← Book details Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 14

Sashe 7

Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hajiya tun haka bata faru ba nace ki bani mukulli salim alim karatun yankan jaki kika ƙi kullum ke kenan so kike kiga muna faɗa da mazajanmu kamata yayi sai kin fi kowa farin ciki a ce muna zaune lafiya..,

kuka Hajiya tasaka harda face majina tace

"IZZATU ni kike faɗawa wannan maganar bara hamza ya dawo wallahi in be ɗauki mataki ba ni zan dauka shegiya mikan kwakwa...,

zama izzatu tayi a jikin ɗan dandamali tana jiran ikon Allah duk abin nan da take karfin haline tana son mijin'ta tana fatan su kare rayuwar'su da shi ta zuba ta gumi hajiya ma na zaune har kusan karfe goma takaici ne ya kama Hajiya ta zaro waya da take jikin'ta ta fara cewa

Lallai Hamza be cika namiji ba ace har yanzu yana waje ashe lalacin da matar'sa ta samu daga gun'sa ne tab duk wani namiji me hankali bayan la'asar ya dawo wani kuma mayan magariba ace shi har ya kai karfe goma gaskiya Hamza bashi da hali sam kira ta danna mai har ta gama ringing ɗin'ta ba'a ɗauka ba taja tsaki yafi cin kwando

tashi tayi ganin bashi da niyar dawowa itama ta gaji tana so tayi sallah dan haka ta cillawa izzatu mukulli ta fara tafiya

dauka izzatu tayi ta fara sheƙewa da dariya ta buɗe ta shiga......

*__ ____ ___CHAINA*

_Chaghai Pudong_

Ya maida hankalin sa kwacokan kan kallon CNN NEW da yake wayar sa ce tayi ƙara alamar shigowar messages be duba ba ya ci gaba da kallon labarai ƙara kira akai a ƙa'ida baya amsa bakuwar number amma ganin kiran yana neman ya sa shi ciwon kai ya ɗaga ba tare yayi magana ba ji yayi an saki nannauyiyar ajiyar zuciya daga can bagaran cikin sassanyar murya tace

"Assalamu alaika ASIF barka da wannan lokaci nasan baka gane me magana ba nuriya ce...,

Zunbur yayi ya tashi yawa wanda aka tsikare shi kafin yace wani abu kit ta kashe wayar number yayta try amma not available jiyayi kamar yayi jifa da wayar zama yayi duk uban AC da take aiki amma tuni gumi ya jiƙe shi sharkaf tabbas akwai wani abu duk sanda yaji kiranta akwai abin da ke faruwa amma bata sanar da shi to wacce ita me take takama da shi ne tashi yayi ya ɗauko system ɗin'sa ya shiga operating notification ɗin daily trust ne yaga yana yauwo a saman system ɗin'sa da yaso share amma sai ya shiga gaban sane ya waɗi da labarin da yaci karo da shi
Kamar haka.......

*_labari da ɗimi ɗimin'sa yanzu yanzu yan fashin daji suka shiga gidan director general na DSS A.K SARDAUNA dake Abuja suka sakarwa gidan albarushi amma anyi sa'a ba wanda ya mutu sai matar sa da taji rauni yayin da sukai awan gaba da masu tsaron gidan_*

*_Abin mamki rashin tsaron kasar nan harka kai haka a shiga gidan babban mutum ayi mai wannan ta'addacin yayin da wasu talakawan ke cewa ai gwara su dinga ɗaukan me kuɗi su kyale takalawa mene ra'ayin ku game da wannan abin_*

da sauri ya tashi gumi ya wanke shi wayar'sa ya dauka kiran Aysha yake amma ba'a picking juya akalal kiran yayi kan akram cikin sa'a ya same shi

Cikin girmama akram ya gaishe shi amsa wa yayi still muryar'sa bata bayya weakness ɗin'sa ba ba ta yadda za'ai mutum ya fahimci ina ya dusa sanin halinsa bazai taɓa tambayar'sa ba ya rasa me ke damun brain ɗin yayan nasa wani zubin yawa me jinnu dan haka yace

"Yaya ƙaddara ta waɗawa aunty Ayesha yan kidnapping sun shiga gidan ta sami ciwo a kafa sakamaƙon taka glass ɗin da ya fashe tayi yanzu haka tana international hospital sannan sun ɗauki wasu daga cikin masu tsaron gidan fita kenan na manta wani file a Company zuwa dare zan yi aiki akan'sa daman shi Faisal jiya ya koma gida..sun tafi da wayar ta...,

Iska ya furzar me huci sai da ya gama fitar da rai da cewa yayan nasa zai magana sannan yace

"Insha Allah zan yi bincike zuwa gobe zan dawo ya su umma...,

Suna lafiya qalau...

kashe wayar yayi batare da ya mai da mai da amsa ba messages ne ya shigo wayar sa amma number prevent ce kurawa rubutun ido yayi

Ak sardauna uban wayo saidai duk wayon ka baka kai mu ba abin da kawai muke so kasakar mana yan uwan mu dake gunka kin kaƙi za mu ƙarar da dangin ka sannan ka samana hannu a wannan takardar da muka turo maka mudai buƙatar mu kawai duk abin da za mu yi kar ka sake kasa wani daga cikin jami'in ka su kama yan uwan mu tun da mun maka tayin kuɗi ka ƙi amsa

*Sai mun jika*

ransane ya ɓaaci fuskar'sa har ja take lallai mutanan sun raina mai hankali to umarni suke bashi ko me ganin maganar zata bashi ciwon kai ya kawar da zancen..

Washegari

Karfe tara jirgin su ya ɗaga zuwa Abuja ba wanda ya fadawa zuwansa bayan Akram a hankali yake saukowa daga matattakalal jirgin abin mamaki yawa ansanarwa da yan jarida zuwan'sa sun cika damƙam picture ɗin'sa sanya yake cikin black blue suit ya saka baƙin glass wanda ya ƙawata farar fatar sa duk da ya saka face mark bodyguard ne a bayan'sa dan haka su suke kare mai

Yan jaridar da ke san magan da shi buɗe mai kofar mota sukai ya shiga motar kasa samin hanyar hucewa tayi dan haka dole ya tsaya duk saurin kuwa da yake dakyar suka samin hanya da gudu
Kamar zasu tashi sama mota hudu ce suka sa tasa fara a tsaki har asibitin da aka kwantar da ministan ilimi Aysha Ak Sardauna parking suka a harabar a asibitin wani daga cikin bodyguard ɗinsa ne ya fito ya buɗe mai

ziro kofarsa yayi cikin ƙasaita yake tafiya yawa me tausayin ƙasa yayin da sauran security's ɗin suka zagaye asibitin da bindigogi

Hmmm 🤔 mutum ɗaya ke bashi wannan tsaron

Sauran kuma suna biye da bayan'sa har suka shiga reception ashe akwai wasu yan jaridun dake jiransa a gun tasowa sukai inda wani yace

"harkar tsaro ta talalace a ƙasar nan ta inda kuma kan ku yanzu ke cikin wannan barazanar yan fashin dajin nan...wanne takaici kaji da abin nan da ya faru...?,

Wani kallo bodyguard ɗin'sa yayiwa ɗan jaridar haɗi da ture shi suka shiga ciki a baƙin kofar ɗakin da aka kwantar da Ayesha suka tsaya ɗaya daga cikin su ya buɗe mai kofa ya shiga...

tana kwance ta rufe idanuwanta jin kamshin mayatatcan turaransa mont blanc legend me sanya kwanciyar hankali ga duk wanda ya shaƙe shi buɗe idon'ta tayi ta zuba mai yayin da ya zuba hannuwan'sa a aljihu da kyar ta iya buɗe baki tace.....✍️

*Kuyi following ɗina domin samin ci gaba da zarar na ɗora*

*GIDAN MAGAJIYA*

*_Oum yasmeen_*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

*Episode 11*

My maganar ce ta maƙale mata sakamakon wani zugi da kafar ta ke yi da sauri ya ƙarasa gunta yace

"Sweet ya jikin naki...?,

runtsai idon'ta tayi tace

"ba sauƙi...,

rufe mata baki yayi da tafin hannun'sa yace

"ki dena faɗar haka yawa ba musulma ba...,

lafewaa tayi ajikin'sa tana shaƙar daddaɗan kamshin'sa tace

"sun tafi da wayata akwai kuɗi a account ɗina kar su daukar min...,

gyara mata kwanciya yayi yace

"yace karki damu komai zai dai-dai'ta zan tsananta bincike abin ya ban mamaki yanzu abin har ya fara matsowa kan mu tun ana yiwa talakawa har sun waiwayo kan manyan ƙasa...,

limshe idanuwanta tayi ba tare da tace komai ba kwantar da ita yayi yace

"zan koma saukata kenan zuwa dare zan shigo yanzu tare nake da security ba dadi in shanya su kuma kinga ana shigi da fice sun hana komai ya tsaya...,

buɗe idon'ta tayi tace

"Allah ya kiyaye hanya...,

sosai yaji daɗin addu'ar ta amsawa yayi ciki ciki bata damuba sanin halin abinta kiss yayi mata a kumatu yace

"Take it easy mind one's health...,

murmushi tayi tace

"If Allah wills...,

murɗa handle yayi ya buɗe kofa ya fita da sauri suka mara mai baya ko safa tafiyar sa zaka fahimci shiɗin namijin duniya ne da sauri wani ɗan jarida yace

"zuwa yanzu kunji ta bakin yan fashin daji...? ina security din da suka ɗauka suna raye ko sun mutu...?,

masu tsaronsa ne suka kare shi ya yi gaba buɗe mai kofa yayi ya shiga ransa duk a ɓace tabbas bashi da baƙin magana sune ya kamata su kare al'umma amma suma abin ya ritsa dasu wannan babban abin kunya ne

kai tsaye babban headquarter su dake Abuja nan suka nufa motocin nasu sai shara gudu suke har suka isa buɗe mai akai ya fito ko ina yabi sai rasa mai ake gurin da ake ajiye masu manya laifi ya shiga wani cell aka buɗe mai gurin duhu diɗim ko tafin hannun mutum baka iya gani haske ne ya gauraye gun da sauri wannan mutumi ya rufe idanuwan'sa

inda yake kan wasu katafina motsi kaɗan zai yi ya afka wata ƙatuwar rijiya kallo masu tsaron nasa yayi da sauri suka matsa gefe suka huru huru da bindiga

ɗurƙusawa yayi yace

"ka gwammace zaman ka anan da ka faɗamin gaskiya...wacece nuratu bayanai sun nuna dukkan wasu hare-hare da aka kai da sa hannuka amma kai taurin kai kaƙi faɗa mana gaskiya..,

shiru mutumin nan yayi juyawa Asif yayi ya fara tafiya masu kula da gun mai da kofa sukai suka rufe...

*Kano ta dabo unguwar kofar mata*

tun daga kofar gida ana jiyo ƙarar Radio kahu bulama takaicine ya ishi magajiya batirin na sanyi ita zai takurawa ta bashi ya siya kwafa tayi dole ta gyarawa kahun nata zama wallahi dinana ne ya shigo a guje yace

"Magajiya albishirin ki...,

kallon'sa tayi tace..

"Kaga faɗa min in zaka faɗamin basai ka tsaya jamin rai ba...,

lahi na siya a gun kaska to wallahi tun jiya nake waya kuɗin sunƙi karewa ga data sai tiktok nake gani haka ma rabi tare da shi muka siya yace akwai waya clean me kyau in zaki siya tunani ya shiga yi can ya tambayi rabi yace

"rabi yama sunan wayar da yan Film yanzu suke yayi...,

rabi da ya ɗuƙufa kallon tiktok yace

"iPhone 16...,
Chapter 7 · 0% Book details