← Book details Haka Nake Sanki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 14

Sashe 12

Haka Nake Sanki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummanta ce ta saida gidanta da filinta ta bata gashinan burina nayi makarantar lpy ko karatu kan lpy na bude pharmacy ashe diyata na cima burin nasani inkin bude ko bayan raina baxakiyi kuka kan rashin abinda xai rikeki ba koda kuwa baxakiyi aikiba ta rungume umman tana kuka tana godiya tasani ummanta tafi karfin uwa kawai saidai uwa da uba dan wani uban vaxai yi abinda take mata ba koda tajema da jafar da batun yafi kowa farin ciki danshi daman bayaso tai aiki shine ya shige mata gaba kan komai inda ta bude katon pharmacy dinta.

Kafin kace mene har ta bude wasu branches din bakuma wai kanana ba harsun fi na farko magani kuwa duk tsadarsa kasameshi a gunta.

Shekaraesu uku da aure khadija tasamu ciki murna gurin jafar ai ba'a mgn aranda yasamu labarin cukin ai duk wanda yasanshi yasan da cikin kai kace har anyi haihuwar dan yaxuma in khadija batace dadyn baby ba bama tako kallonta.nakasa

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Khadija tasani duk wani farin ciki da mace ke nai ma ta sameshi abu daya ya rage mata cikin burinta shine tanasan ganin babanta na asali tanasan kosau daya ne yace yanasanta koda kuwa baxai karbeta matsayin diya va tanasan kosau dayane yau ace itama taga yan uwa daga ban garensa yau ta dauri aniyar komai wuya konai rintsi xataje ta tunkari ummanta da batun abban nata.

Umman na tsakar gida tana wanke wanke khadijan tashigo vayan sun gaisa ne tace umma yanaga kina wanke wanke ina binton tai dariya aini da kuka kawota naga antauyeta ace yarinya karama anbarta se aikatau shi yasa nasanyata a makaranta yanxu tana can umma kenan basai ki bari ta dawoba banda abinki intadawo abinci xataci ta tafi islamiyya intadawo ta gaji tana aiki anman se alhamin juma'a da asabar da lahdi umma kenan kawo na wanke basshi kiji da cikin nan ace haihuwa ko yau ko gobe mutun yana yawo tai dariya umma kenan kigama gurin ki naxo ai nagama ta fada tadauke kwanukan tai kicin taso mushiga ciki.

Suk kara gaisawa kafin khadija tace umma daman xuwa nai kitai maka ki fadan inxa xan samu babana ko wani nasa xumbir ta mike kina haukane ko asharia baki da uba nice komai taki kima cire aranki kinada uba kinji ko khadija tasa kuka ummana dan Allah ki tai maka ko daba xaki yafe masa ba ni kimin ixinin xuwa inda yake na miki alkawari baxan taba cewa kimai a fuwaba umma ki taimaka kodan kar awratayya ta shiga tsakani inda be halattaba ina ruwana tama shiga shine da hakki duk yadda khadija taso umma ta fahinta taki.

Gun abban umman taje tasameshi har gida yaxo yaita mata nasiha dakyar ta yaddarma kadija taje kan sharadin baxata taba kawo mata mansur neman afuwa ba.

Misalin karfe hudu jafar ya sauketa a kofar gidan gidane babba a kofar gidan ya tsaya tashiga yadda taga gidan batai xaton da mutane ciki ba dashi da kango duk daya tai kamar baxata shiga ba ta daure ta karasa taje daf da falon tajiyo kamar hayaniya dan haka ta kusta ta shiga wani ta gani kwance da alama baida lpy sai wata budurwa baxa wuce shekara ashirin da daya ba tana tsaye kansa tana fadin kaga baba ni ba ciyarni kake ba babu ta yadda xa'ai kace xaka hani abinda nake so bataji mai yace ba taji yarinyar na fadin dan kai haifeni sai akace naxama baiwarka ni na dora ma cutar fuuu tayo waje xata fice taci karo da khadijar ba khadijarba harma ita fiddausin saida taja ta tsaya dan bata taba ganinta ba anman kamarsu ta baci dan dai kawai khadija ta girme mata khadijan ce tai saurin riko hannunta dan Allah karki fita ki xo muti mgn inkina da kudin bani ba matsala sena tsaya karkiji komai muje sun xauna ta kamo baban nasu ta kawo inda suke xaune yana ganin khadijar yadan wattsake fiddausi ta mike bari nakira wancan banxan yayanta kenan tana tsaki da fada fada ya fito kasan dai kai baka da matsayin da xanje inkiraka dan bukata ta taxo ta xauna kadija tamasa ya kara ji da jiki sannan ta masa bayanin kanta sai kuka haba ni jiki na yabani wallahi tinda naganki furtawa ce nakasa.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Kuka kawai yake dakyar yai shiru nayi danasanin bin shawarar hamxa na cuci kaina tundaga abinda naima saliha nai sallama da farin ciki gashi har yanxu a dana sani nake banjin kuma xan dena haba baba kayi hakuri kadija kitai maka kice kin yafe min koda naji sassauci a rayuwata nine sanadiyar kawo ki duniya ta hanyar banxa nasa mamarki kuka nasani kema kinyi watakilma kina kanyi koda ita vaxata yafenba ke kice kin yafe ko xanji sauki dan Allah baba na dade da yafe ma ban taba rikeka ko tunanin ka cuceni ba na rika na yadda kaddara tace ahaka da gaske kin yafe min nadade da yafe fatana ummata ma ta yafe maka kayya khadija bantaba tunanin akwai randa saliha xata yafen ba.

Wadannan sune yaya ba fiddausi da ismail kannenki ne su kadai na haifa sin xame min har nake tunanin gwara ace bani da da dadaisu wallahi haba baba addu'a xaka dinga masa basshi duk tsiya baka isa ka koremu ba dan bamu mukace ka haifomuba inji ismail kinga kiban kudin da kikace xakiban dan kin hanani fita nemowa yunwa nakeji kadija ta bude jaka ta kirgo dubu goma ta vata ta baima ismail ma aiko ta daka tsalle ta rungumeta thanks sis ta fice ismail ya bi bayanta dakinyi shawara dani da baki basu ba.

Nayi dana sani mara misaltuwa tun lokacin da nasamu labarin haihuwar saliha naje nadinga xuga babanta dan sanin yadda sukai da bavana babu ta yaddaxa'ai ya yadda nace kedin yatace burina be cika ba na mutuwarki sedai naji dadin korar saliha da babanta yai sedai mai abinda nake tunani xata rasa matsuguni har muje mu kwaceki kamar yadda hamxa ya tsara be yuwuba.

Batafi watanni da aureba na auri iklima auren da be karar dani komai ba sai dana sani tun da na aurota nake danasi har yau bandena ba .

Watanmu tara da aure ta fara laulayi shekara na xagayowa ta haifi danta yaci sunan babana ismail rashin ta idonta tasa mahaifina yakwace ismail ita kuma yace nasaketa haka kuwa akai duda na saketa bamu rabuba mahaifina da kansa yaban yan kanwarsa ita ta haifi fiddausi gurin haihu ta rasu dan haka yarta ta karba tashayar nakasa rabuwa da iklima kaxalika na kada aure duk yadda namaifina yai yayi nanaki aure duda besan ina tare da iklima ba.

Bansan wanda yaje yasanar masa ba be yarda ba dan haka kuwa ya xo dan tabvatarwa ya yarda aikuwa yana komawa gida akace ya fadi iklima ta hanani xuwa xuwa duda kuwa burina be huce naje na ganshi ya yafe minba.

Ita tasanya na karbo yarana muka sake aure mafarar lalacewr tar biyarsu kenan domin kuwa ita kanta bata da tarbiyar balle tabaima wasu.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Bawata sana'a nake ba da mahaifina na dogara shima jiki yaki sauki xara bata barin dami komai na kare takai ansayar da komai nasa dan masa magani babu sauki iklima tace babu yadda xa'ai nasaida gidan da muke ciki baxai yiwuba yayata ce tadauki babana wanda matsayinta na mace ba ita yadace ta daukeshi ba duda kuwa banbancin da yake mana kansu matane komai yasamu nine sai gashi sudin sune suka xama gatansa.

Kwata kwata iklima ta daina ganin girmana bama tajin maganata in nai magana tace ai ni ne matar itace mijin abokaina duk sun gujeni yarana sun rainani babu wanda na isa nace yayi yayi.

Bankara danasanin abinda nai abaya ba sai randa na kama iklima da kato adakina nai kuka nai danasani tun daga wannan ranar cuta taki barina nai magana taci mutuncina tabar gidan.

Ahankula duk wani abin anfani na gidannan su fiddausi sun debe sun saida gidanma sai sun gadama nake ganinsu balle insaka ran xasu kula dani dan yayata muhd ne kawai yake xuwa yakula dani duda iyayensa basu sani ba nasan duk sanda suka sani ranar xan dena ganinsa yaron yanasaona katsam iyayensa suka daukeshi suka kaishi waje karatu naci wuya sosai dan banda mai kuladai baufi wata biyu dawowa ba da akwanaki ne baxaki iya shigowaba domin xuwansa yagyaggyara ni.
Yanxuma dan dare yayi ne daxaki ganshi yaxo bankara firgita da hakkin wani ba sai yadda naga hamxa ya koma wanda har gara ni sau dubu daganin irin mutuwar dayai ta wulakacin alokacin na tabvatar lallai hakkin wani ba abin wasa bane ko ya yafe ma balle bai yafeba.

Baba tare nake da mijina shine bakice yashigo ba tai dan murmushi ai yace xe shigo inyaxo daukata to shikena ta mike dakyar tace ina kitchen yake yanuno mata baxai shigaba yadda yake tsami har wani wari wari yake alamar andade ba'a shigesa ba anbar abubuwa sun rube ciki.

Wayarta tasa ta kira jafar inbakai nisa ba dan Allah kaxo ai ina kofar gidan au kace xaka kadawo fasawa nai tai dariya to shigo shi ya tai maka suka sanya shi mota fa'ams special hospital suka kaishi kasantuwar su masana ga kowa basu sha wata wuyaba aka bashi gado satinsa biyu yawar ware har yana tafiya yana iya cin abinci.

Khadija ce taxaunar da fiddausi da ismail tai tamusu nasiha da kwatanta musu abu buwa na rayuwa hartasamu suka dan fiskance ta tadauki fiddausi takaima maman jafar dan tasan ummanta baxa karbeta ba tamata bayanin komai taji dadi ta jin jina kadijar shi kuma ismail shi yake jinyar abban nasu intaxo shi kuma ya rafi gida dan yin wanktaba.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Yau khadija ce agurin abban nata burinta yamata bayanin inda yanxu kakansa da sauran danginsa suke dan tanasan ta shiryasu tanasan kakan nata ya yafema abvan nata anman yaki saurararta inta takura masa da maganar saima kuka ko ya rufe idonsa kamar me bacci yanxunma hakance ta kasance ya rufe idon kamar mai bacci baisan taci gaba da maganar da take ms.
Chapter 12 · 0% Book details