← Book details Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kahu ka faɗamin abu ɗaya a aka faɗa da ka amfana dashi mu talakawa ba wannan ne a gaban mu ba a inganta mana tsaro rayukan mutane nawa a kullum suke salwanta....? muna tsaka da bacci aka kore mu aka yanka wasu daga cikin mu yara ƙanana suka zama marayu...mata nawa aka kama aka yi musu fyeɗe sannan aka yi musu kisan hulakanci....yara da yawa sun na ƙasa so muke akawo mana ƙarshen wannan zaluncin ba wannan shirman banzan ba a kawata titi su haukan titin adin gayi musu jiniya turawa su zo.....

zuga suna aiki a kasar su su hau kan gada su shiga su ɓulla yawa wasu kurege kahu dan amfanin kansu suke gyara titi badan amfanin mu ba wallahi kahu ace zan shiga siyasa kuma a zaɓe Ni sai *NAKAWO KARSHEN WANNAN ZALUNCIN......*

Allahu akbar ba shakka malama falmata ai kamata yayi ki tara mutanan ki ki musu faɗa kafin kizo kan shuwagabani...,

ɗaki ta shiga hawaye na bin kuncinta karewa ɗakin kallo tayi duk irin daular da take ciki tana ji tana gani ta baro'ta tabar abu mafi muhimmanci a rayuwar'ta jin maganar mahaifinta tayi ta dawota sabuwa fil tana amsa kuwa a kunnanta

Bazan shiga ƙungiyar ku ba saidai in Ku kasheni bazan zaɓi farin ciki na ba in sulhuntar da rayukan musulmai ba....karya kuke wannan abin da kuke ba jahadi bane cin zarafin Musulmi ne......✍️

*Yan aljanna a dinga yi min sharing Allah ya bawa kowa abin da yake nema duniya da lahira*

GIDAN MAGAJIYA

oum_yasmeen

✧⁠☆typing....

✷⁠✷✷✷✷⁠✷⁠✷⁠✷

EPISODE:.6

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

Kanta ta dafe dayake tsananin mata ciwo zama tayi salamar Sama'ila ce ta dawo da ita duniyar da muke tashi tayi ta ɗauro alwala salla ta haɗa azahar da la'asar ko tsayawa addu'a bata yi ta fito

Lokacin uwani ta gama shan wahalar hura huta ta ɗora tattasai sauke tukunyar tayi ta zuba ruwan wanka ta tsaya agurin tana girgiza kafar ta jin motsin sauke tukunya a sukwane uwani ta fito daga bayi tace

"Wanne shegen ne ke buɗamin tukunya....?,

shiru tayi ganin magajiya girgiza kai tayi ta koma alwala ta ɗauro shiga ɗaki tayi

sauke ruwa magajiya tayi ta zuba a botiki mai da tukunyar da ta sauke tayi
Sannan ta juya ruwan a botiki

shiga daki tayi ta ɗauko kwandon wankan ta ta shi ga bayan gida

✧✧✧

******CHAINA SHANGHAI PUDONG

miƙe ƙafafuwan'sa yayi akan Centre table sosai yake jin daɗin karanta jarida wayar sa ce tayi ringing gaban sane ya waɗi ganin wacce take kiran shahada yayi ya ɗaga kiran cikin ladabi yace

"Assalamu alaiki Barka da war haka hajiya....,

Bata tsaya amsa gaisuwar'sa ba balle sallamar'sa ta zarce da cewa

Asif ya kukai da kai wata fa ba ƙoƙarin cika banji ko ɓatan wata wannan juyar tayi ba

lumshashun idanuwasan ya buɗe ya maida su yawa na masu jin bacci yace

"Ki hakuri hajiya komai nufi ne na Allah..,

ai kafin ya ida zancen'sa tace

"Wallahi wata na cika sai kai aure....dan mu dangin mu irin haihuwa ne damab tun farko kafiyar ka ban ga abin so a silindar gas ba ba kyan fasali amma ka nuna kafiya dangin turawa ai su tun yaro na ciki suke kashe mai kwaikwayon haihuwa....kaf cikin ahalin mu kowa na haihuwa ban da kai ƙannan na baya wanda akai musu aure bayan auran ka daga me ya'ya biyar sai me huɗu....dole inga jikan babban ɗana....,

cije lips ɗin'sa yayi besan wacce tsana hajiyar sa tayi wa aysha ba duk da wani zubin da laifin aysha ƙasa yayi da muryarsa yace

"hakan ma baza ta faru ba insha Allah zaki ji kyakkyawan sakamako....,

Allah yasa ta kashe wayar ba tare da taji me zai ce ba

jikin'sa a sanyaye ya ajiye wayar ɗaga kansa sama yayi kallo ɗaya zakai mai kasan buzune ga hutu da ya ratsa fatar'sa har ɗaukan ido ji yayi karanta jaridar ya ishe shi tashi yayi dogune ga jikinsa duk a murɗe laptop ɗinsa ya janyo ya zauna duba saƙone ya shiga yi

wani sako ya gani Niheela M.S banza yayi da saƙon ya ci gaba da duba masu mahimmanci wani saƙon ne ya sake shigowa dafe kansa yayi dake tsakanin

ciwo buɗewa yayi kurawa rubutun ido yayi yana karantawa

_assalamu alaika amincin Allah ya tabbata a gare ka ya wanda zuciya'ta take so ina fatan a yau in sami a bin da na dade ina jira a ko wanne lokaci ina tsammanin ganin saƙon ka duk da nasan kana tarun aiyuka_

*daga masoyiyar ka ta har abada NIHEELA M.S*

takaici ne ya kama shi waya ya ɗauka cikin ba da umarni yace

"Zan turo maka wani email kai min bincike a kansa....,

Okay sir kashe wayar yayi ɗaya wayar'sa ce tayi ringing ɗauka yayi ganin my love CE ɗauka yayi ya kara a kunne batare da yayi magana ba tace

"Honey nayi kiwar ka....,

Shafa lallausar sumarsa yayi yace

"hmmm yanzu in nace ki biyoni cewa zaki aikin ki.....,

gaban tane ya waɗi karfa yace ta biyo shi bazata iya tafiya wata ƙasar ba ba aikin'ta ne ya akai'ta ba tace

"Ak aikin al'umma ne duk randa nayi ritaya zan buɗe Foundation ne in nemi guri in zauna in kula da kai sannan in Allah yayi min nuɗifin'sa sai kaga na haifa mana baby's masu kama da daddy su....,

ajiyar zuciya ya sauke ya gyara zama yace

"Aysha lokacin karfina ya kare a lokacin buƙatar sanyin idanuwa nake wa yanda zan kalla naji dad'i.....,

iska ta furzar me huci ta gyara zaman'ta tace

"A kullum ƙara zamar min wani fure kake wanda yake yaɗo baza ka taɓa waɗiwa ƙasa ba kai mazajene a cikin maza me isa wani zubin kake da saurin karaya....?,

rufe laptop ɗinsa yayi yace

"Aysha bakya tsoro rashin kulawar dakike bani a masu farauta ta su sami nasara....?,

Dariya tayi ta juya sitiyarin motar ta tace

"Zuciyar ASIF ba ko wacce mace face matar'sa na baka duk wata yarda....,

Murmushi yayi har ana iya gano jerarrun haƙoransa yawa sankara saboda haske da ɗaukar ido yace

"yanzu ina aiki in ajima muyi yawa....,

Okay nima ina kan hanyar zuwa gida wallahi na gaji gobe na kiraka tana kaiwa nan ta kashe wayar...

bin wayar yayi da kallo duniyar tunani ya lula

inda ake ni kuma ta tawo kanon dabo

NNDC Quaters

Tun daga farkon layin zaka san cewa unguwa ce ta masu hannu da shuni wani ɗan kareran estate in aka yi rubutu a jikin baƙar gate din gidan aka rubuta...SAUDAUNA ESTATE da ruwan gold wata mota ce ash ta fanno a guje horn ɗaya mamallakin motar yayi ba shiri masu tsaron estate ɗin duka buɗe mai.

ko daidai ta parking be tsaya yi ba ya fito a fusace duban ma'aikantan gidan yayi ya shiga surfa musu ashar yace

"She gu munafukai har da ku....har ni za a sa a kulle min gida bazan shiga ba....

Ƙwafa yayi tare da cewa

Ai duk da laifin yaya har mace ta dinga juya shi kamar ni za a mai da min da kaya na guest house bakomai Zan yi maganin yar kutumar....uba

Cikin isa Hajiya jamila ta iso tsawa ta dakawa ma'aikatan gidan da su ka daina komai suka tsaya suna kallon'sa kama hannunsa tayi suka fara tafiya

har hadadɗan floor ta zama yayi tsayawa tsaye tayi ta fara kai kawo ba tare da tayi magana ba haka shima sai ajiyar zuciya yake sauke wa can da ta gama isar ta tace

"Me ya dawo da kai.....?,

Mom yan zu abin da ake min a gidan nan yayi dai-dai kenan

Tsawa ta daka mai tace

"Faisal cewa nayi me ya dawo da akai....?har kana faɗa da kasƙantantun mutane abin yayi min ciwo lokacin da talatu a faɗa min ka dawo har ka tusa yan aiki gaba kana zagi.....,

Au yanzu na fahimta har da ita ke nan a sahun munafukan gidan nan

Zama tayi tace

"Har yanzu baka ban amsar tamabayata ba....✍️,

Iya comments din ku da sharing iya yawan read more ɗin ku

*GIDAN MAGAJIYA*

*_Ban yarda wani ko wata ya yi min amfani da shashina na wannan littafin ba masu dai haɗa document ku haɗa ko sa shi a website amma ban da mai damin da shi audio wannan hakkina ne kubar min kayana_*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

EPISODE 7

Yanzun nan na dawo daga Company na tarar waccan me kama da taliya me sirisiri ta sa a kwashe kayana amai damin guest house wai ta gaji da halina me ruwanta da ni ban da shi yayan ya nuna mata bani da daraja ai bata isa tayi min haka ba...amma ba damuwa zan saita mata zama

Gauran numfashi ta sauke tace

"Faisal da ace ka zama mutumin kirki da nafi kowa jin dadi kalli a yarda ka dawo daga kai sai three-quarter sai riga me ƙaramin hannu ga wannan uwar sarƙar ko nauyita baka ji ...,

ɗaga sarƙar huyansa yayi yace

"Mom wannan kinsan kuwa kuɗin'ta ai fashion ce wallahi kowa ya ganni ba raini...,

cikin takaici ta buga Centre table tace

"Wallahi duk halin da nake ciki kai ke jamin Faisal da ace ka zama mutumin kirki zan kwatar maka hakkin ka amma yanzu fa....kalli muna wani yunkuri za a gane mu bamu da kataɓus da ko shiga jikin'sa kayi mu samu wani sirri amma ka tsaya shashanci...,

tashi yayi ya buge rigar'sa yace

"Mom faɗi wani abun ba wannan ba nifa ina kaunar ɗan uwana ato baki isa ki haɗani da shi ba matar'sa ce matsala ta da dai ita kike so mu haɗa hannu mu kifar da ita nayi....yana kaiwa wannan ya fita

kiran shi ta shiga yi amma ko wai wayowa be ba naushi ta kai wa iska idanunta sun ƙaɗa sun yi jaaa kai kawo ta shiga yi

__ __ __ __ __

Hajiya yi ce ko kin kora mai bayani haba kullum ai ta abu ɗaya mace ba mace ba sai aukin hura hanci yawa yar gidan me kuɗin duniya cewar Jidda

Tsiran ta zuga ta tauna bata ƙarasa cinyewa tace

"Kyale ni dasu jidda wallahi zan maganin su very soon zan nema mai yar gidan girma wallahi....,

da dai yafi amma Ni wannan aunty Ayesha ban ga mafaninta ba
Chapter 4 · 0% Book details