← Book details Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai ke ke kina da amfani shegiya munafuka wai me kike so jidda ki zama kullum sai tusa hajiya kike a gaba kina hure mata kunne gaskiya be dace abin da kuke ba

Hamza Hamza fito fili ka zageni damam tun shekaran jiya nake lura da kai sai cika kake kana batsaiwa dan na taɓa yar gwal ƙarya na fada kullum sai dai taitayawo yawa yar bijilanti ni daman da aka zo neman me bijilanti na bada sunan izzatu ai a lokacin da ta musamin sa'a taci ban zubar mata da haƙora ba.....ta rasa na tarɓar miji

Allah ya huci zuciyarki amma ki duba ki dena biye wa zancan jidda

Salati ta saki tace

"wato ni gani mara hankali ko tana hure min kunne nagode Hamza....,

ajiyar zuciya ya sauke ya rusuna yace

"Allah ya ja da ranki hajiya ba haka nake nufi ba kinga jidda yarinya ce be kamata tana shiga hurumin da bana'ta ba ASIF iya ƙoƙari ya yi matar nan tasa matsalar ta ɗaya bata son wani ya raɓi mijin'ta bata shigowa dangin'sa to mu rabu da ita ita duniya hankali take koyawa mutum kar kije ki ɗauko mana kara da kiyashi....,

Allahu akbar masha Allahu Hamza ashe daman ka iya wa'azi ka tsaya kana kogawa da takardu maza ga hanya nan koma inda ka fito dole inga
ya'yan me sunan malam ace sardauna guda ba ya'ya....

tashi yayi be ƙara ce wa ƙala ba tujarar hajiya ba salla take ba waya ta ɗauko tace

"Jidda nemo min number Akram...,

karɓa tayi ta fara nemo mata kee dakata ki lura sosai kai ki kirawo min wannan me fuskar shanu

waya jidda ta ajiye tace

" Na fasa tun ɗazu nake miki abu kike kushewa ke kira shi...,

janyo jidda tayi tace

"haba yar jikallena acikin jikokina daga ke sai sardauna ku nafi so....shiya nake son ganin ya'yan'sa....dan ma ya tsotso nonon baƙin hali zuri'ar Fulanin daji...masu yin kiddinafin...,

haɗe rai tayi ta ƙarɓa ta fara duba wa bugu ɗaya biyu be ɗaga ba tsaki Hajiya ta ja tace

"Ko ubansa ina kira yaƙe ɗaga min balle shi maza kiramin Kabiru....,

kamar an hullo ta ahak ta shigo auzubillahi minal tsari Inteesar lafiyar ki ko gamo kikai...?

hajiya ya faɗa tana zaro Ido dafe da kirjin'ta

gyara zama inteesar tayi tace

"Hajiya umma ce ta biyo ni....,

da sauri hajiya ta tashi riƙe hannun inteesar tayi suka fara tafiya bin bayan su jidda tayi har shashin umma dake kofar kitchen hannunta riƙe da muciya bata lura da hajiya ba tace

"Wallahi inteesar sai naci ubanki ni zan haɗa kulli kina tsalle tsalle ki ɓarar min...,

A'a wallahi ubanta yafi ƙarfin ki ci shi saidai kanwar uwarki jimmai dubai ita za ki ci ubanta in banda iskanci ki biyo tatsitsiyar yarinya da muciya yawa kin kama ɓarawo anya ZARA'U kina son shiga aljanna kuwa

ƙasa dakai umma tayi tace

"Yi hakuri Hajiya bazan ƙara ba...,

Kima ƙara wallahi gun wayan nan mala'ikun duniyar (Dass) zan kai ki su sauya miki halitta su sassamaki wallahi

Iska ta furzar me huci tace

"Yi hakuri insha Allahu zan kiyaye...,

taɓe baki Hajiya tayi ta gyara zaman glass ɗin'ta tace

"Da time wanne be san halinki ba kina sumi sumi sai kabiru da har yau be gane ki ba.....,

ya'yan albarka ku shige mu tafi ai ba adaji muka ɗauko ku ba munsan darajar ku...Ni ban taɓa ganin wannan baƙar jarabar ba a yiwa yarinya aure ko kirgar dangi bata fara ba Allah ya kawo rabo aka sani a tashin hankali kwana nake ina leƙa ƙata kar haihuwa tazo ba ƙugun haihuwa.....

Cije lips ɗin'ta umma tayi har yau Hajiya ta kasa dene Mata wannan gorin ko da yake inteesar ce ta jaja mata juyawa tayi ta koma kitchen in da sabo ta saba cin mutuncin Hajiya ba wanda ya kyale

Atsaye Kyam take duk kuwa da tarin shekarunta ji tayi an rungume ta ace granny granny
da sauri ta banɓare hannun Faisal zaro ido tayi tace....✍️

*Comments and reacting my lovely fan's mu haɗu a shafi na gaba....*

*Sauran page 9 in dena sawa a ko wanne group kuyi maza kuyi following ɗina*

*GIDAN MAGAJIYA*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

EPISODE 8

"To rasa kunya wato ga tsohuwar wotiwo ko wacce bata da gata bara ka karya ni...,

sakin'ta yayi yace

"Granny nayi missing ɗin ki ne....,

batare da ta tanka shi ba nayi gana abin'ta su inteesar da jidda na biye da ita har part ɗin'ta zama sukai jidda tace

"Hajiya yau she za mu abuja....?,

sai lokacin da Sardauna ya dawo kinsan yanzu me nake so da ke....

kai jidda ta girgiza alamar aa

nasan ke ce zaki iya wannan aiki zauna a kusa da ɓangaran izzatu kiyi kamat wasa kike tana fita ki faɗamin yau zan tabbatar wa da mijin'ta abin da take aikatawa amma baya gani

t inteesar tace

"Hajiya bani kuɗi na siyo alawa....,

Singa zaki siyo ta ci gaba da taunar goranta

tashi tayi ta fita a baƙin shashin izzatu ta zauna tana wasa da dutsuna fitowa izzatu tayi tana waya tace

"Allah ko ai kuwa gani nan kice yau raƙashewa ake ...?,

sai ta saurara dan jin wacce amsa za'a bata tace

"harda yan daudo kai kice abin nayi ne gani nan bani minti goma ta kawo ni unguwar ku...,

tana faɗar haka ta kashe wayar bata lura da jidda ba ta fara tafiya tana gyara mayafin'ta da gudo jidda ta shiga floor hajiya tace

"hajiya ta fito...inaga ba dadewa zata yi ba bata saka mukulli ba...,

tashi Hajiya tayi tace

"masha Allah yau hamza zai san wace ita shiga bedroom ɗina ki ɗauko min mukulli....,

to tace bata dade ba sai gata da mukulli fita tayi ɓangaran izzatu kamar yadda jidda ta faɗa bata saka mukulli ba saka kwaɗo tayi ta kulle kofar shashin nata tace

"Shige mu tafi....,

ba musu jidda ta bita.....suka tafi

Osokoro Abuja

kuka take wewe ganin kukan bazai kaita ba tayi kundunbala ta tura gate ɗin gidan abuɗe yake kai tsaye inda aka tanadarwa ma'aikatan gidan ta shiga talatu da larai suna tsaye sai laraba da take zaune ta zuba ta gumi wani irin nauyi baƙin'ta yayi dakyar ta iya sallama

ko amsawa ba su yi ba laraba tace

"Yau zainabu mun shiga uku an sace wayar hajiya neeheelah...,

hamdala tayi ganin ba'a gano ita ta ɗauka ba tace

"na shiga uku wane ya ɗauka....?,

ina muka sani cewar larai

talatu tace

"yanzun nan ta aiko wai kije....,

to ni da bana nan me zan mata

kafaɗa talatu ta gyaɗa tace

"Owo...ina za mu sani...,

kinsan ke kaɗai kike buɗe mata waya take ce miki ki karawo mata wani ko ki mata wani abun to kinsan password ɗin shi ne take zargin ko ke ce

Cewar larai...

gaban tane ya shiga lugudan uku uku ta ƙasa magana sai juyawa da tayi ta fita
wani katafaran floor ta shiga da ya gaji da haɗuwa hajiya na'ima tana zaune da uban kaya a gabanta tana lissafi sallama

ciki ciki ta amsa fuskarnan kamar an mata bushara da gobe zata mutu ɗurƙusawa zee tayi tace

"Barka da hutawa Hajiya....,

yauwa ta amsa a daƙile tashi tayi ta hau sama tana kyautata zaton nihila tana bedroom ɗin'ta kwankwasawa tayi ciki ciki tace

"Come in...,

buɗewa tayi ta shiga tana kan gado ba wasu kayan kirki bane a jikin'ta sai wata ƙawarta da take danna waya jikin'ta a sanyaye ta gaishe su

da hallacan rufemin baki kinzo sim sim kin kina sunna kai yawa ta kirki ina kika kai min wayata....?,

wallahi Allah ban ɗaukar miki ba

Karya kike kai ce mutum ta karshe da kika shigomin ɗakina tun muna mu biyu ki fito min da ita kafin in ɗebo miki police

ƙawar niheela ce ta kalleta tace

"Calm down ki barta in bincike yayi bincike a san waya ɗauka...,

ajiyar zuciya ni sauke tace

"huce ki bani guri....,

tashi tayi zata tafi surayya tace

"tsaya zo ki matsamin kafafuwana...,

ranta ne ya ɓaci amma sai ta danne ta ɗurƙusa ta fara matsa mata kafa ƙara miƙe kafarta tayi tana danne wayar'ta tace

"yanzu kin kira commissioner ɗin....?,

gaban zee ne ya waɗi amma sai ta mazai ta ci gaba da tausar da surayya ta sata nihilah tace

"yan zunan zan kira shi dole a fito min da wayata ni wallahi ba ma satar ce take damuna ba anan nasaka number A.K ba kuma akan email nayi saving ba akan sim ne....,

kai zee ta jinjina tace

"Gaskiya kina cikin garari..,

ba ƙarami ba wallahi...

kasa kunne tayi tana sauraron su ba zato ma tsammani taji hannun surayya a cikin rigar ta sauri ɗagowa tayi ta wata tsawa nihila ta daka mata tace

"Mene haka surayya kinsan bana son wannan abin ku ko ina sai kin nuna halinki....,

ajiyar zuciya ta sauke ta cire hannun'ta tace

"okay...,

ranta a ɓace daukar jakarta tayi ta rataya tace

"bye....,

gaban nihila ne ya waɗi karfa wannan maganar da tayi ta hanata cikar burinta kuma a yanzu surayya ce tsani kafa ɗar ta ta dafa tace

"haba sister daga magana sai fushi...,

akan me bazan yi fushi ba ina iya bakin kokarina akan ganin kin sami abin da kike so amma Ni kin hanani..

kallo zee tayi ta ɗaura fuska tamau tace

"tashi ki barnan...,

Jikin zee har rawa yake har ta kai hannu zata buɗe kofa NIHEELAH tace

"kar ki zaton kin tsira wallahi na gano kina da hannu gurin daukar wayata hmmm sunan ki sorry..,

shiro tayi mata ta buɗe ta fita jikin'ta na rawa domin bata san me wanna kawar nihila ke nufi ba

bayan fitar ta surayya tace

"tafiya zanyi in kin yanke shawara ka sanar dani baki da wata mafita da ta huce wannan .....,

tunani nihila ta shiga yi tabbas tana son cinye jarabawar'ta ko dan daddy'ta bata son daddy yasan ta kwaso carry over zai yi mutukar baƙin ciki in yaji wannan labari jikin'ta a sanyaye tace

"Na'amin ce....,

da sauri surayya ta dawo ta rungume'ta tace

"Kwata kin samawa kanki ba mafuta bake ba karatun jarabawa sai dai ki ga an kafe kin tashi da pass A....,

Allah ka raba mu da kururuwar shaidan

sakin ta tayi ta zauna tace

"Allah ya saka...,
Chapter 5 · 0% Book details