← Book details Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 14

Sashe 1

Gidan Magajiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GIDAN MAGAJIYA

Perfectly pen's

Episode 1

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

Unguwar kofar mata dake kwaryar birnin kano

Hadarine ya haɗo ta gabas gari yayi wani irin duhu ga iska na kaɗawa amma duk da hadarin nan magajiya ita da maƙarrabanta ko a jikin su wai an tsikari kakkausa suyar wainarta take gefenta dinana ne zaune yayi zaman dirshan a ƙasa sai aikin rubutu yakai

ture kaga tsiyarta ta gyara ta juya wainar'ta ta dubi dinana tace

"Dinana wai lafiya tun da ka shigo gidan nan kake ta aikin rubutu wannan ai takardar kampo ce me za kai da ita......?,

dariya ya sheƙe da ita ya ɗaga paper nan wacce take cike tab da rubutun chaina yace

"Uwar shagalallu wannan wasiƙa nake wa mara yar gidan honourable jiya ta yomin wasika cike tab da turanci kin ganta nan ya ciro takarda a aljihunsa ya ci gaba da cewa

shine nake bata amsa da chainanci tun da nasan kaf gidan nan in bake ba ba me iya fassaramin wannan turancin ke ma wallahi wannan turancin yayi miki tsauri......,

gabaki ɗayan su suka sa dariya ban magaji da ta haɗa rai sai ban kawa dinana harara take tace

"Dinana fitar min daga gida tun da abin naka rashin mutunci ne ina laifin ka tsaya iya kanka sai ka haɗo har da ni....,

abin juya waina ya dauka ya kwashe mata ganin tana shirin konewa yace

"to yar hau kina masifa wainar tana kokarin konewa.....,

fakar idonta yayi ya gutsire gefe kasa kasa yace

yar masara ina tare da ke kullum hayaki na baɗeni ko rabin fafe ba zaki iya ban ba to bara inci ta haram

Ahayyye rasss wani ɗan daudo ya shigo yana wata iriyar rausaya da sauri kahu bulama ya fito da hannu ya nuna mai hanya yace

"Maza koma inda ka fito wallahi ba zan yarda da wannan iskancin a gidan nan ba.....,

rataya jakarsa yayi ya kama haɓa yayi wani fari da idanuwansa yace

"Kahu wa kake wallahi gyara baƙin ka gurin magaji nake zuwa ba gun Ka ba cin arziki ya kawo ni ato.....,

da sauri ya yo kansa matsawa yayi yace

"auzubillahi me zan gani shi yasa masifo sukai mana yawa ina mace kana ƙoƙarin taɓani innalillahi magajiya....,

sororo kahu bulama yayi magajiya ce ta taso gyara zanin da ta ɗora akan doguwar rigar ta tayi sai taunar chingum take ƙwai ta saki ya bada wani sauti ƙasss ƙas tusssh tace

"ki rabi ba ruwan ki wannan fa kahuna ne kai kahu ba ruwan ka da rabi ciniki tazo tai min a unguwar nan ba akwai masu sai da waina ba amma ta tsallake ko ina ta zo guna gaskiya kahu ka dinga jan girman ka.... kullum sai kai faɗa da wa'yanda suke zuwa guna....,

Zani rabi ya bankaɗe yace

ato faɗa mai kullum yana mana kallon hadarin kaji gurin wasu yan mata dake kan tabarma suna hura taba suna caca ya zauna yana taunar chingum

babbar rigar'sa ya gyara yace

"to nace ba ....dan Allah zan sami wannan wainar sai ki ci gaba lissafi duk ranar da muka koma Maiduguri lokacin da komai ya lafa sai in biya ki..akwai huluna na dana saka mantawa nayi ban dauko suba lokacin da muka tawo gudun hijira garin nan zan siyar in baki bashin ki.....,

da sauri ta kallesa tace

"Kahu...,

Na'am magajiyar ya'yan Allah ya shirya

Kahu.......kahu

hularsa ya gyara yawa an kifa lotsassiyar tasa yace

"Magajiyar karuwai ina jinki....,

cikin hausarta mara fita tace

"wallahi kahu ai kafin ta ƙarasa yace

"Haba yar gidan faɗimatu dan Allah temaka min.....,

kai dai wallahi malam Allah ya shirye ka me zanyi da abin da ya fito daga hannun yan daudo da karuwai da yan sane wata mata ta fito tana masifa

jin dan shin huka tayi a huyanta jiyowa zata yi taji waya sa mata huku ji tayi ance

Kina jiyowa sai na burburma miki huƙa a hanci ta huce ta maƙoshin ki magajiyar kike faɗawa haka yana wani cije baki alamar rikakkan ɗan daban

Wata uwar buɗa magajiya ta saki tace

Manjagara sauke huƙarnan wallahi nasan in har ina tare da ku bani da sauran damuwa maza sauke'ta kallonta yayi yace

"Magajiya da kin barni da yar hau wallahi in ci kutumar....ubanta la'ada waje yasin.....,

Manjagara nace ka sauke ta nace

sauke'ta yayi tace

"Innna gobe ma in halinki ne ki ƙara tana faɗar haka ta koma ta zauna

Kahu bulama da yake tsaye a ransa kuwa wani irin takaici ne ya kama shi daman magajiya ce ta ɓata ba yar uwar'sa ba da ya huta da wannan tashin hankali da magajiya ke sa shi kullum ba shi da nutsuwa yan iska fal a gidan wannan gidan shine gida na goma sha biyu da suka kama dan ma ita ke biyan kuɗi ko wanne gida kuɗin su baya ƙarewa ake tashin su duk saboda magajiya

Wata me kama da kilaki ce ta shigo ta saki uwar buɗa tace

"Kaga magajiyar ya'yan haram an buga dake an barki maƙiyan ki fadawan ki kin ci dubu sai ce to wallahi ke zamani ce dole a tafi dake.....,

kai ta dinga rausayawa dinana yayi karab yace

gama kirarin ki sai kin biya za kice waiiina ato bama bada bashi

mayafin'ta da ta aza a kafaɗa tace

"To me matatciyar zuciya ka zauna a katarar mace sai dai taci ta rage maka....,

Dariya ya saki yace

"Ai arziki wani yayi yaga in zai ci riba sai de ya kare a hisba...cin bashin ki yayi yawa...,

wani kallo take mai tace

"uhmm wato rashin mutuncin ka har ya kai haka ka dube ni nayi maka kama da wacce zan ci bashi never wallahi.....,

tashi yayi yace

"to tsohuwar kilaki waya faɗa miki yanzu ana yayin irin ku ki bari masi jini a jika suyi irin su saudat me idon nera....,

tashi saudat tayi tana wata rausaya ta juya kugu ta liƙi ta shiga yiwa dinana tace

"Yanzu duniyar bala ja'u mu take yayi wallahi ba wata tsohuwa ba....,

Ai kafin ka ce me fada ya kaure an shiga bawa hamta iska botiki rabi ya ɗauka yana rawa yana cewa

Kutaso babban ku taso kai ku tasu ba me raba ku a zamanin nan na yanzu

Cikin kunar rai magajiya tace.....✍️

Kuyi following ɗina dan samin ci gaba kullum zan dinga yi muku update

GIDAN MAGAJIYA

EPISODE 2

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

Na shiga uku so kuke wannan gidan ma a kore ni to wallahi ba zan lamincin wannan iskancin ba kai Rabiu ga hanya nan ka koma inda ka fito......ke sauda zo ki fita.....,

Rabi'u gatsal ya kike neme ki sani jinsin rijalu gaskiya ba ki min adalci ba

Kahu bulama da yake gefe yayi garaf yace

"ai wallahi ina gab da kai ka hisba daman irin ku suke kamawa....,

Ayyiriiiyi ya saki buɗa ya buga cinya yace

"yanzu in ka ɗabe mu ya zaku ku maza ai wallahi namiji sai da nisa'u....,

sakar baki kahu bulama yayi yace

"Ina neman tsari da wannan bak'ar ƙaddarar.....ni da auran jinsin na....,

harda kafa yayi ya gyara ɗaurin kansa yace

"to mene aci wannan abu na headquarter kana da chaja ina da socket....,

RABI'U magajiya ta faɗa da karfi tace

"Wallahi nagaji da iskancin da kuke min...,

yarfa hannuwa yayi yace

"Allah ya baki hakuri nayi nan ya nemi guri ya zauna sauda ma neman guri tayi ta zauna.....,

ganin sun dena fadan ta koma ta zauna ido hudu tayi da dinana ya zage sai ci mata waina yake karkata ɗauri tayi tace

"wallahi ka gama ci ka biya ni kuɗina ko ficika baza suyi ciwo ba ta koma ta zauna zare ido ya fara domin ko kobo bashi da ita

dariya hindu ta daki tace

"Alhamdullahi mu da akewa kallon hadarin kaji za mu iya ci da kan mu....,

Nawa ne kuɗin wainar da ya ci miki

Cewar sauda

ba tare da magajiya ta dube'ta ba tace

"₦500...,

zaro kuɗin tayi tace

"Dinana nawaje na zo ka amsa....,

Au kai zuwa zakai ka amsa ko da yake zuciya ta mutu.... Hindu ta fadi haka tana shekewa da dariya

Be ce mata ƙala ba ya shige ya amsa to yar bala'i ga shinan kin so ki kunya'ta ni ina tare da ke ana ce min me yiwa mace aiki

fisga magajiya tayi ta tura mai ragowar ta ci gaba da yin wainar ta

***********ASOKORO
Villa Toscana Restaurant Plot 73, Usuma Street, Off Gana Street

Tissue ta yaga ta goge gefe da gefen baƙin ta tace

"zee kin tabbata A.k yana zowa gun nan...,

ɗagowa tayi ta janyo glasses ɗin ta ajiye wayar'ta tayi akan table ɗin da tace

"ni da na ganshi ido da ido....kinsan dai fuskar'sa ba boyayyi bace musamman wanda yake social media....,

ajiyar zuciya ta sauke tace

"Allah isa yau yazo yau ita ce damata ta ƙarshe gobe zan bar abuja na koma Sokoto...,

wasu samarine su biyu suka shigo cikin restaurant ɗin sanye da riga blue da wando baƙi ajikin rigar an rubuta

*A.K SARDAUNA CONTRACTION COMPANY* da sauri wannan matashiyar ta tashi sanye take da fitted gown ta ɗan yafa shantili a kafaɗar ta sai taunar cingum take kafin ta isa gere su tuni sun shiga wani guri cikin sauri ta dubi zee tace

"Zee wayan nan daga gani ma'aikatan sane ko za mu sami wani information akan'sa.....muje gun su....,

girgiza kai zee tayi ta riƙo hannunta tace

"Wallahi nabeelah kar ki gigin zuwa gunsu kin san wane kuwa A.K Sardauna....? a yanzu shine shugaban DASS fa ni wallahi bansan me isa kike neman saba kar ki jajamin gidan da nazo cin arziki su koreni.....,

kallon'ta tayi tace

"Ke wallahi kin fiye tsoro wata kila ma kiga yana da sauƙin kai....,

dariya zee ta saki tace

"Haba kawata mutum kamar'sa kiyi tunanin zaki same shi cikin sauki canza wannan tunanin.....,

takardar bill ɗin abin da suka ci aka ajiye musu saurin zaro ido nabeela tayi tace

"Zee wannan ɗan abin da muka ci 12k....,

da sauri ta ɗauki jaddawalin suna nayan abin da suka ci farin gani tayi Grilled Chicken with Roasted Vegetable₦12,000 tace

"Wallahi haka yake ni dake 24k....,
Chapter 1 · 0% Book details