← Book details Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 14

Sashe 13

Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lallai kahu wallahi sun raina ka wallahi sun mai dakai yawa kakan su tofa dole ka tashi tsaye wallahi sumayya ya fada tana gyara riƙon katin karta na hannun'ta

Insah Allahu bazaki ci ba Shegiya me kan jimina ke dai anyi sheɗaniya muna da uba sama da kahu ne dan a shararle ya fada yana nunota da huƙa.....

tashi tayi tana tan gaɗi tace...

"Kai ƙaramin kwaro wallahi sanin kan kane yau na ga dama sai ka koma inda ka fito ni nake tare uban gayya....,

da hallacan rufen baki dan uwar....ki har Ni zaki faɗawa manya nine yaron dan siyasa me fada a ji a ƙasar nan wallahi

ai shi ya saka ya barka Kai wata shidda a gidan gyaran hali bata ƙarasa ba taji saukar mari be ajiye hannunsa ba ta dauki botikin karfe ta loda mai a gadon baya botikin rabi ya ɗauka yana waƙa kamar yadda ya saba yana kutaso babban kutaso ku taso ba me raba ku wannan fadan manya ne

zaro huƙar nan yayi da sauri.....✍️

*Ɗomin samun ci gaba da zarar na ɗora kuyi following ɗina*
*GIDAN MAGAJIYA*

OUMYASMEEN

Episode 18

Da sauri kahu ya riƙe mai hannu yace

"Sani sani karufawa kanka asiri wallahi kar kazo kana dana sani....ka kashe gawar da ba taka ba....ka kyale ta da halinta...,

Alkuran kahu da Ka barni na burburma mata huƙa a ciki na kanannaɗo hanjinta tace ba suna na Sani ba

karɓe huƙae kahu yayi yace

"Ke zo ki tafi maza ki bar gidan nan....,

kahu ba inda zani da ka kyalesa bilahillazi yaga ba dad'i Ni bakar fura ce dakan ibilisai har ni zai fadawa dabanci sai da nayi shekara hudu a lagos a ƙarƙashin gada mene ban gani ba ɗan iskan karya

fisgewa yayi daga hannun kahu da sauri kahu ya ruƙo shi a shar yake ta ɗurawa sumayya itama na mayar mai magajiya ce ta kashe hutar wainar ta da yake ta gama a kullum tana karar da fulawa kwano biyar tun daga safe har dare ban da kiras ɗin kwai ga abincin siyarwa tace

"Narantsai in baku dena abin da kuke yi ba zan tafi in kirawo yan vijilanti tun da yan sanda kun raina su haba wannan bala'in da me yayi kama a kullum in ba ai fada kadan ai yi gudu biyar na gaji ina fita ana nunani da Baki.....,

ai kema sai ki nuna su da bakin ba Ubangiji yayi miki shi ba rabi ya bata amsa jefomai ludayi tayi tace

"Innalillahi anya kuwa Rabi'u kasan abin da yake maka ciwo....,

Kallon mutanan gidan yayi yace

"Ku a cikin ku a kawai Rabi'u to dai koma mene Rabiu kacan za hali wallahi...haba wannan abu har ina...,

mayafin ta ta cira a kan igiya ta cire zanin da take sawa akan kayanta ta fita da sauri dinana ya riƙota yace

"Mun shiga uku haba uwar mu yanzu in kika fita kika kirawo mana wayan nan su kamayen ai kin cuce mu wallahi suna zuwa kwashe mu za su yi su ba a wannan ɗaki me uban sauro kin ga dawo kowa ya kama gaban sa dare yayi....,

rabi ne ya tawo yana gyara zani yace

"Wallahi mun dena ni yanzy wanna kashin na kaina sai sun aike min shi tas wallahi yar masa kuwa tab wannan direct hisba za su kai ta in ta dawo da fata jikin'ta sun mata me kyau...da imani...,

dafa kirji ta masar yayi yace

"Kut mele sin ubancan ni kaɗai ka raina kaf gun nan kana yi min mugun baki da alkaba'i....me kan sigari...,

ya faɗa yana cigaba da cin chingum tare da yarfa hannu awarwaron hannunsa suna bada sauti

Cika sani sani kahu yayi yace

"Allah yayi muku albarka ya gyara ku maza ka tafi... sai da safe...,

Ba tare da yaci komai ba ya fice sauran ma fita sukai aka bar wannan shabta sai kuma gobe ruwan wankan'ta ta juye ta zuba wani ta shiga bayi wanka tayi ta fito rataye sosonta tayi ta shiga daki sama'ila ne ya shigo ya rufe gidan ya shiga dakinsa

Osokoro..... Abuja

Laptop ɗin'sa ya buɗe ya kunna datar'sa wayar'sa ce tayi ringing da sauri ya ɗaga saboda issue ne me girma ne cikin girmamawa wanda ya kirashi yace sir muna kan online....

kashewa yayi ba tare da yayi magana ba shiga cikin inda suke meeting yayi kowa yana kai da alama shi kadai ake jira gyara zama a yana jiran me za su ce gai she shi sukai ya amsa jabir yace

"My colleague Habib M Jigirya and I have been investigating on the project from sending us now. Any time they can be caught, they will come out and find out where they got the stolen sim and phone....,

gamsuwa yayi da bayanan jabir yace

"Habib you confirmed that they kidnapped Nazeer....?,

There is someone who brought the phone to them and they bought it. We can investigate but when they come in, they will explain about it and they found it and we investigate

cewar habib

Kai Asif ya gyada cikin gamsuwa ya dubi chief of security yace

"So, in the morning, arrest them and we will investigate further, even though your information shows that you have arrested them for the crime...,

Chief of security yace

"Insha'Allah, we will intensify the investigation, as long as their blood is gone, we will end kidnapping in Nigeria...,

Jin daɗin abin da yace yayi sai ya ce

"May God seek us and cook for us...,

Amin suka amsa dashi sannan sukai sallama aiki ya ci gaba da yi ringing wayar'sa ta kara yi dauka yayi ganin aysha ce ta kira kukan ta ne ya ya doki kunnan'sa da sauri yace

"Sweet lafiya me ke damun ki...?,

cikin shagwaɓa tace

"Wallahi zaman asibitin nan ya ishe ni gashi kai baka samin time ɗin shigowa guna ko wannne lokaci baka da lokacin kan ka sai na al'umma in zaka zo kazo da masu tsaronka lokaci kalilan ka tafi.....Asif Kai na ke so ba kuɗin ka ba bana buƙatar kuɗi kullum Cikin turomin da kuɗi kake.....yau hajiya ta bugo min ba zagin da bata yi min ba...ta ƙara fashewa da kuka wai ni haihuwar nan ni naƙi bawa kai na ne...?,

dafa kansa yayi ya tashi daga inda yake komawa bedroom ɗin'sa ya zauna akan gado yace

"tun kafin ki aureni kinsan irin yadda aikin mu yake...sai kin ƙara hakuri in nayi ritaya za ki sameni kamar yadda kike so...kiyi shi ru kinsan bana son kukan ki...,

share hawayen'ta tayi tace

"daman nasan ba son laifin hajiya kake ba nayi maka maganar'ta kayi buruss dani....,

ajiyar zuciya ya sauki cikin kakkausar murya yace mata A'isha har yanzu kin kasa gane wace hajiya a guna duk wannan ni'imar da kike ciki ita ce sanadi domin duk wani karatu danayi ita ta ɗauki nauyina baki ga tsohuwa bace sai kinyi haƙuri da ita tsofa ne amma kin kasa yarda bana son wannan korafin

kashe wayar tayi ta jefar a da ita kallon'ta hidaya tayi tace

"ai gwara da kika kashe wallahi in baki tashi tsaye akan wayan nan banzayen yan uwan mijin naki wallahi son da yake miki sai ya dena ....,

Hidaya ya zanyi da su kina gani a gaban ki nayi wayar nan amma me yace min duk abin da kika kwatantamin nayi

ai wallahi tun farko ke kika bari yasan cewa kuɗin'sa kike so haba ga shinan ya sakar miki kuɗi amma ba farin ciki ko gaba zai iya yi miki gori kudin'sa kika gani kika manne masa

Hidaya nasan nayi kuskure ya zanyi da wannan result nifa ke da matsala bashi ba ko wanne lokaci ya gani zai iya karo aure saboda haihuwa yake so

ai shi yasaka nace miki za mu nemo mafita dole ki canza ki dinga yi mai biyayya fiye da da sannan dole mu bi malam mai su rufe mai baki duk wanda zai mai maganar haihuwa yaji ya tsane sa

nagode sosai kawata

Washe gari kano

da asuba kahu ya fito daga Masallaci bayan an idar da salla abin mamaki wasu mutane ya gani a cikin mota wasu kuma na dan zazzagawa rayawa yayi wata kila wani taron ya shige gida samin magajiya yayi a zaune ta idar da salla sai uwani da take tsakar gida tana wanki yace

"yau kuma da huri haka....,

Eh wallahi alanguburo ai gwara inyi da huri ya bushe da huri garin nan na damuna ko wanne lokaci ana iya yin ruwa

hakane wallahi kinyi da bara magajiya yau da huri haka

murmushi tayi tace

"kahu wallahi yau da huri na kwanta...,

ai gwara ki dinga haka ita sallah asuba kariya gareta

hakane kahu shiga ciki yayi haka kurum taji gaban'ta na waɗuwa amma sai ta ci gaba da addu'a gari ne yayi haske waje kuwa tuni ma'aikata suka zagaye gidan da bindigogi duk fuskarsu a rufe da baƙin yanki ga baƙin glass mutane suke liƙe ta sama domin ba damar zuwa ma'aikata ne guda hudu suka tiso keyar su dinana rabi sai kuka haka dinana har da majiya shiga cikin gidan sukai fitowar malam daga bayi kenan a guje ya koma yana cewa innalilahi yau na shiga uku ɗaya daga cikin su ne yace

"Baba fito ba abin da za muyi maka...,

jikin kahu yana rawa ya fito sauran kaɗan ya saki gudawa ɗayan yace

"Ina magajiya....,

"Gani me za a siya da sassafen nan Ku ishi mutane...ta fada tana fito daga daki turuss tayi ta zaro ido kirjin'ta na yin sama yana ƙasa kallon dinana wani daga cikin su yayi yace

"Wannan ita ce....?,

aa yallaɓe sunana falmata lawan maina wallahi kai dinana ni zaka gogawa kashin kaji wallahi ban taba aikata wani laifi ba bata ƙarasa ba taji dayan ya saita ta da bindiga yace

"kina kara wata magana sai na fasa kanki ina wayar da kika sata....,

da sauri ta miƙo mai daman tana hannun'ta ankwa wata mace a cikin su ta shigo ta sa mata kuka take sosai takalli kahu tace

"Kahu....✍️

labari ya zo tsakiya na kusan dena posting a ko ina ku hanzarta following ɗina

*GIDAN MAGAJIYA*

Oum yasmeen
Chapter 13 · 0% Book details