargon dallah malama tashi xumbur ta mike dan tagano bawai mafarki takeba tasa ihoo yaukamar kun hada baki da sassafennan saiga Aisha ta shigo rike da les a hannunta wayyo wai dagaske ba bacci nakeba watakil baccin kike lokacin da Fatima ta shigo ta fadi haka wai ace amarya guda har goma tana sharar barci ko wanka bataiba amarya kuma mu suka basar ke yanxu haka ake tarar baki immu kina ganinmu Aisha fa yau kimanin shekaru biyar ba'a haduba anman baxaki tashi ki mata oyoyoba kyale mara mutunci inji rahma maxa mike nakai miki ruwa kiyi wanka ta saki vaki tana kallonsu tana wankan tana tunanin meyasa sukaxo atare haka.

Muryoyin datake jiyowa yakara sata hanxartawa ta fito su rukayyane da wasu course mate dinta na bayero kwalliya kam tashata tai kyau sosai ta fito amaryarta sosai ita kanta tasan tai kyau duda ranta ba dadi abinda yan uwan muvarak suka ma ummanta na ranta anman yadda taga kawanta har wanda ta manta dasu nata xuwa anata cafta kamar a sch yasa ta ware taketa warkajaminta itama.

Ke abinki dagwas in an daura aure basai ankaikiba tunda gaki gidansu ango tadan kalli Maimuna kamar yafa suka sheke da dariya xaki gane ne kunga bari naje nagaida mama na dawo ko najiyo dadlilin wannan taro haka auke saida dalili xamu kawo miki xiyara ta fice batare da basu amsaba.

Yadda taga gidan dankam yakara bata tabbacin da dalilin wanban taro kamar daga sama taji maroka na fadin Alhamdulillahi an daura auren kadijatu da angonta jafaru bata kara yadda ba saida taga anata faman fadin amarsu amarya bakya lefi saima yanxu ta tuna yaunefa ranar da tai dai dai da ranat da'aka sanya ta daurin aurenta da mubarak.

Kafin kace mene maxan daurin aure sun cika gida anata hotuna abinda yabata mamaki yan class dinsu da dama sunxo na buk su umarma duk sunzo na nursing gaskiya da'ace tanasan bikinnan datayi farin cikin yadda aka mata kara saida maxa suka dan watse umar yaxo suka gaisa yabata wata leda inji abba yaso xuwa suna exam ne daurewa kawai take dan kadan take jira ta fashe da kuka fuskantar hakan yasa bilkisu janta xuwa daki aikuwa suna shiga ta fashe da kuka saida tai mai isarta sannan bilki tai ta mata nasiha dakyar tasamu tasha kanta tasa tasake wanka takira rukayya tasake mata kwalliya tafito fes tai kyau abinta baxaka taba cewa tai kuka ba.

Ita dai tasan batai gayyaba anman yadda taga kawayenta yabata mamaki tasan bakowa keda wannan aikinba sai rahma bilki da rukayya itakam ba'abinda xata cemusu sun mata halacci dan dabadansu ba bikinma balallai ayishi cikin kwanciyar hankaliba dan yadda inta tuna mijinma sau biyu suka taba haduwa shima bada sunan soyayya va yadda taji ana fade benasan da batun aurenba se jiya itako wane irin aure aka mata wane irin xama xatai da addu'aba.

Haka nake sanki
F.A.Ya'u

Da yanma yan uwansu sunxo gidan tai mamakin ganin yan uwan ummanta takumaji dadi sosai burinta yakusa cika tunda gashi dalilin bikinta har yan uwan ummanta da suka jima da rabuwa sunxo cika kam ancika sosai burinta yadda haihuwarta ta cire ummanta daga dangi haka take san taxama sanadiyar maida ummanta abarso ga yan uwanta.

Washe gari kayatacciyar dinner aka hada duk wanda yasamu xuwa yanada tsarabar smart phone da atampa biki kam ya kayatu ango kawai yai masa cikas sakamakon yana da karashen abubuwan da zaiyi yasa sai wani watan xai dawo.

Ranar lahadi takoma gidansu dan ummanta acan xatai yininta nanma biki akai na alfarma gidansu ba masaks tsinke amarya amakota tai taronta da daddare aka kai amarya gidanta dake sultan road gidane da yagaji da haduwa tsayawa bani bata lokacine kowa ya watse sauran ita dasu bilkisu ra rungumesu tana kuka gami da godiya kunmin abinda kun wuce kawaye kunxama yan uwa bani da bakin gode muku ko kadan bilki tadan dagota dalla mu kimana shiru ance miki dan kigode mukayi ai kin wuce nan wallahi wai ya'akai kuka san da bikin kinsan safiyya duk tasanmu tasan gidajenmu nida rahma taxo ta samemu ita da mama suka fada mana sunasan mugayyato kawayenmu dan ba'afasa biki ba kinsan kin fada mana anfasa nadau nauyin gayyato na secondry dana islamiyya rahma tagayyato na nursing tace xata samu rukayya ta bata kati ta gayyato duk wanda tasan kuna gaisawa a bayaro tabkalli rukayya wato ke kinsan da vatun baki fadanba ko tai dariya ai ance yaxama sirri suka saka dariya safiyya ce taxo lokacin da kowacce mijinta yaxo daukanta sukai sallama cikin kewar juna.

Mamace tace naxo natawo dake sabida jafar sai nanda wata guda xai dawo batasan barinki ke kadai cikin gidannan hankalinta vaxai kwanta ba tai dariya mama kenan bata gajiya suka tawo.

Yau umman khadija tafi kowa farin ciki domin ita da kanta taima diyarta nasiha tasata motarda xa'akaita dakin mijinta mexatama Alkah inba godiyaba.

Khadija kwance kangadonta na gidan mama ta xurfafa tunani tabbas ko jafar baisanta xata xauna dashi kodan karamcin family dinsu xata daure ta xije duk rintsi bayan ummanta da abbanta da basir dinta sai bilki da rahma vataga wanda ya nuna mata kaunar da mamansu jafar taimata va tayadda nazir ba mijinta anman haduwa dashi aikairi ne ga rayuwarta komai taxana sanadiyarsa ne komai tasamu sanadiyarsa ne baxata taba mantawa dashiba baxata taba dena masa addu'aba.

Haka nake sank
Na F.A.Ya'u.

Sanye take da ruwan hanta tai mata kyau sosai ta yafa mayafinta shima kalar rigar sai takalminta mara nauyi rike da jakarta wadda daga inda kake xakaga abinda ke ciki itama tadau dige digen kayan takyau sosai ta fito mama ni xan wuce to sai kin dawo af ban fada mikiba jiya jafar yadawo shima nace yakaiki tadan kalli mamar taga ba ita ma take kalloba to mama yana ina yanxunnan yafita tace kisameshi a mota yawwa mama xan biya ta gidan bilki haba khadija daga aure sai yawo kibari ki kara lokaci danma illimi illimine ai da ba inda xaki dinga xuwa to mama sai nadawo Allah ya bada sa'a tafice.

Tunda ta fito idonsa na kanta har yakasa daukewa yarinyar nan mekyauce ya fada a hankula mama bata kyautaminba datamin aure nasan kowace xata auran baxatakai khadijaba yadanyi tsaki tariga karyan tsari banda tsarin mata biyu but dolema na auri kadija kowa ta auramin danna fiskanci tanasan matar data auran dan yanxuma da yaje gaisheta tamai maganar amarya yafara kunkuni tai xuciya tace ya fita yaba guri. Baima tsaya yaji wace amaryar tasa ba ahankula ta bude motar gami da sallama yah jafar ina kwana baxan amsaba tunda bakixo mun sannu da xuwaba wallahi bansan kadoba amin afuwa toshikenan anmiki suna tafe yana janta da hira sama sama take amsa masa yanxu sauran shekara nawane karatun naku shekara daya da watanni masha Allah gaskiya kunyi sauri nikam naga dadewarmu duk nagaji wallahi yai dariya haka karatu yake kuma xakiyi aiki inkin gama tadanyi shiru na cika magana ko tai dariya sai hakuri to yanxu aurefa yaushe xakiya tadago dasauri ta kalleshi sai na gama ok bakyasan hada karatu fa aure ko eh da wuyane sosai ma tace inda yai dai dai da tsayawarsu inda xata sauka tama godiya ta wuce.

Tun da taxauna take tunanin hirarsu watoma baisan ita matarsa bace ko ya raina mata hankali ne.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Tun daga wannan ranar jafar ke jakaita sch ya daukota komai yaso natane koda yadauko jakarsa tsabarta tafi ta kowa yawa koda hajiya tace ina na matarsa cewa yai se daya jakar taxo tai dariya kawai dan tafiskanci inda yadosa aurenne beso khadija yake so tace dani kake xance.

Yau bayan ya kai khadija sch ya biya ta gidan kanwarsa safiyya tare da tsarabarta tai murna sosai kafin kace mene ancika masa gaba da kayan kwalama saida yaci yasha suka dan taba hira kafin safiyya tace yaya wai yaushe khadija xata tarene wacce khadija kenan khafini saninta Allah ban saniba khadijan yaya nasir mana what ya fada gami da mikewa tadauka ko kishine na kiran matarsa da sunan wani hi hakuri yaya vansan na batama ba no no wai daman khadija nada aure tadan kalleshi gami da shekewa da dariya lallai yaya wai daman bakasan itace matar ba me kikace ta mike tadauko aibin bikin ta nuna masa yakaranta sunansa ne tadaiko jaka shine da khadija jagwab yaxauna na kwafsa yaya mekayi yabata labarin yadda suke da mama kan amaryarsa lallai yaya ka kwafsa keni barni naji da kunyar data isheni bansan daya xan kalli umma da khadija va.

Ya tafiya safiyya ta kira umma ta fada mata yadda sukai dashi tai dariya ai nadade da ganoshi santa yake baisanma tasa bace xan maganinsa.
Kai tsaye gida ya wuce bayan yaci abinci yasamu mama suka gaisa kamar vatasan ya sukai da safiyya va yaxauna yanata xuba mata hira so yake tai maganar amarya taki ita kuma dayaga baxatai ba yace tawwa mama yaushe amaryar xata tare talleshi sheke ke wacce amarya mata ta mana au daman kana da mata yai saurin kallonta aini bansan kana da mataba in kuma wadda na aurama ce ai nafasa jira nake daman kaxo kabama yar mutane takardarta haba mama nifa bantaba cewa bansanta va eh bakace ba anman aika nuna ko inkula dan Allah mama kiyi hakuri Allah insan mata ta nikaga tashi kaban wuri.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Sin sin ya fice daga dakin kai tsaye sch ya wuce dan dauko khadija bai wani jima ba ta fito lah yaya jafar ashe har kaxo yadanyi murmushi eh ke nake jira suka wuce.

Harkin dawo eh mama dake yah jafar ya kawoni au saida yaje kince karyaje jeki kici abinci naga agajiye kike ta wuce daki.
Chapter 10 · 0% Book details