← Book details Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 12

Sashe 9

Fin Karfi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun koma hutu nan suka ci gaba da karatu, samarin makaranta sun sha cuso kai ba fuska, don haka sai su haƙura wasu su ci gaba da naci, fannin ƙawaye ma sai da ta tantance sannan ta zaɓi Munira M Bash da kuma Sadiya Armaya'u, dukkansu law suke karanta ƴaƴan masu kuɗi ne sosai sun zata Ruƙayya ma ƴar masu dashi ne, amma da kanta ta gaya musu iyayen ta talakawa ne. Sun sha mamakin jin haka don sunyi la'akari da shigar ta da kuma yanda take koman ta zuwa shopping ɗin ta,ta ce Affanta da Yayinta sune rufin asirin ta don haka take karatun ta yanda yakamata saboda kar suyi asara Sadiya Armaya'u ƴar Kano ce ita ko Munira M Bash ƴar Abuja ce mahaifinta minista ne, amma ƴan asalin Gombe ne, yanda take basu labari baima daɗe da samun muƙamin ba suka koma Abuja, Sukan je gidan su Armaya'u sunan da suke kiran Sadiya kenan Munira ma M Bash suke ce mata yayin da suke cewa Ruƙayya Muhammadu Sani, Hajiyarsu Armaya'u ta yarje ma Armaya'u da taje musu suma, Kaduna suka sauka gidan su Ruƙayya suka yi ƙwana uku Umma ta yaba da yanda suke tafiyar da rayuwar su haka ma Affa, Armaya'u da M Bash sun sha mamakin ganin gidan su Ruƙy M basu zata gaske ne su Ruƙy talakawa ne ba sai yau,dan ma Murja da Fati da Amina sun haɗu sun gyara gidan tare gyara ma Ruƙayya ɗaki sutura kam har yau tana ɗin ka na aƙwatin Dady gashi ta danka su gwanin sha'awa sai da ma su M Bash suka yi mata tsiyar aƙwatunan, ta ce son sune yasa na siya da yawa dan bata basu labarin Dady ba, sun kuma sha mata tsiya aka zoban hannunta wai ta cire tunda ya yi mata kaɗan ta ce tana son shi bazata taɓa iya rabuwa da zoban ba.

Sai dai sun yaba da tsaftar Umma tare da abincinta kalolin gargajiya masu shegen daɗi,ƙwana uku suka yi a Kaduna Affa ya yarje mata zuwa Abuja. Sun sha mamakin ganin gidan su Munira M Bash masu kuɗi ne na gaske,su huɗu ne ƴaƴan gidan,Yayanta Zuyad M Bash,sai ƙannan ta guda biyu Mom mahaifiyar su tayi murna da ganin Ruƙy da Armaya'u dan tana shan labarin su gurin Munira an musu sauka mai ƙyau tare da basu girma.

Tun gurin cin abinci Ziyad M Bash ya ƙyallo Ruƙy, don haka sai ya shiga mika mata saƙonni cikin gaggawa, ta ganoshi, sai dai ta basar, amma ya ɗan birgeta saboda ɗan sajenshi ya tuno mata da Dady, ya ce "Munira kin taɓa faɗa ma Ruƙy tana da ƙyau kuwa?"

Munira ta yi dariya ta ce "Itama ta sani bros zayid ni kaina ina son yanayin Ruƙy kaf B.U.K babu mai ƙyaun Ruƙayya dan ƙyaun ta dabanne.

Cikin dariya Ruƙy ta ce kai M Bash kina so sharri fa."

Armaya'u ta ce "wane sharri ke ba fara bace ba kuma baƙa ba kina da yanayi da Black American ko Etopia."

Ya ce gaskiya kuke faÉ—a tama wuce nan,ni dai zan so ku mini compain dan mu samu iri a Abuja tunda babu a nan É—in." Duk suka saki dariya.

Ya shagala yana kallon yanda take dariya, komai nata birgeshi yake yi.

Munira ta ce "Zan so haka bros Zayid ko dan mu samu golding Baby gidan nan."

Ruƙy ta tashi ta wuce tana cewa "Har na ƙoshi saboda zagin yayi yawa."

Kallo Zayid ya bita dashi kafin ya ce Mom, sister Munira komai na yarinyar nan eto ne,ina sonta."

Munira ta ce "To aƙwai aiki fa dan Ruƙy bata son samari kaga yanda yarinyar nan take gara maza? Sorry kaine ma naga tai maka dariya.

Ya ce "Ƙila rabo na ne."

Suka ce "Allah yasa."

Munira ta ce "To bros ya zamuyi da jalala kasan fa angama komai."

Ya ce "Ni miji mace nawa ne?"

Ta ce "a'a bamason kishiya." Ya ce "Yes zan iya barin jalila."suka sa dariya.

Armaya'u ta ce "Shikenan kabar komai a hannun mu."

Ƙwanansu uku suka yo sallama da Abuja cike da begen juna da kuma kaya niƙi-niƙi na tsaraba surutu da kayan shafa ciye-ciye da kuma lashe-lashe, musamman Bros ya zagaya dasu gurare suka sha yawo,kai sun ji daɗin zuwa Abujan nan. Bayan sun koma daga hutu sun haɗe sun cigaba da gudanar da karatun su cikin tsari suna matuƙar son junansu da gaskiya. Saurayin Munira dake England Mustapha Ƙasim ɗan Alhaji Ƙasim ne abokin M Bash course ya je na shekara biyu kuma saura ƴan watanni ya gama.

Ita ko Sadiya Armaya'u coursing ɗin ta ne zata aura Shitu M.D suna zaune Fatakot,can ma yake aiki, cikin su Ruƙayya ce bata da dahir gashi Affa ya ce ita ma tasan me take ciki kafin ta gama.

Dad ya dubi ɗan nasa wanda ya cika har ya batse da ƙyau ga ƙoshin lafiya baya ga hawan jini dake damunsa baya da wata matsala. Ya ce "Son wannan satin za'a kawo sababbin injinan da kake magana akai, ina so ka isa Legos akan kari da zaran sun iso bana son ɓata lokaci."

Ya ce "To Dad da nima ina da zuwa Germany a wannan satin sai dai zan É—aga sai next week na je."

Ya ce "kuma Momy É—in ka tana son ganin ka."

Ya yi murmushi "Zan zo very soon aiki ne yayi yawa kuma ga costomers muna samu."

Dad ya yi murmushi "Son ai kai komai naka akwai sa'a a cikin shi,you are very lucky akan komai, gashi yanzu Companynka yafi kawo riba, duk da daɗe war nawa naka fa baifi shekara biyar ba,niko nawa ya kai goma kuma ina ƙoƙari gurin aiki mai ƙyau."

Yayi dariya ya ce "Dad ai kowa da lokacin sa, kafin nasa yayin ya wuce shiyasa nike son tsiro wasu abubuwan kafin zuwan ƙurewar lokacin sa na dasa sabon zamani."

Dad ya ce "Kayi tunani Son."

Dad Ya miƙe "Ni zan tafi sai kazo,Dad ai ita Momy nasan damuwarta zan kirata a phone insha Allah kuma zan zo mata da labari mai daɗi. Ya yi dariya.

Zan kira phone naka Dad sai in komai ya yi normal.

To shikenan na wuce.

Ya ce "Ka gaida min da Hajja zan zo kada ta damu."

Bayan sallamar su da Dad É—in ya koma ya zauna shiru ya yi yana tunanin sam ya manta ya yi ma Dad maganar bikin cikar Company shekara biyar da yake son yayi a watan gobe,ba komai dole ma yaje Kadunan kodan ya duba babban Companyn shi da za'a canza ma injina.

A gida bayan ya fito daga wanka yaronsa Sunday ya gabatar da dinner akan table,ya zauna ya soma ci white rice da miyar chiken sai kayan shaye-shaye musamman Hollandia wanda har Office akwai ta cikin fridge É—in shi, don haka ne ma yasa a other É—in shi da yawa don shi yake son ya sha lokacin partyn Companyn shi.

Bayan ya gama ya wanko baki,a bakin gado ya zauna shi kanshi yasan suna shirye-shiryen bikin Hussain,ya ɗan yi tsaki son ranshi ya huta amma yasan dole ne su je gurin ƙawayen amarya don suyi musu lissafin abubuwan da suke shiryawa. Gayu sosai ya yi don shi tun dama aƙwai Gayu shiyasa abokanshi suke kiran shi Son Guy.

Yasa turarenshi special Gold ya É—auki key É—in Hummer ya yi gidan Sagir.

Zina matar Sagir tana musu tsiya ba wani sallamar Æ´an matan amarya taÉ—i zasu, Dady ya ce "To muda muke da right É—in huÉ—u har zakiyi wani abu." Ta jawo Sagir "gaskiya bazan yarda ba gara shi, yanzu zainab bata shiga gidan shi ba."

Dady ya ce "Ai na gaya mata tanada kishiya."

Zina ta ce "To ni banida ita,kai je ka." Dariya suka shiga yi mata ganin da gaske take.

Dady ya ce "Kaima sai ka ce ba namiji ba sai wani lallashin ta kake ka zo muje kawai."

Ta tura baki ta ce "To ku tafi É—in."

Sagir ya ce "Ban isa ba,yama zan tafi bada iznin ki ba, salon in dawo ba wajen hutu, kiyi haƙuri tawan ƙarfe nawa zan dawo."

Dady ya fita yana cewa "Kai amma fa ba namiji bane, ka zama zauna nan mijin ta ce ni na fita inta barka to,in ko baka fito ba nan da minti uku to ni zan tafiya ta, kada inyi biyu babu gashi ance mata tantsa tantsa.

Sagir ya dubi Zina ya ce "Zinarin zuciyata na je? Allah bazan jima ba,kin ji tawan?"

Ta ce "To ka je amma minti ashirin."

Ya ce "Nagode." Ya yi waje.

Sannan ya ce "sai na dawo."

Sun isa gidan su amarya dake can Asokoro bayan sun shiga sun yi parking Æ´an matan amarya da suke zaune a falo suna hira suna jiran zuwan abokan ango.Gogaggun Æ´an mata ne Æ´an jami'ar Abuja, É—aya mai suna Bintu ta É—an É—aga labule ta ce "Kai gasu nan ku zo mu fita."

Wasu suka ce "a'a mu bari su iso."

Ƴan matan su goma ne cif, phone ɗin amarya Dady ya kira, ta ɗauka ya gamu, sun fito dukkansu, Sagir ya soma rawar jiki, "Kai kaga babys kuwa?.

Dady ya ce "Kama kanka fa," Dady yasha kunu, fuska ba walwala shi dama in yana gaban mata magana ma yinta yake kamar zasu siya,yana matuƙar kama ajinshi, kai ko Zainab da zai kai maganarta ga iyayenshi baya sakar mata fuska sosai, ita ko son shi take kamar me.

Suna isowa da yawan su Dady suke kaima hari,shi kam yasha kunu tamkar jinin sarauta, ya ce "Nawa ku kayi lissafi.?"

Bintu ta yi tsalle ta ce "Kasan fa abubuwan da zamuyi suna da yawa fa,ga dinner ga....."

Ya katse ta "Kar kisa dinner don namu ne, kuma da zaki sauwaƙa ma kanki da kun faɗi kuɗin kawai don sauri muke yi."

🖊️🖊️🖊️
[7/29, 12:56] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 2*

*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

Page 6

Wata a cikin su mai suna Mina ta ce "Kai ko yanzu zaka tafi da wuri bawan Allah ka bari mu gaisa." Tayi tana fari.

Ya yatsina baki ya ce "No ma gaisa next time,nawa ne kuÉ—in?."

Suka ce "One million."

Ya ce "Ok, ya buɗe mota ya ciro check ya rubuta musu ya miƙa ya ce "Sagir zo muje."
Chapter 9 · 0% Book details