← Book details Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yauwa kinji dai sunan'ta gwara kema ki faso gari ace kamar ke kina yawo da rakani masai

zaro ido tayi tace

"kai dinana bana son iskanci wato Ni zaka mayar wata bi tacan ko ka kawo min maganar banza yau she taska yayi kuɗin da har zai dinga kasa irin wannan wayoyi masu tsada...?,

Kahu da yake kwance ya tashi yace

"Dinana nima ina son layin nan zan siya...,

zama yayi akan farin botiki yace

"wato kahu baza ka gane amfanin lahiin nan ba sai kira ya kama ka zakai ta magana da shi ba iya ka wallahi ɗazu ba muna waya da abokina nace ya jirani wallahi na gama uzurin gabana sannan na dawo muka ci gaba da waya amma ko girgiza kuɗin nan ba suyi ba...,

tsaki magajiya ta ja ya ci gaba da suyar'ta domin maganar da dinana yake yi bata ɗauke ta a hankali ba tuni wa yanda suke ca'ca suka tsaya da yin ca'ca suna shan labari abin takaici kahu da girman'sa ya tsaya ana zuga mai karya

tashi rabi yayi ya saita zanin da ya ɗaura ya sauke shi karaf suka haɗa ido da kahu da kullum al'ajabin halin Rabi'u yake kiri kiri ya maida kansa mace yau harda jagira da jam baki

da sauri rabi ya juya baya yace

"haba kahu kana kwanci kana kare mana kallo tsofe tsofe dakai kai da zakai wa su fada har wani karkata kai kake kana kallona ni wallahi kunya nake ji....,

sakar baki kahu bulama yayi ya tashi yace

"sannu dan kwal'uba wallahi ina jiye maka ranar da Allah zai maka babbakar tsire...,

juyowa rabi yayi ya saki kwai yayi wani fari buga hannu yayi a cinya yace

"ban sa baki da me dattin hula ba...,

yowa kan'sa kahu yayi da sauri ya dauki hijabin uwani ya saka wani chabka kahu ya kai mai yace

"dan uwarka cire min yau nake jij sabuwar shegan'ta ka hijabin matar tawa zaka saka.....,

shikke nan karshan duniya yazo ba'a kunyar cin zarafin ya'ya mata wallahi daga nan hum right (human right) zan kai ka ko hisba dole suyi min tsakani na dakai yana fada yana matsar kwallah

wallahi kana zuwa kama ka za suyi kama saukaka musu aiki ai daman irin ku zuke nema kwaton banza wallahi magajiya ki rufawa kanki asiri ki dena tara masu laifi a gidan nan wata ran da zasu jajamiki ko su kawo miki kayan sata ki siya....✍️

Kuyi following ɗina domin samin ci gaba da zarar na ɗora

*GIDAN MAGAJIYA*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

*`EPISODE 12`*

Dasauri dinana ya kalle'sa ya bude baki zai magana rabi yace

"Wallahi kana magana sai na dauke ka na bugaka da kasa da wani shegen kugunsa yawa an tada akuya tsaye....,

magajiya da abin su ya ishe ta tace

"wallahi Allah zan kirawo yan sanda su kwashe ku ni zaku tozarta ɗazu nan sai da masu gidan nan su kazo wai ina tara mutanan banza..,

da hallacan sake ni shaƙe huyan'sa yayi a cikin hijabi sannan ya cire da yake a yanzu ba shi bane a gabansa ba ya kyalesa kallon magajiya yayi ya kama haɓa yace

"wanne dan durin uwarne yake mana kallon hadarin kaji har yake ce mana mutanan banza billahillazi magajiya sai kin tashi tsaye akan ya bani na iya...,

yana faɗa yana buga cinya hadi da rausaya da fari

kyale su rabi wallahi zan iya da ko wannen shege zama daram ya na me na ƙuda a nan gidan sannan gobe dole muci uwar sabada sheɗan ma ɗan kallone

shoki ya kwaso yace

"Wa bikin dawowar ɗan ashararle ai dole sheɗab ya zama dan kallo Alkur'an dole mu bawa maraɗa kunya...,

kai kahi ya girgiza ya koma ya zauna yana kallon kuɗurar Allah daman ba faɗimatu ce ta ɓata ba falmata ce ta ɓaɗa wannan abu da me yayi kama haka kurum ta barsa da jaraba dinana ne ya katsai shi daga tunanin'sa jin yana cewa

kinaga yan daba yan daudo karuwai masu dan malele yan balaja'u impart ma ba wanda baza mu gayyato ba indai shima irin mune gobe iwar haka unguwar nan ta cika da ƙamshin wiiwiii

gyara ɗaurin ɗan kwalinta tayi ta daɗa kar kace shi tace

"ashe naka wasa ne har kamru...uwar laifi sai ansha ta yarda za'aji dadin harka...,

Ke magajiya

ɗago kai tayi tace

"Yees kahu what happend to you....?,

Eh Lallai iskanci ya ci uwar nada to wallahi buɗe kunnanki ki auro fahimta baliga ki sawa ƙwaƙwalwar ki yasin ba a gidan nan ba ni zaku jawo ayi sama damu sai anje can a tantance uban laifi to banyar da ba ban laminta ba

wani kallo tayi mai ta koma ta zauna shewa saudat me idon cin naira tayi tace

"Allah ya bar mu dakai tsoho ka fiye shiga sabgar da ba ruwanka dole muyi bikin dawowar dan ashararle daga gidan dan kande...,

to mara kunya fitsararriya ke kikiyaye ni wallahi na kusan kawo muku yan hisba wannan wanne irin sheɗanci ne

Uwani ce ta fito tace

"Haba alanguburo kadena biye musu kai ma sai kaza su....tunda dai gaskiya ce basa so ka barsu ai ita duniya tafi bagaruwa iya jima...,

Allahu akbar duk kansu suka hada baki suka faɗa magajiya ta cafe zancan tace

"Ina uwani take to wallahi kar kiga ina raga miki ban ƙiba in cire zani inyi zigidir mubawa hambata iska aga sabon jini ke burin ki kullum ki haɗamu da kawo bayan iya biyayya muna yi mai....,

rasa bakin magana kahu da uwani sukai anya Magajiya kanta be taɓoba tab in iskanci yayi iskanci mutum zama yake mahaukaci rabi ne yace

"Fada dai mata Allah ya barmu da kahu kaga aurena...,

sai ya janyo zaninsa da yayi ɗaurin kirji ya rufe fuskar'sa wai yaji kunya gabaran ku dai masu gida da sauri ko wannan su ya jiyo ashone yake wata irin tafiya riƙe da akuya a hannun'sa cikin muryar wanda ya sha yayi manƙas yace

"yau magajiya ya kanwar uwata da nace miki zan kawo miki ya kunbo yar liti....,

me zasu yi in ba dariya ba magajiya tace

"Ehhhhh bashakka ka sha wacce tafi ƙarfin'ka akuyace fa a hannunka...,

da sauri ya kalle hannun'sa fuskar kanwar mahaifiyar'sa ya gani yace

"Wallahi zanci mutuncin ki magajiya yakunbon nawa kike cewa akuya....,

tashi tayi ta fara mici mici da ido ta kankan CE shi tace

"Kul kul asho faɗa da aljani ba riba ban shiga dawa ba sai da na shirya ta faɗa tana dunamai dantsan hannun'ta ta ci gaba da cewa Wallahi ina naushin ka sai ka dawo cikin hayyacinka mutuncina yayi yawa ka cishi....,

zama yayi ya janyo kan akuyar cinyar'sa wani kuka ta saƙa na wahala rarrashin'ta ya soma yi yace

"wallahi dole ki kuka wacce kike ganin kin yi jika da ita ta zata kalleki ta ci miki a kuya...,

Dinana ne ya taso yace

"Gaskiya kam amma kasan me asho...?,
kai ya girgiza mai be damuba ganin halin da yake ciki yace mai

samu za kai ka siya mata wainar nan tunda kaga magajiya mu da muke mata aiki bata bamu ba balle kai da ba cas ba as ko ta dubu ce ko bakin cikin da take ciki zai yaye

kuɗi ya zaro dubu biyu yace

"Miƙawa yar hau ɗin nna ta bani ta naira ɗari ita naga zan iya siya mata....,

da sauri dinana ya amsa yace

"to ki bawa yakumbo yar liti akuyatun ta dari sauran kuma sai ki miƙo min in saka a bakin salati tun da banza ta samu....,

amsa magajiya tayi ta soƙe a kugun'ta soya mai tayi ta miƙo mai sakawa wannan akuyar yayi a gaba aikuwa akuya ta faraci

Buga kofar gidan akai da karfi da sauri magajiya ta ɗago yan sanda ne guda biyu sai babar dan asabe da shi dan asabe tana ta sababi wallahi bazan yarda ba in banda iskanci sata har da rana a kwace akuya a hannun yarona saboda shi bashi da ta ido har da cewa wai kanwar mahaifiyar'sa ce to wallahi yau zanci ubanka daga kai har be taraku...

wata dariya magajiya tayi tace

"Sweet sajan bala kana ji wannan tsohuwar kilakin na cewa za tayi magani na shin bata san wacce ni ba ko bata san wannan gidan ba me kayan aiki in da arziki kazo mu tareka inda tsiya ce mu tare aka zo dai-dai da kai....,

dariya yayi ya shafa fuskar'sa yace

"Beb ina zata sani saidai yau ta ganewa idon'ta ke hukuma ce sai rarrashi kinyi taki kinyi ta wasu....,

rausaya kai tayi tace

"Maza ɗauke wannan shagalallan kayi gaba dashi inban da iskancin asho ina shi ina satar a kuya memaƙon ya sato abu me kauri maza wartsake dan uwarka....,

ta faɗa tana saita shi da farantin silver saitawa akuyar nan ledar waina yayi dan shi beyi zaton ma dashi take ba

bazato na tsammani yaji anyi sama dashi da sauri ya saki wani ihu yana cewa wayyo yakumbona kina gani ana yi min rashin arziki

kama a kyar'ta babar dan asaba tayi ta fara tafiya da sauri sajan bala ya sake asho ya tare hannua yace

"bani kuɗin man mota....,

da sauri ta kalle'sa tace

"daga wambai ne i zuwa wannan sai na baka kuɗin mota ai naga a kafa muka zo....,

haɗe rai yayi yace

"kar ki raina min hankali ƙafafuwana ba mota bane har da kuɗin wankin takalmi kin jawo takalmina yayi darty......,

wallahi ko karfanfana bazan bayar ba ai gwamnati ita ta dauke ku dan haka ita zaka faɗawa ta baka kuɗin mai bani ba

ofisa gaskiya wannan matar ta raina ka kana faɗa tana faɗa dole ka saita mata kai ko a bayan kanta ne ka sata ta fahimci me ce duniyar.....cewar rabi.....✍️

Domin samin ci gaba da zarar na ɗora kuyi following ɗina na kusan dena posting a kowanne group sai channel ɗina Please yan aljanna a dinga sharing

*GIDAN MAGAJIYA*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

*`EPISODE 13`*

Gaskiya kam yannan kuwa basai an jima ba zan koya mata darasi mafi girma sanin halin yan sanda badai sharri ba ta ciro kuɗi a kugun'ta ta bashi amsa yayi dubu uku ce ya sakar mata akuyar'ta tafiya tayi tana Allah ya isa a zuciyar'ta....

da sauri rabi ya tashi yace

"Ofisa bani nawa kason...,
Chapter 8 · 0% Book details